← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 238

Sashe 65

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bari na kawo maka dinner dinka nasan kana jin yunwa, but pls ka shiga toilet ka wanke fuskarka bana son ganin hawayen nan" ta fada tana nuna face dinsa da yatsa amsa mata yai da toh da sauri ya sauko daga kan gadon Ya nufi toilet.

Tana ta bin bayansa da kallo har ya shige kafin Ta mike ta fito daga dakin

Kitchen ta shiga ta shirya masu abinci ta fara kaima jazz a room dinsa kafin ta dauki na sir mubarak ta nufi dakin su

Lokacin da ta shiga a tsaye ta same shi hannun shi ruƙe da wayarshi Yana daddanata har ya sanya kayan baccinsa

"Ina kika je ne" ya fada ba tare daya kalle ta ba

"Na shiga kitchen shirya maku abinci ne," ta fada tare da ajiye masa tray din bisa table, murmushin gefen fuska ya dan saki batare data ankara ba, abun da bata sani ba tun time da ta shiga dakin jazz Ya fito Yabi bayanta gaba daya ya ji maganganun da su ka tattauna har recording voices dinsu yayi a wayarsa, yayi mamaki abun da yaji suna tattaunawa, maganganun sun tsaya masa aransa, wani lokaci turai tana da zurfin ciki, in har ba la6e yayi mata ba ita da jazz bayajin damuwarsu sai in tura takai bango tukunna take sanar da shi.

_______________________________✍️

Aneelerh har tayi shirin kwanciya bacci, sautin ringing din wayarta ya dakatar da ita, A hankali ta kai hannu ta dauki wayar ganin sunan surukar arziƙi yasa tayi saurin picking call din idanunta na akan baby junaid dake kwance kan mattress Yana sharar baccin sa

Cikin girmama suka gaisa da junansu

"Aneelerh kwana biyu? Ya ki ke Ya su mamin"?

"Alhamdulillah, muna nan lafiya lou"

"Ina jikan nawa ko har anyi bacci"

"Yayi bacci tun ɗazu"

"Allah sarki nayi missing nashi, Ya maganar zuwan naku?

"In sha Allah, cikin week din nan zamu zo"

"Allah yakaimu lafiya" ta amsa mata da ameen daga bisani sukayi sallama taso ta fada ma hajiya adama zancen dawowar benazir amma ta bari sai benazir ɗin tazo gidansu sai ta kira ta awaya suyi magana don ta bata mamaki, murmushi tayi tare da ajiye wayar kan nightstand, ta janyo junaid on her chest ta rungume abun ta.

_________________________________✍️

_Dare Mahutar bawa, sai dai bakowa ne ke samun kwanciyar hankalin runtsawa a cikin sa ba, saboda akwai wanda ya manta yaushe rabon da idanunsa su runtsa saboda rashin kwanciyar hankali_

*👹GIDAN KURKUKUN ƘADDARA👹*

Daki ne madaidaici mai fadi da tsayin gaske, irin ginin dutsen nan ne dayai shekara aru aru, daga saman dakin fitilun kwai ne guda uku masu haske idan ka kalli bangon dakin ta ko'ina jirwayen jinine da ya daskare, kai harta iskar dakin ta gauraya da karnin jini da warin jikin mutanan dake rayuwa a cikin sa.

Matasan Ƴan matane zazzaune kan gadajen ƙarfe, kowaccen su tana asanye da guntuwar riga launin ja wadda bata rufe gwiwar ƙafarsu ba sun rame sun ƙanjame fatar jikinsu duk sahun yakushi da kurajen fata kai gaba dayansu sun koɗe baka gane fari acikin su saboda duhun da fatarsu tayi wanda bakomai ne yajawo hakan ba face uƙubar da suke fuskanta, wadannan bayin Allahn babu irin tashin hankalin da ba su gani ba sunga bala'e da masifa tsirararsa, gaba daya an salwantar da rayuwarsu, tun lokacin da aka kaddara masu rayuwa agidan kurkukun ƙaddara amfani ake da su kamar injina, babu wani sassauci.

gaba ɗayansu babu wacce ta haura shekara sha bakwai dukansu matasan Ƴan matane gwanin ban tausayi, dukkan gabban jikinsu sun raunata, ko tafiya ba su iyayi sai dai adauke su akai su inda za'a yi amfani da su in angama a dawo da su😭 zuciyarsu da fargaba take bugawa, numfashin su da tashin hankali suke buso shi, idanunsu sun kumbura suntum sun ƙafe saboda tsabar kukan da suke sha wanda tun sunayi hawaye na zuba har takaiga ruwan hawayen sun daina fitowa sai dai kukan zuciya mai ɗacin gaske, basu da wani burin dayawuce Allah Ya dauki ransu su huta.

Biyo bayan da Garkuwa Ya gudu tare da wasu daga cikin prison haƙiƙa ran Elders yayi mugun 6aci matuƙa sun harzuƙa evil heart dinsu ta hasala, wanda silar hakan Yaja suka fara azabtar da sauran prisoners dake agidan kurkukun ƙaddara, babu imani ko miskala zarratin yanzu ko abinci mai dadi babu a gidan kurkukun ƙaddara babu wani jin dadi ko na daƙiƙa sai baƙar izayar rayuwa, Allah ne kadai Yasan adadin jinin da suka zubda na yaran da suke raino, da kuma Yaran da suka gur6ata ma rayuwa, wani shiri suka fara yiwa kansu saboda suna hasashen akowani lokaci za'a iya kawo masu farmakin bazata, kuma suna da tabbacin asirin su yana dab da tonuwa, basu ta6a fuskantar barazana da tashin hankali irin na wannan lokacin ba!!

