Sashe 82
Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Eyyah! Na sanya wayar a silent lokacin da zan shiga meeting...' tai maganar tare da kai dubanta ga su aneelerh"su wanene? Ina fata dai lafiya? Ta fada cike da son jin karin bayani
"Auntyna ne da ƙanina mahboob, wani abune mai mahimmanci Ya kawo mu .."
da sauri Aneelerh da mahboob suka karaso bakin motar hajiya saratu cikin girmamawa suka gaishe da ita, fuskarta asake ta amsa masu wato sunci albarkacin zahra shiyasa ta sakar masu fuska
"Pls kuyi hakuri sun shanya ku arana, Yanzu ku shiga motar, mu tafi. " wani irin dadi Ya lullu6e su, da sauri suka nufi motarsu, bayan sun shiga a jere motocin suka nufi cikin estate din babu wanda yayi gigin dakatar da su cikin securities din sai ma gaisuwar da suke mika ma hajiya saratu wadda ko kallo basu ishe ta ba.
Bayan sunyi parking, kowan nan su Ya fito, Aneelerh sai faman satar kallon katafaren estate din takeyi kamar a dubai, Inaga mahboob wanda Yake ta jinjina kai aranshi Yace"Wai dama haka daular obie estate take? Gari guda, Tabɗijan Daga gani anyi almubazzaranci wurin ginasa, Mutane kamar bazasu mutu subar duniya ba? Yo ni Allahna na tuna ko amafarki ban ta6a ganin katon gini irin wannan ba! Kai jama'a..sai faman santi yakeyi acikin ranshi
Gaba hajiya saratu tayi da sauri suka bi bayanta, zahra hada kar6ar handbag dinta ta ruƙe mata ita, irin fadancin nan
Ashe mahbbob baiga komai ba, suna shiga falon kiris Ya rage ya zabga salati saboda ganin makurar kayan alatun da aka baje ta ko'ina...har wani zazzabi yake ji ajikin shi
Ga masu aiki dake kai komo cikin uniform
"Bismillah ku zauna, Ku ɗan bani mintina kaɗan, Yanzu zan fito..' amsa mata sukai da toh, ta nufi daki zahra tabi bayanta don ta kai mata handbag dinta..
Ya rage saura mahboob da Aneelerh, zama sukai akan tamfatsa tamfatsan royal sofa din falon...
"Karshen duniya yazo aunty aneelerh" ya faɗa yana kishingiɗa bayansa jikin sofa, duk da halin damuwar da Aneelerh take aciki sai da ɗan murmusa jin abunda Mahboob Yace, ita kanta ta girgiza da ganin katafaren ginin
"Alhamdulillah Ya Allah.."ta furta aranta"Ya Allah kamar Yadda ka bamu ikon shiga gidan nan lafiya, Ya Allah ka bamu ikon ganin Yarinyar nan cikin sa'a ba tare da mun sha wahala ba" har cikin ranta wani irin sanyi takeji, fatanta Allah Yasa su dace
Kallon mahbbob tayi wanda ke ta bin ko'ina da kallo baki asake kamar lehen sakarai
"Mahboob! Pls kaja aji mana, kada kai mana kauyanci, duk fa abinda suke da shi mu ma muna shi agida...." tashin Farko Ya ce"muna da lifter..? murmushi aneelerh tayi"a'a amma ai akwai stairs ko"?
Girgiza kai yai"ba irin wannan ba duba fa kiga ni har hawa uku, ga yan aiki ta ko'ina..." murmushi tayi tana kallon shi" nifa aunty aneelerh bawai kyawun gidanne Ya ruɗe ni ba, no kawai almubazzarancin da akai wurin ginasa shiyafi komai 6ata min rai, Allah ba karamin mai imani bane zai zauna agidan nan kuma yaci gaba da yin sallah..." yar dariya Aneelerh tayi
Kafin wani Ya ƙara magana sofia ta nufo wurinsu hannunta ruƙe da tray na cool drinks tare da snack ta ajiye masu kan table
"Inayi maku barka da zuwa" amsa mata sukai da yawwa
"Hajiya saratu ce, ta bada umarnin akawo maku drinks, idan akwai abun da kuke bukata ku sanar dani..." har suna haɗa baki furta"a'a mungode,
Bayan ta bar wurin Mahboob Yace"munci darajar Zahra wlh da ko kallo bamu ishi matar can ba, daga ganin ta zatai ji da kai..."
