Sashe 68
Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fitowa yai daga bathroom, waist dinsa daure da towel fari, gaban dressing mirror Ya tsaya zuciyarsa cike fal da tunanin halin da sajeed ke aciki, saboda Ya damu da yaran musamman wadanda ke acan gidan kurkukun ƙaddara sun tsaya masa a zuciyarsa, ayanzu baya da wani buri da ya wuce su kai masu ɗauki, shaf shaf Ya shirya kanshi cikin dark jeans tare da v neck shirt ta ɗame fatarsa.
Hayewa yai kan gadonsa ya daura kansa bisa pillow, hannunsa ruke da wayarsa, layin Boss Ya danna ma kira bayan yai picking suka gaisa da juna
"Inason ganinku, tare da salsabeel a room dina" amsa mashi boss yayi da toh"
Bayan wasu ƴan mintuna, wayarsa tai alert, unclock Ya danna a hankali kofar ta buɗe suka shigo su uku, cikin girmamawa suka gaishe da shi ya amsa masu
"Have a seat" ya fada Yana nuna masu couch, zama sukai suna fuskantar sa... Ya ɗan dauki lokaci kafin ya dan bude idanunsa dake a lumshe ya dubesu daya bayan daya kafin ya tsayar da idanuna akan salsabeel
"me yakamata mu yi? bana son abun yadau lokaci, ko dan saboda sauran yaran dake fuskantar barazana da buƙatar mu kai masu dauki....." babu wasa akan fuskarsa yai maganar
Calmly Salsabeel Ya fara magana"yalla6ai, ni bani da hanyar da zan iya jagorantar mu zuwa gidan kurkukun ƙaddara, saboda garkuwar sihirina ta karye kuma ina da tabbacin daga wajen su ne suka yi min hakan, amma nasan ɗan uwana zai Iya taimaka maku, shi kadai ne yasan hanyar da zai shigar daku Gidan kurkukun ƙaddara amma fa dole mu bi komai asannu kada muyi gaggawa saboda gidane mai hatsarin gaske, wani irin kurman ginine idan har baka da ilmi akansa kai kuskuran shiga kwakwalwarka zata iya ta6uwa"
Jin wannan maganar daga bakin salsabeel Yasa Taj da big guy suka kalli junansu da alamun rudani.
"Amma idan har Garkuwa ne zaiyi maku jagora shi ya san ta yadda zai shigar daku ba tare da kun sha wahala ba, amma fa da wuya danish Ya bamu haɗin kai, mutum ne mai wuyar sha'ani yana da kafiya, kuma har yanzu shi garkuwar su ne zasu iya sarrafa shi daga can kurkukun, ni dai ashawarata tun yanzu ku fara jan shi a jiki kuna koya masa abubuwa masu mahimmanci kamar rubutu da karatu tun da baisan komai ba ta hakanne zai fara sakin jiki da ku har asamu abun da ake so" gaba ɗaya sun gamsu da bayanin salsabeel.
Numfasawa chief yai kafin ya ce"in sha Allah zamu yi ƙoƙarin jan shi a jiki,"
Big guy yace"ni abunda ke ɗaure min kai da yaron kwata kwata baya son mutane su rabe shi in ba yan uwansa ba, kuma baya son wani ya rabi yan uwansa, meyasa"? ya tambaya yana kallon salsabeel
"Rashin sabo ne, idan Ya saba da ku zai daina, amma fa da buƙatar ku guji bata masa rai, in har ya nuna baison abu to kada ayi masa in ba haka ba komai zai iya faruwa, idan ransa ya 6aci evil heart ɗinsa zata iya motsawa abun da bana fata" ta6e baki big guy shi dai har yanzu bai yarda da Danish ba.
