← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 238

Sashe 5

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bazan iya sabama mahaliccina ba faryat, Ina jin tsoron Allah, kiyi haƙuri, Nima inajin abun da kike ji amma bazan iya ba, Kina bani wahala faryat, kema kuma kina cutar dakanki, saboda kina sona, Kina son kasancewa dani, amma kin haramta ma kanki aurena akan wani dalili naki mara ma'ana, Meyasa bazaki tausaya mana ba daga ni har ke? Faryat ki cika mana burinmu na ganin mun raya soyayyarmu, kada ki bari shaidan Yaci galaba akanki, ki fi karfin zuciyarki faryat, ki zauna kiyi tunani... " daƙyar ya ƙare maganar muryarshi na sarƙewa ya daddage ya 6an6are hannayenta daga ruƙon da tayi mashi, da sauri ya ruƙo handle din ƙofar ya fuce daga dakin

A jikin kofar Ya jingina kanshi hawaye masu ɗumi suka shiga zarya akan kuncinsa.

Sautin shessheƙar kukan faryat ne ya cika kunnuwansa, baisan ya zaiyi da ita ba, yasan da irin mugun sha'awar dake gareta sai dai shi bazai amince mata su aikata sabo ba, saboda babu ɗa'a ga abokin halitta wurin sa6ama mahalicci Allah! Bazai juri sauraron kukanta ba, zuciyarshi karaya take yi, da sauri Ya sauko down stairs Cikin takun sauri Ya Nufi part din baba Obinna, zuciyarshi na cigaba da tafarfasa, Abakin kofar dakinsa Ya tsaya da yin tafiyar Ya zaro hanky, Ya goge kwallarsa, Kafin ya daidaita nutsuwarsa, sallama yayi mashi.

Daga Ciki Ya jiyo muryar baba obie

"Shigo daga ciki" Buɗe kofar yai tare da shiga Ciki, adai dai lokacin Baba Obie, Yana zaune saman darduma hannun shi ruƙe da cazbaha.

Ba zato ba tsammani, Yaji saukar Jazz saman bayanshi, gaba ɗaya ya rungume shi tare da cusa fuskarshi saitin kafadarsa, Hakan ba ƙaramin ɗaga mashi hankali yayi ba, saboda a duk lokacin da jazz yayi mashi irin wannan rungumar to an 6ata masa raine," Yana Iya jiyo sautin fitar numfashinsa, dakatawa yayi da jan cazbahar, Ya ruƙo hannun Jazz Ya zagayo da shi ta gabanshi, tare da rungume shi ya kwantar da kansa saman kirjinsa tamkar ɗansa na cikinsa ko jikansa.

Cikin sigar lallashi yake bubbuga bayansa batare daya furta masa ƙala ba, har saida Yaji alamun Ya fara samun nutsuwa tukunna Ya soma magana

"Waya ta6a min shalelena"? Muryarshi adisashe Ya furta"Baba ka ta ya ni da addu'a, ita kadai nake bukata daga gare ka" ya fada batare daya raba jikin shi daga na Obie ba.

"Jazz kasan bana son damuwarka, Ka fada min koma menene nayi maka alkawarin indai baifi karfina ba wallahi zanyi maka shi," babu wasa a kalamansa

Jazz yayi fatan ace zai iya fada mashi abunda ke damunshi amma bazai iyaba, Yasan muddin baba obie yaji zancen Yana son faryat sai ya aura mashi ita, koda kuwa Iyayenta basa so, shi kuma abunda yake gudu tada husuma, saboda ba lallai hajiya saratu da Pravin su amince mashi ya aureta ba, komai zai iya faru.

Shafa bayanshi baba obie yaci gaba dayi yana fadin"Ina sauraronka, Fadamin meke damunka rabin raina"

Ɗagowa yayi da fuskarshi wadda tuni ta jiƙe sharkar da hawaye, cikin rauni na murya yace"baba, Bana jin daɗin yadda wasu suke guduna saboda rashin asalina, meyasa sauran mutane ba kamar kai da daddy mubarak suke ba"? Zuciyar baba obie ba karamin karaya tayi ba, nan take ya gane gori akayi masa, bawan Allah tsantsar tausayinsa ne yakama shi.

