← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 238

Sashe 117

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

haɗa ido su kayi da juna da sauri dr. Shureim ya kau da idon shi gefe ɗaya, hakan bai dame shi ba yaci gaba da magana cikin tausasa harshe"inaso komai ya wuce shureim, ni bana son duk wani abu da zaisa mu samu sa6ani atsakanin mu..." sai da yai wannan maganar shureim ya dube shi dakyau yace"uncle ni wannan duk ba damuwata bace, bana ruƙe mutun a zuciyata, tabbas banji dadin kalaman daka jife ni da su ba, sun bata min rai, saboda ban ta6a tsammanin zaka iya furta min su ba, da ace wani na waje ne ya gaya min su bazan ji komai ba, amma kai da kanka uncle why? Saboda na fita da zeenatu yar uwata? Ko dan saboda rungumar da nayi mata wanda nikaina bada son raina nayi ba.." idanun shi cike tab da kwalla ya fada yana kallon cikin idon shi"saboda zafin kalaman daka furta min jiya ko bacci banyi ba, da bakin cikin su na kwana azuciyata" mood din fuskar Alhaji musa Ya canza sosai, kalaman shureim sun karya mashi zuciya sai yaji duk ba dadi.

Ruƙo hannun shi yayi a cikin nashi ya ruƙe su gam na ɗan wani lokaci kafin ya fara magana a tsanake"Allah ya huci zuciyarka shureim, na gane kuskurena kuma in sha Allah zan gyara.."ya faɗa yana ɗan jinjina kan shi.

"Da akwai wata tambaya da kayi min ajiya, dangane da kullan da ni ke yiwa zeenatu, kace ka fara kokwanto akaina! Shureim ina son jin dalilin dayasa kace haka? Wani irin kokwantone kake yi akaina..." ba tare da jin shakkar shi ba yace"ban yarda da kullan da kake yi mata ba, raina yana bani kamar akwai wani abu da kake 6oyewa shiyasa nake kokwanto akanka, ka hanata cigaba da karatu, ka hanata yin kawance da kowa, sannan ka hana ta fita, kamar baka son kowa ya ganta, ita kanta zeenatun ta fara korafi kan kullan da kake yi.

Shiru Alhaji musa yayi tamkar bazai yi magana ba, can kuma ya saki Murmushin gefen fuska kafin yace"zan fada maka dalilin dayasa nake kullanta, in har hakan zai goge zargin da kakeyi akaina.." ya fada yana kallon shi.

Kafin ya ɗaura da cewa"Dalilin dayasa nake kullan zeenatu, is that I'm a famous politician with many enemies who want to harm me. Zeenatu is my weakness, bayan haka itace ƴa ɗaya tak da nake da ita akusa dani, in har ban bata kariya ba, rayuwarta tana a cikin hatsari saboda akwai masu bin diddiginta, bana so inyi ganganci da rayuwarta, makiyana sun sha turo min sako akan zasu halaka zeenatu, shureim taya bazan killace ta agida ba"? Maganar Uncle musa tayi tasiri a cikin zuciyar shureim jikinshi yayi sanyi zuciyarshi ta karaya, hankalin shi ya tashi da jin abunda ke faruwa da rayuwar zeenatu!

"May be zeenatu ta manta bata fada maka ba, lokacin da tana zuwa high school, kusan kullum in zataje makaranta sai an samu wadanda suka kai mata farmaki, don ma Allah yasa akwai bodyguards da suke kula min da ita ay da tuni zeenatu babu ita araye" ya faɗa tare da dukar da kan shi ƙasa ya marairaice fuska kamar ba Alhaji musa ba.

