← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 133 OF 238

Sashe 133

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Meke damun shi ne"? Kafin ta bashi amsa junaid ya fara mutsu mutsu kamar zai farka hakan yasa tay shiru tana kokarin lalla6a shi don ya koma baccin.

Cikin kulawa dr shureim yace"Allah ya bashi lafiya" ta amsa mashi da ameen.

Tags
Kurkukun Kaddara
YOU MAY LIKE THESE POSTS
[14/10, 6:06 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: Novels Elite

Home
Kurkukun Kaddara
Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 43 Complete by Boss Bature
by
Novels Elite Admin
September 05, 2024
Sponsored Link

Takun Ƙarshe
DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE

Bayan ta samu ta lalla6a junaid ya koma bacci, tun da motarsu ta haura kan titi suke ta satar kallon juna tsakaninta da Benazir ta cikin mirror din motar kamar wasu munafukai, kwata kwata hankalin dr shureim baya akansu ya tattara nutsuwarsa akan driving din da yakeyi, hakanan ranshi ya raya mashi ya dubi fuskar Benazir, ta wutsiyar idanun shi ya ke kallon ta adaidai lokaci sun kura ma juna ido ita da Anila da alamun rashin gaskiya atattare da su, duk dagowar da zaiyi sai ya kama su suna kallon juna ta mirror, gyaran murya yayi masu da sauri suka dube shi.

"Ban yarda daku ba! Ku faɗamin gaskiya meke faruwa ne? Meyasa kuke satar kallon juna ta mirror? Ina fa lura da duk wani motsinku acikin motar nan, kamar baku da gaskiya, ku ji tsoron Allah ku sanar dani abun da kuke boye min"!

Shiru su ka yi suna ta ƴan kame kame an rasa me bude baki ya bashi amsa duk sun sha jinin jikin su.

"Da ku nake magana? Me zamuje yi a obie estate? In har baku fadamin ba zan dakata da yin driving din..." fuskar shi adaure yayi maganar batare daya kalle su ba, kallon juna suka sake yi ta mirror, kafin su yanke shawara da junan su dr shureim ya yi parking din motar a gefen titi Ya kashe ta tare da jingina kanshi jikin headrest.

"In har ba zaku fadamin abunda kuke boye min ba, to kuwa zamu kwana anan ne.."

yawu Anila ta hadiya tare da kallon benazir da hankalinta ya gama tashi,

Cike da fargaba benazir tace"yaya shureim..dama ummm gidan su Azeezaty zamu je..." Dakyar ta ƙare maganar ganin ya juyo dakai ya kalle ta tuni ya hade rai, annurin fuskarshi ya gushe rai a6ace yace"meyasa baki jin magana ta? Har nasiha nayi maki nace ki yi hakuri tun da yar nan ba taki bace ki hakura mana, ni dama tun da naga take takenku raina ya bani gidan su yarinyar nan zaku je, to wlh bada ni ba, da nasan gidan su azeezaty zamuje da ban biye maku ba." kallon juna sukayi hankalin su atashe damuwa ce ƙarara akan fuskokin su.

Juyawa yai tare da kallon Anila cikin sanyin murya yace"haba anila! Meyasa zaki biye mata? Ni nasan bada son ranki ba, itace ta matsa maki, Benazir bata da hakuri ta fiye kafiya da naci, ba irin lallashin da ban yi mata ba akan ta hakura da yarinyar nan amma taƙi jin maganata"

kifa kai Benazir tayi jikin seat din da take azaune ta fashe da kuka tana fadin"yaya shureim na hakura da ita, nasan ba yata bace na yarda da hakan, Anila tayi min bayanin komai dangane da ita kuma na fahimce ta...." ta ƙare maganar tana shesshekar kuka, kafin yayi magana Aneelerh ta riga shi cewa"ka yi hakuri yaya shureim ban nemi shawararku ba nayi gamon kaina, saboda ina tausayin halin da Benazir take a ciki" ta fada tana kallon fuskar shi"shekaran jiya ta kirani awaya take faɗa min ita fa tun a asibiti ta fahimci yarinyar nan ba yarta bace kun ce mata taj ya dauketa sunje mall shiru basu dawo ba kun hana tasan gaskiya kun boye mata saboda baku san 6acin ranta, ni kuma abunda nayi tunani duk daran dadewa dole Benazir tasan gaskiya tun da gashi harta kirani awaya ta fadamin tagane ba yarta bace shiyasa kawai na faɗa mata gaskiyar zance, sannan na kwantar mata da hankali nayi mata nasiha nace tayi hakuri da boyen matan da akai munyi hakanne saboda gudun kada mu rasa ta"!

tun da ta fara magana dr shureim yayi shiru yana sauraronta, jikinshi yayi mugun yin sanyi zuciyar shi ta karaya.

Benazir ta ɗaura da cewa"Yaya shureim bayan Anila ta fadamin gaskiya, nayi kokarin cire azeezaty araina saboda a lokacin na hakura da ita, nasan inda rabo wata rana nima Allah zai bayyanar min da ƴata Angel, amma wallahi nakasa ya shureim Inason Azeezaty, Allah Ya jarabce ni da kaunarta, kai shaida ne akan irin Son da nake mata, ko bayan dana gane ba ƴata bace, ina sane nake yi maku pretending saboda kada ku rabani da ita, shiyasa ko bayan da muka dawo gida na ɗaga hankalina sosai saboda na fahimci kun rabani da Azeezaty" ta ɗan dakata da yin maganar tana kallon dr shureim dake kallon ta,

Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.

