← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 238

Sashe 129

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya faɗa tare da russinawa ya sumbaci forehead dinshi hajiya saratu dake kallonsu ba karamin burgeta sukayi ba, sabanin da da take jin haushi intaga baba obie da owais suna bama junansu kulawa kamar uba da da, abun yana 6ata mata rai saboda ita aganinta baya son twins saboda ubansu ba jinsinsu bane shiyasa yake nuna wariya tsakaninsu, abun da ta fahimta ayanzu owais yana matukar girmama baba obie biyayya yakeyi mashi sau da kafa dama ita zuciya tana son mai kyautata mata.

Tayi zurfi a tunaninta, muryar baba obie ta katseta, firgigit tayi tare da kallon shi, har chief ya fita daga dakin bata lura ba.

"Fada min meke damunki? Tun shigowarki na lura da yanayinki kamar bakya jindadi ko"? Gyara zama tayi, kafin ta fara kora mashi jawabi.

"Baba akan marwa ne! Naga ciwon nata yayi tsauri shine nace me zai hana amaida ita garinsu gaban iyayenta? Ita kanta zataso ta kasance a karkashin kulawarsu hankalinta sai yafi kwanciya, ba kamar nan ba, ba dangi iya bana baba, kuma kaga ciwon nan nata bana lafiya bane, zata iya goga ma wani...." fuskarta ayamutse tayi maganar, kamar irin ta damu da ita din nan.

Shiru baba obie yayi jim kafin yace"Auta, kin taba zuwa duba lafiyarta ne"? ɗaure fuska tayi

Murmushi yai"nayi mamakin jin maganarki, inace tin ranar farkon da ta fara lalurar baki kara leƙawa ba, aranar ma guduwa kikayi daga dakin ko"? Ya faɗa da zolaya, sunnar da kanta kasa tayi batare da tace komai ba.

"Meyasa zaki ce amaida marwa garinsu? Ko dan saboda lalurarta? Da can da take mana hidima bamu guje ta ba sai yanzu da Allah ya jarabce ta? Munyi mata adalci kuwa? Yamutsa fuska tayi"baba ka fahimce ni, nasani ba ita ta daura ma kanta ba, babu wanda yafi karfin Allah ya jarabce shi, amma ni dai aduba mana, saboda lalurarta su twins suka daina kwana gida, kasan su da kyankyami kuma abune da basu saba gani ba, shiyasa duk suka firgice, ni kaina hankalina ba akwance yake ba, wlh dakyar nake iya bacci agidan nan gani nake kamar nima abun zai shafe ni..." da mamaki baba obie ke kallonta, ta haɗe rai ba annuri akan fuskarta, duk zaman nan da ake baisan cewa su twins sun bar gidan ba sai yanzu da yaji a bakinta ay da tuni yasa an dawo da su.

"Indai akansu twins ne zansa su dawo gida, amma marwa bazata koma gurin iyayenta ba, har sai ta samu lafiya, saboda anan ta samu lalurar, kuma anan zata samu warakarta in sha Allah, Ni ba zan bari mutuncina ya zube a idon jama'a ba, yarinya da lafiyarta ta fara aiki agidan nan sai kuma in maida ma iyayenta don amfaninta ya kare uhyum? Kiyi tunani mana, su kansu iyayenta ba za su ji dadi ba, su ga mun maida masu yarinyar su da nakasa a jikin ta.. "

Ran hajiya saratu ya 6aci muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"baba ban taba neman abu agurinka kaki yi min ba, sai yau saboda kawai na nuna bana son zaman marwa agidan nan! Yakamta ka duba lamarin nan baba fisabilillahi saboda ita su twins sun kasa zama gidan nan, nima na rasa kwanciyar hankali, baba kafison farin cikin marwa akan namu kenan..." yunkurawa tayi zata miƙe da sauri ya dakatar ta ita"saratu koma ki zauna" zama tayi fuskarta ba fara'a...

Bottle water ya dauka me sanyi ya tsiyaya mata ruwa a cup ya mika mata, tana faman haɗe rai ta kar6a ta kurbi ruwan sau uku kafin ta ajiye tana kallon shi.

