← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 151 OF 238

Sashe 151

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

yana faɗan hakan ya juya azafafe ya haura kan stairs ranshi ya 6aci da furucin Chief, kalmar daya furta mashi ɗazu daya ce Son danish na kara ninkuwa azuciyar shi yaji haushinta bayan irin cin mutuncin da yaron yayi mashi amma ko kadan ransa bai 6aci ba, shi arayuwarshi bayason wanda zai shiga tsakaninsa da chief, yana matuƙar jin kishin yaga chief yana nunama wani so fiye da shi hakan na kona masa rai yafi so koda yaushe ya zamana na hannun daman shi.

Dafa kafadar chief yai da hannun shi"dan Allah ka kwantar da hankalin ka, bana so kana sanya damuwa aranka, in sha Allah Danish zai dawo ..." lallashin shi ya cigaba da yi, bawan Allah gaba ɗaya ya rasa ƙwarin gwiwar shi.

"Nima Zan bi Omar, Zamuje mu binciko shi"

Numsafawa yai kafin ya dubi Taj da rinannun idanun shi

"Ina sauran Yaran? Sun shigo?"

bai ƙare maganar ba, suka jiyo sautin tafiyar su da sauri taj ya dubi kofar shigowa falon, ɗaya bayan ɗaya suke shigowa kamar yan gudun hijra saboda jigatar da su ka yi, fuskokin su sharkaf da hawaye sun sha kuka bayin Allah har sun gaji sun gode ma Allah, Unaisah tafi su jin jiki har wani jiri take gani acikin idanunta, sun ruke hannun Juna ita da Batool suma sauran sun rurruka hannayen junan su.

"Sun shigo,"

"Pls, Calm them down, I don't want them to worry about losing their brother, ka cigaba da lallashin su, Sannan ashirya masu lunch dinsu"

"Sir kaima kana bukatar hutu, ka koma daki ka kwanta ka huta zanyi magana akawo maka lunch din ka" girgiza kai yai"wallahi bazan iya cin komai ba in har Danish bai dawo gidan nan ba"

Taj yayi mamakin kalaman shi, bai ta6a zaton son da chief yake ma Danish yakai har haka ba, aranshi ya ayyana watakil ko dan saboda sabon da sukai da junan su cikin kwanakin nan.

"Da ka daure.."bai kare maganar ba ya katse shi"Boss ka tafi kawai, Ka kula da sauran yaran, Ka kira auntynsu ka fada mata halin da suke a ciki"

Cike da jin tausayin shi ya amsa mashi da toh.

Lokacin da ya sauko down, A kan sofas Ya hango su zazzaune sun yi shiru kamar masu zaman makoki, tsayar da idanun shi yayi akan Unaisah da ta kwantar da kanta saman kafadar Batool, tayi matukar bashi tausayi, bakomai yake tunawa ba face lokacin data bi bayan Danish ta haura kan titi mota takusa hankadeta ba dan Allah yasa Jami'an su sun yi gaggawar Kai mata agaji ba da tuni rai yai halinsa saboda ta furgice idanunta sun makance bata ji bata gani danish kawai take nema ido rufe, har wani zazza6i take ji ajikin ta mai azabar zafi, ga ciwon kai daya fara takura mata, ta rasa meke mata dadi duniyar nan, ita damuwarta ina Danish ya shiga? Baisan kowa ba agarin abuja, abun da take jima fargaba kada yace zai koma Gidan kurkukun kaddara duk in zuciyarta ta raya mata hakan sai taji matsanancin faduwar gaba ga tashin hankali da firgici.

kwata kwata babu wanda Ya lura da Taj a cikin su saboda damuwar data rufe idanun su.

Har saida yayi masu gyaran murya tukunna suka kalle shi in ka cire Unaisah wadda ta rufe idanunta hawaye sai suntiri suke yi kan kuncin ta.

