← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 188 OF 238

Sashe 188

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*[14/10, 6:06 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: ______________________________🔥💫

Wani irin burki suka ci, ganin babu khala adakin ta, abun daya jefa su arudani gaba ɗaya dakin nata a hargitse yake, harta gadonta Ya jirkice, tukwanan furannin dake a dakin duk an faffasasu, Ga jinin dayake malale kasa.. YA ILAHI❗❗

Alkalamina bazai Iya misalta tashin hankalin da suka shiga ba.

Sun rasa gane meya faru da tsohuwa khala? Jinin wanene suka gani a kasa? babban abun da suke ma zullumi Fursinonin da suka turo akawo gurin ta, basu san awani hali suke ciki ba, fargabansu kada ace jinin fursinonin ne!

badan zuciyar Imani ba da tuni Chief Ya hadiyi zuciya ya mutu saboda bakin cikin da Elders suka kunsa masu.

La66ansa na kerma ya furta"La'haula walaqu wata Illah Billa, Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un....." wani irin zafi jikinshi ya dauka rau...

Cike da ruɗu Commender James Ya furta"ni fa bangane ba, meke faruwa ne? Ina prisoners din da muka kubutar? Ina tsohuwar take? Jinin menene wannan"? ya faɗa yana nuna jinin dake malale kasa...

Yawu mai ɗaci thompson Ya hadiya ga radadi daya addabe shi, cikin sanyin murya yace"bana fata abunda nake hasashe ya zamana gaskiya, Zai iya yiwuwa Matsafan ne suka kawo mata farmaki watakil sun gano hada sa hannunta gurin kawo masu farmaki..."

bai ƙare maganar ba, Chief yai hanzarin katse shi ta hanyar girgiza kai yana fitar da numfashi mai ɗumi ya furta"in kuwa hakane Elders sun kashe ni, sun gama dani..."

kamar zautacce ya dinga nanatawa

Kanshine ya fara juya mashi wata irin juwace ta fara kokarin daukar shi da sauri Ya dafe bangon dake abayan shi, Yana huci hadi da jan numfashi kamar mayunwacin zaki..

"Ba zamu bar Nigeria ba, har sainaga bayan Elders, dole su fuskanci mummunan hukunci mai tsanani"

rai a6ace commender James ya fada...

"Me yakamata muyi yanzu? Bana bukatar mu 6ata lokaci gurin nemo su"! Commender haroon ne ya fada...

Captain lewis Yace"Where should we begin searching for them? Do you think they're still in this prison?"

Dukansu fa arauna ce suke, gabban jikinsu duk sun raunata ga yunwa da bacci dole su jigata tun dare ake gabzawa har gari ya waye batare da sanin su ba, amma saboda karfin hali irin na soja, burinsu su karasa aikin da suka dauko bata kansu suke ba, dare guda ba bacci sai zallar tashin hankali...."

"I don't think they're here, We should return to Nigeria and devise a new plan, we've lost our soldiers, and we're too weak to fight them now. We need to know what's happening with the soldiers we left outside"

(bana tunani suna nan, ni dai shawarar da zan bamu shine mu koma Nigeria, In yaso saimu sake sabon shiri, tunda yanzu duk mun rasa sojojin mu, Mu kanmu a raunace muke bamu da karfin da zamu iya yin faɗa da su a halin yanzu" acewar lieutanant Jackson)

Numfasawa Chief yayi"in sha Allah, karshensu ne yazo tun da har mu ka yi nasarar shugowa kurkukun nan, kuma mun yi masu barnar da ba zasu iya gyarata ba, nasan sun tsoratane shiyasa suka gudu, hakan ma wata nasarace...."

ya faɗa yana jan numfashi kafin Ya ɗaura da cewa"Zaku Iya tafiya amma ni bazan Iya barin kurkukun nan ba, saboda ɗan uwana Danish, zan jira har zuwa lokacin da Allah zai fiddo dashi daga cikin rijiyar zamu dawo tare da shi..."

ya faɗa idanun shi cike tab da kwalla, tsananin tausayin shi ne Ya kamasu, commender james Ya dafa kafadarshi Cikin kwantar da murya yace"ka yi hakuri Chief, bana tunanin zai rayu acikin rijiyar nan, ka daure kayi hakuri ka lallashi zuciyar ka, Mu tafi kawai..."

