← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 195 OF 238

Sashe 195

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

_Dogon voice note ta tura masu mai dauke da bayanin abunda Yaja hankalinta harta musunta tace ita kawai ta kaɗaitu da son addinin musulunci saboda kyawawan dabi'un Aunty Anila, tana burgeta tana sonta tana son yadda take janta ajiki, da yadda take kyautata mata, bata ta6a nuna wariya tsakaninsu ba, tana son tayi koyi da komai nata, yanayin mu'amalarta, kyawawan halayanta, da yadda take karatun al'qur'ani, hatta shigarta ta musulunci burgeta takeyi dama kuma ta ta6a yi mata tayin addinin tun farko farkon fara aikinta gidan Uzair ta nuna bataso, tun daga nan bata kara takura mata ba, tadaice mata tayi bincike sosai akan addinin musulunci zata gane abunda take son fahimtar da ita, kunji abunda yasa na musulunta kuma sai nagane shine addinin gaskiya, kuma Inaso ku musulunta don mu gudu tare mu tsira a tare_

wani chat nasu da Anila ta duba, yan uwan Ana ne su ka yi mata voices da murnarsu suka fada mata sun musulunta, tayi murna kamar kamar me sukace ta za6a masu suna tace ita sunan data canza ma kanta sunan nana Aisha, Ita kuma janet ta sanya mata sunan Khadija, sai Esther Zainab, bayan ta raɗa masu sunan janet tace sufa ko alwala basu iya ba, bayan haka basu san komai ba, tace kada su damu zata dinga koya masu kur'ani da hadissai acikin group din nasu itama da apps na musulunci take amfani da kuma sauraran karatun malamai da wa'azinsu ta haka ta ke samun Ilmi.

Lokacin da Aneelerh ke karanta Chat din, hawayene Cike tab da idanunta, wani irin murmushin farin ciki tadinga saki kamar wata zautatta, aranta ta ayyana ashe ana ta musulunta bata sani ba? Allahu akhbar, Abunda yafi faranta ranta, hada Yan uwanta ta musuluntar.

taji dadi da Ana ta musulunta ta silar ta, A hankali ta furta"Alhamdulillah Ya Allah na gode maka..." har sujjada saida tayi.

yanzu A ina zan samu ana? Ta jefa ma kanta tambayar? yanke shawarar kiran layin Yan uwanta tayi sam ta manta dare ne ta shiga danna masu kira babu wanda yayi picking, Zuciyarta cike fal da farin ciki ta jingina bayanta Jikin gadon su, kiraye kirayen sallar asubahi da aka fara ne yasa ta aje wayar, ta mike ta shiga toilet don tayi alwala.

Bayan ta sallame sallar, ta zauna tayi addu'o'in da ta saba yi daga cikin harda Ana tayi ma addu'a sosai, kafin ta mike ta dauko wayar Ana ta koma kan gadonta, Gallery ta shiga ta dinga budo hotunan Ana dana yan uwanta.

Ta shagala tana kallon su Unexpected yatsan ta ya danno video ba tare da sanin ta ba, shesshekar kukan da tajine Yasa Ta mayar da hankali akan videon..

wani irin faɗuwar gaba taji, Lokaci daya ta zazzare idanunta wadanda bakomai ne acikinsu ba face tsantsar tashin hankali da rudani gami da al'jabi, ta yi matukar razana da jin abun da kunnuwan ta suke jiye mata, gaba daya ta rude, gumin tashin hankaline Ya fara tsastsafo mata ta ko'ina a jikin ta, kafin kace me Tsigar jikinta ta fara tashi haikam, La66anta na kerma ta shiga ambaton inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Allahumma ajirni fil musibati...

tsabar kiɗimar da ta yi ne Yasa tadinga sambatu kowace addu'a tazo bakinta furta ta kawai takeyi, har saida takaiga junaid dake bacci ya farka a firgice sakamakon sallallamin dayaji Mommynsa nayi.

