← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 238

Sashe 10

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Uncle ɗan Iya ya ɗaura da cewa"banji daɗin abun da Ummi ta fada min ba, baki kyauta mana ba, ashe baki ɗauke mu yarda muka ɗauke ki ba, meyasa zaki zauna abu na damunki ki gaza gaya ma kowa? Meye amfanin 6oye mana eye"? Muryarshi da faɗa yake yi mata magana, alamar ranshi ya 6aci.

Sunnar dakai ƙasa Ana tayi yayin da idanunta ke akan Yatsun hannayenta

"Meke damun ki ne, inaso ki faɗi mini gaskiya"? Ya jefa mata tambayar, Su Aneelerh da su mami sun natsu suna kallon ta.

Numfashi taja tare da sauke shi A hankali ta furta"Idan na 6ata maku rai, dan Allah ku yafe ni, Aunty Aneelerh, mami, ummi, Zahra, Mahboob, abie, uncle, Allah ne kaɗai zai Iya biyanku, duk da kasancewata yar aiki agidan nan, Sannan ba musulma ba amma kun daukeni tamkar jinin ku, ko dan saboda nuna damuwar da ku ka yi akaina zan fada maku gaskiyar abun da ke damuna...." ta faɗa tana mai ƙanƙan da kanta, gaba ɗaya duk sun ƙagara da suji meke damunta, musamman Mahboob Ya kasa ɗauke idanunsa daga kan fuskarta, wani irin tsantsar sonta da ƙaunarta yake ji, ga matsanancin tausayinta dake addabar zuciyarsa.

"Cikin kwanakin nan, Ina yawan yin mugayen mafarkai, waɗanda suke neman haukata ni, bansan meyasa hakan yake faruwa dani ba, idanuwana suna gane min abunda yafi ƙarfin gani na wanda silar hakan yasa nafara zaucewa, ni gani nake ma kamar mutuwa zanyi..... " muryarta na rawa ta ƙare maganar nan take ta fashe da kuka mai sautin gaske, Hankalin su ba ƙaramin tashi yayi ba, Jikin kowannansu yayi sanyi

"Kiyi shiru, Kukan Ya isa haka, Ki faɗa mana me kike gani a cikin mafarkin naki"! Uncle ɗan Iya ne yai maganar

Cikin shessheƙar kuka tace"wallahi duk yadda zanyi maku bayani ba lallai ku fahimce ni ba, ni kaɗai nasan halin da nake aciki, ni kaɗai nasan bala'en da nake gani, Ba tun yanzu ba, tun ina ƙaramata idan nayi mafarki mummuna yana zama dagaske, hatta rasuwar iyayenmu saida nafara yin mafarkin zasu yi hatsarin mota, sai gashi ya tabbata, uncle ɗina ma ni nayi mafarkin mutuwarsa kuma ya tabbata, da wuya inyi mafarki mummuna bai zamto gaske ba, ni damuwata mutanan da nake a tare da su bana son wani abu ya sami wani daga cikin ku...." tashin hankalin da ba'a saka mashi date, A matuƙar ruɗe Zahra take kallon Aneeleerh, Ummi ta kalli Mamie, Idanuwansu azare, mahboob kuwa kusan suman zaune yayi.

Shiru tayi Tana faman yin shessheƙar kuka,

Abie dake kallonta, nazarin maganarta yakeyi, yaso ace musulmace ita, kodan ya bata shawarar ta runƙa yawaita yin azhkar, da sauran addu'o'in neman tsari.

Tsawon lokaci falon yayi tsit, babu mai magana acikinsu, sai kallon kallo da suke jefawa junansu.

