Sashe 18
Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read
Idan muka koma cikin hall ɗin kuwa sai dai muce masha Allah, Zahra world of beauty interior designers sun baje basirar su wurin ƙawata cikin ɗakin taron, wasu haddun dinner tables ne rukuni rukuni a kalla sun kai set hamsin kowani table yana a kewaye da rantsastsun kujeru masu nunfashi zubin bean bag chairs, daga kan kowani table an ƙawata shi da Centerpiece wanda ya kunshi Glass candle sticks An kunna wutar su gawanin ban sha'awa a kewaye da containers na furanni launuka daban daban, ga wasu jerin Crystal glasses ƴan uban su masu ɗaukar ido, bayan su kuma akwai Silverware and napkins with table ware a kowani dinner table hada menu card ajiye bisa tables din, komai fa ya tsaru ga wasu Crystal Sparkling chandiliers masu haskaka tsakiyar ɗakin taron da wani irin twinkling lights hakan baƙaramin ƙawata ɗakin taron yayi ba, ga wata ni'ima dake kurɗaɗowa ta cikin na'urorin A.c mai ratsa sassan jikin mutun, idan muka koma 6angaren abun da za'aci hohoho duniyar dadi wato daga can 6angare guda dinner buffet ne jerin nau'ikan abincine da aka killace su a cikin chafing dishes wato wani irin aroma ne ke tashi na daddaɗan kamshin abinci mai cika makoshi, ga jerin large glass bowls na kayan marmari da zungura zunguren glasses na Juice masu sanyi komai fa an tanada, babu ce kadai ke babu a dakin taron, anyi 6arin dollar, naira kuwa ta raina kanta a wurin, dukiyace aka narkar wurin ƙawata ko'ina, idan kuwa nace zan fayyace komai dake a hall din tabbas zamu ƙare takun karshe ne wurin kwatanta haduwarshi shiyasa na takaita da bayani don mu shiga kaitsaye cikin taron.
Sannu a hankali danƙara danƙaran motocin su na alfarma zubin Mercedes benz S. Class suka soma shararowa izuwa cikin garden din a jere suke tafiya yayin da jami'an sojojin dake take masu baya suke bin motocin da kafafuwansu suke tafiya gefe da gefen su, hannayen su ruƙe da jibga jibgan bindigu ga wasu kuma soke a qugunansu sai faman mazurai su ke yi, tamkar a filin daga.
Ƙarasowar motocin ke da wuya A hanzarce Sojojin suka buɗe back seat na motar farko, A hankali sheikha mujeedat ta zuro kafarta dake asanye cikin hadaddun takalman alfarma wadanda kudinsu kadai ya ishi wani talakan jari, kafin ta ƙarasa fitowa tabarakallahu ahsanun khalikin gaba ɗaya sojojin dake a wurin saida suka saki baki kamar lehen sakarai saboda tsabar kallon ta a fakaice.
Embellished abaya ce a jikinta launin royal blue anyi mata adon stones work, fuskarta tana asanye da Gold chain mask, adon dake akan fuskarta kaɗai abun kallo ne, tayi masifar haduwa, daga ƙasa har sama ta ca6a ado nasu na sarauta tamkar ɗawisu a fagen haɗuwa, bata jima da fitowa ba, jami'an suka budewa Prime minister hateem other side din motar ya fito tamkar tauraro a cikin taurari yayi shiga na mutunci, hadaddiyar shadda ce a jikin shi gezna launin blue anyi amshi senator style abun ka ga dogon namiji ga kira kayan sun zauna mashi kamar a jikin shi aka dinka su, wata expensive watch ce a hannunsa sai kyalli take tana daukar ido, Yatsun hannunsa na sanye da zoben azurfa mai shegen kyau, sumar kannan tashi tasha gyara har ta gaji da haduwa,
Bayan fitowarsu motar dake abayansu tasu Yazrin da Nazli ce, Lokacin da suka fito Kiris Ya rage zuciyoyin wasu su buga saboda tsabar haduwar wankan dasuka dauka na emirati abaya launin Silver, kowaccensu ta manna glasses a idanuwanta, ga adon gold knucles rings dake a yatsun hannayensu, sun yi rolling veils a kansu yadda kasan asace su saboda kyau.
