← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 204 OF 238

Sashe 204

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mami tace"Allah Sarki, na ji kin ce kin yi zuwan bazata baki kira kin fada ba, nan ay kamar gidan ku ne Benazir, naji dadin zuwanki..." Still fuskarta dauke da murmushi..

Ummi ta ce"Ga mutuniyar taki can, ta ɗaura aure da zaman ɗaki, dan Allah Benazir in kin shiga ki yi kokarin kwantar mata da hankali, kwanakin nan mun rasa gane kanta,"

"Bata da lafiyane?"

Mami ta ce, "Hmmm, ta sanya damuwa a ranta ne, wai kwanakin nan tana yawan yin mafarkin su Uzair shine fa duk tabi ta hana kanta sukuni..."

"Subhanallah!" Fuskarta da damuwa ta faɗa tare da miƙewa ta nufi dakin Aneelerh..

A bakin kofar dakin ta tsaya, kusan sau uku tana doka mata sallama shiru ba'a amsa mata ba, har saida ta fara gajiya da tsayuwa, a ƙarshe ta yanke shawarar shiga ciki.

Tana Shiga idanunta suka sauka akan Aneelerh dake a kwance kan gado, ta ƙurawa Ceiling idanunta ko kyaftawa bata yi, lamarin ya daurewa Benazir kai, a ranta ta ayyana wannan wata irin damuwace da zata sa aita maka sallama baka ji?

Ta karashe zancen zucin tare da kai hannu saman kafar Anila ta 6aka mata bugu, wata irin zabura ta yi, a firgice ta miƙe zaune tana zare idanunta muryarta na rawa ta furta,"Na shiga ukuna!" hannunta ɗaya dafe da saitin zuciyarta.

Hankalin Benazir ba karamin tashi ya yi ba, ganin yadda Aneelerh ta rame kwata kwata bata a cikin nutsuwarta.

"Ni ce fa..." Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke lokacin da ta sauke Idanunta akan Benazir don sam bata lura da ita ba.

Numfashi ta dan ja tare da sauke ajiyar Zuciya ta ƙaƙaro murmushi kan fuskarta..

"Benazir ke ce? Meyasa baki fada min zaki zo ba?" Bata tanka mata ba har saida ta samu guri ta zauna daga gefen gadon kafin ta maida hankalinta kan Aneelerh.

Duk tabi ta dabarbarce ganin irin kallon da Benazir ke yi mata, washe baki ta shiga yi tana kokarin danne damuwarta ta ce, "Sannu da zuwa Benazir, ya ki ke? Ya su Mami? Ina ya Shureim da zeenatu?"

Cike da damuwa Benazir ta furta, "Don Allah meke damunki haka Aneelerh? sau uku ina doka sallama baki amsa ba, nama yi zaton kin shiga toilet ne ko bacci kike yi, ashe idonki biyu kina a kwance kin takura kan ki, why pls dubi yadda kika rame? Fuskarki duk ta yamutse kamar wata tsohuwa" Ta fada tana ƙare mata kallo..

A rude Anila ta girgiza kai muryarta da in-ina ta ce,"Lafiyana lou ba abun da ke damuna..."

Kaitsaye Benazir ta ce, "ƙarya ne wallahi, Dole akwai abunda ke damunki sai dai idan baki son fadamin ne."

Murmushi ta dan yi,"Bafa wani abu bane, kawai ina yawon yin mafarki akan Uzair...." tunkan ta kare maganar Benazir ta tari hanzarinta, "Mami ta faɗa min hakan, amma ban yarda ba Anila, Look, nifa nasan wacece ke, mafarkin Uzair bazaisa ki shiga damuwa har haka ba, bayan kinsan mafarki ba gaskiya bane, in ma hakanne a yadda nasanki da tawakkali Addu'a zaki dage kina cigaba da yi masa bawai ki tsananta damuwa ba, kawai ni yanzu ki fadamin meke damunki kinsan tsakanina dake babu 6oye-6oye, Kinsan sirrina nasan naki, kuma dai abokin kuka shi ake fadawa mutuwa, pls In har kin yarda da ni...."

