← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 238

Sashe 57

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sun sauke masu cake din akan glass table, ba su tafi ba, tsayawa sukai don ayi shagalin da su.

Cikin harshen turanci ɗaya daga cikin chef din yace"muna tayaku murnar haɗuwa da ƴan uwanku, kuma muna tayaku murnar samun ƴan ci arayuwar ku, sannan muna yi maku fatan Allah ya dawwamar da farin ciki arayuwarku" gaba ɗaya suka haɗa baki wurin yi masu godiya.

"Bismillah, wannan na ku ne, chief ne Ya bada Umarnin A haɗa maku Cake, saboda ku ji daɗin yin shagalin murnar ganin yan uwanku" ɗaya daga cikin chefs dinne Ya faɗa, bayin Allah saboda farin ciki hawaye ne suka cicciko idanunsu waɗanda suka kumbura saboda kukan da suka sha.

Hannayen su ruƙe cikin na juna suka kewaye Cake din, Lokaci ɗaya wani abu ya faɗo masu aransu wanda ba komai bane face farkon zuwan Sabbin prisoners gidan kurkukun ƙaddara, ba zasu ta6a mantawa da lokacin ba har abada, ranar da giants suka kawo masu cake sunata murnar yanka shi akarshe majnoon yayi ajalin shi.

cikin shessheƙar kuka jemimah tace"Genie Ina majnoon ɗina? shi bai dawo ba? Yakamata shima Yazo tun da su deeja ma da suka mutu sun tashi"

kumatunta jawur tayi maganar, gaba ɗaya ta karya masu zuciyoyin su.

"Jemimah wanda ya mutu ba ya dawowa sai dai idan dama kwanansa ne ba su ƙare ba, Majnoob Ya mutu ba zai ta6a dawowa awannan duniyar ba, amma in sha Allah zamu haɗu da shi agidan aljanna" yayin da Unaisah take yin maganar bakomai take tunawa ba face fuskar majnoon da unaizah, hakika ba zasu ta6a mantawa da farkon zuwanta gidan kurkukun ƙaddara ba, lokacin da ta sauko kan stairs cikin shiga ta school uniform red colour, ƴar gayu da ita wayayya ta goya back dinta abayanta.

muryarta ce ta soma yi ma unaisah gizo a kunnanta.

_Hi, Am unaizah ƴar gidan daddy, can i know u_

_that's Impossible, ae ni bana sharing soson wanka, Kuma bana wanka in ba a cikin bathtub ba, I can't stay here i wanna go home, cos daddy ba haka Ya kwatanta min school ɗin ba, Yace min fa komai irin na Gidan mu ne, but why naga banbanci_

Runtse ido unaisah tayi yayin da take jin wani irin kewarta a zuciyarta, tayi fatan ace gaba ɗayansu ne suka rayu sai dai kash Allah baya barin wani dan wani yaji dadi.

Siraran hawaye ne suka wanke fuskar Sajeed tunawa da yar uwarsa Gabriella wadda a halin Yanzu ba shi da tabbacin tana araye kota mutu, lokaci ɗaya sautin muryarta ya soma cika kunnuwansa farkon kasancewarsu agidan kurkukun ƙaddara lokacin da za'a raba su da junansu tana kuka tace

_ My twin bro, Ka kula min da kan ka, Duk inda za'a kai ni zan dawo wurin ka_

Kowa da abun da yake tunawa aran shi, ganin jimamin nasu bame ƙarewa bane yasa sheikh Imam Yi masu nasiha mai ratsa zuciya, ya dinga jawo masu ayoyin kur'ani Yana fassara masu har saida yaga sun samun nutsuwa tukunna Ya dakata...

"Waye zai fara Yanka mana cake din"? boss ne ya faɗa yana kallon su don jin za6in su, Har suna hada baki wurin furta"Unaisah"

Idanunta amarairaice ta kalli faces din yan uwanta kafin ta sanya yatsun hannunta dake kerma ta dauki ƙaramar wuƙa, har taj ya yunkura zai ruƙo hannunta don ya taimaka mata ganin hannun ta na kerma, tunawa da danish yasa shi fasawa don har yanzu bayanshi bai daina yi mashi zogi ba.

