← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 169 OF 238

Sashe 169

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kada ki damu, nasan duk inda taje tana acikin gidan nan" ta faɗa tare da ruko hannunta"mu shiga daga ciki, Ki jira ni in shirya sai mu fito tare" amsa mata tayi da toh.

Bayan shigar su ɗakin, Ummi ta kunna mata kallo a laplop ɗinta, kafin ta shiga bathroom don tay wanka.

Nutsuwa tayi kan gadon tana kallon drama, ta shagala da kallon wayar Ummi ta fara ruri.

Ɗauko wayar tayi daga kan pillow, ta duba screen ɗin bata gane me aka rubuta ba saboda bata iya karatu ba..

Da karan banin ta tayi picking call ɗin kamar yadda taga Unaisah nayi, ashe video call ne, yanayin yadda ta ruke wayar yatsan hannunta yayi hiding front camera, wanda Ya kira bazai Iya ganin ta ba, kura idanu tayi aka fuskar mutumin dake kwance cikin bathtub, ruwan kumfa ya rufe Jikin shi fuskar shi kaɗai take Iya gani yayi shiru yaki magana itama tayi shiru taƙi furta kalma zuciyarta cike fal da tunanin wanene Wannan ƙaton.

"Ummi meyasa kike boye fuskarki? jira kike saina maki magana"? Muryar shi ce ta katse shirun ta..

Jin motsin buɗe kofar toilet, yasa ta danna end Call, da sauri ta mayar da wayar kan pillow ta aje.

Ta yi hakanne saboda Ummi ta ta6a gargaɗinta, akan in ankira wayarta bata akusa kada tayi picking dama bata ta6a kuskuren daukar mata waya ba saboda ta fahimci bataso.

Koda Ummi ta fito bata faɗa mata an kira wayar ba, bayan ta kammala shiryawa atare suka fito daga dakin.

Har wuraren ƙarfe tara, basu ga Unaisah ba, gashi Har time ɗin Yin breakfast dinsu ya yi gaba ɗaya yan uwansu sun hallara a dining ita kaɗai su ke jira sun yi neman har sun gaji kuma babu wanda yai tunanin tana adakin Danish.

Can cikin kunnuwanshi suka soma jiyo mashi sautin tarin ta, firgigit Ya farka da kasala Ya miƙe zaune Yana kallon ta da idanunsa waɗanda suka kumbura.

A hankali ta miƙe zaune tana Hamma Wata Irin Yunwa take ji, kwata kwata bata iya tuna abun da ya faru ba, fitsari ne Ya matse, saukowa tayi daga kan gadon da sassarfa ta shige toilet ɗinshi sai da ta gama tana kokarin fitowa idanunta suka sauka akan shi, Ya zafga Uban tagumi da tafukansa kamar wanda Ya rasa gata a duniya.

Nan take komai daya faru tsakanin su Ya dawo mata acikin tunaninta, gefen fuskarta daya mara ta shafa da tafin hannun ta, harara ta watsa mashi taja tsoki, kafin ta juya zata bar ɗakin.

takun tafiyarne Ya fargar da shi, da sauri Ya miƙe ya shagabanta kiris Ya rage kirjinta Ya bangaji na shi

"Bani bukatar Jin komai daga gare ka, bani hanya na wuce"! tana huci ta faɗa tana neman rabawa ta gefen shi don ta wuce

Cikin sauri ya ruƙo Arm ɗin ta, hakan yasa ta dakata da tafiyar

"I want to ask you one question."

shirun da tayi ne yasa shi fahimtar jiran shi takeyi

"baki tsoron ki rasa ni"?

