← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 238

Sashe 11

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gyaɗa kai tayi"okey, in sha Allah amma baza'ay masu make up ba"?

"Duk kyan da Allah yayi masu"? Ya faɗa da murmushi kan fuskanshi, Itama ummin murmushin takeyi"masu kyaun ma su na yin make up, ko da yake naji ka ce arufe masu ko'ina na jikin su, ba buƙatar yin make up, ɗaga mata gira yai alamar eh.

"Tare da ni zaku tafi ne"?

"Idan kina ra'ayin zuwa"

Girgiza kai tayi alamar a'a

"Meyasa"?

"Nafi so kubarni a gida, nasan Su Unaisah zasu bani labari, har ma su daukar min video na dinner din in gani nima"

"Ban yarda ba, yakamata kema ki shirya mu tafi tare dake, zaki ji dadin shiga cikin family ɗin Obinna," jim ta ɗanyi tana wani tunani aranta.

"Kinyi shiru baki ce komai ba"

Numfasawa tayi tare da cewa"ka yi hakuri amma zuwana ba lallai ya zama alkhairi agare ni da ku kan ku ba, bana so na 6ata maku shagalin ku, nasan ka fahimce ni" jim ya ɗanyi yana jujjuya mug din hannunsa, tabbas ya fahimci me take nufi,shi kanshi yasan ba lallai chief Ya amince su tafi da ita ba, yadai ɗan bugi cikinta ne don yaji idan tana son zuwa sai kuma akaci sa'a bata ra'ayi.

"Alfarmar da nake nema a wurin ku, dan Allah ku barni in fita gobe, Inaso zan ziyarci gidan ƙawata dake aure anan abuja"

"Bani da wannan hurumin, Amma in sha Allah zanyi kokarin nema maki alfarma wurin chief, but inaso kisan da sani duk inda zaki je jami'in mu ne zai kai ki," har cikin ranta taji dadin maganarsa.

"Idan akwai abun da kike buƙata ki faɗa min" cikin kulawa yayi mata maganar yana dubanta.

"Dan Allah ka fadamin shin dagaske ne chief Yasan komai dangane da rayuwana"? Ta fada cike da fargaba.

Jim ya ɗanyi yana dubanta kafin Yace" "I'll give you an assignment. If you can find the answer, then I'll tell you what you want to hear," A ƙagare ta ke kallon shi, A hankali Ya sanya yatsun hannayen shi tare da zame mask din fuskarshi.

Wani irin kallo ummi ta soma binshi da shi, Yau ne karo na farko da ta fara Yin tozali da fuskar Boss man, bata ta6a tsammanin Yana da kyawun fuska har haka ba.

"Dama haka kake da kyau"? da alamun mamaki ta furta maganar, Murmushin gefen fuska Ya sakar mata har dimple dinsa ya lotsa, nan take ta soma kokarin tariyo inda tasan fuskarshi sai dai kash takasa tunawa amma tabbas tana ji aranta ta ta6a sanin shi ko kuma wani ne me kama da shi.

"Ina da aure, Ki daina kallona, matana tana da kishi, zata iya yin komai akaina" da zolaya taj yayi maganar.

Ummi tace"tasan tana da kishi meyasa ta auri namiji mai kyan sura? Ay kamata yayi ta auri mummuna, ni fa bazan 6oye maka ba, ka jima kana bani mamaki kai da abokin aikin ka big guy da chief din ku, tun da nataso rayuwata da wuya a samu namijin zan gifta awuri batare daya bi ni da kallo ba harma ya neme ni, amma ku sam babu wannan tunanin aranku, zuciyarki a tsarkake take, hakan ba karamin daure min kai yake yi ba, shi chief mace ko kallo ma bata ishe shi ba, wata irin dakakkar zuciya ce da shi.

Ƙayataccen Murmushi Taj Ya sakar mata batare daya furta mata ƙala ba

"Wallahi nasan ka, sai dai bazan Iya tuna a ina nasan ka ba, ni hatta muryarka na jima ina son tuna ina na son ta," still face dinsa da murmushi Yake dubanta.