Zafafan hawayene suka wanke fuskar sa, wlh kallonsu kawai yakeyi yasan bazasu ta6a jin irin kunar da zuciyarshi keyi mashi ba.

cikin karyayyar murya ya furta"Bazan Iya tafiya ba, tayama zan tafi in bar Danish acikin rijiya tare da wannan Shaidanin? What if he kills him?"

Girgiza kai yai"Idan Nayi haka banyi mashi adalci ba, saboda mu rayu ya jefa kanshi cikin haɗari, sai kuma mu tafi mu barshi?

Dakyar ya kare maganar, daurewa kawai yakeyi, cike da tausayinshi su ke kallon shi, su kansu hawayen ne cike tab da idanunsu.

"Abun da nakeso ka fahimta, Danish Ya sadaukar da kan shine don mu rayu! Idan har muka bari muka rasa ranmu hakan na nufin burin shi bai cika ba, pls ka jure ka rungumi kaddara" acewar Commender Haroon.

Girgiza kai yai"ba zaku fahimce ni ba! But Danish deserves to live, wai shi mema Ya mora a rayuwarsa ta duniyar nan? Ya zo awahalce yanzu kuma kuna nufin in barshi Ya mutu? Shikenan fa ya mutu baisan iyayen shi ba, Bai ta6a jin dumin mahaifiyarshi ba, Baisan menene dadin iyaye ba, idan Uncle hateem Ya kirani ya tambayi ina yaronsa wata amsa zan bashi? kai Ina, wlh bazai yiwu ba dole naje na ceto rayuwar sa koda zan rasa rainane..."

da alama chief owais Ya fara zaucewa sai sambatu yakeyi masu marasa kan gado, kafin su gama yanke shawara da zuciyarsu chief yai hanzari juyawa da gudu Ya fuce daga dakin da niyar ya koma gurin rijiyar, da gudun gaske suka bi bayan shi cike da tashin hankali suke ƙwala mashi kira haɗi dayi mashi magiya akan ya tsaya kada yaje amma ko waiwayen su baiyi ba, saboda Idanun shi sun makance Danish kawai ya ke son gani, bawan Allah kusan sau hudu yanayin tuntu6e Ya fadi kasa ahaka zai mike Ya cigaba da gudu, Yana kokarin shan wata kwana kwatsam ba zato ba tsammani ginin Kurkukun Ya fara Jijjiga kafin kace me tuni ginin ya fara tsastsagewa, hankalin Su commender ba karamin tashi yayi ba, akan idon su komai ke faruwa yayin da Chief kwata kwata bai lura ba saboda baya acikin hayyacin sa.

wannan shi ake kira da tashin hankalin da ba'a saka mashi rana, wasu irin marmarar duwatsun da akayi ginin ne suka fara 6a66akowa daga sama Kaitsaye suke rubzowa ƙasa da wani sauti suka tartwasewa, duk wanda kuwa tsautsayi yasa suka afkwa kanshi tofa Ya tashi aiki.

Chief daya rikice bai kaiga isa hall din ba, Wani Gingirimeman dutse Ya yanko mai girman gaske Gaba daya ya zube ƙasa, ya shiga tsakanin chief da hall din, ras gaban shi ya faɗi ya zare reddish eyes dinsa sam ya kasa motsawa, Wlh zuciyarshi ta gama karaya ya riga daya fidda rai da Danish.