"Danish, ko da Ina jin tsoron In rasa ka, Ka tuna ranka ɗaya ne tak! da shi kadai zaka Iya taimakon dubban rayuka, ka kuma yi silar tarwatsa gang din azzalumai"

"Angel, baki damu dana mutu ba? Ina kaunar da kike mini? Kin za6i da naje na bada raina"? jinjina mashi kai ta yi"nafi maka kwaɗayin ka mutu a filin yaƙi, kwara mu hakura da duk wani buri da muke da shi, mu bada rayukanmu donmu taimaki bayin Allah, in sha Allah ko bamu ji dadi anan ba, zamuji acan, in ba haka ba mutanan nan bazasu ƙyalemu muyi rayuwar farin ciki ba, saboda mun san sirrin su kuma mune na farko da muka gudu daga gidan kurkukun ƙaddara, mun tona asirin su, zasu nemi hanyar kashe mu ne, ka fada min taya zamuji dadin rayuwa da fargaba a zukatan mu? Kaima fa har yanzu suna atare kai, Ka tuna abunda kayi min rannan, wata rana har kashe ni zaka iya yi ba acikin hayyacin ka ba, dan Allah ka fahimce ni, rayuwa bazata yiwu ahaka ba, kana bukatar ka zama cikakken mutun"❗

duk yadda taso ta jure saida idanunta suka cika tab da kwalla kwata kwata bataso Yaga rauninta, tafi son yasan da gaske take don ta samu ya amince.

Batai aune ba, Taji Ya zube kan gwiwowinsa, A hankali ya jinginar da kanshi jikin laps dinta, ya zagayo hannayen shi kan waist ɗinta ya ruƙe ta gam, da wani irin hucin zafi numfashin shi ke fita ya riga daya sadaƙas Angel had already won him over, dole Ya mika wuya, abu ɗaya da bazai ta6a mantawa ba, munanan kalaman da ta furta mashi, tabbas Yana son wata rana ya bata mamakin da zaisa tayi danasanin abunda tayi masa.

Cikin karyayyar murya tamkar ta majinyaci Ya furta"Na amince, zan basu haɗin kai, all because of you, Whatever happens to me, blame yourself .." kasa ƙarasa maganar yayi saboda raunin da zuciyar shi tayi..

Angel dake tsaye kamar gunki tana kallon sumar kanshi, ruwan hawayen ta dake gangarowa kaitsaye suka ɗiɗɗiga saman sumar kan shi, baiwar Allah duk sai taji ba daɗi, Zuciyarta ta karaya da kalaman shi,.

Ta rasa farin ciki zatay da amincewarshi ko bakin ciki? ita dai tasan Ita da kwanciyar Hankali sunyi bankwana.

Yatsun Hannunta na kerma Ta shafa sumar kan shi, dakyar ta banbare hannayenshi daya ruke waist ɗinta da su, ta fuce daga ɗakin, akan flooe Ya kwanta tamkar babu jini ajikin shi.

maganganun mutun biyu ne sukayi tasiri akanshi, Tsohuwa Khala and his Destiny, yaci alwashin duk runtsi duk wuya sai yaga bayan Elders sannan Yana son yaje kurkukun kodan Ya haɗu da tsohuwa khala saboda yana son ta faɗa mashi su wanene iyayen shi saboda ya fahimci su kadai ne zasu iya bashi abun da akeyi mashi gori akai❓

___________________________________________✍️

Idan muka koma Gidan baba Obie, tun da Owais Ya faɗa ma Pravin zancen tafiyar da yake so suyi tare da baba Obie, Hankalin Shi ya tashi haiƙam, gaba daya ya rasa nutsuwar shi saboda bakin ciki Ya tafi batare da ya ƙarasa aiwatar da mummunar kudirinsa ba, wunin ranar a daki yayi saboda damuwa har hajiya saratu saida ta lura da yanayin shi har tambayar shi tayi meke damun shi yace mata bai da lafiya zazza6i ke damun shi ga owais ya nemi alfarmar ya raka baba Obie lagos, baisan ya zaiyi ba yana jin nauyin yace bazai je ba
Hajiya saratu tace bazaima yiwuwa ba, zatayi ma baban magana anemi wanda zai bi sa suje tunda shi ba koshin lafiya gare shi ba.

kafin hajiya saratu tayi ma baba Obie magana Pravin yaji labari awurin hajjaty, a jiya daya shiga ɗakinta ya iske ta zaune tsakiyar gado tana ta kuka ya tambayeta meke damunta, nan take labarta masa baba obie ya kira ta adakinsa ya sanar da ita gobe kafin ya tafi zaisa jami'ai su maida marwa garin su gurin iyayenta, zata fi samun kulawa agurin su su kuma zasu cigaba da bata tallafi.

