← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 186 OF 238

Sashe 186

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hankulansu ba ƙaramin tashi ya yi ba, ganin yadda aka kashe Sojojinsu, koda Elders suka ga sun ƙaru kuma zasu iya yi masu 6arna ba kaɗan ba ga Danish ya zamar masu masifa sai zubda jinin Giants yake yi, hakan yasa suka fara tunanin buɗe rijiyar da Jeremiah yake a ciki, saboda shi kaɗai ne zai iya ƙarar da su kaf cikin mintuna ƙalilan.

Bawai don su basu da ƙarfin yin faɗa dasu bane, kawai rainine a gurinsu su yi gogayyar kafaɗa dasu gurin yin faɗa, sun fi so su nuna masu ƙarfin ikon su.

Kafin su aiwatar da mummunan ƙudurinsu, tuni U.s armies sun haɗa hannu da Danish duk da ba a suffarshi yake ba sun fahimci shine sanin yana iya canza suffa kamar yadda aka sanar masu kuma gashi sun ga yana farmakar Giants, nan fa suka ci gaba da bada ƙaimi suka ci gaba da kashe Giants ɗin.

Kafin ka ce me, tuni sun wanke Hall ɗin da jinin Giants ya malale ƙasa kamar ambaliyar ruwa...hakan ba ƙaramin tada hankalin Elders ya yi ba, ransu ya kai maƙura a gurin 6aci, Zuciyoyinsu sai tafarfasa suke yi saboda tsabar fusata, ga wani gurnani da suke saki kamar mayunwatan zakuna.

Saida suka ƙarar da Giants ɗin, hankalin Danish ya karkarta akan su Taj, gaba ɗaya sun razana da ganin su cikin jini kamar babu rai, Cikin sauri ya nufi Big guy dake yashe ƙasa, ya taimaka mashi gurin ɗaure mashi kan shi da wani jan ƙyalle da ya tsinta a nan, sai nishi yake yi bawan Allah, Shi kaɗai yasan irin azabar da yake ji, daƙyar ma ya rayu.

Jini duk ya wanke fuskarshi, cikin fitar hayyaci Ya furta,"Danish.... Chief, help him! I don't want him to die, go find him, I want to see him before I die...."

Tsantsar tausayinshi ne ya kama su, duk da halin da yake a ciki damuwar shi akan Chief ne, wannan wata irin ƙauna ce 💔

"Danish ! Ina Chief?" Commender ne ya tambaye shi, Girgiza kanshi ya yi yana huci ya furta, "Bansan ina ya shiga ba, amma zan binciko shi."

Ya faɗa tare da miƙewa, juyawar da zai yi keda wuya yaci karo da Taj wanda ke kwance cikin gawarwaki kamar ba numfashi a jikin shi, Hankalin shi ya tashi matuƙa, cikin sauri ya nufe shi ya taimaka mashi ya miƙar da shi zaune tare da jinginar da shi gefen Big guy, bawan Allah sai sambatu yake yi yana faɗin yar shi, ya bar masa amanarta, ya ruƙe mashi ita, baya so ta yi maraicin rashin shi, kalaman Taj sun karya zuciyar Danish, bai san sa'adda ya ji hawaye sun wanke fuskar shi ba.

In a weak voice ya furta, "Ba zaka mutu ba, zaka rayu, Angel tana buƙatarka, bana so ta rasa ka...."

Ƙafar Taj da ta lanƙwashe ya jata da ƙarfi ta bada wani irin sauti, tsabar raɗaɗin da Taj ya ji ne yasa shi sakin ihun azaba, nan take ya yanke jiki ya faɗi ƙasa sumamme, duk Danish ya bi ya ruɗe, ya kasa gane yana raye ko ya mutu ne? Ya dai samu ya tsayar da bleeding ɗin cinyarsa.

Miƙewa ya yi tare da kallon su Commender da sauran sojojin da suka rayu, gaba ɗayansu babu wanda bai raunata ba, sun jigata sosai, gaba ɗaya sun sare da lamarin.

"Salsabeel!" Hankali a tashe Ya furta lokacin da idanunsa suka hango mashi Salsabeel kwance rai hannun Allah, da gudun gaske ya bi takan gawarwakin dake zube a ƙasa ya nufi gaban benen, yana isa ya zube kan ƙafafuwansa tare da tallabo kan Salsabeel, wasu irin zafafan hawayene suka wanke fuskarshi ganin hannun shi dake a karye ƙiris ya rage ya 6alle biyu, ƙashi har ya 6ullo ta fatar, da ƙarfi ya fasa ƙara mai sautin gaske shatun jijiyoyin goshinshi suka fito ruɗu ruɗu kan fatarsa, Su Commender dake kallon shi jikinsu ya yi sanyi sosai kamar su zubda mashi ƙwalla saboda tausayi.

Unexpectedly Ginin kurkukun Ya fara Jijjiga kamar zai 6a66ako, lokaci ɗaya kunnuwansu suka fara jiyo masu sautin wata shu'umar dariya ta tantirin shaiɗani mara daɗin saurare.

Tunkafin ma su ga wanene suka sha jinin jikin su, saboda tashin hankali gaba ɗaya sun shafa'a sam sun manta da zaman Elders a hall ɗin waɗanda tuni sun jima da 6acewa, 6at babu su babu alamarsu, sun riga da sun san tsiyar da suka shuka, sun tafi sun bar su da masifa.

Cikin hanzari Danish ya miƙe tsaye, zuciyarsa na dakan uku uku, yayin da rinannun idanunsa ke akan rijiyoyin dake a hall ɗin saboda yasan yana ciki.

"Ina Elders suke? Sautin dariyar da muke ji ta wanene?" Canal Herry ne ya yi tambayar a ruɗe.

