Sashe 24
Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read
Babu wanda baiyi farin ciki acikin su ba, Musamman sheikh imam Ya ambaci kalmar alhamdulillah tafi sau a kirga, ya ɗaga hannayensa sama ya dinga zubawa Allah kirari Haɗi da nuna godiyarsa ga nasarar da suka samu, Bayan ya gama ya janyo danish din duk da bai sakar masu fuska ba wannan bai shafe su ba, dama su burinsu ya farfado kuma Alhamdulillah kwalliya tabiya kudin sabulu, Rungume shi shiekh imam yayi tamkar zai mayar dashi cikin sa, ya dinga shafa sumar sa yana karanto addu'o'i yana shafe mashi ko'ina na jikinsa.
Ko da likitan ya duba danish baiga komai ba sai ma wani abun ban mamaki daya gano wato Lafiyar dake gare shi, har ta wuce wadda hankali zai dauka, babu ko ciwon kai a tare da shi.
Bayan tafiyar likitan shawarwari suka tsaya sunayi atsakanin su, kafin daga bisani chief ya raka shi bathroom don yayi wanka, Kafin ya fito aka shirya mashi lafiyayyan abinci a daki aka shigo mashi da shi, atare da chief suka ci abinci, gwanin ban sha'awa kamar wasu yan uwan juna sai daya tabbatar danish Ya cika cikinsa tukunna ya samu kwarin gwiwar sanar da shi dangane da uncle dinsa dake son ganinsa, ya nemi alfarmar yana so su tafi atare, shiru danish yayi mashi dama yaƙi furta masu magana tun da ya farka kamar wani kurma sai dai yabi su da ido.
Tarairayarsa suka dinga yi suna lalla6a shi, duk don ya amince, amma ɗan tahalikin nan yai shiru, dabara ce ta fadowa taj da sauri yace mashi a tare da su unaisah zamu tafi da sauran ƴan uwan ka, kuma duk sun amince zasu je.
Jin ya ambaci zasu tafi da su unaisah ne yasa shi saurin amince masu ta hanyar jinjina masu kai, domin kuwa bazai bari su tafin masa da yan uwansa ba, Murmushi sukayi gaba dayansu ganin sunyi nasara akanshi... Nan fa suka fara shirya shi, kamar wani yarima.
Lokacin da su sajeed suka ji labarin Farkawar danish, Aguje suka watsa da gudu suka nufi bedroom dinshi, Tsabar farin ciki maimakon suyi dariya saima suka fashe da kuka suka dinga rungumar shi, Dadi kamar zai kashe su, Shi kanshi yayi farin ciki da ganin su duk da yaki tanka masu sunyi sunyi dashi akan ya bude baki yayi masu magana amna yakiya sai dai fa kallo ko irin sakin fuskarnan babu
Hakan bai wani dame su ba, tun da ya farka falillahil hamdu, duk wannan mai saukin ne, dama sun riga da sun san halin kayan su, bayan sun gama murnar samun lafiyan dan uwan nasu, Ummi ta tattarasu suka koma dakunansu, kowan na su yayi wanka, Suka soma shiryawa cikin kayan su cike da zumudi, bayan haka dangane da abun da ya faru a hall na kashe Hasken lantarki aikin chief owais ne shine ya tsara komai, tare da interior designers da sukayi decoration na hall din saboda yana son yaga reaction din family nasa, bayan ya gama tsara komai, Shi yafara halartar dinner din, ya riga su Unaisah tafiya kamar yadda ya tsara saboda yana son ya fara yi masu hanyar shiga batare da an samu matsala ba, tun da wurine mai tsaron gaske, su boss da big guy ne da wasu daga cikin jami'an isod sukayi jigilar daukar su Unaisah a cikin motocin su, suka kawo su bakin hall din, bayan tafiyar su tuni Ummi ta shirya saboda ta samu amincewar chief akan fitar da za ta yi, taje ne ya nema mata alfarma, Jami'in isod ne yayi driving dinta zuwa gidan da tace zata je na kawarta.
(Wannan shine abunda ya faru kafin zuwansu dinner hall din)
(CIGABAN LABARI)
Haɗa ido su kayi da prime minister, cikin sanyin murya ya furta"shi ne...?
Jinjina mashi kai chief owais yayi alamar eh, wata nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke, fuskarshi dauke da wani irin annurin farin ciki mara misaltuwa da tafukansa ya tallabo fuskarshi yana bin shi da kallo mai nuni da tsantsar ƙaunarsa, kasa jurewa yayi baisan sa'adda Ya janyoshi zuwa ga faffadan kirjinsa yai huggin insa tightly kamar zai mayar da shi cikin cikinsa, hannayensa biyu dukansu ya tallabe bayan danish dasu, yayin da zuciyoyinsu ke harbawa da bugu mai tsanani, wani irin yanayi mara misaltuwa....
Hakan ba karamin ɗaga hankulan mutanan dake a hall din yayi ba, gaba ɗaya sun ƙara rudewa da ganin rungumarshi da prime minister yayi.
Muryar Hajiya saratu tamkar zata fashe da kuka ta furta"wai ba zakuyi mana bayanin su wanene ba? Kun barmu atsaitsaye cirko cirkon kamar sakarkaru" ta fada tana kallon chief owais don ta fahimci yasan da zamansu tun da taji Pm hateem ya tambaye shi shine....
"Owais su wanene wadannan Yaran! "? Baba obie ne ya furta maganar
Sai lokacin chief Owais ya soma takowa yana tunkaro wurin da su ke atsaitsaye, cikin dakakkiyar muryarsa ya soma magana genlty
"A gafarce ni, nayi laifi ban sanar da zuwan su ba....' ya faɗa awayance yana bin kowan nan su da kallo.
