Sashe 81
Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk sun zuba ido suna kallon benazir wadda tun da likita yayi mata allurar bacci take ta yin shi, har wani firgita take yi kamar mai yin mafarki duk da karfin allurar cikin magagin bacci take ambaton sunan mijinta da yarta saboda sune aranta, baiwar Allah ba karamin jiki taji ba, la66anta sun bushe ƙamas tayi haske kamar ba jini a jikinta, kwarin idanunta sunyi ja da su...
Agaban gadon dr shureim da zeenatu suka tsaya suna kallon ta gwanin ban tausayi, da ace suna da halin da zasu Iya cire mata ciwonta ya dawo jikin su da tuni sunyi hakan...
Wayar hajiya sarah dake a cikin purse ce ta fara ruri da sauri ta curo wayar ta duba sunan mai kiranta My boss wato Alhaji musa.
Picking call din tay ta kara wayar a kunne ko sallamarta bai amsa ba, da kakkausar murya ya ce
"Kin manta Yau kina da aiki a office"? Bata bashi amsa ba, da sauri ta miƙe ta fito daga dakin
Kafin tace"ban manta ba, I'll inform my secretary that I won't be going to work today na ɗauki hutu har sai benazir ta samu lafiya, ay nayi zaton ka kirane don kaji halin da ake ciki game da lafiyarta..." kafin ta ƙare maganar Ya katse da cewa"karki kuskura ki ƙara yi min magana kan benazir! Idan har ba so kike ranki Ya 6aci ba..." ranta Ya 6ace a hasale tace"wai meke damunka ne? Yarinyar nan fa yar yayanka ce, ɗiyarka ce, meyasa kake nuna halin ko'in kula akanta? Sai kace ba jinin ka ba..."? Daƙyar ta ƙare maganar jin wata tsawa da ya daka mata muryarsa da 6acin rai Ya furta"zaki dawo gida ki sameni! Har ni kike ma magana kina ɗaga min murya? Kina cikin hankalin ki kuwa"?yawu ta haɗiya Muryarta adabarbarce ta furta"i'm...so sorry" bata ƙare maganar ba Ya furta"ki faɗawa shurem ya dawo da zeenatu gida, ke kuma zaki zo ki same ni" Duff Yai rejecting call din.
Ya Salam! hankalin ta idan yai dubu toh Ya tashi, bata ta6a hasala shi irin na yau ba, duk tabi tasha jinin jikinta, fargabanta kada taja ma kanta.
_____________________________✍️
Prisoner's shield 👊❤
A hankali Ya ware idanunsa masu ɗauke da bacci da wata irin kasala ya yunkura ya miƙe haɗi da jingina bayan shi jikin pillow, wani irin lalaci yake ji tun karfe 12 bai leƙa ko kofar dakin sa ba, bacci kawai yakeyi, kamar baya jin dadi, short ne kaɗai a jikin shi launin ja, sumar kan shi ta rufe gefen fuskarshi kamar baccin bai ishe shi ba...
Da wani irin kewar unaisah Ya farka, har mafarkinta sai da yayi, sai faman lumshe idanunsa yakeyi, kwatsam hasken ɗakinsa Ya ɗauke ɗuff kamar an kashe switch din dakin Sam bai lura ba ko'ina yayi duhu kamar dare
"Garkuwa namu!...."! cikin kunnansa Yaji wata murya mai kama da ta dattijuwa ta ambaci sunan shi, yayi zaton gizau muryar ke yi masa shiyasa bai mayar da hankali akai ba
"Shield! Shield!! Shield!!! Rass Yaji gabanshi Ya faɗi, A hanzarce Ya buɗe reddish eyes dinsa sosai, a matuƙar ruɗe, sam Ya gaza believing da abun da kunnuwansa suke Jiyo mashi
Durowa yayi daga kan gadon Ya soma bin ceilling din dakin da kallo, a kokarinsa naya gano ta inda sautin muryar ke fitowa.
A hankali Yake bin labulayen ɗakin da kallo farat ɗaya zuciyarsa ta raya masa hanya ɗaya ce zai Iya ganin me Yi masa magana...
