Sashe 59
Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Bro me kake tunani ne? kamar wani abu na damunka? Banza yayi dashi bai tanka mashi ba
"Faɗamin meya faru jiya bayan mommy ta kira ka awaya"
Yamutsa fuska yayi, tamkar baisan maganar ya furta"zaka iya tuna yarinyar nan da mommy ta kawo wurin mu"?
Shiru zaid yayi yana kokarin tuna ta can yai murmushi tare da cewa"kana nufin Zahra"? Ta6e baki zayn yai kafin yace"oho na manta sunanta"
"Itace zahra, yarinyar ta kwanta min araina saboda ina son mace mai kamun kai daga gani iyayen ta sun bata tarbiya" ya faɗa tare da samun wuri gefen gadon su Ya zauna yana kallon zayn
"Mommy ce ta haɗa ni da ita...." bai 6oye masa komai daga abun da ya faru tsakaninsa da zahra.
Har Ya ƙare maganarsa zaid bai ankara ba saboda zuciyarsa da ta karaya, har ga Allah bai ji dadin hukuncin da mommynsu ta yanke ba na hada zayn da zahra, saboda yasan halin ɗan uwan nasa bai jin magana fiye da shi, yarinya mai kamin kai an haɗa ta da ɗan iska, ina ma ace shi mommynsu ta hada da zahra da ba abun da zai hana ya gyara rayuwarsa saboda samun mace ta gari wadda zuciyarsa ke muradin mallaka...
"Zaid? Naji kayi shiru bakace komai ba? Nasan kana tayani jimami ne"
Jinjina kai zaid yai kafin yace"zayn banji dadin abun da kayi mata ba, saboda ba laifinta bane, mommy ce ta hada ta dakai, ni nasan ba itace ta shirya faruwar hakan ba..." ya fada cikin sanyin murya yana kallon zayn dake faman ya mutsa masa fuska
"Me zai hana ka jaraba amincewa da buƙatar mommy, ni nayi imanin ba zaka ta6a danasanin auran zahra ba, watakil ta zama silar shiriyarka...." kafin ya ƙare maganar zayn ya wurga masa harara tare da katse sa da cewa"kana son ta ne?
"Meya kawo maganar so? Kawai daga na baka shawara amatsayinka na dan uwana" guntun tsoki zayn yaja"bani buƙatar shawarar ka, nayi zaton zaka tayani jimamin abun takaicin daya same ni ashe ba haka bane dakai da mommy kanku ɗaya..." ya fada yana cije la66ansa"har abada bazan ta6a sonta ba, zan amince da ita ne saboda mommy, sannan zan aureta badan ina sonta ba sai don in mayar da ita abun biyan buƙata na amma babu maganar mutunci atsakaninmu muddin ta aure ni taga ma jin dadin zaman duniyar nan" muryarsa a kausashe ya furta maganar
Runtse ido zaid yai har cikin ranshi baiji dadin kalaman zayn ba, baisan ya zaiyi ya shawo kan mommynsu akan ta janye maganar haɗa shi da zahra saboda zayn ba mutumin kirki bane, muddin ya auri zahra bakin cikinsa zaiyi silar mutuwarta, dole ya nema mata mafita tunkafin afkuwar lamarin, Indai daddyn su baisan da maganar ba zaiyi kokarin tunzurasa akan kada ya amince da maganar mommynsa....Saukowa zayn yai daga kan gado daga shi sai yar singlet da short Ya nufi toilet Yana huci Ya shige ciki, zaid dake zaune gaba daya kamar an zare lakarsa shi dai ya damu da zahra baya son mommynsu tayi silar jefa ta cikin wani hali
wayar dake a kan side drawer din su, Yakai hannu ya dauka Ya danna wa landline din kitchen tana fara ringing maid ta ɗauka, ya bada umarnin akawo masu breakfast dinsu, Kafin Yai cutting kiran ya ajiye wayar kan drawer
Badajimawa ba, Abla ta shigo dakin da tray mai dauke da kayan abinci, ta ajiye masu kan drawer bayan ta gaishe da zaid ta juya ta fuce..
