← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 238

Sashe 114

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abie ne yai karfin halin furta"kiyi hakuri Anila, basu dawo ba, amma yanzu zamu tafi neman su, in sha Allah zamu dawo maki da yaronki..." runtse idanunta tayi wasu irin zafafan hawaye suka wanke fuskarta...fitowa mahboob yayi daga dakin Ana yana tafiya kafafun shi suna harɗewa saboda rashin kwanciyar hankali, dawowa cikin falon yayi ya tsaya yana kallon fuskokin su.

"Zahra kun kira layin Ana ɗin"? ɗaga mashi kai tay"mun kira akashe" tsoki Ya buga tare da ruƙe qugun shi kafin wani ya kara magana a cikin su, sautin kiran sallar magrib Ya karaɗe kunnuwan su

Uncle ɗan iya yace"dan Allah ku kwantar da hankalinku, in sha Allh zasu bayyana cikin koshin lafiya, yanzu ku je kuyi sallah kuyi masu addu'a duk inda suke Allah Ya kare mana su, in sha Allah idan muka fita zamu bi gidajen makwabta mu duba watakil adace ko sun shiga ciki"

__________________________________✍️

*💋UNAISAH ANGEL💓*

Wunin ranar Unaisah bata jin dadin jikin ta, kamar mai fama da zazzabi tun da idanunta sukayi tozali da zeenatu bata ƙara samun nutsuwa ba, Yarinyar ta tsaya mata aranta tunanin zeenatu yayi mata ƙatutu a cikin zuciyarta, ta rasa meyasa take ta faɗo mata aranta, har takai ga da zarar ta rufe idanunta fuskar Zeenatu take gani.

Tana akwance kan darduma wani guntun baccine Ya ɗauketa bayan ta kammala sallar magrib, gaba daya ta kudundune kanta cikin hijab....

Benazir tana zaune gefen gadonta tana ta kallon ta, yayin da hajiya layla ke azaune kan sofa..

"Benazir..." dagowa tayi tare da kallon mami data ambaci sunan ta, kallon kallo suka shiga jefawa junansu, tuni benazir tasha jinin jikinta, dama tun dazu da abun nan ya faru na zuwan zeenatu ta lura da irin kallon da mami takeyi mata ga wani annurin farin ciki da take gani atare da ita...

"Ya jikin naki? ɗazu naga kamar kin samu lafiya.."

shiru tayi jim tana tunanin ta yadda zata 6ullowa mommyn nasu don bata shirya bayyana masu ta samu lafiya ba, tana da dalilinta nayin haka..

Jin tayi shiru yasa mami ta sake furta"dake fa nake magana? Hannu tasa ta ɗan sosa gashin kanta tare da kyafkyafta idanunta irin yadda masu tabin hankali sukeyi sam ta kasa buɗe baki tayi magana, hajiya layla ta kura mata ido tana kallon ta, ta ɗan rude da yanayin ta aranta ta ayyana ko dai har yanzu da sauranta"?

"Mami ina baby na? Ban ganta ba? ta faɗa tare da saukowa daga kan gadon ta fara ɗaga pillow tana nemanta, hada kokarin yaye zanin gado duk don tayi pretending kada hajiya layla ta gane ta samu lafiya.

Shesshekar kukan karya ta farayi hada yarfa hannu ta juyo ta kalli hajiya layla da ta saki baki sototo tana kallon ta.

"Mami kodai wani ya sace min ita ne? na duba banganta ba.." abun ya ɗaurewa hajiya layla kai, yanzu fa take zaune tana kallon yarinyar amma farat ɗaya ta nuna bata ganta ba.

Jinjina kai tayi aranta ta ayyana lallai haryanzu da sauranta, ganin yadda tabi ta ruɗe ne yasa mami yin saurin kiran sunan ta, a hautsine ta juyo tare da kallon ta

"Gata nan a kwance kan darduma.." girgiza kai tayi"mami ba itace ba, wannan ƙatuwa ce, babyna karama ce" waro ido waje mami tayi can kuma tayi tunani kodai don taganta nannaɗe cikin hijabine, mikewa hajiya layla tayi taje gaban prayer mat din, a hankali ta cire ma Unaisah hijabin ta fiddo da fuskarta.

