← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 238

Sashe 32

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sauke farantan hateem yayi can gefe ɗaya ƙasa, kafin ya mayar da hankalinsa akan danish, rungumo shi yayi ajikinshi, hannun shi ɗaya dafe da bayan shi, ɗayan hannun yana ruke da wayar shi, Camera ya shiga don ya yi masu hotuna ko ya samu waɗanda zai dinga gani yana ɗebe kewarsa, da sauri Danish ya runtse idanunsa alamar baya so, kokari yake ya buge wayar gaba ɗaya hakan ba karamin ɗaga hankalin hateem yayi ba, cikin sanyin murya ya furta"pls ka bari nayi mana hoto mana, inaso na samu wanda zan dinga kallo bayan na koma ƙasa ta," cikin sigar lallashi yake yi mashi magana akan ya buɗe idanunsa, dakyar ya samu ya ɗan buɗe su, maimakon ya kalli camera din sai ya dinga kallon fuskar hateem din, babu yadda baiyi dashi ba akan ya kalli camera amma yaƙiya kamar wani karamin yaro, A haka hateem yadinga daukarsu hotuna idanun danish akan fuskarshi, wasu hotunan ya rufe idanunsa, hada video yayi masu mai ɗan tsayi, ya kwantar masa da kanshi saman kafadarsa, da wanda ya sumbaci forehead dinsa, kamar wani ɗan cikinsa, A kalla ya dauki hotunansu sunkai Talatin, bayan video da yayi masu kusan goma.

Kafin ya gama ɗauke ɗauken hotunan, kwatsam Yaji danish Ya ƙanƙame shi da hannayensa da farko ya ɗan ji fargaba amma daga bisani da yaga yana lumshe idanunsa sai yaji hankalin ya kwanta, wani baccine mai daɗi yayi awon gaba dashi, kanshi asaman shoulder din hateem, A hankali Ya gyara mashi kwanciyarshi, ya rungumo sa, kamar zai maidashi cikin shi, hannayen danish na abayan hateem ya ƙanƙamesa kamar wani yace zai ƙwace masa shi.

Wani kallon so da kauna hateem yake binsa dashi yayin dayake yin baccin, A hankali ya soma shafa bayan shi da yatsun hannayensa kafin ya zura hannun cikin sumar kansa tamkar yanayi mashi susa, harta numfashin danish sai da ya canza saboda daɗin da yaji na abunda Hateem ke yi ma sa.

Bakinsa yakai saitin kunnan danish, cikin muryar raɗa yayi mashi magana.

"Do you feel what I feel about you?"

Ya faɗi hakan batare daya sanya ran danish zai tanka masa ba, a tunaninsa yayi zurfi a baccin nasa.

Kamar daga saman yajiyo daddaɗar muryarsa tamkar ana busa sarewa ta ratsa kunnansa da cewa "Yes, I do. I feel more than you might think"

wayyo Allah dadi prime minister tamkar zai zauce tsabar murna da jin maganar danish, Cigaba da kallon fuskarsa yayi tamkar zai haɗiye sa.

"Nakasa yarda cewa kaine kayi min magana da bakin ka, ko dai kunnuwana ne suke jiyo min ba dai dai ba"? da biyu ya fadi hakan saboda yana son ya ƙara jin muryar shi.

"No, ni na maka magana" danish ya bashi amsa idanunsa a rufe, har time din basu raba jikin su daga na juna ba

"Meyasa ka damu dani"? Danish ne ya jefa mashi tambayar

Murmushi hateem yayi kafin ya furta"tun lokacin da nafara Yin tozali dakai, Naji na kamu da matsananciyar kaunarka, duk da bansan wanene kai ba, amma naji ka kwanta min araina, ka sace min zuciyata, babban abinda yafi jan hankalina gare ka shine kama da muke da juna, Ina jinka tamkar ni na haifeka, Allah ne kadai yasan son da nake maka Danish, wallahi bana son rabuwa dakai, bana son in tafi in barka, don bani da yarda zaniyi da natafi da kai" Kalaman da yake furtawa daga cikin zuciyarsa suke fitowa, abunda ke ransa ne yake bayyana masa ko ya rage radadin da yake ji na kaunarsa .