Jiki asanyaye ya zauna yana dubansu

"Unaisah! " dakyar ta buɗe idanunta da suka rune zuwa ja ta kalle shi

"Meyasa baki jin maganata? Bana hanaki yin kukan nan ba? Ko shi zaisa ya dawo ne"? Yawu mai ɗaci ta hadiya tamkar bata son yin maganar tace"daddy, bana jin dadin jikina ne"

"Ba dole jikinki yaki dadi ba, duk kinbi kin daga hankalinki uhyum! Sai kace ba kisan tawakkali ba Unaisah! Ce maki akai Ya bace ba zaki kara ganin shi ba ne? ya fada yana kallon fuskarta, shiru tayi tana sauraron shi tasan ba lallai ya fahimce ta ba tun da shi a zaton shi sabo ne kadai atsakanin su.

Sassauta muryar shi yayi cikin sigar lallashi yace"kuyi hakuri nima na damu da rashin shi, amma bai kamata ku zauna kuyita kuka ba, ba zai yi maku maganin komai ba saima ya kara jaza maku wani ciwon, ku tayashi da addu'a in sha Allah zai dawo ko dan saboda ku..." sun yi shiru suna sauraron shi.

"Allah Ya kare mana shi aduk inda yake, Allah Ya karkato mana da tunanin shi ya dawo gida .." cikin sanyin murya suka amsa mashi da Ameen

Miƙewa Parveen Tayi boss yace"ina zuwa"?

hannunta dafe da cikinta tace"fitsari ne Ya matse ni" ta fada tare da kama hanyar ta nufi dakin su,

"Nima fitsarin nake ji, tun ɗazu ya matse ni" murya na rawa jamimah tayi maganar tare da mikewa daga kan sofa ta watsa da gudu ta nufi dakin su.

"Time din sallah azhar har ya wuce, Ku tashi ku tafi ɗaki, ku yi wanka ku yi sallah kafin ku fito zanyi magana a shirya maku lunch din ku nasan kuna jin yunwa" cikin kulawa ya faɗa yana duban su.

Bata jin zata iya cin abinci in har Danish bai dawo ba, cike da rashin kuzari ta miƙe idanun ta akan daddynta dake kallon ta bakomai ne ke daure mashi kai da ita ba face haukan da tayi ɗazu ya rasa gane meke a tsakaninta da Danish!.

Ta ɗan tsargu da kallon da yake yi mata, in a weak voice tace"Zan shiga daki, bansan ko zan dawo na iske ka ba, ka gaida min aunty Danejo" bata tsaya taji amsar shi ba, ta juya ta nufi dakin su tana tafiya a harharɗe kamar zata kife ƙasa har sai da ta shige dakin tukunna ya ɗauke ido daga kallon ta.

Knocking door room dinta da akayi ne yasa tayi sauri fitowa waist ɗinta daure da towel, hannun ta ruƙe da wani short towel da take tsane sumar kanta da shi.

Cikin kunnanta ta tsinkayi muryar Batool daga waje tana fadin

"Aunty Ummi ni ce, Mun dawo, ki buɗe min ƙofa..." wani irin sanyi ne taji ya ratsa zuciyarta, taji dadin jin muryar Batool saboda a halin da take a ciki tana bukatar wanda zai kwantar mata da hankalin ta.

"Batool, ki jira ni, Ina shiryawa ne"

"Toh"

Cikin kankanin lokaci ta kammawa shiryaw cikin abaya baƙa mai kyan gaske, ta yi rolling headscarf, ta nufi door room din tana buɗewa Batool tayi sauri faɗawa kan kirjinta, tayi mata wata irin runguma kamar zata koma cikin ta wani irin faduwar gaba taji saboda kunnnata sun jiyo mata shesshekar kukan batool, dama tun da ta rungume ta taji aranta ba lafiya ba.

