← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 238

Sashe 3

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Miƙewa yayi da sauri Ya nufi bedroom dinshi, Da sauri justice Yabi bayanshi, Yana Shiga Ya zura hannayenshi cikin aljihun short dinshi, Yayin da zuciyarshi ke cigaba da tafarfasa

"Bana so hakan Ya dame ka, Yarinyar nan ko tana so ko bata so, Kai ne mijinta, Saboda kafi cutuwa, Tsawon shekara goma sha shidda kuna rayuwa agida ɗaya tamkar ma'aurata? Ka raineta ka kashe mata maƙudan kudi, Idan har ta butulce maka Allah ma bazai barta ba"

Justice ne yayi maganar, yana daga tsaye abayanshi

"Duk abunda nayi mata nayi ne don Allah..." kafin Ya ƙare maganar justice yace"nasan don Allah kayi mata amma wallahi bazan bari ta karya maka zuciya ba, tun da nake da kai baka ta6a nuna kana son wata ƴa mace ba, sai akanta, don haka dole ta aure ka, shi kuma mijinta Ya haƙura ya nemi wata, nasan ma yayi auranshi tun da jimawa"

Juyawo Zaki yayi idanunsa akan justice Yace"nagode da kulawarka agare ni, amma mubar maganar, saboda hakan bamai yiwuwa bane, Ni bazan tursasa mata akan ta so ni ba, ta ɗauke ni tamkar yayanta tana girmamani, tun da nake da ita ban ta6a nuna mata inasonta da aure ba itama haka "

"Ita ai ba makauniya bace, in ba kaiba wani namijine zai dauki dawainiyar baligar mace kamarta almost 16years, idan bazan manta ba, lokacin da naje gidanka a canada, ina lura da duk wani motsinku, Idan ka shiga daki da dare zaka kwanta tana binka bata fitowa har saita tabbatar da kayi bacci take fitowa, kaima kuma haka, sannan baka Iya cin abinci idan ba atare da ita ba, itama haka, kana nufin wani abu bai ta6a shiga tsakaninku ba"? ya faɗa yana bin sa da kallon tuhuma.

"Nadeem, Ba abunda kake tunani bane, nasan nayi kuskure na ajiye macen da ba muharramata ba a gidana, amma wallahi ban ta6a shigarta ba..... " muryarshi na rawa ya ƙare maganar, wani irin yanayi yake jin kanshi tunawa da rayuwarshi da ita.

Numfashi yaja kafin yaci gaba dacewa"Ta saba min da kanta, komai ita take yi min, bansan menene so ba sai akanta, ban fara muradin yin aure ba sai akanta, ashe ita din ba rabona bane...."

"Da ace kuɗi zasu Iya siyamin ita, wallahi har dukiyata zan iya salwantarwa saboda ita, bana tunanin zan samu macen da zata Iya maye min gurbinta, Ni ita kadai nakeso Nadeem" kwallar dake taruwa a cikin idanunsa har sun fara kokarin gangarowa saman kuncin sa.

Hankalin Justice Ba ƙaramin tashi yayi ba, ko a mafarki bai ta6a tunanin mace zata Iya tanƙwara zuciyar Zaki ba.

Dafa kafadunsa yayi da hannayenshi

"Inaso ka faɗamin shi mijinta tsawon shekara nawa su ka yi atare"?

In a low voice zaki Ya furta"ƙasa da 2 years, ta faɗa min aranar data haifa mashi baby tabar gidan badan bata son shi ba, kawai taji ya futar mata arantane"

"Kasan mijin nata"?

"Taya za'ai nasan shi? ni ko sunan shi ban ruƙe ba, saboda kishinta da nake ji"

Murmushi justice yayi tare da ruko hannun Zaki, suka zaune gefen gadon shi.

"Iyayenta masu hali ne"? ya jefa mashi tambayar.