Shiru sukayi na wani lokaci
"I understand that dealing with them won't be easy." gaba ɗaya suka maida duban su ga chief da yai maganar
"in sha Allah, zamu yi zaman tattaunawa tare da chief of army, da kuma commender na america, bayan haka za mu tuntubi rassan jami’an ISOD da ke wasu kasashen, saboda taron ya shafi kowa da kowa. Dole ne mu hada kai kafin mu ci nasara a kansu. "
"Haka Yakamata yalla6ai" suka fada atare
Lumshe idanunsa yai gaba daya sun fahimci damuwar abunne ke addabar zuciyarsa
A lokacin da basuyi tsammani ba suka ji ya furta"na rantse da wanda raina ya ke a hannunsa wallahi duk wanda na kama da sanya hannunsa a kungiyar matsafan kurkukun ƙaddara sai ya ɗanɗani kuɗarsa ko da kuwa mahaifina ne bazan raga masa ba, ..., " yayin da yake yin maganar idanunsa sun kaɗa jawur saboda tsantsar 6acin rai
"In sha Allah sir mahaifinka ba zai ta6a zama ɗaya daga cikin su ba..." kafin taj ya ƙare maganar chief yai hanzarin katse sa yana huci yace"nima ina fatan hakan amma nasan mawuyacin abune, boss bana son na zurfafa bincike saboda fargaban kada inga wanda banyi tsammani ba, Ina jin tsoron ace akwai sanya hannun wani a family dina zuciyata zata karaya watakil ma hakan zaiyi silar da zuciyata zata buga...." ba su ta6a ganin tashin hankali tsantsa akan fuskar chief irin na yau ba, kwata kwata babu walwala atare da shi
Hada baki sukai wurin kwantar masa da hankali suna bashi baki, dakyar suka samu ya lafa yana faman sauke ajiyar zuciya ya kifa kansa jikin pillow... Bai sake dagowa ba, kamar bacci ne yai awon gaba da shi.
Miƙewa sukai atare suka bar dakin, zuciyoyin su cike fal da tashin hankali, su kansu tsoron ranar da asiri zai tonu suke yi saboda sun san dole akwai na jininsa, a kwanakin baya ya ta6a basu labarin kiran sirrin da wani bawan Allah yake yawan yi masa akan Ya binciki danginsa akwai bara gurbi acikin su wadanda suke sadaukar da yaran family ɗinsu har faɗa masa yai yaran da ake haihuwar su a mace ba mutuwa sukai ba suna nan da yaransu, bai ta6a maida hankali akan mutumin ba sai bayan da prisoners suka bayyana tukunna Ya fara gasgata maganar mutumin da har yau baisan wanene shi ba..."
Abakin kofar dakin nasa suka dakata da yin tafiya suna kallon junansu damuwa ce ƙarara akan fuskokin su kowa da abun da yake saƙawa aran shi sam sun kasa magana daga bisani suka fuce.
Chief Har ya fara nutsawa cikin baccinsa Wayarsa dake ajiye kan drawer ta fara ringing kaitsaye sautin ya daki kunnansa
A hankali yadan bude idanunsa wadanda ke lullu6e da yalwar gashi ya kalli ceilling din dakin kafin miƙa hannu ya ɗauki wayar
Motsa la66ansa yai tare da furta sunan Uncle hateem.
Picking call din yai
"Uncle am sorry, jiya na shiga bedroom dinsa na taras yana bacci shiyasa ban kira ka,"
On the other hand prime minister yace"Son ka hanani ganin maganin da zai warkar min da zazzabina....."
"Sorry uncle nayi laifi ay min afwa"
"It is okey, yanzu yana ina ya farka daga bacci"?
"Yanzu zanje bedroom dinsa na duba sa"
"Okey, akwai sako da za'a kawo masa daga company.." tun kafin ya ƙare maganar chief ya furta"uncle wani sako kenan"?
"Idan an kawo zaka gani, nasan idan na fada maka ba zaka bari sakon ya iso ba, zaka hana ne"
"Haba uncle, ni na isa in hanaka yin alkhairi..."