Cigaba da yin magana yayi"Na tsani kaina baba, Rashin asalina Yana neman Yaja min na rasa abunda nakeso, kowa ya buɗi baki sai yace ni ɗan mai aikine bani da asali, Har shege ake kirana baba" daƙyar ya kare maganar wani irin kukane Yaci karfinsa da sauri Baba obie Ya janyoshi zuwa jikinshi sosai Ya rungune shi, Yana lallashin shi.

"Toh toh ya isa ka yi shiru, Bana son Kana sanya damuwa aranka, Kukan Ya isa haka, kowani ɗan adam da ka gani a duniyar nan da irin tashi ƙaddarar, babu wanda Allah baya jarabta, inaso ka rungumi wannan amatsayin ƙaddararka, Kada ka ta6a bari wani Yasa ka canza tunaninka, Allah Shi yake son ganin rayuwarka haka, Kuma shine zai nema maka mafita" nasiha mai ratsa zuciya baba obie Yaci gaba dayi mashi har saida yaji ya daina kukan tukunna Ya raba shi daga jikinshi

Cikin kulawa yace dashi"Yanzu fada min wanene Ya tsokane ka"?

Shiru yayi batare dayace komai ba, baba obie ya fahimci bayason ya sanar da shi, hakan yasanshi cewa"Ko da yake basai ka fadamin ba, ni da kaina zan binciko wanene, kuma zan hukuntashi" ya fada yana daure fuskarshi alamar ranshi ya 6aci.

"Baba," Kallon shi obie yayi ina sauraronka

"Kamar yadda nasaba fadamaka,Yau ma zan maimaita maka, Ni dai inason family ɗinka, Ina alfahari daku, nayi fatan ace nima ina ɗaya daga cikin jikokin ka sai dai Allah bai nufa"

Wani irin annurin farin cikine Ya bayyana akan fuskar baba obie.

"Jazz baka ɗauke ni kamar yadda na dauke ka ba, ko da yake ba laifinka bane, laifin wadanda suke yi maka gorine, sune sukasa kake jin kanka bare afamily dina, amma inaso kasani, baba obie baya yi maka kallon bare, inasonka jazz kamar yadda nakeson jikokina, Kamar yadda kake fatan ka zama daya daga zuri'ata nima haka nake fatan ka kasance" yayin da baba obie ke yin maganar, wani irin sanyi da daɗi ne ke tsuma zuciyar jazz, har abada bazai ta6a mantawa da halaccinsu agare shi ba.

Ganin Ya faranta masa raine yasa baba obie cewa"namanta ban tambayeka ba, Ya jikin naka"?

Fuskarshi dauke da murmushi Yace"naji sauki, nagode na kulawarka agareni"

Jinjina kai baba obie yai"gobe idan Allah yakaimu, Ina fata zaka halacci Dinner din Hateem"

Jim ya ɗanyi harga Allah baison zuwa kodan gudun a ci mutuncinsa, amma saboda yana son ya faranta ma baba obie yasa shi cewa "In sha Allah tare dani za'a buɗe taro"

Murmushi baba obie yai masa"Naji dadin jin hakan rabin raina.

Jan shi da fira baba obie yai, kamar wani abokinsa, tuni jazz ya saki jikin shi.

*💋 UMMIN AMERICA❤*

Duk Yinin Yau Bata fito daga ɗaki ba, ta killace kanta tun safe bata jin daɗin zuciyarta, duk ta ƙuntata kanta, tayi jiran zuwansu unaisah su shigo don su ɗe6e mata kewa sai dai shiru babu alamarsu, tuntana sa ran ganin su har ta fidda ranta, ta ƙundundune kanta cikin lallausar bargonta, Sallah ce kaɗai take tada ta daga saman gado

Har ta fara nutsawa cikin baccinta kwatsam wayarta dake ajiye kan nightstand ta soma yin ruri, da wata irin kasala ta ɗago da kanta, sumar kanta duk ta hargitse babu gyara, laluba Hannu tayi ta kamo wayar batare data duba sunan mai kiranta ba tayi picking tare da kara wayar a kunnanta.

Sautin Muryar NATASHA ne ya Daki Dodon Kunnanta"nayi fushi Kin manta dani ko"? ta faɗa cikin harshen turan ci.

Muryarta da kasala Ta furta"ba haka bane Natasha, Kina araina, dake nake kwana dake nake tashi"

"Ban yarda da kalamanki ba Ummi, Idan Dagaske kinyi kewata meyasa baki kirani ba? Sai da na kira ki ni da na damu dake ko"?

