Sashe 78
Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ga fitsari cike da mararta amma saboda abun da Ya faru Ta hakura da yin shi, ta matse shi kuma cikin ikon Allah wani baccin Ya sake daukarta
____________________UNAISAH ANGEL
Kiraye kirayen sallar asubahin da aka farayi ne Ya farkar da ita, addu'ar tashi daga bacci ta karanta sannan ta miƙe zaune ta ɗan jingina bayanta jikin headboad
Kayan baccine a jikin ta, Milk colour riga da wando masu kyan gaske da alama baccin bai sake ta, sai faman lumshe idanu take Yi
bakomai take tunani ba face Aunty pretty ɗinta, bata ta6a damuwa da ita irin na Yau ba, Wani irin marmarin son jin muryarta take Yi aranta ta ayyana ko awani hali take a yanzu?
Canza akalar tunanin nata tayi akan danish, murmushi tayi tunawa da haukansa na jiya har yanzu inta tuna abun da yai mata sai taji wani irin yanayi atare da ita
Ta ɗau lokaci tana ƴan tunane tunane, kafin ta ware gray eyes din ta, hannu takai ta ɗan bubbuga kafadar deeja dake bacci tana jan minshari
"Sis ki tashi time din salla yayi" cikin magagin bacci deeja tace"Ni ki kyale ni, waike kullum sai munyi sallah ba a hutawa...."
Murmushi unaisah tayi"Pls kada ki wahalar dani..."
Daƙyar ta samu khadeeja ta farka daga bacci, bayan sunyi alwala suka sanya hijabi a jikinsu,
Ko da suka kabbara sallar khaddeeja ba ibadar ce agabanta ba, da zarar unaisah tayi sujjada ko ruku'u sai ta daddage ta ɗuma mata dundu abaya
Baiwar Allah, ahaka ta daure suka kammala sallar, bayanta har wani zogi Yake mata,
Batasan Ya zatai da ita ba, Haris ne Yaja mata shi da ya fara kawota dakin su don ta kwana,
Akan darduma bacci Yai awon gaba da khadeeja
Miƙewa tay da sauri ta dauko wayarta dake ajiye kan mirror cike da zumuɗi ta danna ma aunty pretty call tasan i warhaka ta farka Yin sallar asuba
Almost 3 times wayar tana ringing ba'ay picking ba, duk da haka bata hakuraba ta sake jaraba kira
Cikin sa'a Akai picking batare da anyi mata magana ba
Calmly unaisah tay mata sallama tare da cewa aunty pretty barka da asuba, kin tashi lafiya....." shiru ba alamar za'ay magana
"Naji kinyi shiru bakice komai ba, dan Allah kiyi min magana jiya har mafarkin ki nayi ..." kafin unaisah ta ƙare maganar wata murya ta ratsa ta da cewa"Wacece Ke? Kuma wa kike nema"?
Wani irin shock taji, Har saida gabanta Ya faɗi jin muryar Yarinyar sai taji kamar ta ta6a jinta awani wuri
"I'll hang up if you don't talk!'"
Da sauri tace"sunana unaisah, aunty pretty nake nema"
"Oh ko ke ce kika kira wrong number rannan"?
"Ni ce"
"Okey, me wayar ba ta farka daga bacci ba..".
"Wacece ke"?
"Cousin dinta ce, sunana zeenatu" lokaci ɗaya taji yarinyar ta shiga ranta, ta rasa a ina ta ta6a jin muryarta tabbas akwai wadda ta sani mai irin voice din ta
"Dan Allah, Idan ta farka daga bacci ki faɗa mata na kira,"
"Toh sai anjima" tana fadan hakan tay rejecting call din
Ƙurawa screen din ido Unaisah tayi, yayin da kwakwalwarta ke cigaba da tariyo mata voice din zeenatu.