Da jin wannan maganar, pravin ya washe baki, bai ma tsaya ya karasa jin karashen zancen ba, Ya fuce daga dakin Ya koma dakin hajiya saratu ya tambayeta shin dagaske ne za'a maida marwa garin su tace mashi eh, ay itace ma tayi ma baba obie magana amayar da ita saboda su twins tana son su dawo gidan da zama.

farin cikine ya lullu6e parvin harya manta da karyar ciwon da yakeyi yace mata ay yama ji saukin zazza6in zaibi baba obie suje lagos din, tace mashi a'a gaskiya tafi son ya wartsake in yaso daga baya sai ya bishi, yasa naci akan shi dai zaije tace meyasa zai takura kansa bayan ba koshin lafiya gare shi ba, ya marairaice mata fuska da dadin baki ya shawo kanta harta amince bazata fada ma baba Obie ba.

Washe gari da sassafe, jami'an da za su tafi da marwa, suka doko sallama, a lokacin hajjaty tana adakinta tare da sauran yan aikin gidan sun hadu suna shirya mata kayanta, Baiwar Allah sai kuka take yi su kansu kukan sukeyi na rabuwa da ita, bayan sun kammala shiryata Hajjaty da Abla suka daukota sauran masu aikin na abiye dasu A harabar ajiye motoci su ka iske mutanan gidan sun hallara domin yi mata bankwana.

A lokacin bakowa marwa ke kallo ba face pravin dake ta kashe mata ido yana sakin wani dan iskan shu'umin murmushi duk idan ya fakaici idon mutane, marwa tayi kuka kamar ranta zai fita, saboda bakin cikin zata tafi batare da ta tona asirin wanda yai mata aika aika ba..

har suka shigar da ita cikin mota bata daina gunjin kuka ba, haka ta dinga bugun window glass din motar da hannayenta kamar zata fasa shi.

babu wanda ya fahimci mai marwa take nufi, gaba daya sunyi tunanin zafin rabuwa dasune yasa take yin haka, har alkawari hajjaty tayi mata akan kullum zata dinga kiranta awaya sosai ta kwantar mata da hankali, bayan sunyi mata bankwana Akan idonsu Motar ta fuce daga gidan bayin Allah sunyi kukan Rabuwa da marwa.

Pravin kau ranshi fari tass Kamar ya zuba ruwa ƙasa yasha Hankalin shi ya kwanta baida sauran damuwa, Ya kira zaid awaya yayi masu albishiri na tafiyar marwa, Ya kuma labarta masu maganar tafiyar da zai yi tare da baba obie, sannan Yace su dawo gida Yana son ganinsu kafin su tafi.

Bayan dawowar su twins, murna awurin hajiya saratu kamar ta shekera bata gan su ba, cos tayi kewarsu ko kaɗan batai masu fadan zaman su a hotel ba, haka shima Uban saima tarairayarsu da ya ke yi.

Wuraren ƙarfe shabiyu na yau, gaba daya Yan family din dake a estate din suka yi ma baba Obie rakiya zuwa Airport kamar wanda zai bar kasar, hada Owais da su Senate Lateef kowa da kowa, kamar karsu rabu da shi saboda kaunar da suke ma mahaifin su.
________________________✍️

(After One Day, Bayan kwana ɗaya)

Yana tsaye gaban Dressing Mirror, har ya kammala shirin xuwa Office, jikin shi sanye da kakin shi, fuskarshi kwata kwata babu walwala tamkar bai ta6a dariya ba, saboda matsananciyar damuwar data yi mashi ƙatutu a zuciyarshi, Ga rashin isasshen baccin da baiyi ba jiya idanun shi sunyi ja sun ɗan kumbura.
Chapter 169 · 0% Book details