Yayi shiru yana nazarin maganar ta, arayuwarshi baya son bacin ran ya'yan shi, sannan baya son duk wani abu da zai haifar da rashin kwanciyar hankali atsakaninsu, sai dai bayajin zai iya mayar da marwa garinsu ahaka batare da taji sauki ba, yanajin tausayin ta, bayan haka bazaiso mutuncin shi ya zube agurin iyayenta ba.

"Baba nasan me kake tunani, indai akan iyayenta ne, wlh daga mun basu kudi zasu ja baki suyi shiru, kaga sai suci gaba da yin jinyarta, ni nayi alkwarin zan dauki nauyin duk wani abu da za'a kashe gurin nema mata lafiya, ni kawai gidan ke banaso ta zauna" gauran numfashi yaja kafin ya dubeta"auta" tace"naam baba"

"Kada ki makara, ki tashi ki tafi aiki, zanyi tunani, in sha Allah idan na yanke shawara zan sanar dake" amsa mashi tayi da toh, kafin ta mike tayi mashi sallama ta fuce daga dakin.

__________________________________✍️

Lokaci ɗaya Zuciyarta ta fara bugawa da matsanancin ƙarfi tamkar ana buga ganga, numfashinta ya fara fita cikin sauri, yayin da kirjinta ke harbawa yana sama da ƙasa da kokarin jawo iska a cikin hunhunta, wani irin gumine ya fara tsasstsafowa ta cikin hudojin gashin jikin ta, zufa ta soma gangarowa ta cikin nannaɗaɗdiyar sumar kanta tamkar yayyafin ruwan sama jikinta ne ya fara kakkarwa, Yatsun kafafunta dana hannunta suka kama kerma, idanunta suna arufe gam ta matsesu, fatar kwarin idanunta sai kerma take sakamakon kwayar idanunta dake jujjuyawa, kokari take ta buɗe idanunta takasa saboda raunin da sukayi, jikinta tamkar babu jini saboda rashin kuzari, ga wata matsiyaciyar kasala data daskarar da ita daga yunkurin da take yi na son farkawa, Allah kadai Yasan tsawon makonnin da ta dauka bata acikin hayyacin ta sakamakon duguwar sumar da tayi.

A kalla ta shafe awa cikin mayuwacin hali tana kokarin ƙarfafa kanta donta samu damar buɗe idanunta, ta ko'ina ba sauƙi, jikinta tamkar an daddaure shi da igiyar kaca, sai faman jijjiga jikin takeyi donta samu kwarin gwiwar tada kanta.

La66anta dake a bushe ƙamas fatarsu ta faffashe hada busasshan ɗigon jini, da ƙyar ta iya moving dinsu ta furta"GABRIEL" kwata kwata sautin muryarta baya fita, cigaba da ambaton sunan tayi duk da radadin da makoshinta keyi mata mai azabar zafi, meyasa ta ambaci sunanshi? A karo na farko data dawo hayyacinta? Saboda shi ne aranta.

Lokaci ɗaya ba zato ba tsammani kwatsam tayi wani yunkuri da iya karfin ta na karshe ta daddage ta banbare kanta daga jikin abunda take a kwance tayi wata irin zabura ta miƙe zaune tana faman jan numfashi, sannu A hankali ta buɗe idanunta wani irin duhune bakikkirin ya mamaye ganinta, bata ganin komai tamkar ta makance, batasan a ina take ba? Meya faruwa da ita? ta manta komai, kamar tayi loosing memory din ta, tayi matuƙar rudewa ta rikirkice tunaninta ya gushe, daddafe kanta tayi da tafukan hannayenta cikin rawar murya ta furta"A ina nake? wa ya kawo ni nan? Meya faru dani? Babu mai jina ne? Kuyi min magana bana ganin komai, ko dai na makance ne...." sautin muryarta baya fita dakyau.

Kamar ta fasa ihu haka take ji, saboda takasa gane meke faru da ita? A ina take.

