← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 238

Sashe 60

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ina fata kun sauka lafiya, Ubangiji Allah Ya huta gajiya, Ina ƴan jikokin nawa da surukar arzikin Ina fata duk suna lafiya"? Ya tambaya yana sauraron muryar wanda suke magana da shi.

"Madallah, naji dadin jin hakan, Hateem ka kula min da kanka, tun da ka haura kabar kasar nan nake ta zullumi duk bayan yan mintina saina duba Onn news inga ko kun sauka lafiya don nasan sune nafarkon da zasu fara buga labarin yadda jirginku yayi landing sai gashi cikin ikon Allah Ka kirani...' yai maganar fuskarsa dauke da murmushi

"Muna atare da owais, watakil Ya manta wayarsa agidane, wuni yayi awurina yanzu haka muna a garden..."

miƙa ma owais wayar yayi"uncle dinka ne ke son magana dakai, kar6i kuyi magana kai masa bangajia jirginsu Ya sauka lafiya...."

da sauri chief Ya kar6i wayar tare da karata a kunnansa

"My uncle, Ykk Ina fata kun sauka lafiya"?

On the other hand muryar prime minister ta amsa da cewa Alhamdulillah Myson, tafiya tayi kyau yanzu haka Ina a bedroom dina dakyar na samu jama'a suka ƙyale ni"

"Sunyi kewarka ne, Kai dinne badai farin jini ba,

Yar dariya hateem yai kafin ya numfasa Yace"Ina yarona? tun ina a cikin jirgi nake ta tunaninsa, owais Yanzu haka da nake maka magana zazzabi nake ji a jikina saboda kewar sa, ina ta kiran layi ka donka bani shi mu gaisa bana samu" dagowa yai ya saci kallon baba obie Ganin sun haɗa iso yasa shi saurin canza yare zuwa larabci saboda baison Yaji me zai furta.

"Uncle, zazza6i saboda shi"?

"Hmm ba zaka gane ba, dan Allah Ka hadani da shi"

Hankalinsa adan tashe Yace"pls uncle, ka daina sanya damuwa aranka, bana jin dadi, na manta wayana agida ne shiyasa baka same ni ba, amma in sha Allah idan na koma zan yi kokarin hada ka da shi ko hankalinka Ya kwanta amma kafin nan pls ka sha magani kada zaza6in yai yawa"

"Owais babu wani magani da zai warkar da zazza6in nan kawai ka hadani da shi, saboda shi kadaine warakana" baba obie dake kallon owais ya kura masa ido ba tare da ya fahimci me suke cewa ba.

"Okey uncle, zanyi abun da kake so"

"Nagode owais, and pls abashi kulawa ta musamman, bana so ya nemi wani abu ya rasa, na yarda dakai kuma nasan zaka Iya min abun da nake so" cikin girmamawa ya amsa masa da toh uncle.

Sun ɗan jima suna waya kafin sukai sallama Ya mika ma baba obie wayar, harara Ya galla masa"fadamin me kuke tattaunawa ne naji ka canza yare don kada naji ko"

Girgiza kai owais yayi"ba haka bane....." bai ƙare maganar ba, sallamar Hajjaty ta katse su, ba karamin dadi owais yaji ba saboda bay da amsar da zai ba baba obie akan tuhumarsa da Yakeyi

Tuni kamshin turarenta Ya gauraye hancinansu, Hannayenta ruke da tray ta shigo garden din, Tea set ne akan tray din tare da fresh fruit, bayan ta ajiye masu fuskarta da fara'a ta gaishe sa su,a mutunce suka amsa mata

"Idan kin shiga ciki, Ki sanar da mutanan gidan su prime minister sun sauka lafiya yanzu ya kirani awaya ya fadamin nasan ba lallai suji ba"

Murmushi tayi"in sha Allah zan sanar da su" ta fada tare da mikewa ta fuce daga garden