"Amma meyasa kake yi min kama da Unaisah? Ko dai idanuwana ne suke nuna min badai dai ba"?

"Ba laifin idanuwanki bane, Unaisah Ƴata ce, Jini na ce, Ni mahaifinta ne, asalin sunana Tajuddeeen,"

"I can't believe it, Unaisa fara ce zan iya sanyata a jinsin larabawa, kai kuma daga ganin ka hausa fulani ne"

"A salin sunana Zaheer Tajudeen, Zaheer sunan Mahaifina ne, Tajudden kuma sunana ne, Ki tambayi Unaisah menene full name dinta zata fada maki da bakinta, Ita kanta ayanzu haka batasan cewa Ni mahaifinta bane ƙaddara ce ta rabamu, sai gashi cikin ikon Allah mun sake haɗuwa," murmushi ummi tayi"Allah sarki, Na tayaka Murna, amma mahaifiyarta wani jinsi ce"?

"Hausa Arab ce" Dariya Ummi tayi cikin raha ta furta"hausa arab! Bayan hausa fulani har Hausa rab ke da akwai, ban ta6a ji ba sai akanka"

"Ina nufin Half cast ce, Mahaifinta hausa fulani ne, mahaifiyarta kuma Balarabi ce" gyaɗa kai tayi"masha Allah, shiyasa yarinyar taka takasance fara sol, Ga gashi tubarkalla amma tsakanin kai da mahaifiyarta halin wa ta ɗauko"? murmushi yasaki yana dubanta yace"meyasa kika tambaye ni"?

"Unaisah tana da faɗa, daga ka kalli idanunta zaka shaidan hakan, ga wayau da kaifin basiri Allah Ya bata fiye da sauran ƴan uwanta" haƙiƙa Yaji daɗin Yabon da ummi tayi mata,

"Haka mutane suke cewa, shiyasa nima nake alfahari da ita, Inason Unaisah, fiye da yadda nakeson kaina, A halin Yanzu bani da tamkarta a duniyarnan, Itace ta rage min wadda nake gani naji sanyi araina, silar unaisah nasamu alheri da dama wadanda idan na fada maki su zakiyi mamaki, ɗaya daga ciki Unaisah itace silar haɗuwana da Chief" da mamaki Ummi ta ɗan zaro mashi sexy idanunta haɗi da buɗe baki, Jinjina mata kai yayi" Murmushin gefen fuska tasaki"Ina ƙara tayaka murna, Yarinyarka Jarinka ce, Allah Ya albarkaci Rayuwarta" amsa mata yayi ameen, daga ita har shi sun ji daɗin zaman firar da su kayi, Haƙiƙa taj ya ɗebe mata kewar kaɗaicin dake damunta, ta ƙara ganin mutuncinsa da ƙimarsa a idanunta, Sai dai tarasa gane meyasa take jin kamar ta ta6a sanin shi? Musamman daya faɗa mata sunan shi sai yawo yake mata akai.

Ni'imtacciyar Iskar dake kaɗawa ta ƙara masu ƙaimin firar ta su, kafin wani lokaci taj yace da ita"kada na cika ki da surutu, ko zaki koma ciki ne"? Fuskarta da fara'a tace"no ko kusa, ni baka takuramin ba, saima ɗebe min kewar da ka yi, naji dadi fiye da tunanin...... " bata ƙarasa maganarba sakamakon sautin dirar motar daya ratsa kunnuwanta, kusan atare suka juyo suna duban motar.