Yana buɗe idanunshi suka sauka akan fuskar Aneelerh wadda ta jike sharkaf da gumi, Idanunta sun kaɗa jawur har wani zazza6i zazza6i take ji a jkin ta..."

Kusan sau uku Junaid yana ambaton sunanta bata ji shi ba, saboda kwakwalwarta ta tafi hutun wacin gadi, abune da bata ta6a zata ba.

"Aunty Aneelerh? Kina ina ne nake jin kukan baby junaid" muryar zahra ce ta fargar da ita, a firgice ta zabura ta sauko daga kan gadon ta watsa da gudu ta shige toilet taja ta rufe.

lokacin da zahra ta shigo junaid kadai ta gani zaune sai kuka yakeyi idanunshi akan kofar toilet din dakin.

da sauri ta nufe shi ta zauna gefen gadon tare da daukar shi ta rungume a kirjinta"junaid lafiya kake kuka? Ina mommyn naka kota shiga wanka ne"? Da yatsa Ya nuna mata toilet door din"nan ta shiga da gudu, inata kiran shunanta bata amsa ba..." da ɗan mamaki ta dubi kofar toilet din kafin ta maida dubanta ga junaid"i'm sorry, Yi shiru, mu jira ta fito" kwa6e fuska yayi "to ai jiya nace ta hada min tea bata kawo ba, har bacci ya ɗoke ni" kallon cup din dake ajiye kan Table tayi"Ko shi ne wannan ta ajiye maka" sai da tay maganar ya lura da cup of tea din da Aneeleeh ta ajiye.

Zahra tace"shine ma, amma naga Ya huce, Bari naje na hado maka wani hada noodles zan dafa maka"

Aneelerh dake acikin toilet tafukan hannayenta biyu toshe da bakinta gudun kada kukan ya kubce mata, tana cikin halin ha'ula in nan tajiyo muryar junaid daga waje yana kwankwasa kofar toilet din"mommyn ki fito"

gaban faucet taje ta wanko fuskarta ta buɗe kofar ta fito, a tsaye ta same shi ya ruƙe qugun shi fuskar shi a daure kamar wani babban mutum.

"Junaid, i'm sorry, jiya na kawo maka tea din sai na iske kana bacci" da shagwa6a yace"tea dinma ya huce, aunty zahra zata haɗo min wani kuma ma zata dafa min noodles..."

"Yawwa, Yanzu mu shiga toilet inyi maka brush, kafin ta dawo" amsa mata yai da toh, cikin sauri taje ta ajiye Wayar Ana Cikin rigar pillownta ta zuge ta, kafin ta dawo ta ɗauki junaid ta shiga toilet da shi.

da shigarsu ba'afi minti talatin ba, sai ga zahra ta shigo hannunta ruke da madaidaicin tray mai dauƙe da plate biyu na noodles da zafinta tare da cups of tea ta ajiye kan table din gaban gadon, ta zauna tana jiran fitowar su don taji motsin ruwa a toilet.

Wayar hannunta ta cigaba da dannawa, Har zuwa lokacin da Aneelerh ta fito bayanta a goye da baby junaid, har wanka tayi mashi ta lullu6e shi da towel dinsa.

Yana ganin abunda zahra ta kawo masa ya fara Washe baki, tun da ta fito take ta kokarin kaukauce ma zahra don kada su hada ido..

"Auntyna Barka da safiya kun tashi lafiya?

"Lafiyalou zahra, Hope kina lafiya" da fara'a tace"lafiyalou"

"Sannun da kokari zahra, baki gajiya dayi mana dawainiya" ta fada tare da daura junaid kan gadon.

"Haba Aunty Aneelerh, wata irin dawainiya"? Ta faɗa tare da mikewa ta nufi closet din kayan junaid"Yaushe zai koma school ne?

