← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 238

Sashe 41

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Har yanzu ban fahimci inda zancenka ya dosa ba .." murmushi muhsin yayi kafin yaci gaba da cewa"su ɗin jami'an hukumar ISOD ne, nasan ba zaka rasa sanin CHIEF OWAIS ba, ɗan gidan Sharafudeen Obinna......" wani irin al'ajabi ne ya kama tajudden muryarshi na rawa ya maimaita sunan Chief Owais da tsantsar mamaki yace"muhsin dagaske kake min ko wasa? Tayaya akai ma su kasan da zamana"

Kafin muhsin Ya bashi amsar tambayarshi, Chief owais Ya shigo bakin shi dauke da sallama cikin shiga ta kakin isod, da sauri matasan nan suka buga kafa tare da sara mashi, muhsin kamar zaiyi mashi sujjada tsabar yadda yake washe baki yana yi mashi sannu da zuwa yalla6ai, shi dai taj ya gaza yarda da abunda idanunsa suke gane mashi, kai ko a mafarki bai ta6a tsammanin zai haɗu da chief owais ba, mutumin da a tv kadai yake iya ganinsa, sai gashi yau a zahiri Allah Ya nuna masa shi.

Cike da qasaita, Chief Ya nuna masa sofa alamar Ya zauna" jiki na 6ari taj yaje ya zauna yana ta faman bin shi da kallo a lokacin shima ya zauna kan sofa din dake fuskantar ta shi.

Cikin harshen turanci yace"nasan zaiyi wuya ace baka sanni ba, amma duk da haka zan gabatar maka da kaina, da farko sunana owais sharafudeen Obinna, chief na hukumar Isod...." ya faɗa tare da ɗan dakatawa yana dubansa, tun anan taj ya fahimci ba karamin mutunne bane mai ji da kansa.

"Malam taj, kamar yadda kake mamakin ganina nima haka nake mamakin kasantuwana acikin rayuwarka, ko a mafarki ban ta6a tsammanin akwai ranar da zan hana idona bacci saboda damuwa da mutumin da bansan wanene shi ba...." kalaman chief owais sun girgiza shi matuƙa, har dai ya gaza jure wa yace"dan Allah ka fadamin meyasa ka damu dani bayan baka sanni ba"

da buɗar bakinsa sai cewa yai"ƴarka ce sila" waro idanu waje taj yayi da tsantsar mamaki yake binsa da kallo fuskarsa da rudani yace"meyasa kace haka"?

Numfasawa yayi kafin ya soma magana muryarshi tamkar ana busa sarewa saboda dadin sauraranta....

A washe garin ranar dana dawo Nigeria daga U.S anyi min wani kira da ya tsaya min araina....

Fitowa yayi daga cikin bathroom waist dinsa daure da towel, yayin da dayan hannunsa ke a ruke da wani short towel yana tsane sumar kanshi, a gaban dressing mirror ya tsaya da niyar ya gyara jikin shi, wayarsa dake akan nightstand ta soma ringing, dakatawa yayi da tsane sumar kan da yakeyi a hankali ya nufi wayar ya dauko ta yana duba number din da aka kirasa da ita, yayi mamakin ganin bakuwar number, A matsayin shi na jami'in sirri komai nasu asirrince suke yin shi, harta phone number dinsa special ce, bakowa yasan shi da ita ba, sai mutun yakai yake samun damar mallakar ta, bai yi niyar picking call din ba saboda a ka'idarsa baya ɗaga bakuwar number, ko kiransa akayi indai ba family dinsa bane to baya picking sai anfara neman iznin yin magana da shi......

Amma a lokaci sai zuciyarsa ta kwallafa rai akan son sanin wanene ke kiransa...

Baisan sa'adda Ya danna answer call ba, ko da yai picking ya kara phone din a kunnansa shiru yayi baice komai ba tsabar miskilancinsa jira yake yaji wani isasshen ne ya kira shi batare da iznin shi ba.

Lamarin ya daure masa kai jin anyi shiru ba'ayi mashi magana ba, ko wanene wannan mai karfin halin? Har zaiyi rejecting call din sai kuma Ya fasa calmly ya furta "who is on the line"?

Sautin muryar karamar yarinya yaji ta ratsa kunnansa "Angel ce,"

Yayi mamakin jin muryar karamar yarinya, aransa ya ayyana ko yar wacece ta kirasa,

"kinsan dawa kike magana"?

"a'a," ta bashi amsa atakaice

"Ur age"?

"7yrs" voice ɗin shi da alamun mamaki ya maimaita"7yrs? ina mai wayar yake'?

"Daddyna ne, ya tafi masallaci ni kaɗai ce agidan, shine na hada numbobi na kira don in gaisa da mutanan duniya"

Murmushin gefen fuska yadan saki har dimple dinsa ya lotsa, don ya fahimci ba'asan ta dauki wayar ba, tun daga kan muryarta ya gane irin yaran nan ne masu tsiwa

"Can i call u video"?

Da sauri tace eh,

Nan take ya mayar da kiran Video call, da sauri ya sanya yatsan hannunsa ya rufe front camera din wayar saboda baison taga fuskarshi, baisan ko tarko aka ɗana masa da ita ba, lokacin da fuskar Angel ta bayyana akan faskeken screen din wayarsa wani irin bugu zuciyarsa tayi, bai yi tsammanin zai ganta kyakkyawa ba, fara sol ga manyan idanu launin gray dara dara da su, gaba ɗaya ya kasa kyafta idanunsa daka kallon fuskar ta, a sukwane ya koma gefen gadon shi ya zauna yana ci gaba da kallon ta...