A lokacin da batay tsammani ba, kwatsam ba zato ba tsammani, wani siririn haske ya kurdado ta saman gurin da take, Waro idanu waje tayi cikin tashin hankali da tsantsar rudani take kallon hasken, A hankali hasken ya fara mamaye ɗakin har saida ya karaɗe cikin sa tamkar da rana.

Idanunta suka washe, amatuƙar ruɗe take kallon inda hasken ya fito ashe fitilune na saman ceilling din dakin, da sauri ta dubi inda take a zaune, Metal bed ne (gadon ƙarfe) irin kirar zamanin da na kaka da kakanni, Gadon Yana da girma da tsayi, ga wata lumbutsetsiyar katifa tattausar gaske mai dadin zama hada matassan kai guda biyu, daga saman gadon Yana da rumfa hada labulaye a kewaye da shi, kamar irin gadon sarakuna

Gaba ɗaya ta ruɗe ta rasa gane waya kawo ta dakin? Da sauri ta kalli kayan jikinta, farar riga ce shara shara kamar matacin kwakko, komai na jikinta ana gani, rigar tana da dogon hannu, tsayin ta bai wuci Iya gwiwar ta ba.

Sumar kanta kamar an kifa mata yayi, ta bushe ba gyara duk gashin ya yamutse, ƙoƙarin saukowa tayi daga kan gadon sai dai ta kasa saboda tsayinsa bata san ya zatay ba, matsawa tayi daga bakin gadon ta leƙa ƙasa cikin sa'a ta ga matakala irin ta bene mai hawa shida, numfashi ta ɗan ja tare da sauke ajiyar zuciya, a hankali ta ɗaura ramammun kafafuwanta kan matalar farko ta yunwa zata miƙe aikuwa wani irin jiri ya kwashe ta saboda rashin kwarin jikinta gaba ɗaya ta kundumo ƙasa timmm! ba karamin dakuwa tayi ba, amma saboda karfin hali da kwarin gwiwa irin nata ta daddage ta miƙe tana faman fitar da numfashi mai haki kamar wadda tasha uban gudu

miƙewa tay tsaye tana kallon katafaren ɗakin mai girman gaske, gado ɗaya ne aciki sai book shelve ma'ajiyar littattafai, da tsoffin akwatinan karfe daga gani tsohuwar ajiya ce, ga wardrobe mai girma ta jikin bango, wurga idanu tayi kan tukwanan kasa da ta gani girke a kasa, ɗaya saman ɗaya an jera su daurin ɗaurin sunyi sauro a jikin bangon da suke, hada kwaryaye rufe da faifan su, hada tukwanan furanni masu ban sha'awa daga gani koma wanene mamallakin ɗakin ma'abocin son kayan laka ne ko kuma makerin su ne.

A hankali ta ɗauke idanunta daga kan tukwanan ta bi bangon dakin da kallo, zanunnuka ta gani masu ban sha'awa, a hankali take tafiya tana nufar tsakar dakin tana cigaba da kallon abun mamaki da al'ajabi gami da rudani ita dai batasan waya kawota cikin shi ba! Ta manta komai.

tana cikin jujjuya idanu karaf ta hango Madubi zagayayye yana da mariƙi dake ajiye kasa...takawa tayi cike da fargaba ta nufi madubin yayin da zuciyarta ke cigaba da harbawa da karfi da karfi..tsayawa tayi agaban madubin tana kallon fuskarta, ta tsorata da ganin ramar da tayi, kashin wuyanta ya kwambare kamar zai fasa fatarta, ziraran yatsun hannunta ta daura akan wuyan tana shafa kashin kafin ta motsa yatsun a hankali ta shafa fuskarta, manyan idanunta dara dara launin brown ta zare su tana bin kanta da kallo, tana iya hangen dukiyar fulaninta sun rame sun kanjame bayan ada ba haka take ba, tana da kira irin ta karfafan mata masu jini ajika amma yanzu ta rame ta bushe ta faɗa kamar ba ita ba.

da zata iya tuna mummunan abunda ya faru da ita har zuciya zata iya hadiya ta mutu saboda tana da fusatacciyar zuciya, idan ta rikice babu mai iya sarrafa ta.
Chapter 129 · 0% Book details