Saboda ya rude kokari yake ya nemi hanyar da zai bi ya karasa ga hall din, wani ginin ne ya zazzago daga saman ceilling din dayake batare daya ankara ba, Cikin zafin nama commender james Ya damƙi damtsen hannun shi ya jefar da shi gurin Su captain da sauri Suka rurruke shi Yana kuka Yana kokarin fisge kan shi daga hannunsu ahaka suka sanya karfi gurin ingiza shi.

bawan Allah sai waiwayon ginin hall din daya rushe yakeyi..Yana ji Yana gani ahaka suka tafi da shi kamar yayi hauka sai sambatu yakeyi

_tun da na fara aiki ban ta6a faduwa ba sai yau da nagaza taimakon ka, Naji kunya Danish, i'm a looser, ka sani ba kai kadai bane danish, Kana da Allah kuma kana da dani, Danish bazan bari ka mutu ba, zan dawo Danish, zan dawo dole na ɗaukar maka fansa..........😭😭😭_

(Finally Su Chief Sun yi nasarar fita daga kurkukun kaddara bayan kalubalen da suka fuskanta)

*__________________________ELDERS 🔥*

A zazzaune suke kan Sofas cikin wani Daki mai duhu, saika kura ido zaka Iya ganin su da taimakon wutar Candles dake Ci, round table din dake agaban su shake Yake da kwalaben Giya sun sha sun bugu har ta kai masu karo.

Idanunsu sun kaɗa jawur kamar jan gauta, fuskokinsu babu annuri ko miskala zarratin basu taba fuskantar barazana da tashin hankali irin na wannan lokacin ba, sunyi babbar asara ba kaɗan ba.....❗

"Sune na farko da suka fara kawo mana farmaki! sun latata ginin da nayi wahalar kafawa tsawon shekaru! Sun san komai da muke aikawata, sun san sirrin mu, sun gani da idanunsu, sun kuma kashe rabi da kwata na Giants din mu, bayan irin 6arnar da sukayi mana na, sun 6ata shagalin black Night, sun kashe dubban matsafan da basu ji ba basu gani ba..."

ya faɗa yana jan numfashi cikin fushi, kafin ya daura da cewa"hakan bai ishe su ba, sai da suka kwashe Fursinoni da muka raina tsawon shekaru don mu amfana da su, sun tarwatsa duk wani shirin mu"

"Yaron da muka raina da hannun mu don ya zama garkuwar mu yaci amanar mu ya koma garkuwar su, tsohuwa Tamira da Salsabeel haka suma suka ci amanarmu, abunda yafi karya min zuciyata, wadda na damƙa ma yarda ta da amanata, hada ita cikin waɗanda suka bada gudummuwar kawo mana farmaki! meke shirin faruwa da mu ne? Meyasa waɗanda muka yarda da su suke cin dunduniyar mu"?

bai karasa maganar ba Yana huci Ya ɗaga kwalbar giyar dake a hannun shi Ya rotsa ta kan table din gaban shi nan take ta tarwatse.

Ran Elder yayi mugun 6aci, a wannan gabar komai zai iya faruwa.

Hankulan sauran Elders din ba ƙaramin tashi yayi ba, wata irin kururuwar ihu Ya fasa tare da tallabe kan shi da tafukan sa.

Lallashin shi suka fara yi cikin kankan dakai da girmamawa dakyar suka shawo kan shi.

Gyaran Murya Jan harshe yai kafin ya furta"Karaya ba tamu bace, Ba'a san elders da rauni ba, har yanzu muna da damar da zamu Iya dawo da ran kurkukun ƙaddara...."

bai ƙare maganar ba, Elder Yana huci Ya tari numfashin shi da cewa"tayaya zamu iya yin hakan? Bayan sun riga da sunsan komai, sanin ka ne muddin wani yasan sirrin inda muke yin tsafinmu abu na farko da zai faru lalacewar ginin kuma ya riga daya faru, abu na gaba shine karyewar sihirinmu In har hakan ta faru cikin sauki zasu shafen tarihin da muka daɗe muna kafa shi...."gaba daya sukayi shiru suna sauraranshi, da alama sun kadu sosai.
Chapter 188 · 0% Book details