"I can't see u" ta yi maganar tana faman gwale masa ido, murmushi yasaki yana kallon ƙananun la66anta tausasan gaske launin pink, chief Ya shagala da kallonta, tamkar a mafarki yake bin fuskarta da kallon ƙurulla kamar zai haɗiyeta, A can 6angaran Angel taji shiru ba'ayi mata magana ba, a tunaninta rashin network ne, yasa bata ganin shi a video din, batasan cewa shine ya toshe front camera din wayarsa don kada tagansa, da sauri yayi screenshort din fuskarta ba tare da sanin ta ba...

Zuciyarsa ba ƙaramin sosuwa tayi ba, ganin tayi rejecting call din, sam bai gaji da kallonta ba, da wata irin kasala ya kwantar da kansa bisa pillow, Ya bude hotonta yaci gaba da kallon fuskarta....

Baiyi tunanin kiran layin ba, haka ya wuni da tunaninta aranshi, tsawon kwana uku baya iya bacci batare daya kalli hoton fuskarta ba, sometimes a rungume da wayarsa yake kwana, sai da takaiga harta daddynsa da mommynsa sunsan da hoton yarinyar daya kwallafa rai akai, mahafinsa ne Ya bashi shawarar Ya nemo ta idan hakan zai kwantar masa da hankalinsa, Ya ji dadin shawarar daddynsa, maimakon ya tuntu6i layin tajuddeen kaitsaye su yi magana da shi, sai ya fara bincike ta hanyar amfani da phone number din da Angel ta kira da shi, anan ya sami bayanan taj hada shafukansa na social media da yake amfani da su wurin yaɗa aikinsu na ƴan jarida, cikin sa'a ya gano address din gidan radion da taj yake aiki, bai samu damar zuwa joss ba saboda kiran gaggawa da akayi masa tafiya ce ta kama shi zai bar kasar ba don yaso ba.

Gaba ɗaya ya tattara komai ya damka a hannun Big guy, wanda ya kasance ɗaya daga cikin na hannun damansa, amintattunsa, Ya fada masa komai dangane da yarinyar data kirasa a wayar sannan yace mashi yana son yaje har can joss din Ya bincika mashi inda suke rayuwa, saboda yana son sanin komai dangane da ita........

Atakaice big guy shine mutumin da ya siya ma angel piano da kayan zane, a ranar da sukaje kasuwa da su taj ta sanya masu rigima sai ansiya mata su gashi basu da kudi, ashe shine ke bi biyarsu duk wani motsinsu akan idanunsa, chief shine ya bada umarnin komai suke bukata yayi masu shi sannan bayaso su san cewa shine yake bibiyarsu har zuwa lokacin da zai dawo kasar.

Duk wani abu da unaisah tayi sai big guy ya turama Cheif ta wayarshi, hakan ba karamin dadi yake yi mashi ba ....

Kafin chief ya dawo Nigeria wannan tsautsayin ya ritsa da su tajuddeen wanda yayi silar 6acewarsu, hankalin big guy ba karamin tashi yayi ba, lokacin da labarin ya riske shi, har sai da yaji fargaban sanar da chief saboda yasan yadda ya ƙwalla fa rai akan kaunar yarinyar, gashi saura kwanaki kalilan ya rage mashi ya shigo nigeria, Yaci burin haduwa da ita tare da mahaifinta, Allah bai nufa ba . ...

Dakyar Big guy ya sanar da shi abunda ke faruwa na 6acewarsu, tsabar tashin hankalin daya fuskanta na jin mummunan labarin har zazza6i sai da yayi, duk da haka bai karaya ba, yabar komai nashi, ya dawo nigeria bai sauka a abuja ba, kaitsaye ya sauka a joss, big guy ne yaje tarbo su a airport, tare da jami'ansu dayazo da su...

A katafaren gidan da big guy din yake da zama suka sauka, dama chief ne ya biya kudin gidan a lokacin daya tura shi neman gidan su Angel.

Kwana uku da zaman su agidan kafin suka fara nasu binciken, basu tsaya bata lokaci ba suka nemi alfarmar Inspector General of CID da ya damka masu case din su tajudeen a hannun su, tuni suka amince masu saboda sunsan hukumarsu ta musammance, duk wasu bayanai nasu tajudeen saida suka tura ma chief hada makullan gidajensu da suka kar6a.

Muhsin yana ɗaya daga cikin wadanda jami'an isod suka tuntu6a har gida suka kai mashi ziyara don jin cewa shi ɗayane daga cikin aminnan tajuddeen bayan sunyi mashi tambayoyi ya amsa masu wanda ya sani sai kuma sukace mashi ko bayan tafiyarsu idan yaji ɗuriyar tajudeen ko abokinsa uzair yayi gaggawar sanar da su, saboda sunsan zasu iya tuntubarsa tun da shi amininsu ne, contact dinsu suka bashi kafin sukayi mashi sallama kun ji yadda akai har muhsin ya samu damar sanar da jami'an isod zancen zuwan tajuddeen ba tare da shi taj din Ya sani ba, saboda ya fahimci baya son kowa yasan da zamansa, shiyasa bai sanar da shi dangane da jami'an isod dake nemansa ba...

Bayan chief owais ya kammala bashi labarin, saukko yayi daga kan sofa din Ya zube saman gwiwowinsa hawaye nata sintiri akan fuskarshi cikin sanyin murya yace"dama angel itace silar da kasan da zamana"? Muryarsa na rawa ya furta maganar, baisan sa'adda ya fashe da kuka ba, dama zuciyarsa a raunace take,

"Allah sarki angel, ashe da rabon wata rana rashin jin ki ya yi min amfani...." kasa karasa maganar yayi,
Chapter 41 · 0% Book details