← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 238

Sashe 120

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Eh, bakaken aljanune a jikin ta, sune suka haddasa mata ciwon..." waro idanu waje su hajjaty sukayi wani irin tsorone Ya kamasu murya na rawa abla tace"dama Aljanu suna iya canza ma mutun halittar shi" jinjina mata kai sheikh imam yayi"fiye da haka ma zasu iyayi.." kallon kallo suka jefawa junansu.

Aruɗe baba obie ya furta"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un!

Zuƙunnawa sheikh imam yayi daga gaban katifar marwa idanun shi akan fuskarta Ya soma magana"kada ki sanya damuwa aranki, Allah yana atare dakai, duk wani abu da kika ga ya faru dake mukaddarine daga Allah, bana so ki kuntata kanki, ko ki ƙyamaci kanki, balle kiyi tunanin illata kanki saboda wannan lalurar data same ki, kiyi kokarin cinye jarabawarki kada ki gaza, Aljanun da suka haddasa maki ciwon nan suma bayin Allah ne, babu abunda ya fi karfin mahaliccin mu...." tun da ya fara magana idanun marwa suka cicciko tab da kwalla ita kadai tasan me take kitsawa aranta.

"nayi alƙawarin zan taimaka maki amma fa dole sai kema kin taimaki kanki, kiyi kokarin bin abun da Allah da Manzonsa sukace ayi domin samun kariya daga sharrin su, da zuciya ɗaya in sha Allah zaki ji sauƙi, jikinki zai dawo kamar yadda kike ada" jinjina mashi kai tayi alamar ta gamsu da maganar shi.

"Ma.. malam muma ataimaka mana dan Allah, ka faɗa mana hanyoyin da zamu kare kan mu daga sharrin su"

cikin shesshekar kuka abla tayi maganar.

murmushi sheikh imam yayi tare da kallonsu ɗaya bayan daya sai yaji sun bashi tausayi ganin yadda jikinsu ke ta kerma kamar mazari

"Ku samu wuri ku zauna zanyi maku bayani" da sauri suka kewaye sheikh imam suka zauna kan ƙasa suna jiran jin me zaice.

Miƙewa yayi da sauri ya ɗauko kujerar mirror Ya ajiye agaban baba obie don ya zauna.

"Nagode sheikh" ya fada tare da zama kan kujeran.

Tun shugowar pravin dakin sheikh imam bai ɗaga ido Ya kalle shi ba, sarai ya san da zaman shi, dama tunfil azal basa jituwa tsakanin su ko gaisuwa bata ta6a haɗasu ba,

Shiru yayi kamar akwai abunda Ya hana shi fara magana, wayar pravin ce ta fara ringing daga cikin aljihunsa da sauri ya fuce daga dakin don ya amsa kira.

Fitar shi keda wuya sheikh Imam Ya fara magana yana duban marwa cikin tattausa harshe yace mata"kiji tsoron Allah! Rass gabanta Ya fadi, su hajjaty suka kalle shi da alamun rudani akan fuskokin su.

"Idan akwai wani abu da kike aikatawa badai dai ba to ki daina! Sau dayawa mu muke ja ma kanmu shiga cikin masifa, Allah ya gatanta mu ya bamu hanyoyi da dama da zamu iya ba kanmu kariya amma muna wasa damar mu...." ga dukkan alamu Sheikh imam Ya canza maganar daya dauko da farko hannunka mai sanda yayi mata kuma ta fahimce shi hakan yasa ta duƙar da kanta ƙasa hawaye suna cigaba da wanke fuskarta.

"Kina yin azkar? Girgiza mashi kai tayi alamar a'a

"Baki iya ba ne"? Ɗaga mashi kai tay alamar eh.

"Ya salam! Wannan wani irin ganganci ne? Da ranki da lafiyarki? Wallahi da ace kina kokarin kiyayewa babu wani mahalukin daya isa ya cutar dake in ba Allah ne ya kaddara za'ayi galaba a kanki ba, azkar garkuwa ne agare mu, ita kuma addu'a da kike gani takobin mumuni ce kuma ita addu'a tana iya canza kaddarar mutun, daga mummuna zuwa mai kyau.

