← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 206 OF 238

Sashe 206

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 7 min read

On the Other Hand Anila ta zabga salati tana fadin, "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, dan Allah Taj ka taimaka ka bada iznin a barmu mu shiga ciki, wlh zamu jira har zuwa lokacin da zaku dawo gidan, Don Allah Taj, wlh wani abune mai mahimmanci ya kawo mu, It's urgent, please help."

Ta fada tana kallon Benazir data yamutsa fuska kamar zata sanya kuka.

Shiru Taj ya yi yana nazarin maganarta, tun daga kan yanayin muryarta ya fahimci da akwai wani abu da ya kawota gidan,

"Okay, ku ɗan jira"

Ta amsa mashi da toh, rejecting call din ya yi, ya shiga tuntu6ar layin Chief, almost 5 times tana ringing bai yi picking ba, ana shidda ne ya ci sa'a Chief ya ɗaga kiran..

"Yalla6ai mun yi baƙi, Anila ce tare da Benazir, Wlh bansan da zuwansu ba saboda basu faɗamin ba, sai dai kawai ta kira a waya ta fadamin suna a bakin gate an hanasu shigowa, wlh da nasan da zuwan da bazan bari suzo ba, amma na ji Anila tace matsalace ta kawo su."

Koda jin wannan maganar Chief ɗin ya ce zai yi magana a basu iznin shigowa ciki.

Godiya Taj ya yi masa bayan sun yi sallama, ya zura wayar Cikin aljihun jallabiyar sa.

A hankali Motar Dr Shureim ta karaso cikin parking space, bayan ya tsayar da ita. suka fito daga ciki, kallon kallo Benazir da Anila suka jefawa junan su.

"Yaya Shureim ko zaka jira mu anan?" Benazir ce ta yi maganar saboda basa son su shiga dashi ba don komai ba sai don kada su ƙetare iyakarsu ga kuma gargadin da aka yi masu.

"Ba damuwa, ku shiga zan jira ku, but pls kada ku daɗe."

Amsa mashi su ka yi da toh kafin suka nufi main door na falo, suna ƙarasawa ƙofar ta zuge suka shiga bakinsu ɗauke da sallama, wani sanyayyan sanyin Ac ne na daban ya ratsa fatar jikinsu har wani lumshe idanu suka yi.

Time da suka buɗe idanun nasu kaitsaye suka sauka akan Taj dake a zaune kan Sofa ya nutsu yana jiran ƙarasowarsu, Ba zaka ta6a gane yaji rauni a cinyarsa ba saboda ya lullu6eta da jallabiyar jikinshi, Sofa ɗin ma daƙyar ya samu ya yi dubarar da ya zauna akanta, da ɗayar ƙafarsa me lafiyan ya tura wheelchair din ta koma tsakankanin sofas saboda baya son su ganta.

Ta wutsiyar idanunshi ya ke hangosu yayin da suke nufo shi.

Anila ta yi mamakin ganinsa bayan ya ce mata basa nan ashe yana nan, komi yasa ya boye mata da farko? Ta ayyana a cikin ranta.

Har saida suka ƙaraso kafin ya ɗan ɗago da niyyar ya kallesu karaf idanun shi suka shiga cikin na Benazir, har saida ya ɗan ji gaban shi ya faɗi saboda kyan da ta yi ma shi, amma da yake namijin duniya ne sai ya haɗe rai tare da kawar da idanun shi.

Murmushi Anila ta yi kafin ta gaishe shi ya amsa mata fuskar shi asake.

Cikin sanyin murya Benazir ta gaishe da shi a daƙile ya amsa mata..

"Ku zauna."

A kan Sofa mai mazaunin mutun uku suka zauna suna fuskantar shi....

Gaza jurewa Benazir tayi idanunta cike tab da ƙwalla ta ambaci sunan shi"Taj!" Shiru bai tanka mata ba..

"Nasan har yanzu fushi kake dani, amma meyasa idan na kira baka picking? Har saƙo na tura maka akan ka taimaka ka haɗani da Unaisah saboda idan na kira bana samun layinta amma kwata kwata ba response..."

Hannu ya ɗaga mata tuni ta haɗiye maganarta, "Dama wannan ne abun da ya kawo ku?"

Ƙasa-ƙasa da murya Anila ta raɗa mata "pls ki aje wannan maganar gefe, ki yi haƙuri mu yi abinda ya kawo mu, kinga daƙyar muka samu aka bamu damar shigowa ciki." Jinjina mata kai ta yi alamar ta gamsu.

Mayar da dubanta ta yi akan Taj, "Dama issue ne akan yar aikin gidan mu Ana data 6ace yau wata Uku kenan."

Jin wannan maganar Yasa Taj ya maida hankali akan Aneelerh.