Bayan fitowar su Nazli, sojojin suka cigaba da buɗe ma sauran motocinsu, gaba ɗaya zaratan samarin family din maza da iyayensu ankon shadda gezna su ka yi, matasan ƴan matan kuwa arab abaya suka sanya masu kyau da tsada na alfarma na kuma kece raini da fita tsara, wasu sun sanya lace abaya, wasu embellished abaya wasu open front abaya, wasu kaftan abaya, wasu egyptian abaya kowa da kalar nashi wankan, kowaccen su tayi lagin gyale akanta, wasu ma babu gyalen zallar sumar kansu ce har gadon baya kamar indiyawa, duk wadda ka kalli wuyanta zaka ganshi manne da ziririyar sarka ta diamond wasu kuma ta zinari, gayu mutanan Allah, Hajiya saratu fa ta dauki kur adakanta rantsastsiyar dubai abaya ce a jikinta tsadaddar gaske launin maroon rigar harta gaji da haduwa abunka ga manyan mata masu dirin jiki kayan sun ladabtu a jikin su kamar donsu aka kera su, kwansu da kwarkwatansu suka jera izuwa cikin hall din, iyayen su maza kowannansu yana ruke da hannun matarshi, wani irin daddaɗan sautin kiɗe kiɗe da raye raye ne ya karaɗe ko'ina na ɗakin taron, Hada wani irin busa tamkar na sarewa Suna tafiya suna taka rawar dattako, cikin nishadi da raha, fuskokinsu dauke da annurin farin ciki da annushuwa.
Prime minister Hateem ne yafara shiga hannun shi ruƙe dana gimbiya mujeedat, daga bayan su Nazli da Yazrin ne, bayan su sai Mai girma sharafuddeen shima ya shiga hannun shi ruƙe dana gimbiya malikat, ɗayan hannun nashi ya ruƙo hannun uwargidansa Hajiya laurat daga bayan su Chief Owais ne wanda zan iya cewa shine farkon haduwa saboda kyawun surar shi, Shaddar jikin shi ta bayyana zazzafan kyanshi kamar shi ya ƙera kanshi, hannun shi yana a ruƙe dana kanwarshi Hindu itama ta dauki wankan abaya.
Bayan wucewarsu Sir mubarak Ya shigo hannun shi ruke dana Mom turai, daga bayan su Zaki ne tare dr Jazz sai Ibad.
Fuskar kowan nan su da fara'a, bayan shigarsu Senate lateef ya shigo shima tare da Mom madina hannun su ruƙe dana juna, Yayin da zulaihat da Ziyad suke abiye da bayan su.
Abun gwanin ban sha'awa, bayan suma sun shiga His excellency abdul Razak ya shigo tare da her excellency Muhibbat, suma sun dauki nasu wankan, atare da ya'yan su suka shigo Captain Yaseer da Yusra.
Daga su sai His excellency Deen Ya shigo fuskar nan awashe da annuri yayin da yake a ruƙe da hannun her excellency Hajiya Jameela, daga bayan su Dr nawaz ne da ɗan uwansa justice Nadeem sun dauki nasu adon.
Basu jima da wucewa ba, Hajiya saratu tamu ta mutunci ta shigo hannunta ruƙe dana Pravin sunyi matuƙar haɗuwa abunka ga ba'indiye shaddar tayi mashi kyau.
Daga bayan su Twins ne zayn da zayn wohoho wanka Yabi jiki, na madina masu kamshin zamzam tsayawa fasalta kawunsu a cikin shadda 6ata baki ne, Hannayensu na ruƙe dana kanwarsu Faryat, ta ca6a uban ado ciki riga red colour duk matasan wurin babu wadda tayi shigar fitsara irinta, abayar jikinta ta matse kirjinta, ko arziƙin ɗan kwalli babu akanta sai zallar kitson kalabarta, gaba dayan ƙamshin turaren su ya gauraya da na iskar A.c wata irin ni'ima ke tasowa.