Shiru Anila ta yi jim tana tunanin kodai ta fadawa Benazir watakil ta taimaka mata su nemi mafita, ruƙo hannayen Benazir ta yi acikin nata, suka ƙurawa juna ido..

A hankali hawaye suka fara zarya kan kuncin Anila, hakan ba ƙaramin ɗaga hankalin Benazir ya yi ba.

"Zan fada maki saboda na yarda dake, amma dan Allah ki rufa mini asiri Benazir, bana so kowa ya sani mu barshi a matsayin sirri tsakanina da ke.." A ƙagare Benazir ta jinjina mata kai.

Nan take Anila ta fayyace mata komai, tun daga ranar da suka je gidansu Hajiya Adama da abunda ya faru bayan dawowarsu game da 6atan Ana, da inda suka ga Baby Junaid a sume cikin drawer shelve da yadda Junaid ya burkice masu suka rasa gane kanshi, komai saida ta sanar da ita, har wayar Ana ta curo daga cikin pillow case ta kunna mata videon ta mika mata don ta gani da idanunta.

tunkan ta Ƙarasa kallo yatsun hannunta keta kerma kamar wayar zata kife kasa, idanunta azazzare cike da tashin hankali ga wani irin faduwar gaba da take ji, labbanta na kerma take ambaton Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, Allahumma ajirni fi musibati wa'akhlifni khairan minha..., bata ƙare sallallamin ba Anila ta yi saurin toshe mata bakinta da tafin hannunta gudun kada wani ya ji yo su.

Tuni hawaye sun wanke fuskar Benazir, Sai faman girgiza kai ta ke yi.

Cikin muryar rada Anila ta ce,"Allah abun tsoro dan adam abun tsoro, muna nan sake da baki ashe muna a tare da mugun iri acikin mu! Benazir ki fada min taya hankalina zai kwanta? Wai Uncle dina shi ne yake aikata wannan fasikancin a cikin gidan nan? Babban tashin hankalina Ina Ana? Yau kusan wata uku babu ita Benazir, ina jin tsoron ace ya kashe ta...." Ta fada tana kuka ƙasa kasa.

A hankali Benazir ta zame hannun Anila data toshe mata baki da shi.

Hawaye wasu na bin wasu akan kuncinta ta ce, "Anila dama Ana ta 6ace shine baki fadamin ba tun lokacin da abun ya faru?"

"Na yi zaton da son ranta ta gudu shiyasa ban fadamaki ba saboda na saka ran zata dawo."

Jinjina kai Benazir ta shiga yi.

"Mugu bashi da kama Anila, munafuki kamar na Allah, wlh bazamu kyale shi ba, dole mu ƙwatarwa Ana hakkinta sannan mu maka dan iska gurin hukuma...."

bata kare maganar ba Anila ta yi saurin katse ta, "Pls ki daina ɗaga murna bana so wani ya ji, yanzu me yakamata mu yi? Kin dai ji ta ce mutunne mai hadarin gaske in har muka yi kuskuren da maganar ta koma masa zai iya salwantar da rayuwarmu tunda ba imanine da shi ba, Allah kaɗai ma yasan munanan ayyukan da yake aikawata bayan wannan da Ana ta fada."

Jinjina kai Benazir ta yi yayin da kwakwalwarta ke tariyo mata abubuwan dake faruwa da ita a gidan Uncle Musa, yunƙurin kashetan da ake yi ga kuma kurciya da aka yi mata, tun rana ta farko da aka fara yi mata take zargin akwai wanda ke bibiyar rayuwarta.

Anila da ta zuba mata ido ganin ta yi shiru bata da niyar yin magana yasa ta dafa kafadarta, "Benazir kin yi shiru ba ki ce komai ba?" Numfasawa Benazir ta yi kafin ta ce, "Aneelerh, akwai damuwa, nima fa akwai wanda ke bibiyar rayuwata a gidan Uncle Musa, kusan sau hudu ana yunkurin kashe ni....."

