← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 238

Sashe 88

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Shurem muje ko"? Alhaji ubaid ne yayi mashi maganar, Sam baya son tafiya, Gani Yake kamar in ya tafi wani abu zai faru da benazir,
"Toh daddy" Yayi maganar, Tare da ruko hannun hajiya layla
"Mommy, nasan ko ban fada maki ba, zaki kula da ita, amma inaso ki sanya ido sosai, dole sai kin hana idonki bacci in ba haka ba..." bai kare maganar Ba Alhaji ubaid Yace"meyasa kace haka"?
"Daddy akwai wani abu da nake zargi akan benazir, zan sanar daku amma ba yanzu ba, saboda bana son ɗaga maku hankali, kawai abinda nakeso mommy kada kiyi gangancin kula da ita, in ba haka ba za'a iya samun matsala, duk da munsan Allah ke tsare bawansa amma da bukatar muma mu kula"
Hankali atashe Hajiya Layla ke kallon shi, Muryarta na rawa tace"Shureim dan Allah ka fada min meke shirin faruwa da Benazir dina, ni dama najima ina zargin akwai wanda ke bibiyar rayuwarta, so ake akashe min ita, ko faduwar da tayi a toilet sai da raina ya bani wani mugun abunne Ya faru da ita, in ba haka ba taya za'ace ta fita hayyacin ta? Bata gane kowa dake akanta?..." maganganunsu sunso rikita Alhaji ubaid Ya rasa gane inda zancen su Ya dosa
"Dan Allah kuyi min bayani meke faru ne"?
Da ido Hajiya layla tayi ma dr shureim Alamar yayi shiru saboda tana zargin ba hakanan Aka kyale Alhaji ubaid ba, kada su saki baki su sanar da shi zargin da suke Yi Yana iya zuwa ya sanar ma Alhaji musa, tunda Ya zama kamar ubansa komai zaiyi sai ya nemi shawarar shi
Jinjina kai dr shureim yayi alamar Ya fahimce ta,
"Daddy, Muje gida zan sanar da kai komai" Ya faɗa tare da ruko hannun shi, Hajiya layla tayi masu Allah Ya kiyaye hanya, tana atsaye tana kallon motarsu har suka fuce daga hospital din,
Da sauri ta koma ɗakin benazir, tana shiga, ta iske Nurse agaban gadon ga benazir zaune jikin ta sai kerma Yake tana ta sambatu
"Daddy, mommy, ku kira min taj, Ya kawo min babayna dana bar mashi, dan Allah ku bani ƴata, kada na mutu ban ganta ba...." lallashinta hajiya layla ta cigaba da yi sam bata fahimtar komai, sunan ƴarta da mijinta kadai take ambato,
Har abinci nurse ta kawo mata, kwata kwata ta kasa cin shi, duk yadda mami takaiga lallashinta abun Ya faskara, Addu'oi ta koma tana tofa mata, har dare Ya tsala mami tana zaune kan kujera tana kallon ta, Har dr ya shigo ya kara duba jikinta, Ya bata magungunanta dakyar suka samu ta sha, daga bisani bacci Yayi awon gaba da ita, lokacin da aka fara kiraye kirayen sallar ishai'a, mami ta shiga toilet cike da zullumin kada wani ya shigo dakin Ya cutar da benazir, saboda ta razana da jin kalaman dr shureim, jin motsin mutun adakin yasa tayi wuff ta bangaje kofar toilet din ta fito tana haki, Ko alwalar bata karasa ba..

*Daga alkalamin Boss Bature mu haɗu next page✍️*

*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne dukanshi za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*
[14/10, 6:05 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: Y

Home
Kurkukun Kaddara
Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 29 Complete
by
Novels Elite Admin
August 07, 2024
Sponsored Link

Novels Elite English
✍️

Dafe kirji tayi tare da sauke ajiyar zuciya, ganin likitan dake kula da benazir ne

"Are you okey"? Daga mashi kai tayi alamar eh,

Ganin tana mashi kallon kamar bata yarda da shi bane yasa shi cewa"zan tashi daga aikine, Na shigo na kara duba lafiyarta ne, kafin na tafi...." murmushin Yaƙe ta sakar mashi"mungode dr, Allah Ya saka da alkhairi, agaida gida" ya amsa mata da toh, harya fuce daga dakin Yana mai mamakin Hajiya layla, abun ya daure masa kai yadda ta fito daga toilet a haukace anya kuwa tana da lafiya"?