"Kana sonta ne? Naga kana kallon ta" muryar chief ce Ta ratsa kunnansa da sauri ya kau da idonsa daga kallon bayan hajjaty ya wurga masa hararar zolaya"dan Allah ka daina wannan maganar, kawai daga na kalle ta? Ta6e baki owais yayi batare dayace komai ba, Ya dauki Tea pot Ya tsiyaya masu a cups, atare suka zauna suna sha gwanin ban sha'awa

___________________________________BossBature✍️

A6angaren Aneelerh wunin ranar da farin ciki tayi shi, babu wanda baisan da zancen bayyanar benazir ba, Harta su mami da abie sai da ta sanar da su, sunji dadi har addu'a sukai mata akan Allah ya ƙara tsareta daga sharrin wadanda sukai mata kurciya da kuma fatan Allah Yasa suma su Taj su bayyana kamar yadda benazir ta dawo.

Tun bayan da ta kammala sallar la'asar ta duƙufa tana kallon hotunan benazir da ta tura mata awaya, kamar yau tafara ganin ta, gaba daya zumudin son ganinta takeyi, akwai abubuwa da dama da take son taji daga gare ta, tana son tasan meya faru da ita bayan guduwarta? Sannan A wani hannu ta faɗa? Murmushi tasaki yayin da take yin zooming fuskar benazir tayi haske jawur ta ƙara jiki ta zama big mama..

"Ya Allah kamar Yadda Ka nuna min benazir da ranta da lafiyarta Ya Allah ka nuna min su Uzair haka, har Yanzu ban fidda rai da su ba, saboda Inaji araina suna araye, Ya Allah ka tsare min mijina da dan uwansa da angel dina aduk inda suke, Ya Allah Idan sun riga mu gidan gaskiya kajiƙansu ka gafarta masu alfarmar annabi muhammd SAW......"

muryarta na rawa ta ƙare maganar saboda kukan daya ciyota.....

"Aunty Aneelerh" muryar zahrace ta katse mata kukan nata, da sauri ta sanya tafin hannu ta share hawayen don batason zahra taga kukan ta, hakan zai iya sanyata damuwa, murmushi ta kakaro akan fuskarta ta dago ta kalli zahra dake shigowa.

"Na'am Sisterna"

"Auntyna Ina ƙara tayaki Murna, Aunty benazir ta bayyana saura Angel dinmu in sha Allah itama zamu ganta, Ni nasan yau dakyar zaki iya runtsawa saboda zumudin haduwa da Aunty benazir" cike da nishadi zahra tayi maganar, tare da samun wuri gefen Aneelerh ta zauna tana dubanta.

"Nagode zahra, ki cigaba da tayani addu'a Allah Ya bayyana su uzair, bana jin zan ma Iya bacci adaren yau, in sha Allah zanyi nafilfili akan su..." ta fada tana ɗan yamutsa fuskarta dake a kunshe da damuwa.

"Lokacin da yayan benazir Ya fada min cewa kurciya akai mata har ta gudu tabar gida, wallahi bakomai ya fado min araina ba face 6acewar su taj, farat ɗaya aka neme su aka rasa, a tsakar dare, zahra baki tunanin suma kurciyar akayi ma su"? Idanunta Jawur ta jefa mata tambayar, shiru zahra tayi jimm alamar tana nazari kafin taɗan jinjina kai tace"nima nayi tunanin hakan, zai iya yiwuwa, amma kada mu dogara akan hakan tunda bamu da tabbaci"

"Kin fadi gaskiya zahra"

Shiru suka danyi na wani lokaci..

"Zahra, dazu muna cikin yin magana bamu ƙarasa ba abie Ya kira ni..." murmushi zahra tayi

"Ni ma sham na shafa'a...." labari ta fara bata na dinner din hateem tun daga farko har karshe ta dire mata.

Bakomai ne Ya tsaya ma Aneelerh arai ba face yarinyar da zahra ta bata labarin sun haɗu har sunyi hotuna.

