← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 238

Sashe 86

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yau mun dawo gida atare, ya gajiyar aiki" dagowa sukayi atare suka dube shi
"Daddy Ba dadi, wallahi, na gaji, ni fa kasan bana son wahala.." zayn ne yayi maganar,
Zaid Yace"Alhamdulillah daddy, kaima ya gajiyar naka aikin"?
Murmushi yayi kafin yace"ay ni bana aiki, ina da masu yi min komai, illa Iyaka in karshen wata yayi in kwashi Albashina...." kallon juna sukayi da mamaki akan fuskokin su,
Ko ajikinsa Yaci gaba da fadin"tuntuni naso In wayar maku da kai amma kuka ƙi yarda, Kunfi so ku yi ta wahala akan albashin da bai taka kara ya karya ba, har atm dina na baku don kuyi irin rayuwar da kukeso amma kuka ki kar6a saboda baku yarda dani ba ko.."
Shiru sukayi suna kallonshi, kafin Zayn yai kafin halin cewa"daddy ta yaya zamu kar6i kudinka? Bayan ba halal dinka bane!! Baka aiki kuma kana kwasar albashi, hakan na nufin haramun kake ci, daddy kaji tsoron Allah, ka riga da kasan hukuncin wanda Ya gina kansa haram..." bai ƙare maganar ba, Pravin yayi saurin dakatar da shi ta hanyar ɗaga mashi hannu, da kakkausar murya ya furta"Enough! Don't you dare repeat what you just said to me!! Gidan ubanwa nake cin haram? duk wani kuɗi da nake da su, Hakkina ne ina da goyan bayan waɗanda suka ɗaura ni akan muƙamin da nake da shi. ..." Yana faɗin hakan rai a6ace Ya nufi cikin gidan, da sauri zaid yabi bayanshi tare da shan gaban shi.

"Daddy ka yi hakuri, naga ranka ya 6aci, Dan Allah ka yi hakuri da abun da zayn yace maka! ka yafe masa kada ka ruke sa a zuciyarka..."

Murmushin gefen fuska pravin yayi"kada ka damu my son, komai Ya wuce"
Ajiyar zuciya zaid Ya sauke, Tare da ruko hannun daddyn nasu suka shiga parlour.

Zayn dake kallon su har sai da suka 6ace ma ganin shi, kafin ya jingina bayan shi jikin motarsu, kalaman zahra ya fara tariyowa, a lokacin da ta kira shi Yana a office, ya gama watsewarsa tare da abokiyar aikinsa yana akan network shiyasa Ya zazzaga mata masifa son ranshi aranshi ya ayyana ko sun samu shiga estate din? Ta6e la66ansa Yayi irin bai damu din nan ba, Ya wuce Ya nufi cikin gidan

"CHIEF OWAIS💪💋*

Yana a cikin Katafaren Office dinsa dake a isod Headquater, office ɗin Ya haɗu, an ƙawata shi da high-end supplies komai na cikinsa launin blue sky ne kalar da yafi so, office din Yana da mugun tsaro gaba daya na'urori ne ke sarrafa komai na cikin sa.."

Daddaɗan ƙamshin turarensa Ya gauraya da ni'imtacciyar iskar dake ratsa saƙo da lungu na office din, a yayin da yake azaune kan wata tamfatsetsiyar Excutive chair Ƴar ubansu, Ya ɗaura kafarsa ɗaya bisa ɗaya, daga gaban shi luxury table ne mai ɗauke da High-end computer da sauran kayan amfaninsa dake a baje kan table din

A hankali Ya buɗe idanunsa dake a lumshe, Ya cigaba da operating computer din gabansa,

Adjusting webcam dinsa yayi, kafin ya danna video call Ya dan dakata Yana jira a amsa mashi.

a hankali fuskar commender ta bayyana ta cikin screen din

Murmushi suka sakar ma junansa, Cikin harshen turan ci suka fara magana
"Commander, good to see you, sir," ya faɗa tare da sarah mashi da hannu

"Chief, good to see you too," shima ya sarah mashi.