"Hakane, amma bazan fada ba" ya faɗa da zolaya
murmushi chief yai"andai hanani jin menene bakomai in an kawo zan gani, bari naje na basa ku yi magana"
"Video call zamuyi zanfi jin dadin ganinsa" amsa masa yai da okey, janye wayar yai daga kunnansa Ya nufi desk ya dauko ƙaramar laptop dinsa Ya sauko down babu kowa sai masu aiki dake zaryar kai abinci kan dining, ta elevator ya hau ta sauke sa second floor........
Abakin ƙofar ya tsaya yai masa knocking, shiru ba abasa iznin shiga ciki ba, yanke shawarar shiga yai a hankali ya tura kofar a zaton sa bacci yake yi, yana shiga ciki yaji alamun motsinsa a toilet, har ya juya zai fita da niyar anjima zai dawo sai kuma yaji an bude ƙofar, fitowa yayi daga ci ki jikinsa asanye da kayan baccin sa
Ganin mutum adakinsa Yasa shi cin burki ya tsaya yana kallon bayansa cike da mamakin wanene ya shigo masa bedroom dinsa...
A hankali chief Ya juyo suka fuskanci juna, nan take danish ya ƙara daure fuskarsa tamau babu annuri.
Takawa yai zuwa gabansa Ya miƙa masa hannu don su gaisa, maƙe hannunsa yai alamar bazai bayar ba,
"Ba ay min haka" ya fada tare da sanya hannu ya janyo danish yayi huggin dinsa kamar zai maida sa cikin sa, kamar wani mugun abu ya rungumesa sai kankame jikinsa yake yi, bayan chief ya raba jikinsa daga nasa ya soma yi masa magana.
"Barka da safiya, Ina fata ka tashi lafiya" shiru yayi bai tanka masa ba, wani kallon ƙasan ido yake jifa masa da ace chief baisan halinsa ba da sai yace ya tsane sa
"Ba magana? Ko da ya ke nima dalili ne Ya kawo ni roon dinka, kar6i nan uncle dina ke son magana dakai" ƙin kar6a yayi,
"Ina nufin uncle dina Hateem, mutumin dana hada ka da shi shekaran jiya, ina fata ka tuna sa" zare masa idanu danish yayi, sarai ya fahimci wa yake nufi abun da bai gane ba ta ina za suyi magana da uncle din nasa?
In a low voice ya furta"yana ina"?
Miƙa masa laptop din yai" anan zakuyi magana da shi ta video call"
wani kallon rainin wayau danish yai masa arude ya furta"tayaya zanyi magana da shi ta wannan abun" ɗan zaro ido chief yayi, can kuma ya saki fuskarsa tunawa da wanene shi
"Oh okey na fahimta lemme show you yadda zaku yi magana" bayan ya kira hateem video call fuskarsa ta cika laptop screen din, juyama danish ita yayi"look at him ku yi magana"
har saida danish Yaso Ya firgita lokacin da ya sauke idonsa kan laptop screen din ganin fuskar hateem mai ɗauke da murmushi, muryarsa cike da nishadi Yace"my baby boy danish, ka tashi lafiya? Ya ka kwana jiya? Ka yi kewana kuwa ko kuwa ka manta dani" yatsun hannun sa na kerma Ya kar6i laptop din daga hannun chief Ya kura ma hateem ido yana kallonsa batare daya furta komai ba, shi mamakinsa tayaya har ya bayyana akan wannan abun?
"Ka zauna ku yi magana" chief ne Ya fada tare da nuna masa gefen gado, jiki na bari yaje ya zauna yaci gaba da kallon hateem dake ta faman sakar masa murmushi
"Ka yi shiru baka tanka min ba, ko dai kamanta dani ne? Fadamin sai in tuna maka" shiru yayi bai masa magana ba, mamakin duniya ya cikasa