Nasiha ya fara yi mata jikinta yayi sanyi lakwas, su abla tuni ido ya raina fata don su kansu bakowane keyi ba har kwara hajjaty itada ta musulta daga baya tana kokarin yi akai akai

"Gaba ɗaya inaso ku bani aron hankulanku, ku saurari abunda zan fada maku..." amsa mashi sukayi da toh,

Shiru yayi jim kafin ya fara magana"abunda ya kamata ku sani shine, Zikirin safe da yamma yana da matuƙar mahimmanci sosai, wanda inda Musulmi yasan mahimmancin sa da kuma kariya da yake bashi da bai barshi ba koda na kwana ɗaya ne, don haka ina ƙara jan hankulan ku da Ku yawaita Lazimtar Zikirin safe dana yamma.." atare suka hada baki wurin furta in sha Allah malam zamu kiyaye

Shiekh imam ya ɗaura da cewa"abu na gaba Yin alwala, mutum ya kasance yana yawaita zama cikin tsarƙi domin hakan na bada kariya, bayan haka akwai Qiyamul laili, da kuma Neman tsari yayin shiga bayan gida (toilet) idan zaku yi bacci ku yi alwala, sannan ku karanta ayatul kursiyu bayan ita sai falaki da nasi suna da Muhimmanci sosai..." jinjina kai kowan nan su yayi sheikh imam ya numfasa yana dubansu kafin ya dasa da cewa

"Sannan Faɗin La’ilaha illallahu wahdahu la sharika lahu, lahul mulku wa lahul hamdu wahuwa Ala kulli shai’in kadir sau ɗari safe da yamma

Faɗin Bismillahillazi la ya durru Ma’asmihi shai’un fil ardi wala fissama wahuwa ssami’ul alim” sau uku safe da yamma, Faɗin “A’uzi bikalimatillahit-tammat min sharri ma khalaka” sau uku safe da yamma"

baba obie ya nutsu yana sauraron sheikh imam har cikin ranshi yaji dadin yadda ya zaunar da yan aikin gidan yana koyar dasu yadda zasu kare kansu hakan ba karamin faranta ranshi ranshi yayi ba, shi kanshi ya karu da sheikh imam.

"Malam, wallahi ni yawan mantuwa gare ni, kona yi kokarin yi sai wani abun yaja hankalina..." Sofia ce tay maganar, shiekh imam Yace"akwai islamic apps na waya, da zaki iya sauke wa.." da sauri hajjaty tace"ina da shi zan tura mata nima dashi nake amfani, shi yake tunasar dani lokacin yin ibadata da kuma lokacin yin azkhar" murmushi sheikh imam yayi idon shi akanta yace"kinyi masu wayau, zaman tare baice haka ba, meyasa tuntuni baki sanar da su ba"?

Sunnar da kanta ƙasa tayi

Calmy ta furta"ay ni bansan ba su amfani da shi ba"

Gyaɗa kai yai"haka ya dace, In ka san abu na karuwa ne, to ka yi kokarin sanar da wasu suma su amfana, na tabbata da ace shirin labarina ne aka saki jiki na rawa zaki fada masu koba haka ba"? Gaba daya suka sanya dariya.

Murmushi baba obie yayi, shima sheikh imam din murmushine akan fuskarshi.

Baiwar Allah marwa duk da halin da take aciki saida tayi murmushi fuskarta sharkaf da hawaye...

