← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 210 OF 238

Sashe 210

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

da fara'a Aisha tace meyasa bata fata mata ba, Benazir tace kawai tana son tayi suprising dinta ne, cike da farin ciki tace ta jira ta a falo zata shirya, Benazir na fita daga dakin Aisha ta soma shirya kanta cikin abaya, sai ga Aunty laura ta fito daga daki ta iske Benazir zaune kan sofa, da fara'a suka gaisa da juna har ta tambaye ta meya sanyata farin ciki nan take fada mata yaya shureim da Uncle musa ne suka dawo Nigeria shine ta zo don ta fada ma Aisha, washe baki aunty laura tayi tana fadin Ah lallai manya manyan baki, shine ba'a fada min ba? tana cikin magana sai ga Aisha ta fito sanye da dogon hijab hada nikab akan fuskarta.

fuska adaure Aunty laura tace kefa matsalata dake kenan, kamar kinfi kowa tsoron Allah, kullum cikin nikab, yanzu nan da gidan makwabtan namu sai kin saka hijab da nika..." a karshe ta korata daki tace taje ta sako Mayafi..da damuwa tace ita bazata iya ba, saboda hijab mutuncin ya mace ne, bayan haka baba ya hanata fita ba hijabi har ta soma janyo mata aya, aunty Laura ta mike rai a6ace taja hannunta suka koma daki, adole saida ta tursasa ma Aisha ta saka Wani guntun veil a kafadarta, baiwar Allah duk sai taji ba dadi ganin yadda abaya din ta ɗame jikinta, dirinta nan nata mai jan hankali ya bayyana muraran musamman ta gurin mazaunanta sun fito rudu rudu..

ahaka Banezir taja hannunta suka tafi gidansu, shigarsu keda wuya ta gate din adai dai Lokacin Alhaji musa Yana atsaye gaban dankareriyar motarsa ya dauki wankan shadda hannunsa ruke da waya, kallo daya da Aisha tayi mashi saida gabanta ya fadi saboda ƙwarjinin dake gare shi, wata irin kirar jiki gare shi irin ta yan dambe.

Benazir ce ta gabatar mata da Uncle dinta, duk irin izzar Alhaji musa da yayi tozali da Aisha saida Ya rasa nutsuwarsa saboda shi irin mazan nan ne masu kwadayin mace mai kyawun sura, sanin da yayi mata tuntana karamarta yanzu kuma ta girma, wani irin kallo yadinga binta da shi harya kasa amsa gaisuwar da ta ke yi mashi, A lokacin rudewa Aisha tayi saboda bai kwanta mata arai ba, musamman da ta ga hakoransa ya sanya masu Gold-plated teeth..

ita kanta Benazir ta lura da yanayin da ya shiga. Hakan yasa taja hannun Aysha suka nufi cikin gidan, Uncle musa yabi bayanta ta da kallo yanayin yadda take tafiya jikinta na girgiza ba karamin tayar masa da maitar sha'awarsa tayi ba, kuma tun daga lokacin ya kudiri aniyar saiya mallake ta.

Bayan sun shiga babban falon gidan, anan suka iske Hajiya layla tare da Alhaji ubaid suna zantawa tsakaninsu, bayan sun gaishe dasu hajiya layla tace su shiga ciki su gaida shureim..

Tun da Allah Ya Halicci Aishatu Bintu Imam bata ta6a ganin mutumin daya kwanta mata aranta ba, da kallo ɗaya ta fada tarkon son shi sai akan dr shureim yanayin da suka same shi adakin shi yana zaune kan darduma Ya buɗe al'kurni yana karatu cikin nutsastsiyar Muryarsa ba karamin jan hankalin ta yayi ba, tayi mamakin girman daya ƙara tsawon shekaru a lokacin rabon shi da Nigeria.

Sai da yakai aya, cikin sanyin murya yace masu su shigo yaga sun yi tsaye bakin kofar dakinsa, Jan hannunta Benazir tayi suka zukunna agaban dardumarsa ta gabatar masa da aminiyarta yar makwabtansu diyar sheikh Imam, ganin kamar bai gane ba don tun suna kanana Yabar Nigeria, Aisha ta gaishe da shi tare da yi mashi bangajiyar tafiya, da murmushi akan fuskarshi ya amsa mata, abunda bata sani ba Dr shureim yasan da zamanta, Yana yawan sauraron kira'arta da take yawanyi a taron musabaka, wanda mutane ke yaɗa videon a social media amma saboda miskilancinshi sai ya nuna kamar bai gane ta ba.

sun ɗan jima Yana jan su da fira, lokacin da ta tashi tafiya dr shureim ne ya yi mata rakiya tare da Benazir har kofar gidansu, saida suka ga shigarta kafin suka koma gidan su.

a daren ranar Alhaji musa Ya kira Benazir ya soma tambayarta dangane da Aisha, ko tana da tsayayyan da zata aura"? Benazir tayi mamakin tambayoyinsa saboda tasan Uncle din nata mugun miskiline bai cika shiga sabgar da bata shi ba, In fact mata basa agaban shi bata kawo komai aranta ba ta fada masa komai dangane da Aisha, Hankalinsa ba karamin kwanciya yayi ba jin cewa bata kula samari, fargabansa daya Sheikh Imam malik saboda basa ga maciji.