Komawa cikin toilet din tayi, sam babu nutsuwa atare da ita, shaf shaf ta ƙarasa alwalar ta fito da sauri ta nufi closet din dakin ta dauko darduma ta shimfiɗa tare da kabbara sallah.

Da zarar taji motsi adakin sai gabanta Ya faɗi, bayan ta ida sallar, ta zauna tayi addu'o'i ta kai kukanta wurin Allah,

Kafin ta mike ta koma kan chair din dake fuskantar gadon benazir ta zauna tana kallon ta, patient gown din dake ajikinta launin light blue tayi mata kyau, A hankali ta kai hannu ta shafa gefen fuskarta, tuni taji ƙwalla sun cika idanunta.

Idan muka koma bangaren su Aneelerh, bayan komawarsu gida, A falo suka zauna kowa Yana jimamin halin da Benazir take a ciki, Ummi ta fito daga daki hannunta dauke da Baby junaid bawan Allah tunda Mahboob ya dauko shi daga makaranta, Ya dinga kuka Yana ambaton mommynsa, dakyar mami ta samu ta shawo kanshi Har yaci abinci tayi mashi wanka, har bacci Yayi, sauke shi ummi tayi da gudu Ya nufi Aneelerh ya faɗa jikinta Yana kuka, Ta rungune shi tana lallashin shi, dakyar ta shawo kanshi har suka sasanta junansu...

Lokacin da hajiya sara ta shiga falon gidan, kasa yin sallama tayi saboda fargaban hukuncin da Alhaji musa zaiyi mata, Cikin sanɗa ta nufi bedroom din su ko sallama batayi ba, ta shiga ciki,

A kwance ta same shi kan shimfiɗeɗan gadon shi, Ya tada kanshi bisa pillow, zeenatu na arungume da shi, ta daura kanta bisa kirjinsa, daga ita har shi kayan bacci ne a jikin su

Tayi tsammani bacci suke Yi, ajiyar zuciya ta sauke, ta lalla6e ta nufi cikin dakin, ta daura key dinta akan mirror, ta nufi toilet ta shiga, alwala tayo tana kokarin fitowa daga toilet din suka ci karo da shi, wani irin bugu kirjin ta yayi, tuni gumi ya lullu6e fuskarta, la66anta na kerma tace"yanzu na shigo, nayi tunanin bacci kake Yi, fatan na same ka lafiya..." tsare ta da idanunsa yayi masu matukar gigitata, gaba daya yayi mata kwarjini

"Ki faɗa min wani hukunci Ya dace Inyi maki"! Rass taji gabanta Ya fadi, marairaice mashi fuska tayi"am sorry bazan ƙara ba, wallahi bansan na ɗaga maka murya ba, dan Allah Ka yafe min.."

Fuskarshi babu annuri Ya furta"cewa nayi ki fada min wani hukun ci Ya dace nayi maki"?

Shiru tayi batare da ta furta kalma ba, duk tasha jinin jikinta....fargabanta kada Yace zai turata U.s

Saboda bata son duk wani abu da zai rabata da shi, shiyasa take yi mashi biyayya sau da kafa, duk wani abu da tasan zai bata masa rai, tana kokarin ganin tayi takatsantsan da shi

"Daddy kayi mata hakuri tun da ta gane kuskuranta," muryar zeenatu ce ta ratsa kunnuwansu,

"Kinci sa'a, da yau sai kin yaba ma aya zakin ta" nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke, har zata wuce ya sake shan gabanta, a rude ta kalle shi

"Ya jikin benazir din?

