← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 196 OF 238

Sashe 196

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Junaid dake zaune saman Laps din mami tana bashi abinci tuni ya haɗe fuskar shi muryarshi da shawaga6a yace"Allah ni bazan koma ba, dodo zai ɗauke ni in naje.." dariya su ka yi Abie yace"jikana mai abun ban mamaki! Wani irin dodo ana zaman lafiya"? Yana faman zumbura baki yace"wanda Ya kashe..." a firgice Anila tay sauri katse shi da karfi ta furta"junaid! Ya isa haka, kamanta abunda na fada maka" da sauri ya rufe bakinsa da tafin hannunsa, dariya su ka yi inka cire Uncle ɗaya wanda hankalinsa kwata kwata baya akan su, Anila kam Ajiyar zuciya ta sauke ganin ba su ɗago komai ba sun maida abun wasa, agogon hannunsa ya duba kafin ya mike Abie yace"har za'a fita"?

Uncle yace" Yau hutu nake har gobe ina gida" Ya fada tare da juyawa ya nufi bedroom dinsa.

Mami tace"wai nikam Ina zahra ne? Ko har an tafi aikin"?

Ummi tace"eh tun dazu ta wuce, tazo tayi min magana cikin bacci naji ta" ummi tace"nima kam naso naji ta tana knocking yau fitar wuri akayi kenan, Abie Yace"zahra badai hankali ba, bata iya tafiya aiki batare dabi kowannan mu tayi mashi sallama ba" Mahboon yace"dama tayine don afada" dariya sukayi, Ummi tace"na fahimci kana kishi kaji an yabi zahra" ta6e baki yayi Anila dake kallonsu daya bayan daya wani irin tausayin su ne Ya kamata.

A Obie Estate kuwa, Yau shirye shiryen Tarbar baba Obie su ke yi, kasantuwar yau ne ranar da zasu dawo daga Lagos, maids din gidan tun safe suka fara gudanar da aikinsu.

Tsaye take a gaban dressing mirror tana ɗan jujjuya jikin ta, wani hadadden Saree ta sanya launin ja mai adon duwatsu sai sheki suke, yayi bala'en yi mata kyau kamar amarya, ta zuba adon Zabba da awarwaro a hannayen ta, ga wasu jerin gemstone necklaces a wuyanta masu daukar ido, ta saki doguwar sumar kanta a abayanta baka wulik sai sheki take, A hankali take kokarin gyara Earrings din dake a kunnanta, yayin da idanunta ke kallon cikin madubin, Ita kanta ta yaba da haɗuwarta, Sareen jikinta ya nadu sosai ya zauna mata, ɗan light makeup tay akan fuskarta tayi kyau, daddaɗan ƙamshin turarenta dana bakhhoor burner din data Kunna Ya gauraye iskar ɗakin da wani irin kamshi mai dadin shaka.

Murmushi ta dan saki har dimple dinta Ya lotsa, ta fito sak ba'indiyarta ta usili, wani irin annurin farin ciki ne ya bayyana akan fuskarta, bakomaine yasa ta farin ciki ba face murnar dawowar Pravin Jiya sunsha waya da shi yana fada mata irin kewarta da yai yace mata ta shirya mashi kanta don idan ya dawo sai ya fanshe kwanakin da baya nan.

Cikin harshen indianci ta furta"Ina jiran ƙarasowarka my lovely husbad"

ta faɗa tana yar dariya.

High heels ta ɗauko ta zura a kafafunta ta fito ta nufi kitchen don ta duba masu aikin gidan.

*HAJIYA SARATU*

Tana a kwance kan katafariyar bedmatress dinta tayi nisa a baccin ta, Ta wawware kafafuwanta daya tay dama daya tay hagu sai jan minshari takeyi, Sleeping gown ce a jikin ta, zanen kitson da ke akanta ya kara fiddo da kyawun fuskarta duk da babu annuri akanta.