_Zaman tattaunawa sukayi a karo na biyu a dakin sirrinsu wanda a lokacin suka yanke shawarar za su ba ɗaya daga cikin Evil giant ɗin da suke da su horon zama prison shield saboda asamu wanda zai maye masu gurbin Garkuwar su da suka rasa saboda sun fahimci yayi masu nisan kiwon da ba zasu iya tanƙwara shi ba, da buƙatar su samu wanda zai zamanto abokin karawar Garkuwa, saboda a halin Yanzu Idan aka kawo masu farmaki tare da shi to kuwa tabbas za'a ci galaba a kansu tun da babu wani giant da zai Iya karawa da shi idan ba su elders din ba, amma Idan suka gurfanar da sabon Giant din su mai ruƙe da mukamin prison shield zai yi wuya a iya rusa su in ba wani iko na Allah ba, sannan shi wannan giant din zai iya aikata duk wani rashin imani da suke so, ba a halicci zuciyarsa da imani acikin ta ba, baƙin mugune kuma azzalumin mutun ne shu'umi mai hadarin gaske, baisan menene tausayi ba, kurma ne sannan makahone bayaji baya gani in ba umarnin ubayen gidansa ba wato Elders, Shi fa wannan giant din baida mararraba da bakin shaidanin Aljani saboda sune suka rinjayi halittarsa ta ɗan adam_

*Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️*

*Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*

3196407426

First bank

Bature Hafsat Muhammad,

*bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268*

Sponsored Post
Tags
Kurkukun Kaddara
YOU MIGHT LIKE
POST A COMMENT
Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post
Next Post
GET IN TOUCH
Facebook
twitter
YouTube
Instagram
Whatsapp
SUBSCRIBE US

OPINION
FACEBOOK

COMMENTS
CATEGORIES
Africa
(1)
Al'adu
(1)
Alkamawa
(3)
Article
(3)
Blogger Tips
(1)
Economy
(5)
Education
(2)
Entertainment Gist
(1)
Gyaran-Jiki
(5)
Health
(13)
Jikar Iya
(11)
Kimiya
(1)
Kiwon Lafiya
(54)
Kukan Zuci
(5)
Kwalliya
(4)
Labaru
(23)
Lifestyle
(1)
Ma'aurata
(1)
News
(300)
Nigeria
(5)
Noma
(1)
Opinion
(3)
Picture
(3)
Politics
(15)
Profile
(2)
Q&A
(1)
Ramadan
(9)
Ramadan Tafsair
(1)
Siyasa
(1)
Sports
(72)
Tarihi
(5)
Technology
(1)
Tips
(3)
Video
(3)
YouTube
(5)
Zain Abeed
(1)
Zamantakewa
(1)
Novels Elite
Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content.

Novels Elite
SUBSCRIBE
Posts
Comments
Links
Post a Job

LATEST POSTS

ADVERT
Novels Elite
Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved
DMCA.com Protection Status
Disclaimer
Privacy Policy
Terms and Conditions
Our website uses cookies to improve your experience. Learn more

Accept !
[14/10, 6:05 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: Home
Kurkukun Kaddara
Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 23 Complete
by
Novels Elite Admin
June 29, 2024
Sponsored Link

Novels Elite English
_*~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋*~_

سجن القد💋🔥💞

~Takun Ƙarshe🔥~

Dedicated to Aunty Kubra💋💞

قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع تطورات معقدة💋💘😘

An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘

Daga alƙalamin Boss Bature💋✊

_________________________________E23✍️

Baiyanar sa tamkar bainar mutuwa ne, zaiyi wuya mutun ya hada ido da shi ba tare da zuciyarsa tayi yunkurin dakatawa da bugawa saboda firgitarwar dake gare sa, shin wanene Wannan Evil giant din?

Asalin Sunan sa Jeremiah shi tun fil azal mugun mutunne tunkafin zamantowarsa Giant mugunta da zalunci kaɗai yasa a gaba, inaga yanzu da suka fara ba shi horon zama Garkuwar prison abun ba'a magana babban abun da zai baka mamaki ƙarancin shekarunsa dududu bai fi sa'an garkuwa ba amma a halitta basamude ne saboda girman jikinsa.

A yanzu haka Yana a cikin Rijiyar sirihi, wato mataki na ƙarshe da suke ba mutun na horan zama evil giant, ita wannan rijiyar sihirin bata ruwa bace, mazauni ne na bakaken aljanu da shaiɗanu, kwanan watan da za su gurfanar da shi yayi dai dai da lokacin da suka ɗaga na yin black night, aranar za su fiddo da shi saboda rashin imani da zalunci, nayi imanin ko makiyina bazanyi mashi fatan yakai wannan ranar agidan kurkukun ƙaddara ba saboda musifar da zata afku na bayyanar Jeremiah, rayuka ne za'a salwantar bila adadin ba yara ba ba kanana ba ba tsoffi ba hatta jarirai ba zasu ƙyale ba wa'iyazubillah.....

________________________________✍️

Motsin buɗe ƙofar ɗakin ce ta karaɗe kunnuwansu kamar gumaka babu wanda ya motsa a cikin su sai faman zare idanunsu su ke yi, gaba daya sun sha jinin jikin su saboda sun san ba alkhairi ba ne ya ke tunkaro su.
Chapter 65 · 0% Book details