A hanzarce Ya juya Ya kalli inda madubin dakinsa Yake, wanda tun da jimawa Unaisah Ta rufe masa shi da towel saboda ta gane baison ganin mirror
Walking slowly Ya nufi gaban madubin Yakai Yatsun Hannunsa dake kerma Ya Yakice Towel din Ya jefar da shi
Kyawawan idanunsa Ya ɗaura akan mirror din duhu ne Ya mamaye cikin sa baka Iya ganin komai....
La66ansa na kerma Ya furta"KHALA❗❓..." sautin dariyarta ne Ya karaɗe ɗakin nashi daga ji tsohuwace tukuf
"Garkuwarmu ko da Yake Yanzu Ka koma Garkuwarsu....' A hankali ta bayyana ta cikin duhun madubin kamar Yana kallon tv tsohuwa ce tukuf ta rufe ko'ina na jikinta da fararen kaya ko fuskarta baka iya gani sai dai idanunta da suka kasance farare ƙyal launin reddish irin nashi
Muryarsa na rawa Ya sake maimaita sunanta Khala
"Bani da isasshen lokaci yin magana!" ta faɗa tana kallon cikin idanunshi
"Inaso nima na bada gudummuwata wurin ganin kunyi nasarar ruguza tarihin kurkukun ƙaddara ...." da tsantsar mamaki yake kallon dattijuwar
Cikin harshensu na matsafa ta soma kora mashi jawabi...." a karshe ta furta"I'm waiting for your attack! Don't take time, the lives of the other prisoners are in danger!" (Ina Jiran farmakin ku! kada ku dauki lokaci, rayuwar sauran fursinonin tana a cikin hatsari)..." har Ya buɗe baki zaiyi magana ɗuff madubin Ya dawo suffarsa ta ainihi, da sauri Ya kawar da idanunsa daga kallon mirror din Ya ɗauko towel din daya jefar Ya lullu6e shi.
Jikin shi har tsuma Yake Yi, numfashin shi da hucin zafi Yake fita, Sam Ya gaza matsawa daga gaban madubin, muryarsa da tsantsar al'ajabi Ya ke maimaita sunan JEREMIAH his childhood friend as the new prison shield gaba ɗaya He was extremely confused, Tashin hankalin da ba'a saka mashi rana har wani tangyal tangyal yayi kamar zai faɗi dakyar ya iya tsayar da kansa bisa kafafunsa abunne Ya daki heart dinsa...❗
A cikin bayanan da dattijtuwar ta sanar da shi hada kwanan watan da za su yi black night ! Shin wacece Khala!?? Baku tunanin tarko ne za'a ɗana masu!? in ba haka ba tayaya matsafiya wadda take rayuwa acikin gidan kurkukun kaddara zata neme sa da sunan bashi gudummuwar tarwatsa kurkukun ƙaddara❓
Knocking kofar room dinsa akai da sauri Ya daidaita nutsuwarsa kamar wani abu bai ta6a faruwa ba...
Yayi zaton unaisah ce sai da yaje gaban kofar ya buɗe karaf idanunsa suka sauka akan chief owais Ya ɗauki wanka cikin shiga ta kakinsa Yayi shirin zuwa Office, from head to toe Ya kalle sa kafin Ya haɗe fuskarsa bakomai Ya tuna ba face unaisah da ya gani adakinsa jiya shiyasa ya ƙarajin haushin mutumin
Chief owais baibi takansa ba Ya nufi cikin dakin hannunsa ruƙe da shopping bag, Ya dire masa ita kan gadon shi
A hankali Ya juyo suka fuskanci Juna
"Ba ka Iya gaisuwa ba ne"? wani ɗan iskan kallo danish Yayi masa
Murmushin gefen fuska chief Yai
"Laifin me na maka kamar baka kaunar gani na"?
