← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 180 OF 238

Sashe 180

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariyar mugunta ta saki mara daɗin ji kamar haniniyar jaki, A firgice Gabriella ta kai dubanta ga tsohuwa Inno jin sautin dariyarta, Lokaci ɗaya yanayin fuskarta Ya canza ganin matar da ta tsana fiye da mutuwarta.

Ƙarasowa Inno tayi gaban su da sandarta ta tsaya cike da shaƙiyanci ta ce, "Wanake gani kamar Gabriella? Yarinya mai ran ƙarfe, ashe rai kanga rai? dama saida raina ya bani baki mutu ba, Kina nan da ranki, kai! amma fa nayi mamakin tayaya akai kika rayu bayan tiyatar dana sa giant yayi maki? Wani mai imanin ne yayi jinyarki?

Banza tayi da ita, ta6e baki Inno tayi tare da kallon giants din dake a ruƙe da ita, "A wace Bola kuka tsunto sharar nan"? Wannan kalma ta ƙona ran Gabriella, ta ƙulu sosai.

Ɗaya daga Cikin Giant ɗinne Ya ce, "Daga ɗakin Khala, Elder ne ya bada Umarnin mu dawo da ita cikin yan uwanta." Ta6e baki Inno tayi, "Dama nasani, duk cikin kurkukun nan babu mai zuciyar imanin da zai iya jinyarki in ba ita khala ɗin ba, amma fa na tayaki baƙin ciki, da kin mutu da kin huta."

Ta faɗa tana leƙen fuskarta, warin bakinta duk Ya cika hancin Gabriella, wani irin yunƙurin amai ta fara Ji..

Bin ta da kallo tayi daga ƙasa har sama, saboda tsabar fitsara hada sanya hannu ta ɗage rigarta ta tura kai tana leƙen gabanta don taga aikin da akai ma wurin, duk tayi shiru bata hanata ba...

Ɗagowa tayi fuskarta dauke da shu'umin murmushi ta ce, "Kin ɗinku da kyau, wuri fa yayi kyau, naji dadi kinga yau Manyan Baƙin mu zasuyi badago a kanki..." ta faɗa tana sakin dariya.

Ƙululun baƙin cikine Ya tokare makoshin Gabriella sai huci take kamar zakanya, kashe mata ido tsohuwa Inno ta yi kafin ta kalli giants din dake a ruƙe da Gabriella ta basu Umarnin su tafi.

Kamar jira take Giants ɗin subar wurin dama zuciyarta ta kawo wuya, aikuwa tayi wani irin kukan kura da iya ƙarfinta na karshe ta daka uban tsalle tayi zaman yan bori akan Tsohuwa Inno, kamar Allah ya aikota ta dinga gartsa mata cizo da yakushi tsohuwa inno ta dinga kokarin Kayar da ita ƙasa amma takasa, sai da ta kekketa fatar ƙwalƙwalin kanta, duk ta ciccisge mata yar hurhurar dake a kan, tayi ma kwallan kan rantali da akaifarta duk ya yi jaga jaga da jini...

Wa'iyazubillah! Wata irin kururuwa tsohuwa inno ta saki tare da jijjige jikinta silar hakan yasa Gabriella ta kundumo ƙasa timm! nan take Inno ta rikiɗa ta zama wata mummunar halitta mai razanarwa, gurnaninta kaɗai Ya isa ya rikita kwakwalwar mutun.

Da mugunta ta durfafi Gabriellah, a lokacin so tayi ta kasheta ta hanyar handameta, aikuwa ta watsa aguje ta nufi wata doguwar hanya mai duhun gaske, bin ta Halittar ta yi aguje duk inda ta taka sai floor ɗin gurin ya girgiza saboda girman halittar, gaba ɗaya Gabriella ta rude ta razana ta rasa ina zata boye kanta, don tasan muddin Tsohuwa Inno ta kamata Sai dai buzunta...