Cikin sanyin murya Dr shureim Ya furta"Uncle, hankalina ya tashi da jin maganar nan, yanzu na fahimci dalilin dayasa kake kullanta, ni kaina bazanso abun da zai cutar da ita ba, amma kullan yayi yawa tun da har ta fara takura, bai kamata saboda wasu ahanata jin dadin rayuwarta ba, bayan haka Allah shi yake tsare bawansa aduk inda yake, kuntata rayuwarta agida bashi bane mafita ba, wlh duk tsaron dake agidan nan bazai hana a cutar da ita ba, amma idan muka cigaba dayi mata addu'a, in sha Allah makiyanka ba zasu ta6a yin nasara akanta ba!" wasa wasa dr shureim ya 6uge dayi mashi nasiha har saida ya tabbatar Ya samu nutsuwa Kafin yayi shiru yana jiran jin me zaice..

"Shureim nagode da shawararka, zanyi tunani akai in sha Allah, sannan akwai magana da nakeson yi dakai idan na samu lokaci..." bai kare maganar ba, wayar shureim ta fara ringing,

"Zan ɗaga kira"

"Okey, pls ka sameni a dining, zeenatu tana jiranka, tace bazata iya cin abinci in ba atare dakai ba..." jinjina kai shureim yayi bayan fitar Alhaji musa ya nufi gaban mirror ya dauki phone dinsa Ya duba sunan mai kira, mommyn su ce da sauri yayi picking ya kara a kunnanshi

Tunkafin yayi sallama muryar hajiya layla ta katse shi"shureim wai lafiya tun jiya inata kira bana samunka ko wani abu ya faru ne?

Cikin sanyin murya yace"a'a mommy, kiyi hakuri, wayar tana a kashe ne ban jima da kunnata ba"

Yanayin muryarshi ya sa ta tunanin kodai ba lafiya gidan?

"Ya jikin Benazir din? Ko har dr Ya sallame ku"

"Abun da yasa na kira ke nan, don in tuna maka, karfe 11 da rabi za'a sallame mu"

Agogo Ya kalla karfe 9, ajiyar zuciya ya sauke"In sha Allah yanzu zan shigo asibitin" amsa mashi tayi da toh, da sauri ya karasa shiryawa cikin shigar larabawa, ya ɗauki facemask ya zura a aljihun shi da niyar in sun fita zai sanya ma fuskarshi, don baison mommyn su taga tabon marin da Alhaji musa yayi mashi yasan muddin tagani sai ta tada 6alli.

Adai dai lokacin daya fito daga dakin, sai ga Hajiya sarah ta kimtsa cikin riga da skirt na atampa, ta kashe daurin kallabi mayafinta akan kafada ta daura shi, ta ruke purse dinta a hannu, kasa karasawa tayi gare shi ganin tabon dake akan fuskarshi cos tun jiya da abin ya faru kowa ya shiga dakin shi basu kara haduwa ba, taji nauyin hada ido da shi duk saitaji ba dadi.

"Aunty, barka da safiya, kin tashi lafiya" fuskarshi dauke da murmushi ya nufe ta.

Tuni taji idanunta sun ciko tab da kwalla cikin sanyin murya tace"shureim ka yi hakuri da abunda ya faru jiya, wlh bakin cikine Ya hana in leko dakin ka, banji dadin ganin yadda tabon marin ya bata gefen fuskarka..."

Cikin sauri yace"pls komai ya riga daya wuce, kada ki damu kanki, lafiya kalou, ay uncle dinma yazo har daki ya bani hakuri harma mun sasanta kanmu" kallon shi kawai takeyi gwanin ban tausayi, ta dade bata ga mutumin mai saukin kai da hakuri irin dr shureim ba.

Ganin tayi tsaye tana kallon shine yasa shi furta"nayi waya da mommy ta fadamin karfe goma za'a sallame su, yakamata muyi sauri muyi breakfast sai mu wuce..." girgiza kai tayi da sauri ta share kwallar data zubo mata, tabi bayan shureim suka nufi dining

___________________________________✍️

Around karfe 10 na safe, Unaisah tana a zaune kan kujerar gaban gadon Benazir, har ta kammala shirin ta cikin abaya maroon colour, tayi rolling veil akan ta, baiwar Allah jikinta yayi sanyi, zuciyarta batayi mata dadi, sam bata son rabuwa da Benazir ta kamu da kaunarta, duk yadda take zumudin son tafiya don taga yan uwanta, saida taji ba dadi, sabo kenan turken wawa...

