← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 238

Sashe 69

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Chief dake atsaye ya harɗe hannayensa kan kirjinsa sai kallonsa yake yi zuciyarsa cike fal da tausayin rayuwarsa baiyi tunanin tsayawa ya kammala wayar ba sai ya juya ya fita daga dakin.

"Bazan damu ba, kallon da kake yi min ya tabbatarmin da ka gane wanene ni, shekaran jiyama da muka fara haduwa sai da nasha wahala kafin Ka yi min magana" ya faɗa yana murmushi.

"Nakasa jurewa ka tsareni da wadannan kyawawan idanun naka please ko da zagina ne kayi ni dai burina naji muryar nan taka mai kwantar min da hankali, chief bai fada maka nayi zazzabin rashin ka ba"? Ya fada yana marairaice masa fuska alamar zaiyi kuka...

Yana faman furzar da numfashi Ya dan motsa la66ansa kamar baison furta maganar yace"ina son ganin ka"

"Ba ga ni kana gani na ba" girgiza kai danish yai alamar a'a

"Ka fito kazo nan dakina"

"No bazai yiwu ba, ay bana kasar yanzu ina canada kai kuma kana nigeria, sai na hau jirgi tukunna zan iya zuwa wurin ka" hankali atashe danish Yace"a'a ni dai kawai kazo ka fito daga wannan abun ina son ganinka" waro idanu hateem yai da alamun ruɗani akan fuskarsa.

"Ba yadda za'ae na fito, laptop ce fa, baka ga ƙarama bace taya ni da nake babban mutun zan fito ta cikin ta" kamar zai sanya masa kuka yace"ni dai kazo ina son ganinka" ya fada yana shafa laptop screen din a kokarinsa naya gano kofar da zai buɗe wa prime minister Ya fito waje.....

Chief owais Na awaje Yajiyo sautin fashewar wani abu daga dakin danish....

*Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️*

*Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*

3196407426

First bank

Bature Hafsat Muhammad,

*bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268*

Sponsored Post
Tags
Kurkukun Kaddara
YOU MIGHT LIKE
POST A COMMENT
Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post
Next Post
GET IN TOUCH
Facebook
twitter
YouTube
Instagram
Whatsapp
SUBSCRIBE US

OPINION
FACEBOOK

COMMENTS
CATEGORIES
Africa
(1)
Al'adu
(1)
Alkamawa
(3)
Article
(3)
Blogger Tips
(1)
Economy
(5)
Education
(2)
Entertainment Gist
(1)
Gyaran-Jiki
(5)
Health
(13)
Jikar Iya
(11)
Kimiya
(1)
Kiwon Lafiya
(54)
Kukan Zuci
(5)
Kwalliya
(4)
Labaru
(23)
Lifestyle
(1)
Ma'aurata
(1)
News
(300)
Nigeria
(5)
Noma
(1)
Opinion
(3)
Picture
(3)
Politics
(15)
Profile
(2)
Q&A
(1)
Ramadan
(9)
Ramadan Tafsair
(1)
Siyasa
(1)
Sports
(72)
Tarihi
(5)
Technology
(1)
Tips
(3)
Video
(3)
YouTube
(5)
Zain Abeed
(1)
Zamantakewa
(1)
Novels Elite
Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content.

Novels Elite
SUBSCRIBE
Posts
Comments
Links
Post a Job

LATEST POSTS

ADVERT
Novels Elite
Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved
DMCA.com Protection Status
Disclaimer
Privacy Policy
Terms and Conditions
Our website uses cookies to improve your experience. Learn more

Accept ![14/10, 6:05 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: Novels Elite

Home
Kurkukun Kaddara
Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 24 Complete
by
Novels Elite Admin
June 30, 2024
Novels Elite English
_*~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋*~_

سجن القد💋🔥💞

~Takun Ƙarshe🔥~

Dedicated to Aunty Kubra💋💞

قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع تطورات معقدة💋💘😘

An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘

Daga alƙalamin Boss Bature💋✊

Chief na waje ya ji yo sautin fashewar wani abu daga dakin danish, a hanzarce ya tura kofar ya shiga kwatsam ya taras da abun da banyi tsammani ba

Gaba ɗaya ya fasa laptop din, ya raba ta gida huɗu, hakan bai masa ba sai da Ya zuƙunna a gaban pieces ɗin Ya sa hannu Yana tatta6a su kamar wani zararre komai ya kwance masa

Chief Ya jinjina ma lamarin, abun ya ɗaure masa kai tamau, ta inda ya gode ma Allah laptop ba wadda ya ke aiki da ita ba ce, da kuwa yaja masa babbar asara.

"Meyasa ka fasa ta? why pls ? Ko kallo bai ishe shi ba, damuwarsa akan Hateem ne da bai gani ba bayan yasha wahalar balla abun

Girgiza kai chief yayi"da ita ne zaka iya amfani wurin yin magana da shi saboda baya a Nigeria" ɗagowa danish yayi fuskarsa a yamutse gaba ɗaya ya rasa sukuninsa, shi fa ya fasa ne da niyar ya buɗe ma prime minister hanyar da zai iso gare sa.

"It is okey, koma ka zauna kan gadon ka, a hankali Ya koma kan gadon yana faman bin laptop din da kallo

Ƙarasawa chief yai tare da kwashe pieces din ya fuce daga dakin Ya koma bedroom dinsa Yana shiga wayarsa ta fara ringing

Da sauri Ya ɗaura laptop pieces din kan couch kafin Ya ɗauki wayar yai picking

"Owais meya faru ne? Muna cikin yin magama da shi naji ɗuff ya katse kiran"

"Uncle mai kuke tattaunawa ne da shi"?

