← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 238

Sashe 45

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na cancanci kowani irin hukunci daga gareki, a shirye nake dana kar6e shi, ni dai bana son 6acin ranki"

ya faɗa tare da ɗaura kansa saman kafadarta saboda karfin hali irin nashi

Lumshe idanunsa yai tare da shakar kamshin turarenta.

"Kinyi shiru baki ce min komai ba" sai da ta mula tasha iska tukunna Tace"laifin me kayi min"?

"Kin riga da kin sani"

"In dai dangane da abunda ya faru jiya ne to ka manta kawai, bana son tada maganar, ko alokacin abunda yasa raina ya 6aci saboda ina kishin ka ne banji dadi ba, amma yanzu komai ya wuce"

Tsabar mamakin kalamanta yasa shi saurin ɗagowa yana duban fuskarta ta cikin mirror.

"Amma dai wasa kike min ko"? Murmushi ta sakar mashi tare da cewa"na taba maka wasa irin wannan"?

Girgiza kanshi yai"a'a, baki taba min ba, amma dai nayi mamaki, Allah yasa ba mafarki nake ba" juyowa tayi suka fuskanci juna, fuskar ta dauke da ƙayataccen murmushi ta ɗaura hannayen ta a kan kafadunsa.

Lamarin ya ɗaure masa kai gaba daya ta canza mashi kamar ba hajiya saratun daya sani ba.

Cikin sanyin murya tace"hubby, kada ka ƙara maimaita kuskuran da kayi, bana so, kasan inada kishi, akan ka zan iya komai daga ciki har da kisa"

Zaro idanunsa yayi"in sha Allah hakan bazata faru ba, zanyi kokarin ganin na kiyaye duk wani abu da zai bata maki rai"

Ba zato ba tsammani yaji tayi huggin ɗinsa tare da zagayo da hannayenta kan waist dinsa, tuni yafara jin shi awani yanayi.

Sumbatar wuyansa tayi kafin ta dago da bakinta saitin kunnanshi cikin muryar raɗa mai hade da kwarkwasa tace"fadamin me ka ke so nayi maka wanda zai faranta ranka"

"Nagaza yarda da abinda kike fada min, anya kuwa kece? Ko dai aljanune suka shige ki? Nifa ina kokwanto bana so saina shagala ki canza min ainihin kala dinki"

dariya tayi cike da nishadi tace"ka daina kokwanto akaina, ni ce dai hajiya saratun daka sani, matarka uwar ya'yanka"

Murmushi pravin yai cike da jin shaukinta

"Ka yi breakfast ko insa a kawo mana mu yi a daki nima banci komai ba"

"In ban da abunki ay kinsan bana iya cin abinci idan ba atare dake ba, don ma ke dince wani lokaci baki jira na"

"I'm sorry Yanzu bari na kira akawo mana a daki, me kake son ci"?

Yana faman washe baki yace "Duk abin da zaki ci, zabinki ay shine nawa"

Shu'umin murmushin gefen fuska hajiya saratu tasaki tare dakai hannu ta dauki waya ta kira layin kitchen ta isar da sakon akawo masu abinci, bayan abla ta kawo masu atare suka zauna suna ci, kamar sabbin ma'aurata abaki ta fara bashi har sai da suka cinye kafin ta soma jan hankalin shi.

Gaba ɗaya nema take ta zautar dashi da salonta, kasa jurewa yayi da sauri ya ƙara tighting nata a jikinsa.

_________________________________❤✍️

Bayan shigar chief bedroom dinsa a zafafe Ya faɗa Bathroom dinsa don ya watsa ruwa ko ya samu zuciyarsa ta lafa daga radadin da ta ke yi masa.

ganin ya shiga toilet yasa big guy sauke ajiyar zuciya, yayi tunanin zaiyi yadda ya saba ne idan ransa ya 6aci da wuya in bai yi ma kan shi illa ba, wani lokacin mirror yake kaima naushi ya tarwatsa shi har sai hannun shi ya faffashe saboda tsabar zuciyar dake gare shi.

Kafin fitowarshi da sauri big guy ya fita na tsawon mintuna ya dawo hannun shi ruƙe da wooden tray mai dauke da breakfast din chief.