Shiru tayi na ɗan wani lokaci har sai da Natasha Ta furta Naji kinyi shiru tukunna taja numfashi tana faman sauke ajiyar zuciya tace"bansan yadda zanyi maki bayani ba NATASHA, ni kaɗai nasan halin da nake aciki, ina cikin damuwa, Ina cikin kaɗaici, Rayuwata a ƙuntace take natasha, bani da wani ƴan ci, ba wanda Ya damu dani, tun safe bana jin daɗin jikina babu wanda ya leƙo ɗaki na don Yaga awani hali nake aciki.... "Muryarta na rawa ta ƙare maganar, tamkar zata fashe da kuka, hakan Ba ƙaramin ɗaga Hankalin Natasha Yayi ba, Jin sautin miryar aminiyarta da alamun matsananciyar damuwa..

Cikin saurin mirya ta furta"Ummi, muyi magana ta video Call, Inason naganki ko hankalina Ya kwanta"

"Toh, amma kafin nan zan shiga toilet, Ƴan mintuna kaɗan Idan na fito zan kiraki" natasha ta amsa mata da toh, bayan ta yi rejecting Kiran, ta daura wayar kan drawer, kafin Ta sanya hannu ta yaye bargon data lullu6a da shi, Jallabiya ce a jikinta launin dark ash, saukowa tayi daga kan gadon ta nufi toilet, After Some minutes ta fito fuskarta da alamun lemar ruwa, Laptop dinta dake ajiye kan desk ta dauko ta koma kan gado ta zauna daga tsakiya ta ajiyeta agabanta, kafin ta buɗe ta soma sarrafata, Natasha ta kira video Call nan take ta ɗaga, kallon juna suka soma yi tamkar suna a wuri ɗaya, Natasha tana a kishingiɗe saman beach chair dake a ga6ar teku, babu suturar mutunci a jikinta, dama ita bata cika son sanya suturar da zata rufe mata tsiraicinta ba, tafi sha'awar ta sanya pant da bra.

cikin harshen turanci suke yin magana.

"Yanayin fuskarki Ya tabbatarmin da bakyajin dadin Ummi, Ki faɗamin meke damunki? Waya ta6a min ke"?

Yamutsa fuska Ummi tayi tamkar batason furta maganar tace"kamar yadda na faɗa maki bana jin daɗin jikina, narasa gane meke damuna, amma ina da tabbacin hada kaɗaici, ban ta6a ƙuntataba Irin na Yau, Jin kaina nake tamkar Ina a prison"

Cikin kulawa Natasha tace"meyasa ba zaki janye aikin da Commender Ya baki ba? Ummi dama ni nasan bazaki Iya jurewa ba, tuntuni naso In gargaɗeki saboda ba zaki Iya ba, mu da muka saba da yawo kullum sai mun fita wurin abokan harkar mu, taya zaki Iya jure rayuwar kulle"? Ta faɗa tana mai dubanta,

Dafe kai Ummi tayi da hannu ɗaya"Har yanzu banyi danasanin kar6ar aikin kula da yaran nan ba, Saboda Inaji araina akwai wani alkhairi atattare da zamana da su, shiyasa bana danasani, ni kawai abunda ke damuna rayuwar kullance ke banaso, Yana ƙuntata Rayuwana, hada ƙarin Yaran da suke ɗebe min kewa basu zo wurina ba yau, ni kuma nakasa tashi naje gare su" fuskarta a yamutse tayi maganar

"Har Yanzu ba zaki fahimce ni ba Ummi, Ni inaso na kwatarmaki ƴan cinki ne, Inason farin cikin ki, Kina buƙatar abokan Harka, kefa ba irin matan da za'a ƙuntata ba ne...' tunkan Natasha ta ƙare maganarta, ummi tayi saurin tarar numfashinta da cewa

"Akwai labari mai daɗi, nasan idan na fada maki zakiyi mamaki"

Ta faɗi hakan ne don batason Natasha taci gaba da yi mata zancen Ajiye aikin da take Yi.

"Naƙosa naji labarin nan fadamin mana" ta fada tana sakin murmushin shaƙiyanci.

"Mutumin Ya ziyarce ni Har cikin gidan da nake,"
Chapter 5 · 0% Book details