← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 238

Sashe 62

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Novels Elite
SUBSCRIBE
Posts
Comments
Links
Post a Job

LATEST POSTS

ADVERT
Novels Elite
Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved
DMCA.com Protection Status
Disclaimer
Privacy Policy
Terms and Conditions
[14/10, 6:05 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: Home
Kurkukun Kaddara
Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 22 Complete
by
Novels Elite Admin
June 27, 2024
Sponsored Link

Novels Elite English
_*~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋*~_

سجن القد💋🔥💞

~Takun Ƙarshe🔥~

Dedicated to Aunty Kubra💋💞

قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع تطورات معقدة💋💘😘

An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘

Daga alƙalamin Boss Bature💋✊

_________________________________E22✍️

Ta jima tana kallon hotunan kafin Ta miƙe ɗauke da su a hannunta, da sauri ta juya ta nufi mirror drawer ta buɗe gida na uku ta saka su a ciki.

Tana ƙoƙarin mikewa sallamar Taj Ta katse mata hanzarin ta daga wajen dakin ta jiyo muryarsa.

"Daddy gani nan zuwa na gama shiryawa, waya ta nake nema banganta ba"

"Ina kika ajiyeta ne"?

Watsa hannu tai kamar tana agabansa na manta daddy

"Jiya naso na ganta a hannun ɗan uwan ku sajeed, bari na tambaye shi" amsa mashi tayi da toh aranta tana mai mamakin yadda sajeed yake da nacin son waya, sam baya gajiya da ita."

Badajimawa ba, taj Ya turo kofar dakin Ya shigo hannunshi ruke da wayar.

Face dinsa da murmushi Ya mika mata"Na lura baki son wayar nan taki, saboda ba ki damu da ita ba, me zai hana ki bar ma sajeed din tun da yafi ki sonta"

Muryarta da yar shagwaba tace"wallahi inason abuna, sai dai asiya masa wata tunda Yana so, dr laura fa ta bani ita taya ma zan bada ita" ta yi maganar tare da kar6ar wayar daga hannun sa

"Kin ta6a kiranta ne kunyi magana"?

"Mantawa nakeyi wlh, amma in sha Allah zan kirata in na samu nutsuwa"

"Baki kyautaba yakamata kiyi kokari ki kirata" amsa mashi tayi da toh

"Daddy dani kadai zamu tafi"?

"Eh, next time suma zan kai su gidan"

Ruƙo hannunta yai acikin nashi, suka fito daga dakin, babu wanda Ya lura da su fira taja hankulan su, tana kallon su Deeja dake ta faman sakin murmushi wani irin sanyi taji aranta, yanzu damuwarta akan sauran prisoners ne wadanda ke AGIDAN KURKUKUN ƘADDARA!

Har sun kusa fita daga falon, Kamar ance ta wurga eye balls dinta kan second floor, kwatsam Ta hango Danish dake kallon ta, cikin shiga ta pajama launin blue sky, tayi tunanin ba ita Yake kallo ba, sai tai saurin kau da idon ta, gudun kada ya ga za su fita, tasan halin mutumin nata.

Suna fita daga falon ta sauke ajiyar zuciya, kasancewar baida nisa part din nashi, A ƙafa suke tafiya suna fira hanyar da suka biyo ko'ina hasken electric bulbs ne tamkar ba dare ba ga wata iska mai ni'ima dake kaɗawa

"Daugher, kina jin sautin da nake Jiyowa kuwa"? da mamaki Tace A'a daddy menene"?

"Akwai mutun abayan mu, baki ji sautin tafiya ba" aɗan ruɗe ta furta mutum kuma? Wanene? bata jira ya bata amsa ba tayi saurin juyawa don ganin waye.

Har saida gaban ta ya faɗi idanunta adan zare take kallon shi, Hannayensa harɗe akan kirjinsa, fuskarsa babu fara'a, kayan baccin da ta gan shi da su sune a jikinsa fararen ƙafafuwansa ko takalma babu.