Bayan wasu Ƴan mintuna, Hajiya saratu ta fito har ta canza kayan jikin ta, wata hadaddiyar abayace ta sanya, zahra na abiye da bayanta har suka karaso, zama tayi kan sofa tana fuskantarsu, itama zahra ta zauna.
Ƙara gaisawa sukayi kafin ta ce"Zahra ta faɗa min abune mai mahimmanci Ya kawo ku! ina sauraronku..." cike da dattako tayi maganar.
Gyara zama Aneelerh tayi cikin nutsastsiyar muryarta ta fara kora mata jawabin abun da Ya kawo su...
bayan ta kammala hajiya saratu tayi jimm na ɗan wani lokaci kafin ta dubeta"kun tabbata Yarinyar ce? Shiru sukayi ta kuma cewa" Bana so asamu matsala! Ba ku tunanin ko mai kama da ita ce..."?
Duk da ƙwarjinin da hajiya saratu tay wa aneelerh hakan bai hanata Yin karfin halin furta"muna sa ran itace, saboda ni tamkar uwa nake agareta, Yau shekara shida zuwa bakwai da 6atanta kamar Yadda na fada maki, kuma sunan yarinyar Unasah kamar yadda itama yarinyar da shi owais din yake ruƙo sunanta unaisah, amma muna kiran ta da Angel sunan da daddynta Ya sanya mata..." da kwarin gwiwa Aneelerh tayi maganar don ji take zata iya komai akan yarinyar nan
Numfasawa hajiya saratu tayi abunka ga mace mai izza, bata son abunda zai jawo raini tsakaninta da chief gani take kamar zubda girmane ta nemi alfarma awurinsa shiyasa take jinjinawa lamarin da suka zo mata shi, duk da tana son taimaka masu.
"Ina hoton Yarinyar, Ina son ganin shi" cikin sauri zahra ta buɗe mata hoton awaya ta muƙa mata.
Bayan ta kar6a ta kurawa hoton ido nan take ta gane fuskar yarinyar cikin yaran da owais yazo da su wurin dinner.....
"Ina hoton ita Yarinyar ta wurin ku"? Ta faɗa tana kallon Aneeelerh, yatsun hannunta har kerma sukeyi wurin saurin curo wayarta daga cikin handbag ta buɗe hoton Angel ta yunkura taje gaban hajiya saratu ta miƙe mata wayar
Bayan ta kar6a ta jera wayar zahra da aneelerh akan table din gabanta, a tsanake take nazarta hotonan ita kanta ta gasgata abunda suke hasashe komai iri ɗaya, banbanci ita yarinyar da uwais Yake ruƙe ta fi angel dinsu girma amma duba da tazarar shekarun da yarinyar ta 6ace zai iya yiwuwa itace taƙara girma...
Gaba daya hankulansu Aneelerh akan hajiya saratu duk sun kagara da son jin me zatace masu..
Bakomai take jinjina mawa ba face ta yadda zata zubda girmanta wurin yiwa owais magana, saboda basa jituwa tun time da ta fahimci bai kaunar mijinta, kuma tana jin haushin Yadda ake nuna wariya tsakanin Twins dinta da shi
"Dan Allah ki taimaka mana kamar yadda Allah Ya taimake ki, wallahi baki ga halin da mahaifiyar yarinyar take a ciki ba, yanzu haka tana agadon asibiti kwata kwata bata a cikin hayyacinta, sunan mijin ta da yarta kadai ta ke Iya ambato..."
muryar Aneelerh ce ta katse mata zancen zucin nata
"Meya same ta ne? Ko kina nufin tsawon lokacin da yarinyar ta 6ace bata a cikin hayyacin ta..." ta jefa mata tambayar cike da sonjin karin bayani
Labari aneelerh tafara bata tun guduwar benazir da kuma dawowarta har izuwa kan abun da Ya faru jiya
Jinjina kai hajiya saratu tayi da alama abun Ya tsuma zuciyarta duk da bata nuna ba.