"Ki nuna min hoton in gani" zumbur zahra ta mike tana fadin inna lillahi na manta wayar a hannun baby junaid tun ɗazu tana a wurinsa, Allah Yasa bai yi min barna ba" da sauri ta fuce daga dakin ta shiga neman baby junaid itace har dakin ummi da mamie duk baya a ciki, har falo bata gan shi ba, da sauri ta nufi dakin abie nan ma babu shi ta dawo ta shiga dakin uncle still ba junaid

Sai da ta gama shan wahalar nemansa har zata juya ta koma daki ta jiyo sautin muryarsa a kitchen shi da Ana suna magana.

"Kinga wannan itace Angel dina aunty zahra ce ta dauko min hotonta"

Adai dai lokacin zahra ta shiga kitchen din kafin Ana Ta kar6i wayar don taga hoton Angel din motsin shigowar zahra ya firgitar da junaid aruɗe Ya saki wayar ta kife kan floor, wani irin bugu zuciyar zahra tayi ba ita ba hatta Ana hankalin ta, sai da Ya tashi idanunsa azare suke kallon junaid wanda tuni yasha jinin jikin shi.

Muryarsa na rawa ya furta"aunty zahra bani bane, Ana ne ta kada miki waya...' yana magana yana girgiza kansa duk yabi ya rude, Jikinta na tsuma Ta nufi wayar ta dauko ta tare da juyo da ita, gaba ɗaya screen dinta ya tsastsage fatsa fatsa baka Iya ganin komai.....

Kamar ta fasa ihu haka Taji tsabar bacin rai, a fadace tace"junaid hankalinka Ya kwanta ko? Ka fasa min waya! daga abun arziki na baka ita don ka kalli hotuna" ta fada tana zare masa ido fuskarta adaure tuni Ya ƙara firgita.

"Sister zahra kiyi hakuri shima bada son ransa hakan ta faru ba, kada ki tsorata shi" Ana ce ta fada cikin kwantar da murya.

Bata tsaya sauraronta ba, Ta ruko wuyan rigar junaid"don kaga ina maka wasa da dariya ko? Shiyasa har ka samu kwarin gwiwar fasa min phone, muje daki yau saika yaba ma aya zakinta ɗan rainin wayau, dallah jibarka ko kunya babu" la66ansa ya fara ta6ewa alamar zaiyi kuka"kar na kuskura naga hawaye a idonka, wayar wuta zan sa maka" shiru yayi can kuma ya fara mata magiya"bazan ƙara ba aunty zahra, dan Allah kada ki buge ni, na tufa Allah" kiris Ya rage ta fashe da dariya ganin yadda Ya tsorata kamar ta ta6a bugunsa Alhalin tun da ya taso babu wanda Ya ta6a bugunsa

Janshi tayi har zuwa bedroom dinta, Ta zaro wayar charger a jikin socket, kafin ta dawo gare shi da gudu ya fuce waje yana kuka, biyo shi tayi aguje tana kwala masa kira.

Bai nufi ko'ina ba sai dakin mommynsa Yana shiga Ya faɗa kan laps dinta Ya ƙanƙameta yana fadin"mommy kice ma aunty zahra kada ta bugeni, bana so..." duk yabi ya dabarbace, a rude Aneelerh ke kallon bayansa Jikinsa sai kerma yakeyi"fadamin kaida wanene"?

"Aunty kibarni da babyn nan, Allah Yau sai yaji ajikinsa, Har ni zai fasa ma screen din waya? daga abun arziki na bashi aronta don ya kalli hoton Unaisah shine zai fasa min phone"

"Amma banji dadi ba junaid, meyasa zakai mata haka? Ka kyauta abun da kaima aunty zahra"? Ba tare daya dago dakansa ba yace"tayi hakuri bajan ƙara ba, mommy ki siya mata wata wayar cikin kudina da nake tarawa a wurin ki" dariya sukayi gaba dayansu jin abun da Yace.

"Aunty aneelerh yanzu ya zanyi? Ni takaicina hotunan da baki gani ba"
Chapter 60 · 0% Book details