________________________Dattijon Arziƙi🤍
A zaune yake kan lallausar darduma, hannunsa ruƙe da cazbaha, a hankali Yake motsa la66ansa, kusan rabi da kwata na hankalinsa na akan chief owais dake kwance saman dardumar ya ɗaura head ɗinsa akan laps din baba obie, kyawawan idanunsa suna a lumshe tamkar na mai jin bacci, su duka biyun daga ka kalle su zaka shaida tsantsar nishadin da suke aciki, musamman baba obie, ransa fari fat tunda owais ya kawo mashi ziraya yau kusan wuni yayi awurinsa duk inda zasuje atare suke tafiya, ba su jima da dawo daga masallaci ba suka shigo garden don su sha iska, sai faman satar kallonsa yakeyi kamar ya haɗiyesa haka yake ji tsabar kaunarsa da ya ke ji.
"Grandpa, wannan kallon na menene"? Idanunsa a lumshe Ya jefa mashi tambayar.
Fuskar baba obie da fara'a Yace"Kallon so da kauna ne rabin raina, wallahi yau ka faranta min rai, gaba daya ka debe min kewar hateem dake damuna...." A hankali chief Ya ɗan bude idanunsa Ya saci kallon fuskar baba obie karaf suka hada ido cikin na juna
"Baba...." Ya fada ba tare da ya ƙarasa maganar ba
"Na'am sanyin idaniyata, Naji ka kira sunana kuma ka yi shiru" gyara kwanciyarsa yayi batare daya bashi amsar tambayar sa ba.
"Duk cikin jikokina babu wanda Ya more ni kamar ka, kaga cinyar nan tawa tun kana ƙarami kake tumurmusarta, gashi har yanzu baka daina taushe min ita ba' murmushin gefen fuska Chief yai masa har chin dimple dinsa Ya dan lotsa.
"Meya fi raina"? Ya fada Yana kallon fuskarsa.
"Ni fa idan ina atare dakai, sai naii kamar an mallaka min komai na duniyar nan, ni dai Allah Ya jarabce ni da sonka kakana ina fata Allah ya dawwamar da farin ciki atsakanin mu zan cigaba da tayamu addu'a Allah Ya Ya ƙara mana tsawaicin kwana ko dan na cika maka burinka akaina......."
tun da yafara magana baba obie ke kallon shi da wani irin matsanancin farin ciki akan fuskarsa, dakatawa yayi da jan cazbahar Ya ɗaura tafin hannunsa kan sumar Owais a tsanake Ya soma shafata kamar yana yi masa susa.
"Kalamanka sun sanyaya min zuciyata, Owais kai na dabbanne, wallahi yadda nake jinka bana jin ko iyayanka, kai tamkar bugun zuciyana ne, wallahi bansan Yadda zan misalta maka kaunarka da nake yi ba....." kafin Ya ƙare maganar, ruwan hawayen da suka taru cikin idanunsa suka gangaro kan fuskar chief, lokacin da yaji saukar su a ruɗe Ya zabura ya mike daga kwancen da Yake, Idanunsa akan fuskar baba obie
da alamun ruɗani Ya furta"baba meyasa ka zubar da hawayen ka? shiru yayi batare daya iya furta masa wani abu
"Fadamin mana, ko dai maganar da muke yi ce ko kuma akwai wani abu dake damunka"? Girgiza kai yai"a'a owais kada ka damu babu abun da ke damuna, kawai bana son duk wani abu da zai shiga tsakanina dakai, Ina jin fargaban duk wani abu da zaisa ka juya min baya, ni dai bana son 6acin ranka......' ruƙo hannayen baba obie yai acikin nasa yatsun hannunsa har kerma sukeyi"baba bazaka iya boye min komai ba, idan har kana da damuwa kallo ɗaya nake yi maka na fahimta, Ina ji araina da akwai wani abu dake damunka dan Allah ka fadamin habibi na, nayi alkawarin zanyi iyakar bakin kokarina wurin kawar maka da damuwarka...." da ƙwarin gwiwa ya furta maganar Yana kallon idanun baba obie da suka kada jawur gray eyes dinsa sunyi ja tsufansa duk Ya ƙara fitowa.