"Allah ya bata lafiya" suka amsa mata da ameen.
"Zan nema maku alfarmar ganinta, amma kafin nan ina bukatar ku bani zuwa gobe, kunsan yanayin aikinsu na jami'an sirri, kuma yaran kamar suna bincike kan case dinsu ne, ganinsu zaiyi wuya, dole sai na fara yin magana da shi....."
Aneelerh taso ace ta kira chief din awaya sunyi maganar nan take amma dole ta hakura tunda su ne ke nema awurinta dole su yi biyayya
A tare suka haɗa baki wurin yi mata godiya.
har bakin motarsu hajiya saratu ta rakosu ta ƙara jaddada masu gobe zasuji daga gareta
Lokacin da motarsu ta haura kan titi, shiru babu mai magana a cikinsu,
"Wani jinkirin Alkhairi ne, muyi hakuri" zahra ce ta fada ganin damuwa na neman rikita auntynta
"Allah Ya tabbatar mana da alkhairinsa" suka amsa mata da ameen
Dai dai motarsu ta kusa shiga tankameman gate din asibitin saiga motar dr shureim tana fitowa daga ciki, kasancewar window glass din abude Yake da sauri aneelerh ta kwala masa kira Ya shureim...
Ya na ganinsu Ya samu wuri Yai parkin din motarsa, fitowa tayi da sauri ta nufi motar ta ɗan zukunna bakin glass din tana kallonsa
Duk sai taji wani iri ba dadi ganin yadda fuskarsa tayi jawur idanunsa sun kumbura
"Yaya shurem Ya jikin benazir din?
"Da sauƙi, amma har Yanzu bata tashi daga bacci ba...
"Allah Ya bata lafiya
"Ameen..." shiru sukai kafin tace"naga ka fito ko gida zaka koma ne..."
"Bani zan koma gida ba, zeenatu zan maida..." sai da yai maganar idonta Ya hango mata zeenatu dake zaune a backseat ta kifa kanta bisa gwiwowinta yatsun hannunta sai kerma suke daga gani babu nutsuwa atare da ita
"Ina fata badai wani abu Ya same ta ba"!
"Daddynta ne Yace amaida ta gida, shi ne take kuka"
"Allah sarki baiwar Allah...." cikin nuna tausayawa tayi magnar, zeenatu duk tana jinsu saidai bata jin zata iya dagowa saboda gaba daya fuskarta ta ca6e da ruwan hawaye..
"Ya ake ciki game da Yarinyar kun samu ganin ta..."? Ya jafe mata tambayar saboda abun na aransa
Nan Aneelerh ta sanar da shi Yadda sukai da hajiya saratu
Jinjina kai yai"in sha Allah gobe idan ta kiraku awaya tare zamuje estate din....ko su mami ban sanar mawa ba saboda bana so su sanya rai har sai mun tabbatar in itace....
"Shikenan Yaya shureim Allah Ya kaimu lafiya amma zaka dawo ko"?
"Ay dole na dawo aneelerh, Daga na kaita zan juyo..." Allah Ya dawo dakai lafiya
Sallama sukai ma junansu, ta tsaya tana kallon motarshi har ta 6ace ma ganinsa
Komawa tayi cikin motarsu, Mahboob Ya karasa shiga da su ciki tun kafin yayi parking yake ta faman jinjina kai Yana fadin anyi almubazzaranci wurin gina asibitin sai kace ba wurin jinyar marasa lafiya ba, komeye amfanin ƙawata asibiti ...."
yana karasa yin parking suka fito da sauri suka nufi emergency ward sai da suka fara tsayawa wurin nurse's station bayan sun fada masu sunan marar lafiyar da suka zo dubawa, ɗaya daga ciki tayi masu jagora har dakin da aka kwantar da ita, kafin ma su isa suka hango Hajiya layla tare da Alhaji ubaid abakin kofar asitin suna magana atsakaninsu, fuskokin kowan nan su babu annuri sai tsantsar damuwa
Takun tafiyarsu Aneelerh ne Yaja hankulansu ga dubansu
"Aneelerh......" hajiya layla ta fada cike da mamakin ganin ta, ita kanta baza ta iya tuna rana ta karshe da tai tozali da ita ba.