"Kin ganta"? washe baki Benazir tayi tare da sanya tafukan hannunta, ta rufe fuskarta tana fadin"ashe itace ta lullu6e da hijabi, shiyasa bangane ta ba, mami gobe zamu koma gida da ita ko"? Shiru hajiya layla tayi gabanta na faduwa, jin abunda Benazir tace, yanzu ya zatayi gobe idan zasu tafi? Tasan dole Benazir ta sanya masu rigima muddin su ka ce zasu raba ta da yarinyar ba karamin daga za'ay ba.

"Mami kinyi shiru..." murmushi yaƙe ta sakar mata"kinji ki da wata magana, in bamu tafi da ita ba, a asibitin zamu barta ta kwana ne"? Yar dariya benazir tayi tare da jujjuyawa tana fadin"wayyo Allahna naji dadi mami, nayi farin ciki, zamu tafi da babyna gida...." ita dai hajiya layla jikinta yayi sanyi, Da harta fara murnar Benazir ta dawo hayyacin ta ashe har yanzu bata gama wartsakewa ba.

Ringing ɗin wayarta ne Ya farkar da ita, kaitsaye sautin ya daki kunnanta, a hanzarce ta tashi zaune ta cire hijab din jikin ta, idanunta har sun ɗan kumbura, ganin hajiya layla agabanta yasa ta ɗan firgita kaɗan.

"Yanzu nake shirin tada ki daga bacci naga ko dinner baki ci ba, sai gashi kinma farka da kanki..." hajiya layla ta fada da murmushi akan fuskarta.

"Babyna..."
Benazir ce ta kira sunan ta, a hankali ta dube ta muryarta da kasalar bacci ta furta"na'am mommyna..." murmushi Benazir tayi"naji wayarki tana ringing, ki duba ki ga wanene ke kiran ki" amsa wa tayi da toh, ta mike ta nufi backpack dinta ta curo wayar a lokacin har kiran ya katse.

kallon su hajiya layla tayi sam bata son yin waya agabansu, kamar mara gaskiya ta zura wayar a aljihun rigarta, ta juya ta nufi toilet ta shiga daga ciki taja kofa ta datse.

Call ta danna mashi yana yin picking tace"daddy, barka da marece? Ka wuni lafiya"?

On the other hand taj Yace"lafiyalou daughter, halan daga bacci kika tashi naji muryarki wani iri"

"Eh, bayan na kammala sallah ne bacci yai awon gaba dani"

Okey, dama na kirane don in kara kwantar maki da hankali, daga gobe ne in sha Allah za'a sallame ku da wuri, mun ma yi magana da chief ya fada min shi zaizo daukarki...." murmushi tayi har cikin ranta taji dadin jin hakan

"Allah yakaimu lafiya daddy, amma zanyi kewar mommyna..." ta fada kamar zata sanya mashi kuka, dariya yayi"ke fa da kanki kikace kingaji da kallon ki da matar keyi..."

"Wallahi daddy ina sonta sosai, bansan rabuwa da ita, jiyan ma dana fada maka ta bani tsorone ina fa bacci ta tsareni da ido amma ni ina kaunarta"

"Kada ki damu, ko bayan kin dawo gida zan iya kaiki gidan su ki gidan ta" dadine Ya lullu6e ta, sun ɗan jima suna waya kafin sukayi sallama.

Tana sauke wayar daga kunnanta, idonta ya sauka akan text message din da aka turo mata da bakuwar number, cike da mamaki ta danna sakon ya buɗe kura ido tayi tana kallon jagwalgwalon rubutun

Daya bayan ɗaya ta fara karanta shi.

