← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 238

Sashe 17

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 7 min read

A dining room ya taras da su gaba dayan su sun hallara, tun daga kan momynsa malikat tare da younger sis dinsa Hindu ƴar matashiya ce da bazata wuce 22 Years ba, Black beauty tana asanye cikin shiga ta jumpsuit Dark navy, kitson zanene akanta wutsiyar gashin har kan shoulders din ta, Allah yayi ta da ruwan kyau kamar ita ta zana kanta, Komai nata ƙaramine ɗan pink lips dinta da Asian eyes din ta, ga dogon hanci, Bata da ƙiba siririya ce, a haka structure din jikinta ba karamin kyau ne da shi ba, Kamannin ta sak dana Mommyn su Gimbiya Malikat Sarauta.

ɗaya bayan ɗaya yayi hugging dinsu cikin mutunta juna suka gaisa, kafin ya zauna sukayi breakfast dinsu, daddy sharafudden yaji dadin cin abinci tare da ɗan nasa, har abaki yake bashi bayan sun kammala yayi masu sallama agurguje Ya nufo gidansa.

_________________________✍️

A 6angaren su Unaisah kuwa bayan kammala sallar asuba, bacci mai nauyi yayi awon gaba da su kamar matattu, har wurin karfe tara babu alamun zasu farka, ummi sai faman yin zarya ta ke yi daga dakin ta zuwa nasu don ganin ko sun farka, saboda tana son ta fara gyara masu jikin su, ganin baccin nasu bamai ƙarewa bane yasa tabi su ɗaya bayan ɗaya ta farkar da su, wani abu da ya ɗaure mata kai, duk wanda ta tada daga cikin su sai taga ya watsa da gudu ya nufi upstairs second floor, da sauri tabi bayan su don ganin ina za su je, a dakin danish ta same su zuƙunne bakin gadon shi suna kuka kamar ran su zai fita, hankali a tashe ta tambaye su meya faru suke kuka? Cikin shessheƙar kuka suka ce mata meyasa danish din su bai farka ba? Sun hana idon su bacci jiya sun roƙi Allah akan ya bashi lafiya amma shine Allah bai kar6i addu'arsu ba bayan wahalar da su ka sha ko dan saboda danish baiyi imani da shi ba ne....." waro idanu waje ummi tayi tana kallon su, ita dai unaisah ko magana ma takasa furtawa lamarin yafi karfin ta ashe har yanzu akwai sauran rina akaba, abun ka ga masu ƙarancin ilmin addini

Lallashin su ummi da unaisah suka dinga yi suna basu baki, akan su yi hakuri su daina fadin hakan babu kyau, gaggawa aikin shaidan ne, indai sunyi imani da Allah to su bi komai a sannu in sha Allah ɗan uwan su zai farka..." daƙyar su ka shawo kansu har suka samu komai ya lafa, ta sanya suka fito daga dakin ta rufe mashi ƙofa

Ko da aka shirya masu breakfast kasa ci su ka yi saboda fargaba da zullumin kada su rasa ɗan uwan su, Hankalin ummi duk ya tashi saboda tausayin su da ya kamata, Kamar marasa lafiya haka suka koma, lalla6a su ta dinga yi har ta samu suka ci abincin kaɗan bayan sun gama ne ta tarasu a falo ta fada masu dangane da Farewell dinner din da zasu halarta na uncle din chief, sun ji dadi yau zasu shiga cikin family din chief koba komai zasu ɗebe kewar abun da ke damun su, duk cikin su mutun ɗayace batayi farin ciki da fitarsu ba, hakanan take jin gabanta na faduwa, babban abun da take jimawa ba lallai su samu kar6uwa a wurin family din chief ba, bugu da kari rashin wayewar ƴan uwanta, yafi komai ɗaga mata hankali, tana jin tsoron su shiga bainar jama'a su yi kauyacin da zaisa a gane jahilcin su harma a goranta masu ko a ƙyamace su.

Hankalinta sam yaƙi kwanciya, har sai da taja aunty umminsu gefe ɗaya ta faɗa mata abunda take zullumi tace tana neman alfarmar abarsu su zauna a gida kada aje da su wurin dinner din nan.

Ummin tace ta kwantar da hankalin ta, ba abun da zai faru saboda basu kadai zasu tafi ba, hada su boss man kuma tasan bazasu bari a wulakanta su ba awurin taron zasu basu kariya, sannan tasha jin labarin familyn obinna mutanene masu karamci da daraja ɗan adam don haka kada ta sanya damuwa aranta in sha Allah zasu samu kar6uwa a wurin su.

Jin wannan maganar ya sa hankalin ta ya kwanta, Har ta fara zumuɗin lokaci ya cika don atafi da su.

