← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 201 OF 238

Sashe 201

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Basu tsaya sauraronta ba, Ummi ta haye ta cafko ta tare da daukarta saman kafadarta, tana ta zabga mata masifa akan ta kyaleta hada ambaton sunan daddy.

Shigewa Ummi tayi da ita cikin toilet.

Jim kadan ummi ta fito bayan ta wanke mata gashin kanta, ta barota a cikin toilet din, kafin ta fito Batool ta dauko mata kayan da zata sanya.

Bayan ta shafe mintuna, sai gata ta fito tana ta faman daure fuska, Jikinta a sanye da bathrobe..

Kallo daya tay masu ta wuce ta nufi gaban dressing mirror ta zauna, ummi ta fara gyara mata gashin kanta cikin kankanin lokaci ya fara sheƙi.

"Zaki iya shafa lotion din ko in shafa maki" yamitsa fuska tay"zan iya" murmushi suka saki, kamar babu laka a jikin ta kwata kwata bata da kuzari, dakyar ta shafe jikinta da body lotion bayan ta kammala tace su fita zata saka kaya ummi tace"wani dare ne je mage bai gani ba Unaisah? Time da baki a hayyacin ki kin san sau nawa inayi maki wanka"?

Ras gabanta ya fadi waro idanu waje tay har zata fasa zazzaga masifa Batool tace"zolayarki takeyi"

cije le6e ta yi, dakyar ta mike ta nufi kayan da Batool ta aje mata kan bedmattress ta dauka ta nufi wurin closet dinsu can cikin dakin ta shige don kada su ganta.

Jim kadan suka jiyo takun tafiyarta a tare suka dube ta, oversized shirt ce tare da wando plazzo Green colour, ta daura veil din kayan a saman shoulder dinta.

Ummi tace"ku dai Allah yayi maku ruwan kyau, dama kika rame sai kika kara kyau, musamman Collarbone dinki ya kara kawata kyawun kirjin ki" yamutsa fuska tayi cikin sanyayyar voice dinta tace"Anya aunty Ummi ba sharri kike min ba? Kashin wuya ne abun kyau"?

Batool tace"wlh dagaske yayi maki kyau" tabe baki tayi

"Kizo ki zauna ki ci abincin ki" ta fada tana nuna mata tray din.

Jiki asanyaye ta nufi gafen gadon ta zauna, Batool tayi serving dinta, sam takasa Cin abinci, ko kamshin shi bata son Ji.

"Pls ki daure ki ci ko kin samu karfi a jikin ki" girgiza kai tay"bana jin dadin shi, Ko naci amayar da shi"

Duk yadda sukaso taci abinci takiya, Suna tsaka da rarrashinta su ka ji yo dirar motoci a cikin gidan.

Jikinta na kerma ta mike tsaye ummi na tambayarta ina zataje tace"Su daddy sun dawo zataje gurin su"

"Batool taimaka mata ku tafi, kwarama da suka dawo watakil idan shi ya yi maki magana asamu ki ci abincin"

Fitowar su daga dakin yayi daidai da shugowar su falon.

Taj ne Agaba kan wheelChair dinsa Sai faman gungurata yakeyi, Chief da sheikh Imam suna abiye da bayansa A masallaci suka hadu da shi bayan sun kammala sallah Anan harya yai mamakin ganinsu yace ashe sun dawo sau uku yana zuwa gidan neman sa saidai ace mashi baya nan ya kuma tambayi meya faru da su? Ganin rauni a kafar Taj, Chief yace in ba damuwa yazo su tafi gida sai su karasa magana acan.

Takun tafiyarsu ne Yaja hankulan su Chief ga kallon direction din da suke, kaitsaye idanunsa suka sauka a cikin nata, kayan jikin ta sunyi mashi kyau.

Karasowa sukayi Cikin girmamawa suka gaishe da sheikh Imam

Kasa amsawa yayi saboda hankalinsa daya tashi ganin goshinta a nade da bandage, ta rame ba kamar yadda yasanta ba ita.