Iphone dinta dake ajiye saitin kunnanta ce ta fara ruri da karfi sautin ya addabi kunnanta, har saida ta fara kokarin farka cikin magagin bacci da bacin rai ta dinga katse kiran almost 4 times a na hudu ne ta fusgo wayar ta kara kunne rai a6ace ta furta"wai wanene ke son takura mini ne"?

"Jatuminki ne" ras taji gabanta Ya fadi jin muryar baba Obie, a rude ta zabura ta miƙe fuskarta ya amutse cike da jin nauyin furucin da tay sam takasa magana saboda kunya.

Murya na rawa ta furta"baba i'm sorry, wlh bansan na furta ba, Kiran wayarka ne ma ya tashe ni daga bacci bansan kai bane ka kira..."

bata kare maganar ba ya katse ta"Auta Ko da bani bane abun da kikai ya dace? Idan abokan aikin ki ne fa"?

"Baba ka gane mana, daga bacci na tashi, ban gama wartsakewa ba"

"Pravin bai fada maki yau zamu dawo bane"? Yamutsa fuska tay"ya fada min"?

"Shi ne kuma kike ta baccin asara, ba zaki tashi kije ki gyara kanki ba"?

Haɗe rai ta yi "baba wani irin gyara kuma"?

sautin dariyar shi tajiyo"its Okay, yanzu haka muna akan hanyar zuwa airport"

"Okay, zan zo in tarbe ku, Yanzu zan shirya Allah ya kawo ku lafiya" ya amsa mata da Ameen kafin sukai sallama.

Saukowa tay daga gadon tana ƙuƙuni kan maganar gyara da baba obie yai mata.

"Haba Akan me zan takura kaina, Gyara ya wuce mutun Ya dawo ya iske iyalinsa daya bari cikin koshi lafiya, Nifa ba baiwar Namiji bace ehe.." ta ƙarashe kukunin tare da bude toilet door ta shige.

Lokacin da ta ƙaraso Kitchen din kamshin abinci ne ya daki hancin ta har can cikin makoshinta kamshin ya ratsa.

Sam basu lura da zuwanta ba, gaba daya Hankulansu na akan girke girken da sukeyi.

Gyaran muryar da tay masu"Aikinku na kyau" atare suka dube ta, kamar yau suka fara ganinta tayi masu kyau, murmushi suka saki tare da gaishe da ita cikin girmamawa, da fara ta amsa masu.

"Ya kamata kuyi sauri ku kammala, sun kusa karasowa"

Sofia tace"in sha Allah kafin su karaso zamuyi kokari mu gama"
Hajjaty tace"yanzu dame dame ku ka kammala"? Safa ce ta lissafa mata.

"Okay, naji kince hada dambun Nama, pls Ki dan zuba min shi tare da juice, wlh yunwa nake ji" ta fada tana shafa cikin ta, dariya sukai cikin raha tana lura da satar kallonta da sukeyi tasan da wuya in basuyi gulmarta ba kamar ko ta sani gulmace ke cin su.

Bayan Safa ta zuba mata dambun naman a plate ta haɗo mata da glass na juice a kan madaidaicin tray ta daura mata tare da muka mata tasa hannu ta kar6a tare da yi mata godiya ta juya ta fuce.

fitarta keda wuya Abla tace"wannan gayu haka hajjaty, Kamar wadda zataje gasar kyau"? Ta fada baki asake, sofia tace"ni dai wlh tana burgeni, inason mace mai tsafta da iya daukar wanka, amma abunda bangane ba Wa takeyi ma kwalliya ne? Naga dai ba wani guri take zuwa ba kullum tana a gida"

"Kun cika sa ido, Nifa bansan gulma wlh, naga dai ba yau ta fara yin kwalliya ba" safa ta fada tana jifarta da harara.