A bangaren zeenatu bayan sun gama waya da unaisah, mikewa tay daga kan darduma jikinta sanye da dogon hijabi, hannunta ɗaya ruƙe da wayar cikin sauri ta fito ta nufi dakin Benazir
Kamar yadda suka bar shi jiya haka ta same shi a garkame, dr shurem daya kwana awurin kiran sallar asuba ne Ya farkar da shi lokacin da zeenatun tazo baya awurin sun tafi masallaci
Knocking kofar tayi"aunty benazir dan Allah ki buɗe min ƙofa, inason ganinki, jiya na damu da halin da kika shiga, ko baccin kirki bansamu nayi ba..." shiru babu alamun zata buɗe mata.
"Zeenatu ki daina wahalar Yi mata magana ba buɗewa zatay ba, halin ta ne tun tana ƙarama in Ranta Ya 6aci sai munci wahala kafin mu shawo kanta..." hajiya layla ce tay maganar, baiwar Allah daga ganin idanunta ko bacci batay ba sunyi ja idon Ya ƙanƙance
Muryar zeenat kamar zata fashe da kuka tace"tun jiyafa take a daki kulle! Bata magana, Idan wani abu Ya same ta fa..."
Shigowar Su dr shureim ne Yaja hankulansu ga dubansu, Su ukune tare da Alhaji musa da Alhaji ubaid duk sun sanya jallabiya a jikin su.
Zeenatu na ganin daddynta, da gudu ta nufe shi, ta faɗa kan kirjinshi tana kuka take fadin daddy aunty benazir taƙi buɗe ƙofa tun jiya, dan Allah kasa a balle ƙofar, bana so wani abu Ya same ta...'
Fuskarsa babu annuri Yace"meyasa zaki damu kanki akanta? Ba ita ta kulle kan ta ba ne? Ko wani Ya rufe ta ne..." bai kare maganar ba hajiya layla ta katse shi cikin 6acin rai tace"wai kai wani irin bauɗaɗɗan mutun ne? Baka da tausayi ne kwata kwata arayuwarka? Jiya kana ganin halin da ta shiga har faɗa maka akai amma saboda rashin imani sai cewa kai a kyaleta in ta gaji zata buɗe kofar saboda ba yarka bace ko..."?
bata ƙare maganar ba Alhaji ubaid Yai hanzarin katse ta da cewa"dan Allah kiyi hakuri ki daina ɗaga masa murya, jiya agajiye muka dawo gidan shiyasa Yace haka" harara ta wurga masa"kai ay saboda yarkace jiya ka hana idon ka bacci duk da agajiyen ka dawo gida, na tabbata da ace yarsace ke ahalin da benazir take aciki wallahi ba zaka iya runtsawa ba...." tun da tafara magana Alhaji musa Yake bin ta da kallo, arayuwarsa Ya tsani mutumin dake masa faɗa Yana ɗaga masa murya, babu wanda ya ta6a gigin yi masa hakan sai hajiya layla....
Dr shureim Bai tsaya kula su ba, ya juya ya nufi dakinsa zuciyarsa sam bata masa dadi, lamarin Family dinsa Ya fara gundurarsa kwata kwata ba zaman lafiya daga wannan sai wannan
Jinjina kai Alhaji musa Yayi, ba tare daya tanka mata ba, har Ya ɗaga ƙafa zai wuce Hajiya layla ta dakatar da shi ta hanyar shan gaban shi
Da mamaki Ya dago Yana kallon ta
"Wallahi babu inda zakaje! In har bakasa an buɗe kofar dakin benazir ba ni kuma bazan ta6a bari kabar wurin nan ba..." tana huci ta faɗa haɗi da ruƙe qugun ta, wlh a lokaci niyar kwashe ta da mari yayi amma sai Ya fasa Yatsun hannunsa har kerma su ke tsabar 6acin rai, wai shi yau mace zata tari gabansa? Batare da jin shakkarsa ba? Wacece ita? Dame take taƙama ne"?
"Layla ba haka mukai dake ba! Kin manta alkawarin da kikai mun na cewa ba zaki ƙara shiga huruminsa ba"? Azafafe ta kalli Alhaji ubaid"ban manta ba, amma wallahi Yau bazan raga masa ba, ay shi yasan ta yadda zaisa abude kofar, don haka bazan tsaya inaji ina gani in rasa ƴata ba dole yasa aballe kofar can" ta yi maganar tana watsa masa harara...