"Subhanallah, Unaisah meke damunki"? Murmushi tay,

"Bani da lafiya, amma naji sauki"

Chief yace"mu karasa ciki" gaba daya suka nufi falon kowa ya samu guri ya zauna, Ummi tana a labe bakin kofar dakin su..

"Chief, Hankalina ba akwance yake ba, Inaso nasan meya faru daku? Farmakin da kuka je kaiwa anyi nasara ko kuwa? Naga Taj da rauni a kafa, ga Unaisah ma ba lafiya, kaima haka naga ciwo a goshinka, Sannan Ina sauran yaran suke ne"?

aruɗe ya tambaya yana dubansu.

Gyaran murya Chief yai kafin ya soma magana calmly.

"Ba zamuce bamuyi nasara ba, Alhamdulillah munci rabin yakin munga tasirin addu'a, abubuwa da dama sun faru masu dadi da marasa dadi..."dan dakatawa yai yana kallon Unaisah dake a zaune gefen daddynta ta daura kanta saman kafadarsa lumshe idanun ta tayi don batason jin karashen zancen na shi.

"We lost Danish, Salsabeel ya samu karaya a hannunsa, Umar has a brain injury, gaba daya an kwantar da su a asibiti, su Commender ma Sunyi rashin daya daga cikin sojijin su, sauran yaran suna a part din Taj..."

Muryarsa na rawa ya furta"danish Ya mutu ne"?

"Bamu da tabbacin ya mutu ko yana raye, saboda bamu ga gawarsa ba" tashin hankalin da damuwane tsantsa akan fuskar Sheikh Imam, Ya girgiza da jin basu dawo Danish ba, wlh yaji zafi acikin zuciyar shi..

Girgiza kai yai idanunsa cike tab da ƙwalla.

Ya dan jima batare daya furta kalma ba, Can ya numfasa cikin karyayyar murya yai masu nasiha akan suyi hakuri da rashin da sukayi Su mika lamuransu gurin kada su sare, Danish kuma zasu tayashi da addu'a in ya mutu Allah yajikan shi In kuma yana araye Allah ya bayyanar da shi.

Sannan Ya bukaci yana son yaje ya duba su Salsabeel chief yace idan suka tashi zuwa zai kirashi sai suje atare su duba jikin su saboda asibitin ba a kusa yake ba.

Shiru sukayi falon yai tsit kowa da abunda yake sakawa acikin zuciyar shi.

"Ina auntynku? Ko itama tana a dayan bangaren ne"? Kaitsaye maganar shi ta dira a kunnan Ummi tayi mamakin Jin sheikh Imam ya tambayeta.

"Tana anan tare da mu" Batool ce ta bashi amsa..

Batay niyar fitowa ba amma saboda maganar sheikh Imam yasa ta fito jikinta sanye da dogon hijabin data dauko a cikin closet din su Unaisah.

Har kasa ta zukunna ta gaishe da shi fuskarsa da fara'a ya amsa mata, ta danyi mamaki mutumin da ko kallonta baisonyi amma yau haryake tambayar tana ina.

"Hateem Yasan da maganar"! Girgiza kai chief yai"ban sanar da shi ba ko da zaiji ba yanzu ba,"

Sheikh yace"Allahu akhbar, Allah baya barin wani don wani yaji dadi, Hateem yaso yaron nan kamar dan cikinsa, nasan in yaji hankalinsa ba karamin tashi zaiyi ba"

ya fada fuskarsa da damuwa jikinshi duk yai sanyi, Zuciyarsa ta karaya, saboda shi kan shi yaso yaron kuma bakomai yafi daga masa hankali ba face kin kar6ar shahadar da baiyi ba.

"Sheikh ga Unaisah nan, Har yau bata daina sanya damuwa aranta ba, dakyar muke samu tayi bacci, dan Allah ay mata nasiha.." Taj ne yai maganar.

Ya tambayi meye silar ciwonta, Taj ya fada masa komai.