"What can I do for you?"

Numfasawa chief yai kafin yace"I'm calling to extend an invitation to a high-level meeting in Nigeria, dangane da yaran da kuka damƙa mana case din su" Ya ƙare maganar, Cike da sa ran zai amsa mashi

Jinjina kai commender din Yayi na ɗan wani lokacin Kafin Ya furta" okey, What's the current situation?...bayani ya fara kora masa dangane da halin da ake ciki na binciken prisoners.

Tun da ya fara commender Yake ɗan jinjina kanshi alamar gamsuwa, bayan ya ƙare maganar yace"yanzu wani mataki zaku fara ɗauka"?

Chief yace"That's what we'll discuss during the meeting"

"Tunani mai kyau, zanyi magana da na sama dani, idan har na samu goyan bayan su, zamu halaccin meeting din, yaushe ne kuma a ina za'ayi"?

"Upper week, in Abuja. I'll send over the details. Thank you, Commander..." Ya fada tare da sara ma shi da hannu.. Shima commender din Ya sara mashi
bayan sunyi sallama Ya kwantar da kansa jikin kujerar

"DDG Is coming" Muryar na'ura ce ta ratsa kunnansa, A hankali Yakai idonsa ga duban Glass door ta office dinsa wadda ke kokarin zuge kanta

Big guy ne Ya shigo sanye Cikin kakinsa, Cikin girmamawa Ya sara mashi.

"Sannu da aiki Yalla6ai, Na ji shiru baka fito ba, ko baka lura da time ba ne"? Kallon agogon hannunsa yayi ƙarfe biyar na marece, har time din ta shin sa yayi bai lura ba.

"Have a seat"

Zama big guy yai kan kujerar dake fuskantar chief kamar yadda ya umarce shi
"Munyi waya da commender..." a ƙagare big guy yace"ina fata Ya amsa buƙatarmu"!
Calmly ya zayyana masa tattaunawar da su kai, wani irin farin cikine Ya bayyana akan fuskar shi"Allah Yasa mu ji alkhairi" Ya amsa mashi da ameen

Shiru sukayi na wani lokaci kowa da abunda Yake saƙawa aranshi

"Ya kamata ka tashi muje in kaika gida, burina ka huta..." murmushi chief yayi"nagode da kulawarka agare ni, Ina boss ko har ya tashi aiki"?

"Tun wuraren huɗu ya koma gida, kasan mutun mai Iyali, ba kamar mu da muke tazurai ba..." da zolaya yayi maganar, harara chief Ya dan watsa masa batare daya furta wata kalma ba

Ya miƙe Ya nufi kofar fita, da sauri big guy yabi bayansa a tare suka fito daga office din.

Tsayawa fasalta haduwar isod headquarter bata baki ne, abun sai wanda Ya gani, lifter suka hau ta sauke su down, ta ko'ina ka kalla Jami'an isod ne sanye cikin kakinsu tun daga senior agents dinsu har izuwa jenior agent, duk inda suka bi cikin girmamawa jami'an suke sara masu, Har suka fito daga headquater din, kaitsaye suka nufi katafaren parking space din su, dankara dankaran motocine makil tare da bikes dinsu killace a harabar.

Da sauri wani agent Ya bude masu backseat na motar da zasu shiga, bayan sun shiga kowan nan su Ya zauna, agent din dake jigilar daukar su Ya yi wa motar key cikin ƙwarewa Ya fara driving dinsu zuwa gida.....

Dai dai lokacin da motar su ta kunno kai cikin gidan, Wayarsa ta fara ringing, lokacin da ya duba sunan mai kiransa yayi mamakin ganin aunt saratu, Cos Ya manta when last Yar tahalikar nan ta kira da sunan tayi magana da shi.

Picking call din yayi tare da kara phone din a kunne, Cikin ladabi Ya yi mata sallah tare da gaishe da ita

Ko sallamar shi bata amsa ba ta furta"Owais, bayan sallar magbrib, Ka same ni a pool yard, Ina son yin magana dakai"! Cike da bada umarni ta furta, bata jira amsar shi ba, Ta katse kiran.