Nasiha ya cigaba dayi masu akan su daina shagala duk runtsi duk wuya kada su yi sakaci da ibadarsu da kuma neman tsari daga gurin Allah, cike da gamsuwa suke sauraran shi daga bisani yace Idan har ku ka kiyaye zikirorin dana faɗa maku, sannan ku ka kuma ƙaurace wa saɓon Allah toh haƙiƙa Allah zai kare ku daga kowani irin sharri, kuma zaku yi rayuwa cikin kwanciyar hankali domin da Ambaton Allah ne da yimasa biyayya ake samun natsuwa. Allah yasa mudace" atare suka amsa mashi da ameen haɗi dayi mashi godiya

Baba obie yace"sheikh muna godiya sosai, jazakallahu khairan..." da fara'a ya amsa mashi da ameen...

Kafin ya kalli Su abla"ina bukatar mutun ɗaya da zai dinga kula da marwa"

shiru su ka yi kowa tsoron kusantarta ya ke yi, yanzu ma da suke adakin don sunga sheikah imam ne ga baba obie shiyasa suka saki jiki.

"Kada ku bani kunya mana! Kun riga da kunsan lalurar nan ba ita ta daura ma kanta ba! idan har kuka ce zaku juya mata baya ko ku ƙyamace ta zaku sa ta tsani kanta ne harta aikata ma kanta abunda bama fata, ayanzu bata da wasu yan uwa na kusa da ya wuce ku, ku take gani amatsayin yan uwanta wadanda zasu share mata hawaye...."

cikin sanyin murya hajjaty tace"wallahi bani ƙyamar marwa, kawai abune da bamu saba gani ba, muna jin tsoro amma in sha Allah zamuyi kokarin bata kulawa, ni nayi alkawarin zan dinga zuwa dubata...."

Shiekh imam yace"Alhamdulillah, naji dadin jin hakan daga gare ki, zuwa anjima in sha Allah zan aiko maki da magunguna na musulunci, sannan kafin in tafi zan kar6i contact dinki saboda in tura maki addu'o'in da zaki dinga tofa mata aruwan wankanta dana shanta,.."

"Toh malam, muna godiya Allah ya saka da alkhairi..."

miƙewa yayi bayan yayi masu sallama baba obie ya ruko hannun shi suka fita daga dakin....

Kamar jira suke sheikh Ya fita daga dakin da sauri su abla suka gudu zuwa kitchen Ya rage saura Hajjaty adakin.

Bata san sa'adda ta fashe da kuka ba, gashi ba halin Yin magana, da hannu ta dinga bugun katifa tana kuka, da sauri hajjaty ta rukota tana lallashin ta idanunta cike tab da kwallo, wani irin tausayintane Ya kamata.

"Marwa ki daina kuka, In sha Allah zaki ji sauki ki dawo kamar yadda kike ada, nayi alkawarin zan taimaka maki muyi duk abunda sheikh imam yace"

tunda hajjaty ta fara magana marwa tayi shiru tana kallonta wallahi tayi danasani yafi sau a ƙirga, kuma tayi mamakin yadda hajjaty ta amince zata kula da ita sa6anin sauran yan uwansu da suka gudu daga dakin.

Bata ta6a tsammanin hajjaty tana da saukin kai, da tausayi ga mutunci irin na yau ba, sai taji ta tsani kanta, hakanan batai mata laifin komai ba mace mai kyakkyawar zuciya amma saboda abun duniya ta amince zata yi mata leƙen asiri don abata matsayinta akuma koreta daga gidan wa'iyazubullah, bakomai ta tuna ba face hajiya saratu, ita da tayi silar jefata halin da take aciki, amma kwata kwata bata nuna damuwarta akanta ba, ko kalmar sannu ay ya kamata ta furta mata, ayanzu ta gane wasu mutanan sai kana da amfani agurinsu suke kula ka da zarar sunga bazasu amfana dakai ba sai su watsar dakai, tayi danasani taso ace tana da baki da yau saita fallasa asirin wanda yayi silar jefata halin da take a ciki ko da zata rasa ranta ne❗

Amma duk da haka bata makaro ba, ta ɗauki alwashin saita tona asirin wanda ya cutar da ita!

"Marwa"! Muryar hajjaty ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin data lula
Chapter 120 · 0% Book details