Yayi mamakin ganin shi kwance kan gado, jikin shi sanye da bathrobe ya ɗaura hannunsa ɗaya kan lallausar sumar kanshi, ya lumshe wadannan kyawawan idanuwan nashi, bakomai yake tunawa ba acikin zuciyarsa face tarihin rayuwar prisoners, labarin yai matuƙar ta6a zuciyar shi.

"Allah Ya huci zuciyarka Yalla6ai, ga breakfast dinka, nasan kana jin yunwa" cikin girmamawa yayi maganar

Tamkar bazai tanka mashi ba, sai da ya dauki lokaci kafin Ya furta"ka koma da abincin bana jin zan iya ci"

Cikin sanyin murya big guy yace"ka yi hakuri Sir, kasan ni mai biyayya ne agare ka, bana yi maka jayayya amma yau bazan iya bin umarnin ka ba, saboda na damu dakai, abun da ke damunka nima shike damuna..." ya fada yana cigaba da kallonsa.

"Sir, ƙin cin abinci bashi bane mafita, kana buƙatar kwanciyar hankali da nutsuwa, wanda hakan bazai samu ba sai ka jajirce wurin ganin ka kauda damuwarka, sannan yanzu ne ya kamata mu dage damtse mu yi aiki tuƙuru don ganin mun gano su wanene azzaluman mutanan da suke aikata 6arna a kasarmu"

Daɗaɗan kalamai Big guy ya cigaba da zayyano masa yana kara karfafa masa gwiwa da kwantar masa da hankali, A hankali Ya fara jin saukin radadin da zuciyarsa ke yi mashi.

"Sir, har yanzu kana akan bakanka na bazaka ci abincin ba"? Ya faɗa yana duban cute face din Ogan nasa

Slowly ya ɗan motsa tausasan pink lips dinsa in a low voice ya furta"zan kokarta" gyaɗa kai yai

"Zan tafi yalla6ai, Ka huta lafiya" ya fada tare da sara mashi kafin Ya juya har ya kusa ficewa daga dakin muryar chief ta ratsa kunnansa"nagoda da kulawarka agare ni"

Murmushi big guy yai"kada ka damu yalla6ai"

Har zai fuce ya kuma dakatar da shi"please ka duba dakin Yaron nan, kaga Awani hali Yake a ciki, Idan ya farka a tabbatar Yayi breakfast dinsa, idan ya gama ka tambaye shi me yake bukata in ya fada maka ay gaggawar yi mashi, zuwa anjima sheikh Imam zai zo duba shi"

"Okey, Sir"

Ya fada tare da bude door room din Ya fito waje, dakatawa yayi da tafiya yana tunanin tawace hanya zai faranta ran chief? Don ya fahimci har yanzu akwai sauran damuwa aranshi, tunawa da Unaisah yasa shi saurin zaro wayarsa ya danna ma boss kira, tana fara ringing yai picking Call din

Da zolaya yace"masu Ƴa, halan Har yanzu kana nan maƙale da ita"

Sautin muryar boss da alamun dariya yace"To ɗan sa ido, ka fara tsokanar taka ko"?

Dariya Big guy yayi" inatayaka murna abokina"

"Nagode sosai mutumina, Ina chief ne ina fata yana lafiya"

"Ba lafiya, Har yanzu akwai damuwa aranshi, Kuma kasan halinshi mutunne mai zuciya, yanzu haka ina a kofar dakinsa, na kai masa abinci yace min bazai iya ci ba"

Muryar bos da jimami yace"amma banji dadi ba, pls ka yi kokarin kwantar masa da hankali kafin inzo"

da sauri big guy yace"anya zan iya? Ko dai zaka turo unaisah ko da godiyane tayi mashi, watakil hakan Ya kwantar masa da hankalinsa"

"Nima nayi tunanin hakan, yanzu zan turo ta in sha Allah" murmushi big guy yai kafin yai mashi sallama a hanzarce Ya nufi bedroom diny Danish.