A hankali ta yanko cake din tare da ɗagowa tana kallon su idanunsu duk suna akanta, tama rasa wa zata fara bama cake din duk da akwai wanda zuciyarta ta aminta da cancantarsa, satar kallonsa tai nan take idanunsu suka shiga cikin na juna,

"Angel ki ba danish, shi Ya cancanta ki bamawa," muryoyinsu sajeed ne suka cika kunnuwanta.

kau da ido tayi daga kan danish ta kalli daddynta, Lumshe mata idanunsa yai alamar ya amince mata.

Murmushi ta ɗan saki har dimples dinta suka lotsa, matsawa tayi kusa da danish, ta miƙa masa cake din ya buɗe ƙaramin bakinsa ta sanya masa, gaba daya suka soma tafa masu, Bayan ta ƙara cirar wani cake din ta miƙa ma daddyn ta Yaci.

daga bisa ni ta miƙa ma Haris Wuƙar, Ya kar6a Ya datsi cake din ya sanya wa deeja abaki, wani irin farin cikine Ya lullu6e su

Bayan ta gama taune na bakinta, ya bata wukar don ta bashi, abunka game tabin hankali, maimakon ta kar6i wuƙar sai ta sanya hannu ta 6allo ƙato ta duma masa abaki har cikin hancinsa ya shiga, gaba ɗaya suka sanya dariya, cike da nishadi.

Kar6ar wukar batool tai, ta ballo cake din ta ba mubeen Abaki Yaci, Kafin Ta sake gutsuro wani ta miƙa ma Rubina itama taci, ɗaya bayan ɗaya duk sai da suka ciyar da junan su cake din.

Tunawa da aunty umminsu dake ta kallon su, yasa batool ta sake kar6ar wukar daga hannun Sarah, ta yanko cake din taje gaban ummi ta miƙa mata, murmushi tasaki tare da ruƙo hannun batool ta tura shi abaki tana taunarsa ɗagowar da zatayi kwatsam suka haɗa ido da sheikh iman dake ta satar kallon ta, duk sai taji jikinta yayi mugun yin sanyi, tuni taji wasu hawayen sun cika idanunta, muryarta na rawa tace da batool"ba ki ba sheikh imam cake din ba" tana fadin hakan tai saurin juyawa ta nufi hanyar komawa bedroom dinta, sam yakasa janye idanunsa daga kallon ta hatta su taj sai da suka lura da kallon ummi da yakeyi sai dai basu kawo komai aran su ba.

Jiki asanyaye Batool ta ƙara yanka wani cake din taje gaban sheikh Imam Ta miƙa mashi, sai da Ya fara ɗaura tafin hannunsa akanta ya ɗan shafa shi ya furta"Allah yayi maki albarka" kafin Ya buɗe baki ta saka mashi cake din'

Murmushi kowan nan su Yasaki gwanin ban sha'awa.

Da zolaya big guy yace"yau an nuna min wariyar launin fata, Ni babu mai bani cake din"?

da sauri sajeed yace zan baka, girgiza kai yayi"I'm sorry Ni mace nakeso ta bani ba jin sina ba" dariya suka sanya gaba dayan su.

Harara boss yadan jefa masa cikin muryar raɗa Yace"kai bana son iya shege fa, halan tazurancin naka ne Ya motsa" ƴar dariya yai har hakoransa suka bayyana.

"Ni zan baka cake din" jemimah ce tayi maganar, da karfin hali fuskarta sharkaf da hawaye, gaba ɗaya suka sanya dariya,

matsawa big guy yai tare da kai hannu ya dauki Jemimah, kafin Ya bata wukar Ta yanka ta bashi abaki, shima ya karbi wukar ya 6allo cake din Ya sanya mata abaki.

Sautin tafin su Ya cika falon, wunin ranar shagali sukayi babu kakkautawa yadda kasan gidan biki.