Tsananin tausayin su ne Ya kama shi, Cikin sanyin murya ya farayi masu Nasiha har na tsawon mintuna talatin kafin Ya gama gaba daya jikinsu yayi sanyi lakwas, Imani ya kara shigarsu sosai.

Har wurare karfe 9 Shiekh Imam yana agidan daga bisani yai masu sallama Chief Ya rakasa Har cikin motarsa sai da yaga tafiyarsa kafin ya juyo.

Time daya shigo falon ya tsinkayi muryar Ummi tana fada ma Taj Unaisah taki cin abinci.

Da damuwa akan fuskarsa yace"Why Unaisah? Baki so ki samu lafiya ne? Ai ta fama dake akan kici abinci"

Muryarta kasa kasa ta furta"Zuciyata ke tashi,duka abincin da naci da safe dana rana saida na amayar da su a toilet, ban fadi maku bane saboda bana son in tada maku hankali, abincin ma bana jin dadin shi ..."

Kafin wani ya furta kalma muryar Chief ta katse su.

"Gobe idan dr yazo duba ki ki fada masa aman da kike yi, amma bazan bari ki kwana da yunwa ba, Fada min me kike son Ci"

ya fada tare da dafe Sofa da hannayensa Yayin da idanunsa ke akan fuskarta.

Saboda nauyin shi da take jine yasa ta ce"zan daure naci wanda aka kawo min"

"Ina abincin nata yake" Batool tace"yana a daki"

"Je ki ɗauko min" mikewa ta yi da sauri ta nufi dakinsu.

Jim kaɗan sai gata ta dawo hannayen ta ruke da tray ta ajiye shi kan rug.

Zagayowa yayi tare da samun wuri Ya zauna a gaban tray din, mamakin chief ya rukesu Musamman daya Kira Unaisa Ya nuna mata gaban tray din Yace tazo taci abinci"

Ta dan zaro idanu tare da kallon Taj fuskarsa ɗauke da murmushi yai mata alamar taje mikewa tay jiki ba kwari ta zauna tana fuskantarsa, yayin da tray din ya raba tsakanin su.

Coconut water ya dauka da sauri ta mika yatsun hannunta dake kerma da niyar ta kar6i Glass din
Batai aune ba taji ya kanga mata strawa din a baki, wata irin kunyace ta kamata, adan rude ta saci kallon su ummi da Taj fuskokinsu dauke da murmushi..

Ganin ta ki motsa lips dinta yasa shi furta"ki sha" yawu ta hadiya ƙutt kafin a hankali ta fara zukar shi, abunda tagaza sha dazu sai gashi ta kwankwade shi duka batare da ta ankara ba har saida ya janye straw din daga bakinta.

Spoon ya dauka Murya na rawa ta furta"zan iya ci da kaina" ta fada tana kyafkyafta gray eyes din ta
Hakan ba karamin Jan hankalin shi yai ba.

"Ki bari ya baki mana Unaisah, Baki ga yadda hannunki ke kerma ba taya zaki iya ruke spoon" Ummi ce ta yi maganar aranta ta ayyana Samun wuri.

Batool sai faman hadiyar yawu take yi, ba yunwa take ji ba, Amma yadda taga Chief na ciyar da Unaisah yasa taji dama ya bata itama.

Taj kuwa Ransa fari fat da farin ciki kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha, Burinsa yana daf da cika, abun da ya daɗe yana jira abunda yafi burgesa yadda Chief ya nuna kulawa agare ta agaban shi inaga idan sukai aure? Allah kadai yasan gatancin da zata samu a gurin sa, Shi yasan Unaisah ta gama morewa.

Tun tana jin kunyar ya bata abaki har ta dan saji jiki ganin daddynta bai nuna wani abu ba..
duk in ya bata one spoon sai sun haɗa ido da juna launin idanunsa da take kallo bakomai yake tariyo mata ba face kyawawan idanuwan Danish kasancewar launin idanunsu daya hatta shape dinsu kamar an zana saboda kyau.

"My Angel" muryarsa ce tay mata gizau a cikin kunnanta...
Chapter 201 · 0% Book details