Ta fada yayin da take dauko mashi kayan da zai sanya

"In sha Allah next week zai koma"

Riga da wando ta dauko mashi, da kanta ta sanya mashi, Aneeleeh dake a zaune ta zabga uban tagumi kamar wadda ta rasa mafaɗi a duniya

Zama zahra tayi kusa da ita, ta daura junaid kan laps dinta, tea ta fara bashi Ya shanye duka kafin ta dauki fork ta soma nannado noodles tana tura mashi abaki yana ci.

sam bata lura da Halin da Aneelerh take aciki ba, sai surutu takeyi tana fadin"Aunty Aneelerh ba zaki ci bane,? Shiru taji bata amsa bata ba, juyowa ta danyi tare da leƙa fuskar ta, gabanta ne ya faɗi ganin tsantsar damuwa akan fuskarta, idanunta sun kaɗa jawur.

Da karfi zahra ta furta"Aunty Aneelerh"! Firgigit tayi tare da kallonta razanar da tayi yasa Zahra jin fargaba.

Adabarbarce ta furta"am...um...zahra.. Har kin sa mashi kayan..." a ruɗe zahra ke kallon ta duk tabi tasha jinin jikinta..

"Aunty Aneelerh, Lafiyarki kuwa? Kinga yadda idanunki suka kumbura, kumatunki sun yi ja, kamar kinyi kuka, gaba daya ma kin sauya min kwata kwata babu nutsuwa atare dake"

dakyar ta daidaita nutsuwarta cikin sanyin murya tace"bakomai wlh, lafiyana lou, kawai tunanin duniya ne..." girgiza kai zahra tayi"wlh kallo daya mutun zaiyi maki ya fahimci baki cikin nutsuwarki, auntyna in akwai abunda ke damunki, ki fadamin dan Allah sai mu nemi mafita a tare..."

murmushi ta danyi"Zahra ki yarda kawai babu komai" gyaɗa kai tayi"shikenan, ga noodles din nan ki ci pls, kada ki zauna da yunwa ni zan tafi gurin aiki har na kusa yin late"

"Nagode da kulawarki zahra, ki kula min da kanki" tana murmushi tace"kema haka" kar6ar junaid anila tay don taci gaba da ba shi abincin.

Zahra Harta kusa ficewa daga dakin ta tsinkayi muryar Aneelerh"Uncle na nan ne"? Zahra bata kawo komai aranta ba tace"Eh, yana nan dakinsa"

"Okay, " fuce wa zahra tayi daga dakin..

Bayan tafiyar zahra, da rabin awa ta fito Hannunta dauke da baby junaid ta nufi dining area, tunkafin ta karasa ta hango mutanan gidan gaba daya sun hallara akan dining chairs zahra ce kadai babu atare da su.

tsayar da idanunta tayi akan Uncle dan iya daya hakimce kan kujera Ya ƙwama wani uban glases akan idanunsa, Ya tasa farfesun yan ciki shake da plate sai sharbar romo ya ke yi kamar ƙaramin yaro, yanayin fuskarta ne ya canza zuwa matuƙar bacin rai, fusata, da tsantsar tsana Aranta ta furta Mugu bashi da kama, Cike da rashin kuzari ta karasa cikin girmamawa ta gaishe da su da fara'a suka amsa mata, mami ta mika hannu ta kar6i junaid ta zaunar da shi kan laps dinta nan fa ya fara zuba mata shagwa6a.

Tun da ta zauna mami ta yi serving dinta duk cokali daya idan tay sai ta dago ta kalle shi gabanta sai faduwa yakeyi, hakanan yaji kamar Ana kallonsa yana kokarin dagowa tay saurin kawar da idanunta, a dabarbarce ta shiga tura chips abakinta, Mayar da kansa yai ganin ba abunda ya zata bane.

"Aunty Anila ya maganar komawar Junaid School ne? Tun da yaji sauƙi ya kamata amaida shi, karatu yana ta wuce shi"

"Zahrama ta tambayeni dazu, in sha Allah sati mai zuwa zai koma"

Mahboob Yace"Allah Yakaimu lafiya" ta amsa da ameen
Chapter 195 · 0% Book details