*❤GARKUWA💪*

A kishingiɗe Yake kan gadon shi, Ya hakimce kamar wani basarake, wasu hadaddun sleeping dress ne a jikin sa launin red colour sunyi bala'en yi mashi kyau, hannunsa ɗaya rungume da pillow, lallausar sumar kanshi ta lullu6e gefen fuskarshi, yayin da kyawawan fararen idanunsa ke akan hadadden ceilling din dakin, tun da Ya farka daga bacci bai ta6uka komai ba, gaba ɗaya ya shagala da tunanin Hateem, wani irin kewarsa yake ji, mutumin ya kwanta masa aransa saboda yadda ya tarairayesa ya bashi kulawa kamar wani nashi, bai ta6a tsammanin zaiji tsantsar kaunarsa ba, sai gashi zuciyarsa takasa samun sukuni saboda tunaninsa, da zarar ya lumshe idanunsa fuskar Hateem yake gani dauke da murmushi......"

Yana son ya sake sanya shi a idanunsa, kwata kwata bai fahimci cewa prime minister kasar ya bari ba.

Har Yanzu kamshin turaren daddy hateem bai bar jikin shi ba, saboda rungumarsa da yadinga yi jiya kamar zai maida shi jikin shi, fragrance din Yana da karfi sosai shiyasa ya kama jikin sa.

Kalaman hateem ne suka fara dawo mashi

_zan tafi da kewarka, dan Allah kada ka manta dani, inaso ka ɗauke ni tamkar mahaifinka, aduk lokacin da wani abu ke damunka ka sanar da chief zai fada min, zamu dinga yin waya akai akai, daga yanzu inaso ka dinga kirana da sunan daddynka_

A hankali ya dago da yatsan hannunsa yana kallon zoben da ya sanya mashi ayatsa mai kyan gaske, wannan ne karo na farko daya fara sanya zobe,

Daura yatsan yai kan kananun la66ansa Ya sumbace shi a hankali yanayin fuskarshi kamar zaiyi murmushi.

Knocking din kofar dakin da akaine Ya sa shi daura idonsa kan kofar, bakomai Ya fado masa arani ba face Angel dinsa, yasan ita kaɗaice zata Iya zuwa duba shi awanan lokacin, Idan ba ita ba sai kuma yan uwansa, saukowa yai daga kan gadon bayan ya jefar da pillow hannunsa, da sauri Ya nufi kofar don Ya tarbe ta, saboda yayi kewarta jiya, idanunsa sunyi maraicin ganin ta,, shi kanshi baiyi tsammanin zai Iya mintuna batare da ita a gafen sa ba, sai gashi jiya daddy hateem Ya sace zuciyarsa.

Ko da ƙofar ta bude yai arba da big guy tuni yanayin fuskarshi Ya canza, shi da ya taso da zumudinsa don Ya nuna ma Angel dinsa kyautar zoben da mutumin nan ya bashi, sannan Ya bata labarin abunda Ya faru atsakanin su ashe ba ita bace.

"Barka da safiya danish" big guy ya fada da fara'a akan fuskarsa, ko kallo danish bai mashi ba, Hankalin shi na akan bayan shi, burin shi Yaga Angel don har yanzu bai fidda rai da ganin ta ba

Da mamaki big guy ya waiga baya don yaga me yake kallo sai dai baiga komai ba.

"Ina fata ka tashi lafiya" ya fada aranshi yana mai mamakin Girman Jikin Yaron ga tsawo tubarkalla uwa uba ga kyau kamar shi ya zana kan shi.

"Magana na ke yi maka ka yi shiru ba ka ce komai ba, ko har yanzu ba ka jin daɗin jikin naka ne"?

cikin sanyin murya ya furta"My Angel? Tana Ina"?

Dafa kafadarsa big guy yai"kwantar da hankalinka tana nan cikin koshin lafiya, nasan zata zo dubaka..." kafin Ya kare maganar danish Yace"Ina son ganinta, " ya fada yana kokarin bi ta gefen shi Ya wuce, A hanzarce big guy yai saurin Shan gabanshi, gudun Kada Ya ruguza masa plan dinsa na zuwan angel part din chief.
Chapter 45 · 0% Book details