Juyowa taj yai tare da kallon shi, ashe tunda suka fito Yake biye da su, shi taj yasan da zaman shi itace bata lura ba.

Muryarta kamar zata fashe da kuka tace"daddy, mu tafi da shi kawai"

ƴar dariya taj yai tare da cewa"ya zama dole ay, wa ya isa ya hana shi zuwa"?

"mu tafi My man, nayi zaton kayi bacci, shiyasa ban neme ka ba, dama zamu je part din daddyna ne don in gaisa da Auntyna"

kamar jira yake ta bashi damar yabi su, da sauri ya nufe su, a maimakon ya tsaya gefen ta sai ya shiga tsakaninta da taj, yasa hannu ya raba hannayensu dake ruke cikin na juna lamarin ya daurewa taj kai aranshi ya ayyana wannan wani irin namijin kishine? Uban nata ma bai ƙyale ba inaga idan wani ne daban ba? Tun yanzu ya fara jin fargaban yadda zata kaya tsakanin chief da danish tabbas akwai ƙura.

A haka suka jera har suka ƙaraso ƙofar shiga Part din, Komai nasa shigen kalar na sashen da suke ne banbancin kaɗan ne amma fa Ya haɗu, Ita kanta Angel tayi mamakin katafaren Ginin gidan Chief gari guda An ƙawatashi kamar A dubai.

Dafe kofar taj yai da hannunsa a hankali ta zuge masu, katafaren falo ne an kawatasa da furniture, ga wani sanyin A.c na mai sanyaya zukata

Sai ƙara kallon ko'ina take tana ɗan jinjina kanta, har cikin ranta ta ƙara jin ƙaunar chief saboda kyautatawarsa ga daddyn ta.

"Bismillah, Ku zauna bari naje nayi mata magana" ya fada tare da wuce ya nufi upstairs.

A hankali suka zauna kan sofa, kallon sa tai suka hada ido cikin na juna.

"Baki kewata ba? kin manta da dani jiya ko ki neme ni" yana magana tamkar baisan motsa lips dinsa

"Ni da kai waye mai laifi? Jiya ko kallo ban ishe ka ba, ka kama hanya ka bi uncle din chief inata kallon ka ko waiwaye na bakai ba" ta faɗa tana kwa6e masa fuska

Lumshe idanunsa yai batare daya furta mata komai ba

"Har ciwon ciki nayi jiya kamar zan mutu, ni kadai a restroom na kasa bude kofa har na fadi kasa na suma duk kana ina"?

"Ina atare dashi," atakaice Ya bata amsa

Ruƙo hannunsa tai tana kalllon dogon yatsan hannunsa dake asanye da silver ring, yayi matukar yi mata kyau

"Shi ne Ya baka wannan"? Ɗaga mata kai yai alamar eh,

Da fara'a akan fuskarta tace"Bani labarin abun da ya faru tsakanin ku jiya"?

Sai da ya fara kai soft lips dinsa saitin kunnanta kafin ya fara bata labari saboda bai iya ɗaga muryar shi.

Sai faman sakin murmushi takeyi hakika taji dadin kyautatawar da prime minister yayi masa, kuma ta fahimce shima yaji dadi tun da gashi nan da bakinsa yake bata labari mutumin da be cika surutu irin haka ba.

"My man, Ni dai fatana Allah yasa mutumin nan ya zama alkhairi agare ka, wlh tunda nagansa naji ya kwanta min araina saboda kamannin dake a tsakaninku..."

kafin ta ƙare maganar Sautin takalman daddynta ne Yaja hankalin su ga dubansa, saukowa yai down a hanzarce Ya nufe su Yana fadin"daugher, bacci takeyi auntyn naki, ko zaki je ki same ta adaki, Inaso ki bata mamaki" murmushi tayi tare da mikewa da sauri Danish Ya miƙe zai bita, kallon shi tayi cikin sanyin murya tace"ka zauna ka jira ni, Yanzu zan fito ba daɗewa zanyi ba"

Taj dake kallon su murmushi yai tare da ƙarasawa gefen Danish yace"Idan saboda ni ne, To mu zauna gani ka gaka ita sai ta shiga watakli hankalinka zaifi kwanciya,'

Kamar kuwa yasan sbd shi Ya miƙe zai bita, komawa yayi ya zauna hankalinsa akan Angel dinsa Harta haura kan stairs.