Dakatawa ta ɗan yi ganin kuku ya nufo su hannun shi ruƙe da wooden tray na fruit da cool drinks ya ajiye masu kan table, bayan ya tafi Aneelerh ta cigaba da zayyana masa komai da ya faru har izuwa kan videon da ta gani...." tunkafin ta kai ƙarshen zancen yanayin fuskar Taj ya sauya zuwa tsantsar mamaki, tashin hankali da kuma ruɗani...

"Zan iya ganin Videon??"

Da sauri tace "Eh," Ta faɗa tare da zaro wayar daga cikin handbag dinta ta shiga pressing dinta, bayan ta kunna masa video ta miƙe taje gaban shi ta miƙa ma shi.

Bayan ya kar6a, lokaci ɗaya hankalinsa ya tashi matuƙa, saboda tsabar girgiza da kidima duk da sanyin A.c din falon saida ya fara zubda gumin zufa lamarin ya ɗaure masa kai, Lallai sun zo da case mai girma, abun da ya ɗan jefa shi a rudani a bayanin Ana ya fahimci shi Uncle ɗin Anila matsafine kuma abun da yake yi ma Ana yayi kamanceceniya da cin zarafin da Elders su ke yi wa prisoners a lokacin da suke yin jinin al'ada.

A dabarbarce ya furta, "Anila dama Ana tana nan?"

Idanunta cike tab da ƙwalla tace, "Eh, atare da ita muka dawo gidan Uncle din"

Jinjina kanshi ya yi Idanunshi sun kaɗa sun ɗan yi ja,

"Ku sha lemun" Ya faɗa yana nuna masu drinks din..

Miƙa hannu Anila tayi ta dauki Juice ta tsiyaya masu a glass cups, saboda dadin da ya yi masu kusan duka suka shanye..

"Tanimu Ja'afar Falgore, inkiya Ɗan-iya shine full name na uncle dinki ko?"

Ya tambaya yana kallon Anila, Jinjina mashi kai ta yi alamar eh, a ransa ya furta karen yan siyasa zai aikata fiye da hakan, ya ƙarashe zancen zucin nashi tare da aje wayar Ana a gefen sa.

Har ya zaro waya zai dannawa Chief kira maganar Anila ta dakatar da shi...,

"Benazir na ji kin yi shiru baki ce komai ba? ba zaki fada masa abunda ke faruwa dake ba?"

Cikin karyayyar murya ta wanda ke shirin saka kuka tace,"Ba ki ga ko kallona bai son yi ba, Even if I tell him, he won't take me seriously."

A hankali Taj ya dubi Benazir da tayi maganar, idanuwansu suka shiga cikin na juna, da sauri ta kawar da nata idanun gefe ɗaya.

"Ina sauraronki! Faɗamin me ke damunki?" Wani sanyi ta ji ya ratsa zuciyarta jin ya kula ta, aikuwa ta gyara zama ta fara labarta masa abun da ke faruwa da ita, nutsuwa ya yi yana sauraronta, dan dakatawa ta ɗan yi tana haki kamar wadda tasha gudu.

Da hannu ya nuna mata Mineral water,"Ki sha" da sauri ta dauka ta ɗan kur6a.

Bayan ta ajiye taci gaba da bashi labari..

*bari mu koma baya don jin meya faru a ranar da Benazir ta dawo daga gidansu Anila bayan ta fada mata komai dangane da batansu Angel harta kulle kanta a daki, a ƙarshe da aka bude dakin aka iske ta kwance a ƙasa rabin jikinta a cikin toilet👇*

Bayan da ta gama shan kukanta tamkar ranta zai fita, lokaci ɗaya ta fara Jin azababben ciwon kirji, tana jiyo bugun kofar da suke yi mata haɗi da yi mata magiya akan ta bude amma taƙi saboda bata son ganin kowa a kusa da ita, a kan floor ta kwanta tana cigaba da sharar ƙwalla.

"Pls idan kina saurarena ki tashi ki kunna karatun alkur'ani kada ki kwana a haka, yakamata ki yi hada nafila..." Muryar Dr Shureim ta jiyo acikin kunnanta.

Daƙyar ta iya tattara ƙarfin da ya yi saura a jikinta ta mike ta nufi toilet don tayi alwala kamar yadda Dr Shureim ya shawarce ta.

A gaban sink ta tsaya tare da kunna faucet, ta soma yin alwalar sai dai gaba ɗaya hankalinta baya a tare da ita, ta lula duniyar tunanin ina zata ga Taj da ƴarta? Tana tsaka da yin alwalar hasken electric bulb din dake a saman ceilling ya fara wasa ya kawo ya dauke, bata kawo komai aranta ba ta yi tsammanin electricity din gidan ne ya samu matsala, hakan yasa taci gaba da yin alwalarta.
Chapter 206 · 0% Book details