"Cewa yai yana son ganina in fito daga laptop din, nace masa bayadda za'ay amma ya matsamin shi ne fa naji shiru kiran ya katse"

"Uncle Ya 6alla laptop ɗin, gaba ɗaya ta tashi aiki, Allah Yaso ma ba wadda nake amfani da ita bane ay dayaja min asara"

Muryar Hateem da mamaki Ya furta"what? Ya fasata? Amma meyasa yayi haka"?

"Saboda ka ƙi fitowa, may be yana nema maka hanyar da zaka fito daga cikin ta ne"

Kusan atare suka fashe da dariya daga hateem din har chief din saboda abun Ya basu mamaki da al'ajabi......

Dakatawa sukai da yin dariyar, kowan nan su yayi shiru na ɗan wani lokaci, kwatsam sautin shessheƙar kukan prime minister hateem Ya karaɗe kunnansa lokaci ɗaya zuciyarsa ta buga saboda jin abun da bai zata ba, aruɗe ya furta"uncle? Kuka kake yi? Ko dai kunne na ne suka ji min badai dai ba"?

Muryarsa araunace Ya furta"Ina tausayin rayuwarsa owais, ya karya min zuciyata yau, mutum har mutun baisan komai ba, da ace ya taso cikin kulawar iyayensa koda ba dan masu hali bane zai samu ilmin addini dana zamani dai dai gwargwado....." yana magana sautin na fita da alamun kuka maitsuma zuciya.

Lumshe ido chief yai kafin Ya furta"pls ka kwantar da hankalin ka uncle, zanyi iyakar bakin kokarina don ganin ya samu ilmi akansa, kamar yadda nayi maka alƙawarin bashi kyakkyawar kulawa..."

"Owais idan zai yiwu ku sanya shi makaranta, Ni zan ɗauki nauyin karatunsa because I want him to be like everyone else. ni wallahi da zaka bani dama zansa akawo min shi nan canada"

Cikin kwantar da murya owais yace"Uncle zuwansa canada bazai yiwu ba, akwai abun da ban fada maka dangane da rayuwar su ba, amma dan Allah kayi min Uziri uncle nan badajimawa ba zan sanar da kai komai....."

Yana jiyo sautin ajiyar zuciyarsa"Toh zan jira har zuwa lokacin, Allah yasa inji alkhairi, yanzu sai yaushe zan sake yin magana da shi saboda bangaji da ganin sa ba"

"Ka bani lokaci uncle, zanyi kokarin fahimtar da shi yadda zaiyi amfani da laptop din"

"Okey, nagode my son, sannan ina mai baka hakuri amadadinsa"

"Kada ka damu uncle, ay ba yin kansa bane rashin sani ne"

kwantar masa da hankali Yaci gaba da yi har ya samu ya shawo kanshi kafin daga bisani su ka yi sallama zama yai gefen gadonsa zuciyarsa cike fal da tunanin abun da ya faru.

_________________________✍️

"Deeja! Deeja" kamar daga sama taji ana ƙwala mata kira, firgigit ta ware idanunta masu ɗauke da bacci ta sauke su kan ceilling da alama batasan daga ina ake kiran ta ba sai faman ƙyafta ƙyafta idanu ta ke Yi, fuskarta ta ca6e da jan bakin ta

"gani anan tsaye ina kallon ki" wurga ido tai kan Unaisah da ke yi mata magana, tana a tsaye ta ruƙe qugu da hannu ɗaya, wata hadaddiyar riga doguwa ta sanya a jikin ta black colour tabi shape dinta ba karamin kyau tayi mata ba, hada light make up akan face dinta, tayi rolling veil ga wani daddaɗan fragrance dake tashi

Zumbur khadeeja ta miƙe zaune fuskar a jagule take kallon ta

"Sorry na katse maki baccin ki, safiya tayi tun ɗazu, ga shi ko sallar asuba bakiyi ba, yakamata kije kiyi sannan ki yi wanka ko kin ji dadin jikin ki"

Yamutsa fuska Khadeeja tay"to ke din wacece ne? Kin cika ni da surutu Ina yaya salsabeel da su rubina"?

Murmushi unaisah tayi"Yar uwarki ce unaisah baki gane ni ba"? Harara ta jefa mata"ni bansan ki ba Allah, ki fadamin ina yan uwana suke"?

Zuba mata ido unaisah tayi da alama zatai kafiya, don ma tasan halin kayan ta.

"Yan uwanki suna nan a cikin gidan nan, amma waye ya kawoki ɗakin mu jiya"?

Sosa ƙeya tayi kafin tace"harisuna, shine Ya rakoni in kwanta"

"Okey yanzu ki tashi ki shiga ga toilet can" ta fada tare da ɗan juyawa ta nuna mata kofar da hannu, saukowa tayi daga kan gadon tana miƙa tare da hamma ta nufi toilet ta shige, unaisah nata bin ta da kallo har ta shige.

"kin canzamin kamar ba deejana ba, naso ace kina acikin hayyacinki komai Ya faru nasan zakiyi farin cikin saurayin rayuwar da muka samu, Allah Ya baki lafiya my sister"

Bakomai take tunawa ba, face ranar da giant ya tafi da khadeeja da kuma lokacin da aka dawo masu da ita taje gaban gadon ta tana shessheƙar kuka ta tada ta daga bacci taja ta suka shiga toilet har take fada mata abun da akayi mata bayan an ɗauke ta

Tuni taji jikinta yayi sanyi lakwas rayuwa kenan, babu wanda yayi tsammanin zasu kai wannan lokacin araye sai gashi Allah ya raya abun shi, dama ance wuya bata kisa sai in kwana sun kare.
Chapter 69 · 0% Book details