Waro idanu waje Anila ta yi, cike da ruɗani take kallon Benazir ya yin da gabanta ke faduwa rass rass!!!

Nan Benazir ta labarta mata komai da ya faru da ita tun farkon zuwanta gidan..

"Aneelerh wallahi ba don Allah yana kawo min ɗauki ba, da tuni an jima da kashe ni, don ma yanzu babu tabon yatsun hannun mutumin a wuyana ya goge dana nuna maki kin gani"

Hankalin Anila fa ya tashi sosai, duk tabi ta rude, "Benazir! anya ba iska bane? In ba haka ba wanane zai yi maki hakan agidan Uncle Musa? Gidan dake a tsare da Security Officers taya wani bare zai iya shigowa har dakin ki ya yi yunƙurin kashe ki??" ta fada tana zare idanunta...

Girgiza kai Benazir tayi, "Wlh Anila ba iska bane, mutunne! Abunda yasa na kara karfafa zargina saboda abu biyu, na farko kurciyar da aka yi mini! Aka rabani da dangina, Na biyu labarin da Ana ta bada, Shine ma ya farfaɗo da tunanina, koma wanene mutunne kuma yana amfani da sihiri kamar yadda Ana tace Uncle ɗan-iya yana amfani da sihiri gurin sarrafa ta"

Da ƙwarin gwiwa ta yi maganar tana duban Anila wadda gaba daya ilahirin jikinta rawa yake yi kamar mazari.

"Ina zargin mutumin da yayi min kurciya shine yake son kashe ni.."

Cikin shesshekar kuka Anila tace, "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'iun! Banazir mun shiga Uku! Wanene wannan? Laifin me ki ka yi masa da ya ja har ya ke son raba ki da rayuwarki? Wai dan Allah meyasa hakan ke faruwa da rayuwarmu? Daga wannan sai wannan?"

Maganar Anila ta sake tuna mata abunda ta faɗa mata game da Taj, cikin saurin ta ce, "Anila! Kinsan tunanin da nake kuwa??" Girgiza kai tayi da sauri, "A'a."

Gyara zama Benazir ta yi,

A labarin da kika bani na abunda ya faru da su Uzair, kin tuna Alhazawan da suka yi ma leƙen asiri? Har suka rikiɗa suka handame uba da ƴa'yansa saboda yayi masu leƙen asiri...?" Cikin sauri Anila ta jinjina kai,"Kwarai kuwa haka ne!"

"To baki tunanin ko halin da nike ciki nada alaƙa da hakan, sai nike ganin kamar idan muka fada ma Taj komai zai taimaka masu gurin yin binciken da su ke yi akan Alhazawan nan da kuma 6atan Uzair? Kuma kinga Taj yanzu jami'e ne shi, sannan yana a gidan Director General In har muka je masu da maganar wallahi ina mai tabbatar maki zasu dauki mataki akan Uncle dan-iyan, tunda su jami'ai ne sun fi mu sanin ta yadda zasu bullowa lamarin, ko ya kika gani?" wata irin nannauyar ajiyar zuciya Anila ta sauke, Wlh sham ta shafa'a ta manta da cewa Taj jami'in bincike ne ai da tuni ta sanar da shi komai.

"Ban ta6a sanin ni shashasha bace sai yau da kika ankarar dani, Mu da muke da jami'i a hannu, Wlh gaba ɗaya kaina ya kwance tsawon kwanakin nan inata neman mafita, kwata kwata tunanina bai bani in tuntubi taj ba, nama manta da cewa shi jami'i ne sai yanzu da kika tuna min."

Murmushi suka sakar ma Juna.

"Yanzu ya za a yi? Babu buƙatar 6ata lokaci, da zafi zafi ake bugun ƙarfe, ƙwara muyi amfani da damar da muke da ita tunkafin lokaci ya kure mana" A cewar Anila.

Benazir ta ce, "Ay daga nan sai gidan DG, Nifa dama da shirina nazo wlh, na ma manta ban fada maki abunda ya kawoni ba saboda halin dana riskeki..."
Chapter 204 · 0% Book details