A hankali Ta zura kafarta cikin dakin, tana shiga ta soma bin ko'ina da kallo masha Allah, a hankali ta sauke idanunta kan Danejo dake a nannaɗe cikin bargo sai sharar baccin ta take yi.

watsa wa tayi da gudu ta daddage ta haye kan gadon gaba ɗaya ta ƙanƙameta tana dariya, wata irin firgita danejo tayi cikin magagin bacci take fadin"daddyn Angel, wayyo Allahna kana ina wai wanene ke takura min! Nashiga ukuna"

Yaye mata bargon Angel tayi, tana faman haki ta buɗe idanunta waɗanda suka kada jawur saboda bacci, A hankali ta sauke su kan fuskar Unaisah ta ƙura mata ido tana kallon ta, da tsantsar ruɗani take binta da kallo, Itama unaisah kallonta takeyi cike da kewarta, ba zata ta6a mantawa da fuskar denejo ba, ta ƙara haske fara jawur da ita kamar ba'indiya saboda kyau, ga gashin kan nan nata mai tsayi baki wulik har gadon bayanta..

Muryarta aɗan tsorace ta furta"wacece ke"? Mutun ko aljan"!

Dariya unaisah tayi cike da nishadi tace mata"Baki gane ni na"?

Waro idanu waje danejo tayi da ƙarfi ta furta"ANGEL"

tuntsirewa unaisah tai da dariya tare da faɗa mata ta sake rungumeta, daura hannayenta biyu tayi akan bayanta tana fadin"Ni ce, Angel dinki, ashe da rabon zamu sake haduwa danejo na" mamaki Ya hana danejo magana, da sauri ta tallabo fuskar unaisah da tafukan hannayenta, ta kura mata ido tana kallon ta batare da ta kyafta idanunta ba, ko amafarki taga fuskar Angel sai ta shaida ta, duk da ta ƙara girma a yanzu ta zama yar matashiyar budurwa, tuni taji hawaye sun wanke fuskarta, da sauri ta kwantar da unaisah kan kirjinta, itama kukanne Ya kubce mata, sautin shesshekar kukansu duk Ya cika dakin, a hankali take shafa sumar kanta tana faman sauke ajiyar zuciya, Allah ne kadai Yasan irin kaunar da take Yi mata, taso unaisah, tayi kukan rashinta kamar zata zauce, muryarta kasa kasa ta furta"Alhamdulillah Ya Allah, nagode maka wallahi bazan Iya misalta farin ciki da nake aciki ba, Ya Allah nagode maka daka bayyana min Angel ɗina, Ya Allah nagode maka...." cikin shessheƙar kuka ta faɗa, tama rasa inda zata tsoma ranta saboda murnar ganin Angel.

ɗagowa unaisah tayi tasanya tafin hannu ta goge mata hawayen cikin sanyin murya tace"Aunty Danejo, naji dadi da Allah Ya sake haɗa ni dake a matsayin matar daddyna, I can't thank you enough saboda halaccin da kikai min arayuwa Allah ne kadai zai Iya biyan ki, kin so ni kin kuma kaunace ni tsakani da Allah, duk da bakisan koni wacece ba a lokacin amma kin taimaki rayuwa, kiyi hakuri ki yafe min laifin da nayi maki....' tana faɗa tana matsar kwalla.

"Angel laifin me kikai min? Ni ay baki min laifin komai ba...."

Girgiza kai tai hawaye nabin kuncin ta tace"nayi maki laifi, bayan mun shaƙu da juna, na gudu daga rugarku kina ji kina gani har biyo ni ki ka yi kina kiran sunana don in tsaya amma naki sauraronki, ashe da rabon in sha wahala" idanunta acikin na danejo takeyin maganar
Chapter 62 · 0% Book details