Saƙo da lungu ta dinga bi, tana tsaka da yin gudun ta faɗo cikin wani ke6a66en wuri mai tarin komatsai ga shi babu wadataccen haske,

Gurnanin dabbar da ta jiyo ne yasa ta furgice ta soma ja da baya, cikin rashin sani tana ƙara ɗaga kafarta ta taka wani wuri gaba ɗaya ƙasan gurin ya rubza da ita ta zurma cikin wani rami wanda bakomai ne a cikinsa ba face zallar jini mai ƙarnin gaske ga ɗoyi, shi wannan tafkin asalin samuwar shi daga ɗakin fiɗa ne na gidan kurkukun ƙaddara, jinin mutanan da suke feɗewane idan ya gangaro ta cikin pipe kai tsaye yake shiga cikin tafkin anan ya ke taruwa in suka tashi amfani da jinin zuwa suke su dibe shi a cikin tuluna.

Wa'iyazubillahi! kamar zata haɗiye zuciya saboda azabar ƙarnin da ya toshe ƙofofin hancinta, jinin ya mamaye jikinta Iya wuyanta ne awaje sai ihu take tana kokawar fitar da numfashin ta.

Ko da tsohuwa Inno ta faɗo wurin ta hango Gabriella tana ihu cikin jini, nan take ta Rikiɗa ta dawo ainihin suffarta ta mutane, wata irin mahaukaciyar dariya ta saki, ganin haƙarta ta cimma ruwa, Saboda zalunci maimakon tabarta haka sai da tayi mata sihiri ta ƙarasa nutsar da ita cikin jinin kanta ya shige gaba ɗaya, tasan bazata rayu ba, sai dai a fito da ƙasusuwanta in namanta ya gama zagwanyewa.

A bangaren Tsohuwa Khala Hankalinta Yaƙi kwanciya, saboda fargaba da zullumin abun da zai biyo baya in har su Garkuwa basu kawo farmaki ba, baiwar Allah ta kwallafa rai akan zuwansu, ta kasa tsaye ta kasa zaune har gaban madubin ɗakinta ta je ta zauna kan kujerar gabansa, tayi siddabarun da ta saba yi donta samu damar yin magana da shi amma bata ga komai ba a cikin madubin, nan fa hankalinta ya ƙara tashi ganin har dare yayi❗

_______☠️👹☠️BLACK NIGHT💀👹☠️_______

Ƙarfe Goma daidai agogon Gidan kurkukun ƙaddara ta buga, adai dai wannan Lokacin, Dubban shahararrun matsafa suka fara tururuwar fitowa daga masaukin su na gidan kurkukun ƙaddara, adaren ranar duk wata halitta dake bacci a cikin dajin Evil forest da kurkukun saida ta farka saboda sautin bugun ganguna da busar sarewa daya karaɗe ko'ina tamkar za'a fasa ginin saboda Yadda kiɗan ke tashi..

takaitaccen tarihin Daren Black Night, shidai wannan dare, ya samo asaline aranar da Elder Ya Ƙaddamar da gidan kurkukun ƙaddara, Dare ne mai daraja a gurin su, suna alfahari dashi, kuma suna ɗokinshi saboda dare ne na sharholiya, kowa zaiyi bushasha suci karensu babu babbaka sannan a daren suna ƙara ƙarfin tsafinsu, agurinsu kenan, amma agurin Prisoners Daren black night kamar guguwar annobace saboda tashin hankalin da suke fuskanta adaren, kada na cika ku da surutu bari mu leƙa muga meke wakana adaren Black Night❗❓

Ɗaya bayan ɗaya matsafan ke fitowa daga masaukinsu, Wasu a hawa na ukun bene, wasu suna a hawa na biyu yayin da wasu suke a hawa na farko, kowani matsafi Ya ƙure kuri adakansa, ƙarshen wanka na kece raini, matsafan ma jinsi jinsi ne.

Tawagar matsafan yankin Asia ne a hawa na farko, sunyi anko shigar su kamar irinta kayan gargajiya launin jajaye na ƙasar China, ga wani dogon gemu har kan tulun tumbinsu, uban goshin su kamar jirgi ya yi asubanci, ga wani uban sanƙo dake gare su, idanuwan nan nasu mitsi mitsi kamar na kifaye.