"The Elders have disappeared, the only way to escape is to run away before the evil giant emerges from the wall, He's the most dangerous evil giant in the prison of Destiny, and their new prison shield, ba zaku iya ja da shi ba, Ku barni da shi, In ba haka ba, zaku rasa rayukan ku ne!"

Wani irin faɗuwar gaba suka ji, kafin wani daga cikin su ya motsa, Unexpectedly murfin ɗaya daga cikin rijiyoyin ya 6alle da karfi tattare da iska ya yi sama kafin ya ƙundumo ƙasa, gaba ɗaya suka zare ido suna jiran ganin menene zai biyo baya.

A firgice Danish Ya dinga yi masu tsawa yana faɗin su tafi! su barshi da shi, amma suka ƙi tafiya saboda bazasu Iya barinshi shi kaɗai ba.

Lokaci ɗaya wani irin hayaƙi mai haɗe da tartsatsin wuta ya fara fitowa daga cikin rijiyar tuni suka sha jinin jikin su, ashe basu ga komai ba, lokacin da basamudan shaiɗanin ya duro daga cikin rijiyar kusan suman tsaye suka yi tsabar razana da kiɗima.

Wani irin zabgegen mutun, kwata kwata babu sutura a jikin shi, zir yake haihuwar uwarsa, gaba ɗaya jikinshi zanen tattoo ne da zanan aka yi mashi sutura, Ga wasu zaƙo-zaƙon akaifu masu kama da tsinin mashi, lokacin da ya buɗe idanun shi ƙiris ya rage su commender su arce a guje saboda wani irin jajayen idanu gare shi, Idan ka kalleshi sau ɗaya ba zaka ƙara marmarin haɗa idanu da shi ba saboda tsoratarwar da gare shi.

Bakowa bane wannan face sabon Garkuwar kurkukun ƙaddara wato JEREMIAH.

Da ƙarfi commender ya ba sojojin da suka rage umarnin su fara harbin shi, saita shi suka yi da bindigu suka dinga sakar mashi wuta ta ko'ina sai dai ko gizau baiyi ba, har bomb suka wurga mashi ya gangara agaban shi, ya ɗaga faffaɗan tafin ƙafarsa ya murje bomb ɗin, koda ganin haka ai saifa jikin taƙaura ya yi La'asar!

Tun fitowar shi daga rijiyar idanun shi na akan Garkuwa shi kaɗai yake hari, dama da niyyar ɗaukar fansa suka ƙirƙire shi, girgiza jikin shi yayi tare da sakin tsawa mai kuwar gaske, tamkar zai fasa dodon kunnuwansu, duk saida suka girgiza.

Tsautsayi ne ya kai wani soja gaban shi ya ɗaga wuƙa zai caka mashi aikuwa ya damƙi wuyanshi, nan take ya tsinka shi biyu, jini ya dinga tartsatsi ya jefar da gangar jikinsa gefe ɗaya, ai koda ganin hakan nan fa suka fara Ja da baya In ka cire Danish shi kaɗai ne bai motsa daga inda yake ba, ƙarasowar shi kawai yake jira.

Da gudu wasu sojojin suka nufe shi, tunkafin su karasa ya matse yatsun hannayenshi nan take jikinsu ya faffashe kamar anyi jajjagen kayan miya...

Waro idanu waje su Commender suka yi, lamarin ya gigita tunanin su, basu ta6a ganin bala'e da musiba ido da ido ba sai yau da Allah Ya haɗa su da Jeremiah.

Gaba ɗaya gurnanin Jeremiah ya addabi kunnuwan su, Danish dake atsaye ya rasa abun yi, yasan muddin Jeremiah ya baro bakin rijiyar wlh sai ya kashe su kaf ɗinsu da ido kadai zai iya salwantar da su.

Shiru ya yi yana yanke shawara da zuciyar shi lokaci ɗaya ya fara tariyo kalaman Unaisah sai ya ji kamar a lokacin take furta mashi su,

_I love you, Danish! I really love you, i wanna be with you for the rest of my life, I can't live without you, My heart beats for you alone, My soulmate, I'm yours, I don't want you to go and leave me! Please come back to me! don't die! I'll wait for you..."_

Yana so ya gana da tsohuwa khala saboda yaci burin ta faɗa mashi su wanene iyayensa yana matuƙar son ya gansu fiye da komai na duniyar nan, yana kuma son ya rayu saboda Unaisah, amma ya zai yi? Baida wata mafita da ya wuce ya aiwatar da abun da yake ganin dai dai ne.

Su Commender sai kiran sunanshi suke yi don su ji me yakamata su yi kafin Evil din ya farmakesu, Hankalin shi baya atare da su, gangan jikinsa kaɗai suke gani amma ruhinsa yana atare da Unaisah...

Wata irin jijjiga Jeremiah ya yi, A lokacin ya gama daidaita jikin shi, dama abunda ya tsayar da shi kenan, babban kuskuren da zasu yi shine su bari Jeremiah ya baro bakin rijiyar, domin kuwa in har ya dira ƙafarsa duk wani mai sauran rai da babu sihiri a jikin shi sai ya mutu in ba wani iko na Allah ba, aikuwa yana ɗaga ƙafarsa kafin Ya dire ta ƙasa, Danish ya watsa da gudun gaske ya durfafe shi, yana ƙarasawa gaban shi ya daka uban tsalle ya haye kanshi ya cakumeshi da hannuwan shi biyu, da iya ƙarfin shi na ƙarshe ya ingizasu gaba ɗaya suka rubza cikin rijiyar, nan take murfinta ya maida kanshi ya rufe makullinta ma ya datse kan shi, Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!😭😭😭
Chapter 186 · 0% Book details