"Idan ba zaku manta ba, na ta6a baku labarin Yaran da Sojin america suka tsinta a evil forest, suka damƙa case dinsu ga hukumar mu ta Isod, ga wadanda basu san da zaman su ba, to ga su nan, sune yaran da nake ruƙo a hannuna, na gayyace su ne don su gana da dangina saboda sun zama tamkar ƴan uwa agare ni"
Lokacin da ya ƙarasa maganar, hajiya saratu ta zabga salati tana huci ta furta"wlh baka isa ba Owais! Ka haukace ne? da Zaka kwaso mana tsintattun Yaran da ba'asan asalin su ba, ka kawo mana acikin dangi? Anya kuwa kana a hayyacin ka? Rai amatuƙar 6ace tayi maganar, Hankalin su Unaisah ba karamin tashi yayi ba, Masu tsoro acikin su har sun fara Ja da baya jiki na kerma...
A matuƙar firgice Senate Lateef Yace"kana nufin ƴan uwan yaron nan da ya rikiɗa ya koma maciji"? Wannan maganar da senate lateef Ya furtane Yaja hankulan mutanan Hall din, Tashin hankali ne tsantsa akan fuskokinsu, Muryoyinsu a kidime suke maimaita kalmar maciji ga wadanda basu san da zancen faruwar lamarin ba, nan take Pravin yayi wuf ya kwashe komai daya faru ya sanar da su, Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un shine abunda suke furtawa a bakunansu....
Prime minister sam baya gane me su ke cewa saboda idanunsa sun makance, Ya kurmance baya ji baya gani tunda ya rungumi danish a jikin shi bai ƙara ɗago da kanshi ba, Kamar daga sama yaji an damƙi damtsen hannunsa da ƙarfi aka raba shi daga jikin danish wanda bakowa ne yayi hakan ba face Senate Lateef, ya janye shi gefe guda, Yana faman zazzaga masifa"wlh bazamu lamunta ba! Don Na fahimci bakasan ciwon kan ka ba, taya zaka kwaso mana mugun abu ka kawo mana a cikin dangi? Wannan wata iriyar masiface? So kake ka tarwatsa mana farin cikin mu? Ko kuwa so kake ka ƙarar mana da dangin mu ne!? Wai ma wanene ya baka shawarar ka kawo su wurin nan....."?
Tunkafin Senate lafeef ya kare maganar, sautin shessheƙar kukansu Ya soma karaɗe hall din, sun girgiza da jin munanan kalamin da ake fada akansu, bayin Allah da farin cikin su da zumudi su ka zo ganin dangin chief owais sunyi tsammanin suma zasu sosu kamar yarda shima yake son su ashe ba haka bane......'
"Wallahi sai dai ka za6a, ko dai ka tattara su ku koma can gidanka, ko kuma mu mu fita mubar maka hall din ka ƙare dinner din tare da su, don wlh baka isa ka jazamana masifa ba, wannan ay annobace ka kwaso mana" acewar hajiya saratu ta faɗa tana watsa hannayen ta.
Chief owais dake sauraronsu ɗaya bayan ɗaya yake binsu da kallo daman yasan za'a rina ba lallai su wanye lafiya ba, sai gashi ta tabbata, kowa da abun da yake tofawa, mutane ƙalilan ne basu tanka ba.
Hankalin Hateem yafi na kowa tashi, ganin za'a raba shi da muradin ranshi, Ga samu ga rashi, Ji yake tamkar Ya fasa ihu, ƙiri ƙiri su Senate lateef sun rurruƙe hannayenshi gudun kada Ya ƙara tunkarar Danish.
Security advisor din Hateem ne ya tambayi meke faruwa ne? Muryarsa a bubbuɗe yasha ya bugu baya gane komai sama sama yake jin kan shi, Kasancewar basa jin yaren hausa basu san takan zancen ba, da sauri pravin uban Ƴan zigi Ya buɗe baki da niyar Ya sanar dasu, wata irin tsawa mai kama da saukar aradu chief owais Ya sakar mashi, wadda tay matuƙar gigitasu a hanzar ce yaja baki ya yi shiru.
Dalilin dayasa ya yi mashi hakan gudun kada ya sanar da su, don muddin sukaji da zancen Yaron daya rikida ya koma maciji to kuwa nan take zasu sa a dakatar da taron bayan haka zasu sanya jami'ansu su kori su unaisah don ba zasuyi ganganci da rayuwar hateem ba...
Cikin sanyin murya prime minister yayi ma mutanansa bayani da yaren da zasu gane ya kwantar masu da hankalin su, da cewa family issue ne kuma in sha Allah zasu shawo kan matsalar yanzu, iya abun da ya fada masu kenan, dama kuma ba ahayyacin su suke ba, shiyasa abin yazo masa da sauki da tuni sunsa an tada taron gaba ɗaya.
Da kakkausar murya chief owais Ya soma magana babu annuri akan fuskarshi.
"ni ne silar dana kawo su wurin taron nan, bawani ya bani iznin in gayyace su ba, kuma basu suka nuna suna son zuwa ba, face don ni nake so su zo...." bai ƙare maganar ba, Hajiya saratu tayi yunkurin dakatar dashi aikuwa a fusace Ya ɗaga mata hannu alamar tayi shiru, Waro idanu waje tayi ba ita ba hatta sauran mutanan hall din sunyi mamakin rashin kunyar da owais yayi.
"Suma ya'yane kamar kowa! Yaro kuma da bashi da lafiya, Bayin kanshi bane, Aljanu ne suka shafe shi, kuma ya samu lafiya bayan da shiekh Imam ya dau kwanaki Yana duba shi.....' bai ƙare maganar ba, muryar sheikh imam ta karaɗa kunnuwansu a yayin da yake shuowa dakin taron.