Wani murmushi yayi mai ta6a zuciya kafin yace"Idan na faɗa maka abun da ke damuna zaka 6oye min sirri na ba zaka fada ma kowa ba sannan zaka rufa min asiri" jinjina kai owais yai da alamun rudani akan fuskarsa
kamar baison furta maganar Yace"najima inason sanar dakai, sai dai inajin fargaban yadda zaka dauki abun aranka, ka yi min alkawarin ba zaka fusata ba" ya fada la66ansa na kerma, ba karamin rikita tunanin chief owais Yayi ba, gwiwarsa harta sage In a low voice Ya furta"ni mai rufa maka asiri ne babana, bazan bari kowa Ya sani ba, tona maka asiri tamkar tonawa kaina asirine da zuri'armu" jinjina kai baba obie yai sai da yafara kallon garden Din Ya tabbatar babu mai kallon su kafin Ya matsa gab da chief owais Yayi masa raɗa a kunnansa.
Lokaci ɗaya chief ya ɗan janye kunnansa da tsantsar mamaki Yake kallon baba obie wanda tuni yasha jinin jikinsa, ba zato ba tsammani a lokaci ɗaya suka tuntsire da dariya kamar wasu zautattu, Yaushe rabon da inga chief yayi dariya irin wannan ni kaina namanta, komai nasa mai jan hankali ne.
dariyar tayi matuƙar tafiya da imanina, saboda gaba ɗaya ta bayyana zunzurutun kyan fuskarsa, dimpla dinsa duk sun lotsa, fararen hakoransa kamar auduga tsabar hasken su, sun ɗau lokaci suna tiƙar dariya kafin daga bisani chief ya kifa kansa bisa kafadar baba obie, hankalinsa ba karamin kwanciya yayi ba, da farkon yai tsammanin wani mugun abunne zai faɗa masa ashe ba haka bane
Muryarsa tamkar tame jin bacci Ya furta"Grandpa are you kidding me"?
Baba obie na murmushi yace"Wasa nake maka owais, Ni ina ni inayin aure, tsofe tsofe dani, ga tarin ya'ya da jikoki"
"Wannan ba hujja bace, Indai Kana son Yin auren ka fadamin, in sha Allah I will try to find a righteous life partner for you."
Da zolaya baba obie yai masa dundu akan bayansa tare da cewa"Owais wlh wasa nake maka, kawai don inga reaction dinka ne, kuma nagani tunda gayanan na sanya ka yin dariyar da ka dade baka yi taba"
Sauke ajiyar zuciya chief yai kafin ya sake furta"please ko da nan gaba kaji kana bukatar abokiyar rayuwa ka sanar dani, zan goyi bayanka kuma zan nema maka dattijuwa dai dai da kai" dariya baba obie yayi "Allah ya kiyaye In auri tsohuwa, Haba owais Ina laifin Yar sha takwas mai jini a jika, wadda zata sangarta ni, kasan mu tsoffi munfison adinga tarairayarmu kamar irin new born baby, Yanzu ni owais idan na auri dattijuwa kamana me zata min"? da mamaki chief ya ɗago yana kallonsa kai kace ba daga bakinsa kalaman suke fitowa ba.
Kafin Ya bashi amsar maganarsa, Wayar baba obie Ta fara ringing, da sauri ya zarota daga aljihu tare da picking call in ya kara a kunnansa.
Chief owais sai kallonsa Yake yi har yau yana mamakin tsufan kakan nasa, kwata kwata babu rudin tsufa atare da shi, yana da karfi ga kaifin basira, idanunsa kuwa kona matashi albarka saboda yadda yake gani da su ko bai sanya glass ba, harta sandar da yake rukewa ta gayu ce ba dan ya gaza taka kafarsa ba.
"Alhamdulillah Alhamdulillah, almost 3 time baba Obie Ya furta hakan, Hannunsa ɗaya dafe da saitin zuciyarsa alamar Yaji sanyi aransa.