Bayan sojan dake driving din motar yayi parking, Ya fito Ya zagaya ya buɗe mashi murfin back seat dinta, Ƙafarshi kaɗai ya zuro waje Gaban ummi ya faɗi rasss, jikinta ya soma kakarwa, A hankali ya ƙarasa fitowa daga cikin motar, kamar kullum cikin shiga ta malamai magadan annabawa, bai ɗaura idanunsa akan kowa ba sai akan Ummin america, a sukwane ta miƙe tana gyara mayafin da tayi rolling, taj kuwa fuskarshi dauke da murmushi ya nufi sheikh imam yana fadin"Ya sheikh Barka da zuwa tun ɗazu muke ta sa ran ganin ka" Martanin murmushin Shiekh Imam ya mayar masa a yayin da yake kokarin kau da idanunsa daga na ummi ya mayar da su akan fuskar taj, musabaha su ka yi shikeh imam yace"Ay min afwa, ban samu damar zuwa duba mara lafiya na ba, wallahi yana araina da shi na wuni, wani uziri ne ya ruƙe ni"

Jiki na rawa Ummi ta juya ta nufi ƙofar shiga falo, Duk don kada su gaisa da sheikh imam, har ta kusa kaiwa ga ƙofar muryar taj ya ratsa kunnanta

"Ummi, ki zo mana ku gaisa da sheikh imam" tamkar an dasa mata aya ta tsaya cak, tana mai mayar da numfashi, Har cikin ranta bata ji daɗin dakatar da itan da yayi ba, sai dai bata jin zata iya watsa mashi ƙasa a ido, musamman yau daya faranta mata rai.

Tunkafin ta juya ta soma jin takun tafiyarsu bayanta, jiki asanyaye ta waiwayo tana dubansu, lokacin da suka ƙaraso da sauri ta sunnar da kanta ƙasa, muryarta na rawa ta furta"sannu da zuwa"

Cikin sanyin murya ya amsa mata da yawwa

Taj dake dubansu a fakaice yace"sheikh bari na gabatar maka da ummi,"jinjina mashi kai yai alamar toh

"Ummi Tamkar uwa take a wurin yaran da muke raino, ita ce take kula da su"

Fuskar sheikh babu annuri ya furta"anya kuwa sunyi dacen uwa"? Har sai da gaban ummi ya fadi rass jin abun da yace, hatta shi kanshi taj aruɗe ya kalli fuskar shaikh imam

*Daga alkalamin Boss Bature💋✊✍️*

Kurkukun Kaddara
Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 10 Complete
by
Novels Elite Admin
May 25, 2024

_ *~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋✊~*_

سجن القدر💋✊🔥

~Takun Ƙarshe🔥~

قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع تطورات معقدة💋💘😘

An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘

Daga alƙalamin Boss Bature💋✊

__________________________✍️

Har sai da gaban ummi ya fadi rass jin abun da yace, hatta shi kanshi taj aruɗe ya kalli fuskar shaikh imam.

"Ya sheikh ko zan iya sanin dalilin da ya sa ka ce haka? Acewar Taj

Sheikh imam yace "Tun da nake zuwa gidan nan ban ta6a ganin ta taka zuwa ɗakin yaron nan ba, domin duba lafiyarshi, bansani ba ko tana shiga bayan bana nan amma raina na bani tamkar bata zuwa, a matsayinta na maruƙiyarsu yakamata ace tafi kowa bashi kyakkyawar kulawa ko da kuwa addu'a ne take zuwa tana yi mashi akai akai" tun da sheikh imam ya fara kora jawabi hankalin ta ya kwanta jikinta yai sanyi laƙwas.

"sheikh maganarka gaskiya ne, ummi baki kyautawa, kinga har sheikh imam ya fahimci baki zuwa duba lafiyarki ɗan ki" ya faɗa yana kallon ta, murmushin gefen fuska ta saki, cikin sanyayyar murta tace "nagode sheikh da tunasarwa, na gane kuskure na kuma in sha Allah daga yanzu zan dinga zuwa duba shi'

"Masha Allah, yanzu naji magana, bismillah malama ummi mu shiga ciki, kiyi mashi addu'a in gani" ta fahimci sheikh imam kamar ya gano wayanta nason ta gudu, shiyasa yake kokarin ruke ta.

Babu yadda ta iya adole ta amince suka nufi cikin gidan atare tana mai jin wani irin sanyi aranta.
Chapter 11 · 0% Book details