Shiru yayi bai tanka masa ba
Da ace chief yasan unaisah ce Silar dayasa danish Yake haɗe masa rai ay da tuni Yayi masa bayanin da zai kwantar masa da hankalinsa don shi A yanzu mace bata agabansa, burinsa ya gano miyagun gidan kurkukun ƙaddara da kuma kawo karshen su shi ne abunda Yasa agaba
kallon shoppin bag din yai alamar yana neman ƙarin bayani yaga bakon abu adakin sa
"It's a gift from Uncle Hateem. Please don't break them they're not toys," he said jokingly. tare da buɗe jakar ya soma fiddo da kayan cikin ta
"suna da amfani, idan ka bani dama zan nuna maka yarda zakai amfani da su" cikin lallami yakeyi mashi magana
Ganin Yayi tsaye Yaki matsowa Ya duba kayan, Yasa chief Tunkararsa Ya ruƙo hannunsa Ya janyo shi har bakin gadon
"Zuwa anjima zan ware mana lokaci in fara koya maka Yadda zakai amfani da su ko baka so"? Yai maganar Yana dubansa sai wani shan mur Yake.
Daurewa kawai cheif yakeyi amma fa ya fara hasala da halin danish kwata kwata baya sakar masa fuska kuma Yaƙi magana da shi, in banda ma Yana neman alfarma awurinsa ay da bai kai matsayin da chief zai kulasa ba
Fucewa yai daga dakin Ya Bar danish a tsaye Ya kasa ta6uka komai, zuciyarsa har yanzu bata daina ambaton sunan jeremiah ba, kalaman tsohuwa Khala sun tsaya masa aransa sai yake ganin kamar amafarki ta bayyana..
zama yayi gefen gadon Ya zubawa kayan ido har cikin rashi Yaji dadin jin cewa Hateem ne Ya bashi kyautarsu, duk da baisan amfaninsu ba amma sunyi mashi kyau, bai ta6a ko ɗaya ba, ya yanke shawarar sai unaisah tazo zasu buɗe su atare
________________________________✍️
*ANEELERH*
"Mu tafi asibitin kawai, bazan Iya jurewa ba...." gani take kamar zata rasa benazir, shiyasa ta hakura da shiga estate din
Su mahoob daman hanyar da zasu tafi suke nema, jiki na 6ari Ya buɗe motar Ya zauna a driver's seat, Aneelerh ta shiga ciki, Zahra na kokarin shiga kwatsam ta hango dankareriyar motar dake tunkaro estate din dakatawa tayi saboda ranta na bata cewar Motar Hajiya saratu ce....
"zahra ke muke jira ki shigo mu tafi" acewar mahboob
"Kaɗan jira, naga kamar motar Hajiya saratu ce ke tunkaro estate din..." jin wannan maganar yasa Aneelerh yin hanzarin fitowa daga motar shima mahboob Ya fito duk suka ƙurawa motar ido cike da sa ran ganin wanene a cikin ta
Lokacin da motar ta kusa ƙarasowa dab da inda suke gudunta ya ragu slowly window glass dinta na back seat Ya zuge hakan Ya basu damar ganin na cikinta
Wata irin nauyayyar ajiyar zuciya zahra ta sauke mai haɗe da annurin farin ciki
Ita kanta Aneelarh ajiyar zuciyar ta sauke haka shima mahboob duk da basu ta6a ganinta ba Yau ne rana ta farko da suka fara ganinta ido da ido
A hakimce take zaune cikin motar, ta ɗauki wankan lafaya, idanunsa na a manne da farin glass ba karamin kyau yayi mata ba
Da alama su take kallo, Umarni ta ba security din dake driving dinta idan sun karasa kusa da motar su zahra yai parking, ya amsa mata da toh
Daga bayan motarsu zahra yayi parking din motar, jiki na 6ari zahra ta nufe ta, a lokacin ta bude car door din ta zuro kafarta ɗaya waje
Sallama tayi mata cikin girmamawa tace"sannu da zuwa mommy, ya gajiyar aiki...."
Fuskarta da fara'a ta furta"lafiyalou daughter, zuwan bazata akai mana? Amma ya akai naganku a waje..."
Zahra kamar zatai mata sujjada tsabar yadda take magana cikin ladabi da biyayya
"Masu tsaron gate din ne suka hana mu shiga sunce dole sai an basu izni, har layinki na kira baya shiga nasan kin shiga busy ne..."