numfasawa tayi kafin taci gaba da cewa"jiya batare da sanin kowa ba, na kira Aneelarh awaya na fada mata halin da nake a ciki na rashin azeezaty, na roƙe ta akan ta taimaka min ko sau daya ne in ganta, saboda na kasa cire ta araina, shine tace min in jira zata yi magana da iyayen yarinyar idan sun amince muje gidan zata sanar dani, sai yau da safe ta kira ni ta fadamin tayi waya da daddyn azeezaty yace muzo gidan mu ganta, har ce mata yai ita ma yarinyar tana son ganina tun bayan data koma gida kullum sai ta yi maganata kaga itama kenan tana jin abun da nake ji agame da ita, ko da bamuje gidan ba, zata sa daddynta ya kawota gurina ne saboda itama ta damu dani"

Muryarta adisashe tayi maganar tana kallon dr shureim, ajiyar zuciya ya sauke har cikin ranshi yaji dadi da Benazir ta hakura abunda ya kara kwantar mashi da hankali jin cewa da sanin iyayen yarinyar zasuje gidan dama shi abun da yake jima fargaba kada su kwasa su je gidan ba tare da sanin iyayen yarinyar ba, benazir ta sanya masu rigima akan su bata ƴarta, tun da ba hankali gareta ba, yanzu kuma yaji daga bakinta tasan me takeyi ashe dagangan takeyi masu pretending don kada su raba ta da yarinyar, baiyi mamakin jin hakan ba, cos ya riga da ya san halin Benazir tun tana ƙaramarta idan ta kwallafa rai akan abu har aljanun karya take yi masu don ta ɗaga masu hankali kan abun.

yayi zurfi acikin tunanin shi, Benazir ta katse shi cikin rauni na murya tace"ya shureim dan Allah ka taimaka ka kai mu gidan, nasan me kake tunani, in sha Allah bazan bamu matsala ba, nayi maka alkawarin hakan, Ni kawai burina inga Azeezaty, kona samu kwanciyar hankali"

nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, tare da lumshe idanun shi yayi shiru jimmm yana nazari kafin ya buɗe su akan fuskar Anila"ba ki yi laifi ba Anila, kinyi abunda ya dace ne, bansan da wasu kalmomi zanyi amfani gurin yi maki godiya ba saboda naji dadin yadda kika damu da Benazir, wlh kin faranta min rai, saboda kwanakin nan dakyar nake bacci saboda damuwar halin da Benazir take a ciki, amma yanzu kin sama mana maslaha atsakanin mu da ita, ubangiji Allah yasaka maki da mafificin alkhairinsa."

Ajiyar zuciya Aneelarh ta sauke, fuskarta dauke da murmushi tace"ameen ya shureim, ay ba godiya atsakaninmu, mun riga mun zama ɗaya, zan iya yin komai saboda farin cikin ku" har cikin ransu sunji dadin maganar Aneelerh.

Kallon Benazir yayi suka haɗa ido da juna, fuskarta tayi jawur saboda kukan da tayi"kiyi hakuri kinji, ki share hawayenki, yanzu na fahimce ku, kuma naji dadin yadda kika ɗauki dangana, in sha Allah kema zaki gana da yarki wata rana, zamu ci gaba da yi masu addu'a ubangiji Allah ya bayyanar mana da su" suka masa mashi da ameen

Daga bisani ya tada motar ya cigaba da yin driving dinsu, Hankalinsu Ya kwanta sosai, Yanzu basu da sauran damuwa, har yanzu junaid bai farka daga bacci ba, maganganun da sukayi baisa ya farka ba, wani irin bacci yake yi mai nauyin gaske.

_________________________________✍️

*UNAISAH ANGEL💓*

Tana a zaune tsakiyar Bedmattress dinsu, kayan baccin jiya ne a jikinta riga da wando da alama ko wanka batayi ba, gaba daya hankalinta na akan notebooks din da ta jera kan katifar, ta sanya farin glass a idanunta kamar wata malaman makaranta, ta ruƙe red pen a hannunta, ta nutsu tana dudduba notebooks din data kar6a a hannun su Parveen, Assignment ɗin da ta basu jiya shine yau take dubawa, ta rasa gane me suka rubuta, duk jagwalgwalo ne, wani rubutun kamar na ƴan china wani shigen na thailand, tun da tafara checking note books din fuskarta ɗauke da murmushi wani lokacin saita kwashe da dariya hada kifawa kan katifa ba karamin nishadi suka sanyata ba, ta fahimci kwata kwata basu gane abunda take koya masu, kwakwalwarsu bata daukar karatu, bayin Allah sai taji ta karajin tausayinsu da kaunar su.

Motsin buɗe toilet door ne Yasa ta ɗago dakai ta dubi kofar, Batool ce ta fito daga ciki, ta sanya bathrobe kafafuwanta sanye da slippers, ta nannaɗe sumar kanta da farin towel, dakatawa tayi da yin tafiya ganin irin kallon da Unaisah ke yi mata duk saita sha jinin jikinta, da sauri ta bi kanta da kallo don ta ga ko tayi wani abu badai dabai ba, ganin lafiyalou babu wani aibu yasa tace"Sister, meyasa kike kallona? Akwai wani abu ne"? Murmushi ta ɗanyi tare da girgiza mata kai"bakomai wlh, You look so gorgeous, like a pearl" kayataccen murmushi Batool ta saki har dimples dinta suka lotsa, taji dadin yabon da unaisah tayi mata.

"tun dazu nake jira ki fito nima in shiga inyi wankan," ta faɗa tare da saukowa daga kan gadon ta fara tattara notebooks din ta ɗaurasu kan bedside drawer.

"ki zauna ki jira ni, idan na fito zan za6a mana kayan da zamu sanya, har make up zamuyi" dadine ya lullubeta"amma pls kada ki daɗe"

"Toh" da sauri ta nufi mirror chair ta zauna tana jiran fitowar ta.
Chapter 133 · 0% Book details