"Yeah, mahaifinta ya ta6a ruke mukamin Governor a jihar joss, amma bai jima a mulkin ba ya sauka sakamakon ciwon kafar dake damun shi, bayan haka Ƙanin Mahaifinta Former president ne Na nigeria, Alhaji Musa wadata, Yayan Matar Uncle sharafudeen Hajiya Laurat, nima a wurin ta naji labarin ta" jinjina kai justice yayi"Ƴar masu Hali ce, Alhaji musan nan Yana ɗaya daga cikin wadanda suka fi kowa kuɗi a africa bayan family dinmu, amma nayi mamakin da har ta gudu tabar nigeria basu nemo ta ba, meyasa tabar mijinta da ƴarta? Shine abun tambayar"

"Naikaina Labarinta Yajima Yana ɗaure min kaina, Sonta ne Ya makantar dani shiyasa ban mayar da ita ga Iyayenta ba, saima na taimaka mata wurin 6oye kanta agidana, naci gaba da bata kulawa"

Justice ya ce Labarinta Akwai ruɗani Acikinsa, Ta fito daga babban family, ga ta kyakkyawa da ita amma ahaka har ta gudu daga gidan mijinta? Akan wani dalili? Me ta nema tarasa?"

Ya faɗa yana kallon Zaki,

"Nayi kokarin nemanta don inji ya ta koma gidansu? Iyayenta sun kar6eta ko kuwa? Shine fargabana sai dai bani da hanyar da zan Iya kiranta, tabar min wayarta a hannuna, bansan kowa nata ba, in ba hajiya Laurat ba"

Numfasawa Justice yayi kafin yace"kada ka damu ɗan uwana, zan iya yin komai akanka, gobe Idan Allah yakaimu a family dinner zanyi magana da hajiyar laurat din dangane da ita Yarinyar," har cikin ranshi yaji dadin maganar justice, ya kwantar mashi da hankalin shi sosai harya fara tunanin yadda haduwarsu zata kasance da ita, sun jima adakin suna tattaunawa daga bisani suka dawo falo wurin su Captain.

______________________✍️

A hankali Motar Dr Jazz Ta ƙaraso bakin Entry Hall na shiga gidan baba Obie, Bayan yai parking ɗinta ya fito ya nufi cikin gidan, A katafaren Main Falo din gidan Ya taras da Twins zaune saman sofa tare da wani matashin saurayi kyakkyawan gaske kallo ɗaya zaka yima fuskarshi ka shaida ɗan uwan Justice ne, gaba ɗayan su wankan suit ne a jikin su, Cike da jin fargabansu Ya nufe su, Cikin sanyin murya yace"barkanku da hutawa"

Ko kallo bai ishe su ba, Kamar Yayi magana da bango, kuma sun ganshi.

Kusan sau uku Yana maimaita maganar da yayi masu amma babu wanda Ya amsa mashi, hakan Yasa shi yanke shawarar Tafiya yabar wurinsu Har Ya ɗaga ƙafa zai tafi muryar Zayn takatse shi.

"Kai zo nan"! da kakkausar Murya Ya faɗa tare da yafuto shi da hannu, Irin kiran da akeyima kananin Yara, Jazz baiji komai aranshi ba Ya nufi Zayn.

Yamutsa fuska zayn yai yayin da yake binshi da kaskantaccen kallo Yace

"Kai makaho ne? Baka gan mu bane zaka wuce batare daka gaishe da mu ba"? Fuska adaure yayi mashi maganar.

Cikin sanyin murya Jazz yace"Nayi maku magana kusan sau uku babu wanda Ya kula ni"

Harara Zayn ya watsa mashi, Dr. nawaz dake a kishingide yana duban su Yace"zayn dama har yanzu wannan kwandon sharar Yana agidan nan? Nayi tsammanin Uncle Mubarak Ya saki babarsa sun koma kasarsu"

Ta6e baki Zayn yayi"gayanan dai kana kallon shi, baida banbanci da masu gida, Har yafi mu jin daɗi, Uncle Mubarak ya ɗaure mashi wurin zama"

Yamutsa fuska Dr.Nawaz Yai"Kaci sa'a ba'a ƙasar nake zaune ba, da tuni nasa anyi watsi dakai, donni bana son bare ya ra6i Ahlinmu," Jazz dake atsaye yana sauraron Rashin mutuncin da suke yi mashi, tuni idanunsa sun cicciko tab da kwalla.

"Ya isa haka!" Zaid ne Ya faɗa tare da kallon Jazz, Da hannu Yayi mashi alamar Ya tafi, bawan Allah Jiki asanyaye ya nufi Hanyar kitchen din gidan, tunkafin Ya karasa Able ta fito daga ciki hannunta ruƙe da tray na kayan marmari, ganin jazz yasa ta dakata da tafiya fuskarta da fara'a tace"Jazz Ya jikin naka"?