Muryar Uncle ɗan Iya ce ta katse Shirun nasu

"Ki daina sanya damuwa aranki, Mafarki ba gaskiya bane, shaidan ne yake assasashi, Ki yawaita yin addu'a, muma kuma zamu tayaki, Allah shi yake tsare bawansa, in sha Allah babu abun da zai same ki, damu kanmu,"

Ajiyar zuciya ta sauke, Cikin sanyin murya tace"in sha Allah uncle, zanyi hakan"

"Aneelerh, Idan zata kwanta bacci ki rakata dakinta, Ki yi mata addu'a," Ya fada yana duban Aneeleerh, Cikin girmamawa Ta amsa mashi da toh,

Kwantar mata da hankali suka cigaba dayi, Kowa sai da ya sanya bakin shi wurin Lallashinta da bata baki, Har saida suka tabbatar Ta samu saukin damuwarta tukunna mamie tace"daga yau kada ki sake ware kanki a daki! Kina jina ko"? Daga mata kai tayi toh

"Kidaina kuntata kanki adaki, ki dinga fitowa waje wurin su Aneelerh Kuna yin fira, hakan zai ɗebe maki kewa don na fahimci hada kaɗaici ke damun ki" jinjina kai ana tayi alamar toh.

Gyaran murya abie yai tare da cewa"Idan kina buƙatar wani abu, Ki fadama Aneelerh ko zahra, su sanar dani in sha Allah zamuyi maki shi, kada kiji komai ki dauka tamkar Iyayenki ne" wannan maganar da abie Ya furta mata ba karamin ta6a zuciyarta yayi ba, nan take ta fashe masu da kuka mai tsuma zuciya, sautin muryarta dakyar yake fita wurin yi masu godiya.

"Ku tashi ku rakata daki ta kwanta ta huta" Ummi ce tayi maganar tana nuna su zahra, ruƙo hannun Ana Aneeleerh tayi atare suka miƙe, Zahra tabi bayansu, Har cikin dakinta suka kaita, Bayan ta kwanta Aneelerh da zahra sukayi mata addu'o'i, Kafin daga bisani suka yi mata sallama, Kamar karsu barota haka suke ji, bayan sun fito daga dakin sun kulle mata kofar, zahra ta kalli Aneelerh

"Nifa tsoro yakamani aunty na, tun da naji Ana tace mafarkinta yana zama gaskiya, wallahi bana so wani abu ya samu ɗaya daga cikin mu"

Ita kanta Aneelerh hankalinta ba akwance yake ba, zuciyarta taki Aminta da kalaman ana, sai dai tayi kokarin danne damuwarta wurin kwantar ma zara da hankalin ta

"Zahra kin riga kin sani, mafarki ba gaskiya bane, Ni ko kadan hankalina bai tashi ba, kema kuma inaso ki kwantar da hankalinki, In sha Allah babu abun zai faru, face alkhairi"

Cikin sanyin murya zahra tace"Allah Yasa" Ta fada a yayin da suke shiga falon, komawa sukayi saman carpet suka zauna kowa zuciyarsa da fargaban maganar Ana.

Idan muka koma 6angaren su Ummin america tun bayan kammala sallar magbrib, tayi wanka ta shirya cikin Baƙar jallabiya, tayi rolling veil akanta, ta bi ko'ina na jikinta ta feshe da turare, bakomai take jira ba face kiran Boss man, tun da ya fada mata yana son magana da ita gaba daya ta rasa sukuni ta kosa taji me ya ke son faɗa mata, tana cikin yin safa da marwa a room dinta, wayarta tayi ringing a hazarce tayi picking call din, muryar boss ce ta isar mata da sakon ta same shi a down, jiki na rawa ta fito daga dakin ta sauko down stairs babu kowa a falon, duk suna a dakunansu

A falo ta same shi tsaye cikin shiga ta jallabiya, ya goya hannayensa akan kirjinsa, fuskarsa a sanye da face mask.

Da fara'a ta nufe shi batare da 6ata lokaci ba, suka jera a tare suka nufi swimming area din gidan, ko'ina ka kalla hasken fitilun lantarki ne tamkar da rana.

"ina sauraron ka Yalla6ai, tun da muka fito kayi shiru baka ce komai ba" ummi ce ta fada tana kallon Taj dake a gefenta.

"ga dukkan alamu Kin ƙagara da kiji dalilin kiran da nayi maki"

Jinjina mashi kai tayi alamar Eh, A yayin da suke zama saman kujerun dake a bakin pool din masu kyan gaske, suna fuskantar Junansu.