Har sun nufi inda aka tanadar masu kowa ya nannaɗe rigarsa zai zauna, kamar daga sama muryar Mc ta katse su da cewa"ban bada iznin a zauna ba"! Gaba ɗaya suka kai idanunsu gare shi don ganin wani isasshen ne mai walkin Sa, Ruke yake da mic can saman step fuskar nan ta shi a murtuke tsoro tukuf da shi, gashin kanshi duk hurhura hatta jagirarsa da gashin bakin shi hurhurar ce ga wani dogon gemu har kan cikin sa, daga ganinsa ɗan drama ne, ganin shi bakuwar fuska yasa suka soma tunanin wanene wannan?
Hajiya saratu har ta fara karkata baki zata fara zabga mashi masifa muryarshi ta katse mata hanzarinta
Kirari ya soma korowa yana nuna hanyar shigowa hall din da mic din hannun shi, gaba ɗaya suka kai idanunsu don ganin mai shigowa Obinna ne Ya shigo Cikin shiga ta alfarma tare da Babban amininsa Jan kunne.
Lokaci ɗaya suka sauke ajiyar zuciya, tare da sakin murmushi, saboda jin yadda ake yabon mahaifinsu bayan mc din yagama da baba obie Ya koma kan prime minister ya soma koɗa shi yana fadin.
_Tsakin tama gagara tauna Prime minister Hateem Obinna, Shugaba mai cikakken iko, na Mujeedat ba maza a gabanka. Kasar Canada taka ce, Namijin duniya Taka lafiya, hasken wata sha kallo, fari mai farar aniya, adalin shugaba namu na mutun ci_
sautin tafin hannayensu ne ya cika hall din.
Mc din Yaci gaba da yi ma su kirari ɗaya bayan ɗaya
"Ina kike 'yar sarki jikar sarki, basarakiya 'yar mun gada, uwar gida sarautar mata, sarauniya ɗaya tak dake mulkar zuciyar hateem, Damisa ki sabo, Sheikha Mujeedat Al Maktoum, Dubai da kewayenta ikonku ne. Damisa kike, kin ki kallo biyu. An gaishe ki uwar Nazli da Yazrin, ku ne yau ku ne gobe, har kullum ku ne. Sukari kuke ba ku yi farin banza ba.....' yayin da yake yi masu kirarin murmushine dauke akan fuskar Mujeedat, duk da kasancewar bata jin hausa prime minister hateem ne ke fassara mata abunda mc din Yake fadi hakan ba karamin dadi yayi mata ba
Bayan ya gama koɗa Su gimbiya mujeedat Ya koma kan sauran Iyayen family din yaci gaba da cewa.
_Ina ka ke, Sanata Lateef, fari mai farar aniyya, ina ka gane mini His excellency Abdul Razak, farin wata mai haske duniya. Ban manta da kai ba, His excellency Deen, na Hateem. Ku garafa ga manya nan, Soja birgimar hankaka, Sir Mubarak, Soja marmari daga nesa. Soja na gwamna ga rawa ga yaki_
gaba ɗaya filin taron Ya karaɗe da sowarsu, Sir mubarak dai murmushine dauke akan fuskarshi bashi ba hatta mom turai taji dadin yabon da akayiwa mijinta.
_ina kake Sharafuddeen, Namijin duniya, An buga dakai an barka, Namijin uban maza, kaga adalin shugaba, nigeria taku ce ciki da wajen ta, Ban manta da ke ba, auta shalele, Hajiya Saratu. Auta ba kya laifi ko kin kashe dan masu gida. Bushiya kike kowa ya kwana da ke ya kwana salati._
Ƙasa ƙasa da murya hajiya saratu tace"lallaima dattijon nan! ya raina min wayau, wato ya rasa dame zai koɗa ni sai da bushiya"? Ta6e baki tayi babu yabo babu fallasa taja guntun tsoki, Ita da ba'ay mata gwanin ta.
Cikin mutunta juna suke ƙara gaisawa da junansu ga sautin kiɗa na tashi, sun ɗan jima atsaitsaye suna ta fira cikin raha kafin daga bisani kowa ya samu wuri tare da Iyalansa, gaba ɗaya suka natsu suna sauraron mc