Ba tare da 6ata lokaci ba, Ummi ta tattara matan suka shiga Home beauty saloon din gidan, domin gyara masu jikin su, mazan kuma taj ne ya tafi da su 6angaren jami'an isod na gidan acan za'a gyara masu sumar kansu, ɗaya bayan ɗaya ta wanke ma kowan nan su sumar kanshi tagyarata tsaf tayi masu hair style kala kala, Unaisah da batool kalar nasu gyaran gashin all layers around ne yayi bala'en yi masu kyau sumar kan har kyalli take yi tana ɗaukar ido saboda mayukan da aka yi masu amfani da su, gashin ya ciza launin shi dark brown yayi washar washar da shi daga baya ya lullu6e wuyansu da tsakiyar bayansu kamar hijabi, Azeeza da jemimah kuwa kalar nasu styal din braided bun ne, wanda ake dunƙule gashin daga tsakiya sai kaga ya yi kamar donut, gyaran gashin su yayi kyau sai ya ƙara fito masu da beauty baby face din su, sun fito a jar fatar su ta turawa, Parveen da Hannah su nasu gyaran gashin Classy ponytails ne yara sun fito suffarsu ta kyawawan ƴan mata, Sai farin ciki sukeyi tamkar babu abunda ke damun su, bayan an gama gyaran gashin, ummi tafara gyara masu kafafuwansu da akaifinsu, Hakiƙa tayi kokarin yadda kasan ƴa'ƴan ta haka ta dinga tsaftace su ciki da bai, har hakoransu bata bari ba sai tayi masu amfani da tooth care product wurin wanke masu su, dalilin dayasa take yi masu gyara duk da boss yace kayan da za'a sanya masu ya zamanto sun lullu6e ko'ina na jikin su, ita tasan ba yadda za'ay a shiga da yaran nan wurin dinner ta prime minister ba tare da security din dake tsaron wurin su sanyasu cire mask din fuskarsu ba, shiyasa ta dage damtse wurin gyara su, don agansu da mutuncin su, saboda itama maganar unaisah ta sosa ranta, batason ayi masu kallon ƙasƙanci, harta fatarsu sai da ummi tagyare masu ita, Kamar Ƴa'ƴan Furanni saboda tsabar Kyan da su ka yi, ita kanta da take kallon su ba karamin tafiya da imanin ta suke yi ba, inaga idan suka shiga wurin dinner din tabbas zasu Ja hankalin jama'a,

Bari dai in takaice maku zance, Ummi har yadda zasuyi magana ta ƴan gayu wayayyu da yadda zasu yi tafiya mai jan hankali sai da ta koya ma su, duk don kada suyi kauyacin da za'a tozarta su, sai wuraren sallar Juma'a ta sallame su tace suje su yi sallah after sun kammala su kwanta su huta kafin lokaci ya cika, A lokacin itama daki ta shiga don ta yi sallah ta kuma kwanta ta huta, fatanta Allah yasa taj ya nema mata alfarma a wurin chief ko ta samu ta fita yawo anjima

Badajimawa ba, Su sajeed suka dawo atare da taj, Wa'iyazubilla yadda kasan mazan hurul aini a kyau, Musamman masu tarin sumar cikin su, Sajeed da Naufal sai Javed, wani hadadden gyaran suma akayi masu irin na gayun nan, yadda kasan ya'yan wani shege mai ji da naira, shi kan shi haris da bai kai su sumar kai ba, gyaran gashin da akayi mashi ya kara fiddo mashi da Inner beauty dinsa, bayan taj ya rako su sun dawo gidan basu taras da ƴan uwansu a falon ba duk suna a daki suna hutawa A falo suka zauna suna jiran lokaci ya ƙarasa cika, dadi suke ji za'aje da su wani wuri kamar su zuba ruwa ƙasa su sha tsabar murna.

*DINNER HALL*

Wuraren karfe huɗu da wanu abu.

Katafaren Ɗakin taro ne dake a cikin Obie Estate, Aljannar duniya ce mai zaman kanta, saboda tsabar haduwar Hall din idan Ka shiga ciki gaba ɗaya zaka rude ka kasa tantance a ina kake ma, musamman a yanzu da yasha uban decoration an kawata shi da kayan ado masu ƙyalƙyali da ɗaukar ido, gaba ɗaya kewayen hall din Fusatattun sojoji ne majiya ƙarfi ke tsaron shi tare da Canadian polices ga kuma gwarazan jami'an Isod, bayan ga wadannan jami'an hada na'urorin cctv dake a kowace kusurwa har ta cikin fitilun lantarki da jikin kofafi, ciki da wajen ɗakin taron domin ba su tsaro daga dukkan wani abun cutarwa, yadda aka sanya tsaro a hall din bana tunanin ko sauro zai iya haura ƙafa Ya shiga batare da alburushin bindiga Ya tarwatsa kan shi ba, Entry way na shiga hall din tana a cikin Garden din gidan An kawata saman ta da gefenta da adon string lights mai walwali da daukar ido, ga wani shamfidaddan carpet da zai isar dakai cikin dakin taron lallausan gaske daga saman Entry door din anyi wani rubutu da adon furanni aka sanya

*Welcome to the farewell dinner of Prime minister Hateem Obinna*
Chapter 17 · 0% Book details