A bangaren Aisha tun bayan data koma gida tunanin dr shureim Ya hana zuciyarta sukuni, Kwana take da shi aranta, haka zalika in tana koyama dalibanta karatu wasu lokuttan shagala take da tunaninsa har sai daliban su ankarar da ita.

ta bayan fage Uncle musa ya fara ba Banezir makudan kudi masu auki don suje yin siyayya da Aisha, kuma yace mata baya son Aishar ta sani, Benazir bata ta6a fada mata Uncle musa ne ke bata kudi ba, Sai ma in ta tambayeta ina take samun kudi sai tace dr shureim ne ya bata, hakan ya sa ta saki jiki duk da bata da kwadayin abun duniya tayi azan yaya shureim yana son ta ne shiyasa yake ba Benazir kudi don suyi siyayya.

kusan kullum sai Aunty laura tayi masu hanyar fita daga gidan batare da sanin Shiekh Imam ba, don suje Mall suyi siyayya harma da yawon buɗe ido koda Aisha ta nuna bata son fita Aunty laurace ka tursasa mata in ta turje sai ta fashe mata da kuka tana fadin bata mata biyayya saboda ba ta ɗauketa uwa, don taga ita bata haihuwa, in ta fadi hakan jiki na rawa Aisha take bin Umarninta.

Tun bata sake ma Uncle musa in suka haɗu harta fara sabawa da shi, tana matukar girmama shi tanayi mashi kallon Uncle dinta.

Haka zalika shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninta da dr shureim, Benazir tayi mamaki saboda sanin da tayi ma Aisha bata Kula maza sai gashi dr shureim ya ciri tuta, sun saba da juna, Benazir ta sanya masu ido sosai, Ta fahimci dukansu suna son juna, ita Aisha Kunya ce ta hana ta furta mashi Kalmar so, yayin da shi kuma miskilanci ne Ya hana shi bayyana mata, bayan haka Yana jin nauyin yayi soyayya da Aisha saboda yanayi mata kallon Kanwarsa.

A duk lokacin da Benazir taso Ta bugi cikin shureim don ya fada mata In yana son Aisha sai yace mata shi babu soyayya atsakaninsu kallon kanwa ya ke yi mata, haka In ta bugi cikin Aisha don taji in tana son ya shureim sai tace mata ita fa ba son shi ta ke yi ba, kawai tana yi mashi kallon yayanta ne saboda zumuncin dake a tsakaninsu, In Benazir zata shekara tana tambayarsu amsa daya suke bata.

Bayan da suka kammala Secondry School, Alhaji Ubaid ya sama masu admission a wata Jami'a dake a birnin hagen na kasar Jamus batare da sanin sheikh Imam Malik ba sai daga bisani ya same shi har gida ya sanar da shi.

shiekah Imam bai nuna amincewarshi ba, Yace shi bazai bari yarsa ta tafi uwa duniya karatu ba, duk Universities din dake a Kasar har sai an fita waje neman ilmi? Alhaji ubaid ya ce yayi hakuri da bai nemi shawarar shi ba ya tashi ya yanke hukunci dama yaga Benazir ta kwallafa rai ne akan son zuwa can tayi karatu kuma ta nuna tana son suje tare da Aisha shi kuma yayi la'akari da shakuwar dake a tsakaninsu In aka rabasu ba zasu ji dadi ba shiyasa ma har ya nemi Benazir data kar6o ma shi Academic record din Aishah.

A ranar da su ka yi maganar, bayan Alhaji ubaid yayi mashi sallama ya tafi, ranshi a bace Ya kira Aisha ya fara mata fada akan takardun karatunta data kai ma Alhaji ubaid don ya sama mata admission, tace mashi wallahi ba ita ta bashi takardun ba, hasalima ita batasan da maganar ba, ko da jin hakan nan take ranshi ya bashi da sa hannun Aunty Laura, Har daki Yaje ya same ta da maganar, maimakon ta kar6i laifin ta saima ta dinga masifa tana fadin taje ta bada kuma wallahi bai isa Ya hana Aisha taje karatu kasar waje ba, shi ko dan zumuncin dake a tsakanin shi da Alhaji Ubaid bazaisa Ya amince be? Idan Ma yana jin tsoron wani abu ya same ta acan din Ba Allah ke tsare bawansa ba, bayan haka tun da Ba ita kadai zataje ba hada Benazir ya bar ta mana, shiekh imam yace mata ya gama magana bata isa tasa shi canza ra'ayin shi ba.

Ganin da gaske Shiekh Imam zaiyi mata bukulun kudin da take samu agurin Alhaji musa yasa ta kwashi kafa taje gidan kakarsu ta bangaren Uba da ta rage masu mai Suna Hajjo, ta tsara mata karya da gaskiya akan kullan da Sheikh imam ya ke yi ma yarsa, ta ce ita bakin cikinta gorin da ya ke yi mata akan Aisha sai kace ba diyar yayarta ba, In da kara aisha ai yar ta ce tana da ikon juyata son ranta, bayan haka ta fada mata Alhaji Ubaid Ya sama ma Aisha gurbin karatu a kasar germany ita da Benazir amma Ya hana bai dubi zumuncin dake a tsakanin su ba, Hajjo da ranta ya 6aci ta sa Aunty laura ta kira mata imam a waya tace yazo tana son ganin shi, koda yazo ta balbaleshi da fada kamar zata rufe shi da bugu kasancewar shi mai biyayya yadinga bata hakuri kamar zai durkusa mata kasa tace mashi in har yana son farin cikin ta yabar Aisha ta tafi karatu kasar germany, Shiekah imam yayi kokarin ankarar da ita illar dake akwai na tura ɗa karatu kasar waje balle ita da take mace amma Hajjo ta rufe ido tace itafa ta gama magana, kawai yabi abunda tace mashi, ta ko'ina ta matsa mashi lamba ba dan yaso ba ya amince zai barta, don yasan halin Hajjo rikicin tsufa ne ke damunta.
Chapter 210 · 0% Book details