A hankali danish ya ɗan buɗe idanunsa yana satar kallon fuskar hateem dake a dab da tashi, wani irin kallo yake jifar shi da shi mai wuyar fassaruwa batare da prime minister Ya ankara ba.

"Bansan su wanene Iyayenka ba, bansan dalilin dayasa sukayi watsi da rayuwarka ba, amma bana tsammanin akwai wanda zai samu ɗa kamarka ya jefar sai dai idan da wani dalilin"

Runtse ido danish yayi sam baya son anayi mashi maganar iyayen sa.

Muryarshi na dan rawa ya furta"ka daina yi min magana akan iyayena, bana son su bana son duk wani abu daya shafe su, If I could see them, I would kill them."

A ruɗe prime minister ya dubi fuskar danish da tsantsar mamakin yadda kalaman suka fito daga bakinsa, har kokwanto yayi anya shi yayi maganar?

Ko da yai yunkurin tambayarshi meyasa yace haka, sai jinshi yayi shiru alamar wani baccin ya dauke shi....

Haƙiƙa furuncin da ya yi akan iyayen su sun tada masa hankali, sun tsaya masa a ƙahon zuciyarsa, duk da baisan dalili ba amma yaji fargaba aransa, musamman da ya ambaci Idan ya gansu zai kashe su .......

Lumshe idanunsa yayi, tare da ƙara janyo danish ajikinshi, yaci gaba da ɗan bubbuga bayansa kamar mai lallashin ƙaramin yaro a haka harshima baccin yayi awon gaba dashi, wata irin iskace mai ni'ima taci gaba da kaɗa wurin da suke.......

gaba ɗaya abun da ke faruwa akan idanun Yazrin, sai dai basu samu damar jin komai da suke tattaunawa ba atsakanin su saboda akwai tazara.

Nannauyar ajiyar zuciya Gimbiya mujeedat ta sauke tare da kallon Yazrin dake a gefenta"gwanin ban sha'awa, sun burgeni, a yadda suka kwanta kamar Uba da ɗansa, ban ta6a jin zafin rashin ɗa bamiji ba sai ayau dana kalli Hateem da yaron nan, wallahi sunyi min kyau sun tafi da imanina ......." Cikin sanyin murya Gimbiya mujeedat tayi maganar.

Jikin Yazrin yayi sanyi lakwas tamkar wadda aka zarewa laka, idanunta sun ciko tab da kwalla ta soma magana ba tare data janye idanunta daga kan shimfiɗarsu Hateem ba.

"Daddy ya bani tausayi, na tausaya masa mommy, daga shi har matashin nan, Ina kaunarsa Ina jinshi kamar ɗan uwana na jini... " da raunatacciyar murya tayi maganar.

"Mommy abun da yafi ta6a zuciyana, yaran ba su da kowa a daji aka tsince su kamar yarda naji akhi owais Ya faɗa, wallahi banji dadin yadda Su oum saratu suke jifarsu da munana kalamai ba, ni abun da ya daure min kai Yaran sunyi kama da family din daddy sosai"

Jinjina kai Gimbiya mujeedat tayi ba tare da ta iya furta komai ba, Ta yunƙura ta miƙe Cikin takun nutsuwa Ta nufi shimfidar su hateem, Yazrin na zaune bata bi bayanta ba, bakomai zuciyarta ke tariyo mata ba, face lokacin data haifi baby boy din su da suka rasa, haƙiƙa taji bakin cikin da bata samu damar ganin ko da gawarsa bane, taso ace ko da fuskarsa ne ta gani, tuna wannan yasa taji hawaye sun taru cikin idanuwanta

Adai dai bakin shimfiɗar ta ɗan zuƙunna tana kallon danish from head to toe, yayin da zuciyarta ke azalzalarta da kaunarsa, sai kallon shi takeyi babu kyaftawa, ranta ne ya raya mata wani abu da bata da tabbaci akanshi, hakanan taji tana son ta jaraba gwadawa, Miƙewa tayi da sauri ta zagaya ta dayan bangaren da farantan abincin da aka kawo masu suke, ta zaro ƙaramar wuƙa ta yanka fruit, ta dawo bangaren inda danish Yake ta zuƙunna duk akan idon Yazrin da mamaki yagama cikata, zuciya da sake sake arude ta furta me mommy zatayi wuƙa"? hankalin ta yadan tashi tsoron ta kada ta aikata wani abu duk da tasan hasashenta bazai ta6a zama gaskiya ba...