_Deer swit angil, I mis yu soooo mutch Pleeease come hom to me, and I promis to met awl your condisions I wuv yu soooo mutch_

Dafe kai tayi da hannu daya zuciyarta cike fal da tunanin wanene yayi mata sakon? aranta ta ayyana daga gani ƙaramin yarone ya ɗauki wayar babarsa batare da sanin ta ba, ya danna wrong number shine aka tura mata sakon, tuntsirewa tayi da dariya da sauri ta toshe bakinta tunawa da su hajiya layla acikin dakinta...

Murmushin gefen fuska tasaki cike da nishadi ta ƙara maimaita sakon saboda nata fahimci me aka rubuta ba, nutsuwa tayi sosai tana kallon rubutun tiryan tiryan lokaci ɗaya taji gabanta yaɗan faɗi ganin kamar nick name dinta wato Angel

_My sweet Angel, i miss you so much, please come home to me, and i promise to meet all your conditions i love you_

Tabbas sakon ba kuskuren akayi ba, ita aka turo ma shi, ko wanene? Ta jefa ma kanta tambayar da bata da amsarta, a kalla ta maimaita karanta text din yafi sau ashirin batare data iya gano wanene ya turo mata shi ba, reply ta mayar masa"Please, may I know who you are? Bayan ta tura mashi sakon ta fito daga toilet din, a lokacin dr jazz ya shigo duba jikin Benazir yana ganin ta ya sakar mata murmushi da sauri ta gaishe da shi ya amsa mata da fara'a, bayan ya kammala dubata, yayi masu sallama ya fuce daga dakin da sauri hajiya layla tabi bayan shi.

"Dr. Jazz! Ina son yin magana dakai" tsayawa yayi tare da juyowa yana kallon ta, agaban shi ta tsaya suka fuskanci juna

"Dr mungode sosai, kana kokari akan Benazir, ubangiji Allah Yasaka maka da alkhairi, Allah yabiya maka bukatunka..." addu'oi tadinga yi mashi yana amsa mata da ameen, da alama yaji dadin addu'arta

Jin tayi shiru kamar akwai wani abu dake damuntane yasa shi furta"naji kinyi shiru ko akwai wani abu" yarfa hannu tayi fuskarta ayamutse tace"dr bansan ya zanyi da benazir ba! Ta ƙwallafa rai akan yarinyar nan, Ni damuwata halin da zata shiga idan aka raba ta da yarinyar kar akoma yar gidan jiya"

ta faɗa tana marairaice mashi fuska, yama rasa amsar da zai bata don ya fahimci kamar so take abar masu yarinyar su tafi da ita abune da bazai yiwu ba"

Calmly yace"na fahimce ki, amma gaskiya sai dai kuyi hakuri, iyayen yarinyar nan sunyi kokari da har suka iya baku ita na tsawon kwanakin nan, saboda ba karamin so sukeyi mata ba, itace kadai yar su tilo" dafe kai hajiya layla tayi da hannu ɗaya, sai yaji ta bashi tausayi.

"Nasani dr, wlh sunyi mana halaccin da ba zamu iya biyan su ba, ni damuwata taya zamu rabata da yarinyar? Kana gani zata hakura"?

"Kada ki damu, ni nasan ta yadda zan raba su batare da an samu matsala ba, in sha Allah komai zai tafi dai dai" gyaɗa kai tayi"mungode dr, agaida mutanan gidan," sallama yayi mata kafin ya juya da sauri ya nufi hanyar fita daga asibitin.

______________________________✍️

Bayan tafiyar su Abie masallaci, mami ta kalli Aneela dake kwance tana faman share kwalla"kiyi hakuri ki daure anila, bana son kukan nan da kike yi, ku tashi kuje kuyi sallah kuyi masu addu'a...." jiki asanyaye ta miƙe kwata kwata babu kuzari kamar zata faɗi kasa da sauri zahra ta taimaka mata suka nufi bedroom dinta...

Cike da jimami ummi da mami suka nufi dakunansu domin yin sallah....
Chapter 114 · 0% Book details