_______________________________✍️

Safa da marwa takeyi a tsakar dakin ta, fuskarta dauke da tsantsar farin ciki, gaba daya ta shagala da tunanin Yar ta Angel sam ta manta da zancen tafiyar su, zumuɗi Ya hana ta zauna jira take Aneelerh ta tura mata da hotunansu duk tabi ta kosa da son ganin fuskarta

Jin ƙarar shigowar sakonni ta whatsapp din da ta buɗe ne, yasa tai saurin duba screen din wayar dake ruke a hannunta, wayyo Allah dadi, tsabar zumudin ta buɗe sakon Aneelerh yatsun hannunta har kerma sukeyi, lokacin da ta ɗaura idanunta akan hoton Unaisah ƙafafuwanta kasa ɗaukarta sukai, awani slow ta koma gefen gado ta zauna hannunta ɗaya dafe da bakinta take kallon hotunan Unaisah, yayin da zuciyarta ke harbawa da karfi da karfi tun da take a duniyar nan bata ta6a jin son wani ɗan adam fiye da yadda takeson ƴarta, duk da basu taba haduwa ba amma taji wani irin mahaukacin son yarinyar na ƙara shigar zuciyarta.

Hotunan da Aneeleeh ta turo mata na unaisah tun tana jaririyarta nannaɗe cikin farin towel, hada hotunan Birthday dinta lokacin ta cika shekara goma aduniya, sunyi kyau hotunan kamar lu'u lu'u

Wani irin sanyine Ya ratsa zuciyar benazir, a kalla ta shafe mintuna tana kallon hotunanta, kafin ta buɗe na baby junaid din Aneeleeh, Murmushi tasaki tana kallon kyakkyawan yaron kamar sabon fure ya kwanta mata aranta, Bakomaine Ya faɗo mata aranta ba face Fatimar yaya shureim ita kadaice babu acikin su

A hankali ta furta"Allah sarki Aisha ke kadai ce babu jinin ki araye, mun yi babban rashi, Allah yajiƙan fatima Allah Yasa mai ceto ce....." idanunta cike tab da kwalla tayi maganar.

"Benazir zaman me kike yi"? Rass taji gabanta ya fadi jin muryar hajiya layla, a hanzarce ta dago tana duban kofar shigowa dakin, Hannunta ruke da trolley din kayanta, fuskarta babu fara'a sai faman huci take yi, Shigowa dr shureim yayi da sauri yana kokarin shawo kanta"mommy dan Allah ki yi hakuri ki fasa tafiyar nan, kinga daddy bai amince maki ba, Yakamata kibi umarninsa ko dan gujewa fushin ubangiji...." harara ta watsa mashi tana fadin"shureim zan 6ata maka rai wallahi, Idan kai bazaka bi ni ba to ka ƙyale ni in kama gabana, har yaushe ne zan cigaba da zama ana raina min wayau agidan nan? nafa san me nake yi, ni ba shashasha bace..." mai da dubanta tayi ga benazir wadda tuni ta miƙe tsaye damuwa ce tsantsa akan fuskarta.

"Wuce mu tafi, Idan kema ba zaki bi ni ba, to ki zauna tare da su" ta fada rai a6ace.

Cikin sanyin murya Benazir tace"mommy ki yi hakuri dan Allah, kinsan bazan ƙi bi umarninki ba amma bazan iya tafiya ba...." baki asake Layla ke kallon ta.

"Nima ba son zama gidan nakeyi ba, Aneeelerh ce ta kira ni awaya, kiran da muke ta jira, sai yau Allah Ya nufa, dan Allah mami kibarni in hadu da ita inyaso daga baya sai mu tafi"

Girgiza kai hajiya layla tayi"kawai kizo mu tafi, in mun fita zamu fara biyawa gidan su Aneelerhn kafin mu tafi" da ƙarfin hali tai maganar, ita kanta tana jin fargaban zuwa gidansu aneelerh saboda bata so Benazir ta gane karyar da tayi mata nacewa su taj sun bar kasar amma a halin yanzu idanunta sun makance burinta su bar gidan duk abun da zai faru ya faru.

Gyada kai Dr shureim yayi"ki bita ku tafi, Allah Ya kiyaye hanya, Ni zan jira daddy"
Chapter 57 · 0% Book details