A hankali ta ɗaura ziraran yatsun hannunta kan sumar danish ta ruƙo ƙasanta, Cike da fargaban kada su farka, tana yi tana kallon fuskokinsu cikin kwanciyar hakali suke fitar da numfashinsu, bacci yayi dadi

Yatsun hannunta na kerma ta yanki sumar kan danish da wuƙar, ajiyar zuciya ta sauke tare da miƙewa ta mayar da wukar cikin kayan abincin kafin ta juya tana faman sauke ajiyar zuciya ta nufi Yazrin tunkafin ta ƙarasa yazrin ta miƙe tana tana fadin"mommy! Meyasa kika datsar mashi gashin kai"! Idanunta azare ta fada tana nuna ziraziran gashin danish da gimbiya mujeedat ta cira daga kanshi

Fuskarta dauke da murmushi tace "Ki kwantar da hankalin ki, kinsan dai mom dinki ba matsafiya bace," dariya yazrin tayi"ina kyautata maki zato a koda yaushe Rabin raina" lumshe ido gimbiya mujeedat tayi"ki ajiye min gashin nan a wurinki, Idan muka koma gida zan tambaye ki shi" da sauri Yazrin ta kar6i gashin daga hannun mom mujeedat, ta cire cover din wayarta ta ɗaura gashin abayan wayan kafin ta mayar da cover din sosai ta matse shi ta yadda bazai ta6a faɗowa ƙasa ba.

"Yanzu ki zo mu koma dinner hall, kada aji shiru babu ni babu hateem bayan saboda mu akayi taron" amsa mata yazrin tayi da toh" a jere suka nufi hanyar fita daga garden din, suna tafiya Yazrin na waiwayon shinfidar su danish, har saida ta 6ace ma ganinta tukunna ta dauke idanunta daga gare shi.

*Dinner Hall*

Bayan zahra ta kammala yin wayar, Jiki na rawa ta dawo Ciki tana nema unaisah, kamar zata zauce sai ƴan waige waige take yi babu ita babu alamarta, kusan sau uku tana zagaye tsakar hall din wurin neman unaisah amma babu ita, zuciyarta ba ƙaramar karaya tayi ba, Har cikin ranta bata ji dadi ba, saboda taso su sake ganawa da juna, Yarinyar ce ta kwanta mata aranta, musamman yadda ta sakar mata fuska har ta amince mata su kayi hutuna, dabara ce ta faɗo mata, ganin ɗaya daga cikin matasan ƴan matan a tsaye tana kallon masu yin rawa akan dance floor sai murmushi take saki, da sauri Zahra ta nufe ta, muryarta da sanyi ta furta"sannu baiwar Allah" firgigit batool ta dubeta da alama ta razana don bata tsammaci jin muryar wani a kusa da ita ba

"Kiyi haƙuri na baki tsoro ko"? da fara'a zahra tayi mata maganar, batool kuwa sai kallon bakuwar fuskar takeyi taƙi tanka mata, gani take kamar zata cutar da ita ne tun da ta fahimci basa son su

Miƙa mata hannu zahra tayi"ni suna zahra, ke fa"? Cike da rashin yarda ta furta"batool" muryarta da ɗan rawa tayi maganar, ba tare da ta ɗaura hannunta asaman na zahra ba, nan take zahra ta fahinci tsoron ta take ji hakan yasa tace"ki kwantar da hankali yar uwata, Bana ɗaya daga cikin waɗanda suka ci muku mutunci ɗazu...." still bata saki fuskarta ba
Chapter 32 · 0% Book details