"Nasan zakiyi mamaki idan nace maki chief ne Ya bada Sako A fada maki"

A ruɗe tayi mashi farfari da idanunta cikin kagara ta furta"A message from the chief for me? Does he know about me? So what did he say?

Calmly Boss Ya furta"Yeah Yasan da zaman ki fiye da tunaninki, chief da kike gani baya zama wuri ɗaya da mutumin da baisan tarihin rayuwarsa ba," Wani irin bugu kirjinta yayi mata cike da fargaba ta furta.

"I don't understand what you mean! Chief ya san komai dangane da rayuwana! How is that possible?"

Dariya boss yayi ganin yadda ta shiga ruɗani

"Ki kwantar da hankalin ki Ummi, Amsarki tana atare dani, ki natsu ki saurari me zan fada maki" fuskarta a yamutse ta amsa mashi da toh.

Numfasawa yayi kafin Yaci gaba da fadin"sakon da chief Yace A fada maki shi ne, Gobe Idan Allah ya kaimu, zamu fita tare da Yaran nan zuwa cikin estate din su, muna so su halarci Farewell dinner din Uncle ɗinsa Hateem, amma fa bama so kowa yasan da wannan zancen! Zuwan bazata zamuyi tare da su, ke kuma abun da muke so daga gare ki, ki yi kokarin shirya mana su.... " kafin Ya kare Maganar tace"wai kana nufin prime minister Hateem na canada ne za'ayiwa dinner din? ɗaga mata gira yai alamar eh, but amma meyasa naji kace zuwan bazata za'ayi da yaran"? Ta faɗa tana mai neman ƙarin bayani.

Bai 6oye mata komai ba, dangane da budurin da aka sha lokacin da Danish ya rikiɗa, naƙin amincewa da zaman su a family din"

Jikinta yai sanyi"Allah sarki, ashe abun da ya faru kenan, ko da yake dama zaiyi wuya su yarda da su, ni kaina lokacin daya rikiɗa ba ƙaramin firgita nayi ba, saboda abu ne da ban ta6a gani ba, toh su kansu abun da zai sa su ƙi yarda da zamansu kenan, bayan haka hukuncin da shi baba obie ya yanke na raba alaƙar prime minister hateem da danish yayi dai dai, a fahimta na yayi hakan saboda gudun kada ɗansa ya cutu.... " jinjina kai taj yai alamar gamsuwa da bayanin ta, kafin wani ya qara magana a cikin su, sai ga jami'in isod Ya fito daga ƙofar falo, hannun shi ruƙe da plate mai ɗauke da mugs biyu na coffee, akan table din dake a tsakatsakiyarsu ya ajiye plate din kafin yabar wurin

Tura mata mug ɗaya taj yayi"kisha, ni nasa a kawo mana dan muji dadin tattaunawa' murmushi tayi har cikin ranta taji dadin karamcinsa, A hankali ta ɗauki mug din ta soma kur6ar coffee din, shima ya dauki nasa yana sha, bayan ta tsagaita da sha ne taci gaba da magana "kowani bawa da irin tashi jarabtar, Idan kaji na wani kai naka ba komai ba, shiyasa a koda yaushe akeson bawa ya zamanto mai hakuri dakai zuciya nesa, haƙiƙa ina tausayin wadannan bayin Allah, duk da ban kaiga jin tarihin rayuwarsu ba... ' murmushi taj ya ɗanyi tare da cewa"kada ki damu, nan badajimawa ba zaki ji tarihin rayuwarsu, In sha Allah"

Gyaɗa kai tayi "A ina za'ayi dinner din sannan ƙarfe nawa ne zasu je can din"?

"A cikin Estate din nan, Bayan sallar la'asar"

Shiru tayi alamar tana nazarin wani abu, yayin da yake binta da kallo.

"Menene dress code din da za'a sanya a wurin dinner din"? ta tambaya tana kallon fuskarsa.

"abaya matan za su sanya, A cikin suturunsu mun sanya masu abaya na larabawa kala kala, A ciki za'a daukar masu masu kyau na mutunci, sannan bama son suyi shigar da zata baiyana sumar kansu, a rufe masu ko'ina na jikin su.
Chapter 10 · 0% Book details