"Ba yau ta saba ba amma na yau yasha banban, yau fa baba Obie da pravin zasu dawo meyasa zata ca6a adon nan sai kace wadda zata tarbi Mijinta, ko dai hajiya saratu batay gayun nan ba bana tunanin ma ta tashi daga bacci, sai ita zakakka abun nata na nema ya wuce gona da iri ya kamata ta tsaya a matsayinta na yar aiki" Ta kare maganar tana hura hanci
Fashewa sukayi da dariya..
"Pls Ya isa haka Sofia, nasan meke damunki, Bakin cikine da hassada, Saboda kinga hajjaty Allah ya zuba mata ruwan kyau gashi tafi ki matsayi shiyasa kike kishin ta"

tsoki Sofia taja"Allah ya kiyaye inyi mata hassada Ni kawai na fara zargin akwai wanda takeso ta mallaka agidan nan shiyasa take caba ado nan don taja hankalin sa, In kuwa hakan ta faru mu zamu zama bayinta, kuna gani dai haka Harriet ta aure Sir mubarak to wai mu ko bamu da farin jini ne a gurin mazan family din nan" ..fashewa sukayi da dariya.

"Duniya tayi maku dadi, wato Na lura gaba daya kun manta da marwa" acewar Abla, Atare suka hada baki gurin furta Alah sarki marwa ko awani hali take? Safa tace"jiya nayi waya da innarsu ta fada min jikin nata da sauki har ta fara kokarin yin magana"
Sofia tace"baiwar Allah tadaiji jiki sosai, Alah ya bata lafiya, ko ta samu ta dawo bakin aikin ta, In sha Allah nima da anjima zan kira inji ya jikin nata"

_____________________________________✍️

A hankali take tafiya cikin takun dattako, wata hadaddiyar egyptian abaya ce a jikinta mai tsadar gaske, tay rolling head scarf, yayin da Idanunta ke amanne da farin glases, Ko hoda bata shafa ba amma ba ƙaramin kyau ta yi ba, hannunta daya na a ruke da purse dinta, ga wani daddadan fragrance dinta dake tashi.

Har zata gifta idanunta suka hango mata hajjaty, wani uban burki ta ci ganin yadda ta caba ado kamar wata amarya.

"Ke zonan" ta fada da ɗaga murya, hajjaty bata san da zamanta ba, har takusa shiga part dinsu na maids ta tsinkayi muryar Hajiya saratu rass taji gabanta Ya fadi arude ta juya tana kallon ta, da hannu tay mata alamar tazo.

Hankalinta ya tashi don tasan kiran hajiya saratu ba alkhairi bane.
Jiki asanyaye Ta nufe ta aranta tana ta ambaton la'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin.
Koda ta karasa nesa da ita ta tsaya cikin sanyin murya tace"gani aunty saratu" harara ta galla mata har saida tasha jinin jikinta.

"Uban wa kikai ma wannan adon"? sunkuyar da kanta kasa tay, aranta ta furta"mijinki nayi mawa, a fili kuma tace"Aunty, kamar dai yau kika fara ganin nayi kwalliya"? Ji tay kamar ta kwasa mata mari saboda fusata"karki kuskura ki kara kirana da sunan aunty, in banda munafurci sai da kika saisaici ranar da kikasan mijina da baba zasu dawo tukunna kika caba adon nan ko? A cikin su wa kikai mawa"? Ta fada tana cije lips dinta hadi da matsowa kusa da hajjaty, jikinta sai kerma yake tray din hannunta kamar zai kife kasa, Cikin rawar murya tace"Allah shine shaidata, Ni banyi kwalliyar nan don daya daga cikinsu ba, nayi ne saboda in burge kaina" idanunta cike tab da kwalla ta kare maganar.

Da hannu hajiya saratu ta cafko pallu din sareen data laga kan kafadarta..

Ta soma goge mata kwalliyar fuskarta ran hajjaty ya 6aci sosai duk ta cabe mata kwalliyarta.
Chapter 196 · 0% Book details