Fashewa da kuka zeenatu tayi jikin ta har jijjiga yakeyi, cikin shesshekar kuka tace"daddy dan Allah kasa a bude kofar, ni bana son inga kuna samun sa6ani atsakaninku, dan Allah daddy ka taimaka mana..." kukan zeenatu ba karamin tafasa zuciyarsa yakeyi ba
Gauran numfashi Yaja, tare da ɗan jinjina kansa Yana huci kamar mayunwacin zaki ya dubi hajiya layla da tai masa ƙerere kamar zata rufesa da bugu
A fakaice taga Ya sakar mata wani shu'umin murmushi har saida taji gabanta Ya faɗi
Sassauta fushin fuskarsa Yayi"naji zan buɗe ƙofar, ki bani hanya na wuce" matsawa tayi idanunta akan fuskarshi Ya nufi kofar dakin benazir
Yana ƙarasawa bakin ƙofar, Ya ɗaura faffaɗan tafin hannunsa, turata yayi wani iko na Allah sai ga ƙofar ta buɗe
Kallon Juna Alhaji ubaid da Hajiya layla sukai, abun da daure kai tun jiya suke gabzar kofar donta buɗe babu wanda bai jaraba karfinsa ba amma duk abanza ko motsi batayi amma shi daga turawa ta buɗe wani irin ƙarfi ne da shi? Basu tsaya dogon tunani ba, jiki na 6ari suka nufi ɗakin zeenatu da gudu ta rigasu faɗawa a ciki.
Shugarsu keda wuya kowan nan su Yaci burki, Abun da suka gani Yayi matuƙar ɗaga hankulansu, kamar matatta haka suka hangota kwance kan floor rabin jikin ta a cikin toilet dake a buɗe, kamar irin tayi gudu ta kife awurin har kanta Ya daku goshin ta Ya fashe
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji!"un"! hajiya layla ce ta zagba salati tana tafa hannayenta, zeenatu da ta gama ruɗewa agaban benazir ta zube bisa gwiwowinta, takai hannu tana tatta6ata Aunty benazir! Meke damunki dan Allah ki tashi inna lillahi..mami daddy ku ce ta tashi dan Allah....
da sauri Alhaji Ubaid Yaje Ya ɗago da ita, jikinta duk Ya saki ya ɗauko ta da hannu biyu ya kwantar da ita akan gadon ta, sumar kanta duk Ta yamutse
Fita hajiya layla tayi jim kaɗan ta dawo da robar ruwa ta buɗe murfin ta kur6i ruwan tare da furzar da shi kan fuskar benazir
Ruwan na dura tayi wata irin zabura tana ambaton sunan taj ... adai dai lokacin shureim Ya shigo dakin ganin su tsaitsaye bakin gadon ta yasa shi saurin karasawa
Tunkafin yayi magana Hajiya layla tace"shureim ka gani ko? Abun da nake gudu kenan! bansan ya akai ta faɗi kasa daga cikin toilet, kanta Ya bugu..."
Hankalinsa atashe Yake kallon Benazir yatsun hannunta sai kerma suke, ta runtse ido tana sambatu kwata kwata bata acikin hayyacin ta
Zeenatu duk ta damu, Hannunta ruke dana benazir sai faman shesshekar kuka take
"Ya akai kofar ta buɗe"?
"Uncle din ku ne Ya buɗe kofar," ta bashi amsa ataikaice, Alhaji ubaid Tuni Ya fuce Yabi Alhaji musa don Ya fada masa halin da benazir take ciki
A lokacin Har Ya koma Part dinsa, sallamar Alhaji ubaid ce ta katse sa kamar bazai fito ba, don saida Ya ɗau lokaci har sai da hajiya sara tace da shi baiji ana sallama bane? Tukunna Ya mike cikin takun izza Ya fito daga dakin
"Me kuma zanyi bayan na buɗe ƙofar"? A faɗace Ya faɗa Yana ƙanƙance idanunsa
"Dan Allah ka yi hakuri da abun da layla tayi maka, bata jin maganata naja mata kunne taki bansan ya zanyi da ita ba..." ya mutsa fuska Alhaji musa yai"naji, Yanzu awani hali benazir din take a ciki?