Aruɗe ta furta"My Babe, meya faru? Baki da lafiya ne"? Ta faɗa tare da tallabo fuskar Batool da hannunta, hankalinta ya ƙara tashi da ganin yadda fuskarta ta yi jawur ta jike da ruwan hawaye

Jijjiga kafaɗarta tayi"meke damunki ne? Wani abu ya faru ne? Fadamin mana waya ta6a min ke"? Ta fada akagare da son jin amsarta.

La66anta na rawa ta labarta mata abunda ya faru a head quarter dangane da batan Danish.

Hankalinta Ya tashi matuƙa muryarta na rawa ta furta"inna lillahi wa inna ilaihirraji"un Amma banji dadin abun da big guy yayi mashi ba, bai kyauta ba Allah, da hankalinshi da komai sai kace baisan wanene Danish din ba..." rai a6ace tay maganar.

"Yanzu Ina su Unaisah din"?

"Duk suna adakin su, gaba ɗaya basa jin dadin jikin su saboda abunda ya faru, munyi kuka har mun gaji"

tsantsar tausayinsu ne Ya kamata ga damuwar bacewar Danish tana jin shi kamar kaninta saboda kaunar da takeyi ma su
Da tafukan hannayenta ta share ma batool hawayen dake sintiri kan fuskarta.

"Ki daina zubda hawayenki, bana so pls, ni nasan zai dawo ne in sha Allah, mu tayashi da addu"a" ta fadi hakanne saboda tasan bazai iya jure rashin Unaisah ba, tun shekaran jiya data ga abunda ke tsakaninsu tasan ba karamin abu ne zai iya raba su ba.

"Aunty Ummi ko sallah banyi ba.."

"Okay, ki shiga ciki ki yi, bari naje gurin yan uwan naki, nasan zasu neme ni" a hanzarce ta fuce daga dakin, sam ta manta bata gyara gadon ba, saukin ma ta bar bargon a toilet.

_________________________________✍️

*ANEELERH💓*

a Zaune take kan gadonta jikinta sanye da riga bubu, ta yi shiru tana kallon baby junaid dake zaune gefen ta hannun shi ruƙe da plate din wainar fulawa wanda zahra ta soya mashi ita, sai tsantsani yake saboda dadin da tayi mashi dama ya iya kwaɗayi, kadan yake balla ya ɗan dangwala yaji saiya tura a cikin karamin bakin shi

Shekaran jiya izuwa yau ya ƙara samun lafiya walwalar shi ta dawo tun da yaga Angel dinsa ta cika shi da farin ciki, ko bacci yake yana ambaton sunanta, tun da suka dawo gida ya addabeta akan ta kira Angel awaya tace mata tazo yana son ganin ta, dakyar take samu ta shawo kan shi, sai dai har yanzu bakowa yake yarda ya ɗauke shi ba, daga momynsa sai zahra da mami amma su abie kam ƙiwuya yake yi masu abun yana daure mata kai, har mahboob bai cika yarda ya dauke shi ba.

Tayi zurfi acikin tunaninta Muryar shi ta katse ta

"Mommy, wannan sauran wainar dana rage na Angel ne, wa zai kai mata? ko ni zakisa mahboob yakaini a mota in kai mata..."ya faɗa yana nuna mata rabin wainar da ya rage a plate din

Murmushi tasakar mashi"na fada maka ba Angel bace, bana so wani yaji kana kiran sunan Angel, ita yarinyar da ka gani sunan ta Azeezaty suna kama ne da Angel din mu"

yamutsa fuska yai tare da maƙe mata kafada"wallahi wayo zaki min, Angel dina ne ita ay har tambayarta nayi tace mun eh itane ko" ya faɗa da shagwa6a yana hade fuska.

Ƙura ma juna ido sukayi batasan ya zatay da shi ba tana son ta tambaye shi meya faru amma tana jin fargaban kada akoma yar gidan jiya, zai iya birkice mata tun da ta fahimci baison maganar kwata kwata.
Chapter 151 · 0% Book details