"Jikin nata yayi tsauri, kwata kwata bata a hayyacin ta, baiwar Allah tana jin jiki"

"Allah Ya bata lafiya, in sha Allah gobe da safe zanje dubata" har cikin ranta taji dadin jin zaije dubata,

"Allah ya kaimu lafiya.."

"Kije kiyi sallar, kafin kin kammala zan kira tani ta shirya maki dinner dinki, nasan kina jin yunwa, kin wuni baki ciki komai ba" ya fada tare dakai hannu Ya shafa flat tommy dinta, aruɗe hajiya sarah take kallon shi, kamar ba Alhaji musa ba,yadda kasan badaga bakinshi kalaman suke fitowa ba,

Kamar sakarya haka ta kura mashi ido tana kallon shi, murmushin gefen fuska ya sakar mata, gaba daya ya nemi zautar da ita, dakyar ta samu nutsuwar sanya hijabi ta kabbara sallah,......"

Sallamar su Alhanji ubaid ce ta karaɗe kunnuwansu, da gudu Zeenatu ta diro daga kan gado ta fuce kamar walkiya, tunkafin ta karaso dr shuriem Ya hangota, murmushi ya saki tare da bude mata hannayenshi ta faɗa kan kirjinshi tana dariya

"Yaya shureim sannu da dawowa, naji dadin ganinka, dama ina ta zullumin kada kaki dawowa gida.." bata ƙare maganarba, Alhani ubaid Yayi mata gyaran murya, waro idanu tayi don gaba daya ta manta da shi awurin cike da jin kunyarshi ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta

Dariya Alhani ubaid Yayi"zeenatu, meya hanaki yin bacci..." muryarta da yar shagwa6a tace"yaya shureim nake jira ya dawo..." kafin ta kare maganar Alhaji musa Ya shigo falon Ya nufe su cikin takun nan nasa na isa

"Sannunku da dawowa, ya mai jikin"?

Alhaji ubaid Yace"da sauki, kafin mu dawo ta farka sai dai bata ahayyacin ta...." cikin nuna tausayawa ya furta"Allah Ya bata lafiya, gobe zanje asibitin, Ina Hajiya laylan ne"?

Dr.shureim yace acan zata kwana" shiru yayi bai ce komai ba.

wani abu daya daurewa dr shureim kai tun da ya dawo gidan zeenatu bata tambaye shi Ya jikin benazir ba, kwata kwata kamar irin ta manta da zancen ta, bayan tafi kowa nuna damuwa akanta, har magana yayi mata banji kin tambayin auntynki benazir ba, sai tayi shiru bata tanka mashi ba kamar bataji me yace ba, kusan sau uku yanayi mata maganar tana share shi, amma idan yayi mata wata maganar daban saita amsa mashi.

Bayan shigar shi daki, kasa runtsawa yayi, har saida Ya kira mommynsu a waya ya tambayeta awani hali suke ciki? Ta tabbatar masa da komai lafiya kafin ya samu nutsuwar Yin bacci.

*EX-PRISONERS*

Around ƙarfe 10 na dare, ummi ta sauko down, har ta shirya cikin kayan baccin ta,

Tunkafin Ta karasa Ta hango wasu daga cikin su kwance ka lallausar carpet din falon suna bacci, tun da zu tabarsu suna ta shan fira atsakaninsu tayi tunanin in sun gama zasuje su kwanta sai kuma ta taras da su kwance suna sharar bacci, wasu asaman sofas wasu akan carpet

Murmushi tasaki haɗi da girgiza kanta, tama rasa tayaya zata fara tada su,duk sun sanya kayan baccin su..., ɗaya bayan ɗaya ta fara farkar da su

"Batool My baby, wake up, Parveen! Hannah ku tashi dan Allah....! Ni bansan ya akai kuka bari bacci Ya dauke ku a falo ba, salon kawai ku wahalar da auntyn naku..." dakyar ta samu batool ta miƙe tana ƴan soshe soshe

"Wuce kije daki" ta amsa mata da toh,
Chapter 88 · 0% Book details