Gaba ɗaya ta shiga zurfin tunanin rabuwa da ita, benazir dake zaune gefen gadon ta ƙura mata ido tana kallon ta ko kyaftawa batayi, ta fahimci kamar wani abu yana damun yarinyar, ita kan ta faduwar gaba take ji kuma ranta yana bata kamar wani abu zai faru

"Babyna me kike tunani"! Cikin kun nanta ta tsinkayi muryar Benazir, wadda tayi silar dawo da ita daga duniyar tunanin data lula..

Numfasawa tayi a hankali take kallonta, tuni taji hawaye sun cika tab da idonta, hajiya layla tana a tsaye bakin kofar toilet tana kallon su fuskarta duk ayamutse, damuwarta halin da Benazir zata shiga idan aka raba ta da yarinyar, ita kanta ta shaku da yarinyar tana son ta, sai dai ba yadda suka iya dole su yi hakuri su rungumi kaddara.

Tattausar murmushi Unaisah ta sakar mata, tare da miƙa mata kwayar maganin dake a hannun ta"mamana ki sha maganin ki," dakyar ta ƙare maganar tamkar zata fashe da kuka saboda tasan maganin bacci ne dr jazz ya bata don ta ba benazir tasha, duk don su samu tayi bacci ko sun tafi da unaisah....

Baiwar Allah Benazir kamar tasan me suke kokarin yi gabanta sai faduwa yakeyi, buɗe baki tayi unaisah ta sanya mata kwayar maganin, ta kanga mata glass din ruwan hannunta ta shanye shi, ƴan mintuna ƙalilan Benazir ta fara gyangyaɗi idanunta suka fara kokarin rurrufewa wani irin karfi maganin ke gare shi dr jazz ya iya aika aika...cikin karyayyar murya ta furta"babyna, kada ki tafi ki barni, inaji ajikina kamar tafiya zakiyi..." ɗan zaro ido unaisah tayi da sauri tace"ki daina wannan maganar mamana, ina atare dake babu inda zanje" dafe kai benazir tayi da hannu ɗaya, dakyar take buɗe idanun ta masu ɗauke da matsanancin bacci ta ƙurama unaisah ido cikin sanyin murya tace"dan Allah ki yafe min Angel, nasan ban kyauta maki ba, amma kada kice zakiyi fushi dani, kada ki tafi ki bar ni, wallahi ina sonki, Allah shine shaida ta bada son raina na tafi nabar ki ba, nayi maki alkawarin zan baki gatan da kika rasa na rashin uwa atare dake, zan tarairaye ki in baki kulawa Angel" a matuƙar ruɗe Unaisah ke kallon Benazir, kalamanta sun ta6a mata zuciya, sun fama mata ciwon dake a zuciyar ta, amma sai tayi tunanin watakil tana sambatune akan yarta da ta rasa.

Kukane Ya kwacema Hajiya layla da sauri ta toshe bakinta da tafukan hannayenta saboda batason ta ɗaga masu hankali.

Baccin ne Ya rinjayeta, jikinta ya saki a sukwane ta kwantar da kanta saman pillow, ta lumshe idanunta har lokacin bata daina yin sambatu tana ambaton sunan Angel.

A hankali unaisah take binta da kallo zuciyarta na harbawa da karfi da karfi gani take kamar in ta tafi ba zasu ƙara haduwa ba, lokaci ɗaya taji tsantsar tausayin matar ya kamata, tayi fatan ace zata cigaba da kula da ita sai dai tasan daddynta bazai barta ba, after that yan uwanta suna bukatarta ita kanta bazataso tayi nesa da su ba, ruwan hawayen da suka taru acikin idanunta ne suka fara yar tseral kan kuncin ta.
Chapter 117 · 0% Book details