Kurawa screen din wayar ido yayi ba tare da ƙyaftawa ba..."

"Yalla6ai, Mun ƙaraso"! Big guy ne Ya fargar da shi, sam bai lura sun karaso ba, Fitowa yayi da sauri Ya nufi Cikin main falo din gidan

Yana shiga bedroom dinsa, Ya rage kayan jikin shi, Ya shiga toilet domin Yin wanka,

*HAJJATY*

Safa da marwa Take Yi atsakar dakinta, tun safe take sa ran zuwan pravin shuru bai leko ba, Hankalin ta ba karamin tashi yayi ba, gani take kamar wani mugun abunne zai faru da ita, saboda abun da ya faru jiya yayi matuƙar daga mata hankali.

Yanke shawarar fita neman shi tayi, da sauri ta dauko mayafi ta yafa akanta, Tana kokarin fita suka ci karo da juna har saida ta bangaji kirjin shi, da sauri taja da baya tare da dafe gefen kanta da hannu daya

"I'm sorry wifey, Ina zaki je ne"? yayi maganar yayin da yake nufar cikin dakin idanunsa akan fuskarsa

From head to toe Ya kalle ta, farat ɗaya ya gane akwai wani abu dake damunta, da alama ko wanka batayi ba.

"Baki da lafiya ne" ya yi maganar tare da ruƙo hannunta suka zauna gefen gadon ta

"Baki ji ina magana ba? Fashewa tayi da kuka tare da kifa kanta akan kafadarshi

Hankalin shi yayi matuƙar tashi jin kukan hajjaty, yana daga cikin abunda Ya tsana arayuwarshi.....

Cikin shesshekar kuka tace"pravin ina cikin tashin hankali, Saboda akwai mai bibiyar rayuwata, daren jiya bana acikin kwanciyar hankalina, a tsorace na kwana, ko baccin kirki banyi ba, ina ta jira ka dawo shiru baka zo ba..."

Tuni yanayin fuskarshi Ya canza zuwa tsantsar 6acin rai,

"Fada min meya faru dake a daren jiya? Wani ya shigo ne"?....ɗagowa tayi da kanta hawaye na sintiri kan kuncinta ta kwashe komai ta sanar da shi...

Tafukan hannayensa ya daura kan fuskarta,A hankali Ya fara share mata hawayen ta

"Ki yi hakuri, in sha Allah koma wanene ke naman ki da sharri kan shi zai koma, Allah Yana atare dake wani bai isa Ya cutar min dake ba! ...." bai kare maganar ba, tace"bansan ya zanyi ba, wallahi ina jin tsoron ranar da asirinmu zai tonu, pravin bana son abunda zaija mu rasa kimarmu da darajarmu a idon mutanan gidan nan, saboda ina ji araina akwai wanda ke son ya tona mana asiri shiyasa aka fara bibiyana.." ta faɗa tana jan numfashi kafin taci gaba da cewa"saboda fargaban abunda Ya faru daren jiya, ko abinci banci ba tun safe har yau kamar mai azumi, wanka ma nakasa yin shi...."

Ta ƙare maganar, tana kallon cikin idanunshi

"Tuntuni saida naso In siya maki gida daban inda zakiyi rayuwarki cikin kwanciyar hankali, amma sai kika nuna bakison rabuwa da su....abunda nake jiye mana kenan...

"Duk laifinka ne, Abunda kayi min awurin dinner din hateem shine Yaja har wasu suka fara zarginmu, kuma ni gaskiya bazan bar gidan nan ba, kawai ka nema min mafita ..."

Jinjina kanshi yayi tare da ruko hannayenta acikin nashi"zan tambaye ki wani abu" daga mashi kai tai alamar toh

"Idan kika kama 6era adakin ki Yana yi maki 6arna, kuma kinsan zai iya haifar maki da gagarumar matsala wani hukunci zaki masa"?

"Meyasa kayi min wannan tambayar"?

"Kedai ki bani amsa"!
Chapter 86 · 0% Book details