Fuskar shi babu walwala Yace"da sauki"

"Allah Ya kara lafiya" ya amsa mata da ameen, ganin Yana ƴan kalle kalle Ne yasa ta fahinci akwai wani abu da yake nema don haka tace"ko akwai wani abu da kake bukata ne"?

Ɗaga mata kai Yai haɗi da cewa"Eh, Ina neman Faryat ne,"

"Muje na raka ka, Nima wurin su zanje kai masu Kayan marmari," amsa mata yayi da toh, ta yi gaba yabi bayanta, aranta ta ayyana ko me zai kai shi wurin faryat? Tantiriyar Yarinyar nan da babu Allah aranta"

Upstairs suka hau, bayan sun sauka third floor, suka nufi Balcony dake acan sama,Tsayawa fasalta kyawun wurin 6ata baki ne sai wanda Ya gani, tunkafin su karasa Jazz Ya hango Su zazzaune saman wasu hadaddun Kujeru Bugun Dubai, Matasan Ƴan mata ne masu ji da kansu, A kalla sun kai su uku Kowaccensu Ta dauki wanka na kece raini, Kamshin turarensu tuni Ya soma Cika mashi hancinshi.

Kaitsaye idanunsa suka sauka akan Faryat, wadda ke asanye da mini skirt ya matse jikinta, daƙyar skirt din Ya wuce Ass dinta, Rigar jikinta kuwa Ko cibinta bata rufe ba, ta bayyana shape din kirjinta hatta nipples dinta kana iya ganin tsininsu, babu mayafi akanta Kitson kalabar da akayi mata ne mai kyan gaske ansanya mata sparkling stones masu jan hankali saman gashin kanta, yatsun hannunta yana asanye da gold knuckle rings, Haka zalika Hancinta na amanne da nose ring, wata ziririyar sarka ce a kafarta, Yarinyar karshe ce wurin Iya barikanci, Hatsabibiyar gaske bata jin magana ko miskala zarratin, sai dai fa akwai kyan sura, komai nata irin na hajiya saratu ne banbancinsu girman jiki da shekaru.

Matashiyar dake a gefenta, Yusra ce Ƙanwar Yaseer, Kallo ɗaya zakai mata saika sake kallonta, Tsabar haɗuwarta, itama fara ce sol, kamanninta sak dana mahaifiyarta Her excellency Muhibbat, gata doguwa tubarkalla, bayan ita sai Zulaihat kanwar Ziyad Wankan tarwaɗa ce alaunin fata tana da saukin kai ko a fuska ka kalle ta, babu wanda Ya lura da Jazz A cikinsu Hankalinsu na akan firar da suke Yi.

able ce tayi masu sallama, Tare da ajiye masu tray din kayan marmarin saman round table din dake a tsakiyar kujerun su, juyawa tayi da sauri ta fuce tabar wurin.

Wani irin shakkar Yi masu magana Yake ji, Sai faman bin Faryat Yake Yi da kallon ƙurulla.

"Na jaraba kiran layin Sister Hindu bata yi picking ba, may be ko bata a kusa ne da wayar, ita dai Yazrin nayi mata uziri, saboda tafiyar da suka sha nasan haryanzu gajiyar tafiya bata sakesu ba" Zalaihat ce tayi maganar tare dakai hannu ta dauki tufa tana ci

"Ina ga mezai hana mu shiga gidan yi masu bangajiyar tafiya, Su mommy ma suna acan"

"Ni dai ba inda zanje, sai zuwa gobe idan mun haɗu wurin Dinner din daddy Hateem" Acewar Faryat Tana faɗa tana farfari da idanunta.

"Gobe akwai shagali, zamu yi sharholiyarmu son ran mu, Har nakagara goben nan tayi," Yusra ce ta fada tana karkaɗa kafarta.

Har Faryat Ta buɗe baki daniyar tayi magana, Sautin ringing din wayar Jazz Ya dakatar da ita, Kusan atare suka wurga idanunsu kan fuskarshi, nan take yaji gabanshi ya faɗi rass saboda kwarjinin da suka yi mashi.

Yamutsa fuska Yusra tayi tare da kau da idonta

Zulaihat kuwa Murmushi tasakar mashi
Chapter 3 · 0% Book details