A hawa na biyu kuwa tawagar Matsafan India ne, Sun buga adon su kamar malaman majami'u, wasu irin mutane ne masu ƙaton tumbi da manyan mazaunai burguza burguza ga wani uban rantali akawunan su, Munanan gaske, duk sun yi fentin ja da baƙi a jikin su, kwata kwata babu sutura a jikin su, zir suke haihuwar uwar su sai jan fentin da suka shafe jikinsu da shi, ga mutum mai ƙyanƙyami in ya kallesu sau ɗaya bazai sake marmarin kallon su ba.

Tawagar matsafan kurkukun ƙaddara, Su kuma nasu wankan wasu dogayen rigunane a jikinsu baƙaƙe har ƙasa suke ja, sun lullu6e kawunansu da hulunan rigunansu, sun rufe fuskokinsu da mask mai suffar ƙwarangwal.

Tawagar matsafan yankin Europe da America suma ba'a barsu baya ba, suma sunyi ankon su na kece raini.

Gaba ɗayansu sun hallara a tsakar kurkukun, ƙwansu da ƙwarƙwatar su ko'ina ka kalla sune birjik.

Babu masaka tsinke, saboda shagalin yau, ko'ina na kurkukun saƙo da lungu wasu irin dakarun Giants ne majiya ƙarfi ke sintiri sai mazurai suke, Jira suke kawai suga badaidai ba su aiwatar da aikin su.

Ko sauro bai isa Ya ratsa kurkukun ba batare da sun gan shi ba, hatta dakin maduban tsafinsu makil yake da giants sun kasa sun tsare suna kallon komai dake wakana a kowace kusurwa ta kurkukun da dajin Evil forest don tabbatar da tsaro, duk da basu sama ransu wani zai kawo masu farmaki ba, saboda ba'a ta6a gigin yi masu kutse ba, shiyasa suka daɗe suna sheƙe ayar su.

Surutunsu Ya karaɗe ko'ina, da wani irin Yare mara daɗin Ji suke magana cikin harshen su na matsafa, sai raha suke suna hira cikin nishaɗi.

Daga kan ground floor ɗin gurin wani haɗaɗɗen red carpet ne aka shimfiɗa tun daga fadar mai girma Elder har zuwa ƙarshen bango inda aka ƙawata wurin kamar karagar sarakuna, ga wasu jigunannun Armchairs guda shida an ƙawatasu da kayan ado.

Daga can gefe ɗaya a tsakiyar Ground floor din wani zungureran Table ne ɗauke da tsadaddun kayan shaye-shaye masu haɗarin gaske ga tulunan Jini da aka girke kan table ɗin, ga farfesun nama cike da farantai nau'ika daban daban irinsu, farfesun naman ɗawisu, na naman shanu kai hada farfesun yan cikin mutun, soye soye kala kala da kayan maƙwalashe.

Yayin da makaɗan suke ta yan kiɗe-kiɗe da raye rayen su, wasu gungun yan rawa manyan mata masu dirin jiki suka fara fitowa Kwata kwata babu sutura a jikinsu zir suke haihuwar uwarsu, wata irin rawar qugu sukeyi mai jan hankali, nan fa matsafan suka fara washe haƙora suna kallon su..

Gaba ɗaya sun ƙagara a fara shagalin, fitowar Elders kaɗai suke Jira..

Idan muka koma cikin fadar Elders kuwa, tattaunawa su ke yi a tsakanin su, Elder yana a zaune kan kujerar mulkinsa yayin da sauran Elders din suka kewaye shi suna a zaune kan carpet din fadar, Gaba ɗayansu sunyi shiga ta alfarma irin ta mai girma Elder, sun rufe ko'ina na jikin su baka iya ganin koda akaifar su ce, su shida ne cuf ba ƙari.

Cike da nishadi Ya soma magana Yana dubansu, "Me ya rage mana"? Ya faɗa yana bin su da kallo..

"Babu komai Elder, Mun riga da mun toshe kowace Hanya da za'a Iya kawo mana farmaki, dama duk burga ce, wane yaro! rijiya ay ba wurin gaɗar makaho bace, ƙananun kwarine su, in banda ma hauka ina su ina ja da mu? sunyi tunanin sauƙi ne Ja da mu, ko Dajin Evil forest basu isa su ƙetare ba, mune masu ƙarfin iko, da izinin mu komai ke wakana, in muka so Da kalma ɗaya zamu shafe babinsu mu mayar da su tur6aya!"
Chapter 180 · 0% Book details