Sashe 79
Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar mai jin shakkarsa Alhaji ubaid Ya furta"mun sameta akwance kan floor, rabin jikin ta a toilet, kamar faɗuwa tayi don har kanta Ya daku sosai, ta farka sai dai kamar bata a hayyacin ta shiyasa nazo don na sanar dakai...." ta6e la66ansa yai kafin yace"zanyi magana da likita na, zaizo Ya duba ta" godiya ya yi masa kamar zai masa sujjada, komawa cikin dakin yai hajiya sarah dake a zaune kan darduma ta miƙe tana tambayarshi meya faru ne? Ko benazir ta buɗe kofar ne' amsa mata yai da eh jiki na rawa ta fuce daga dakin don taje dubota...
Gaba ɗaya sun hallara a dakin Benazir kowan nan su Ya shiga hali na damuwa, bada jimawa ba Dr Mark Ya shigo gidan, wani basamuden Likita ne irin african american din nan, yadda kasan Jinin Alhaji musa, Fuskarsa babu fara'a, sumar kansa hada kitson zane, tun da Hajiya layla tayi arba da fuskar dr mark kuma taji cewa Alhaji musa ne Ya kira shi don Ya duba lafiyar benazir, tace wallahi bazai ta6a benazir ba, ai kwata kwata ita baiyi mata kama da likita ba, ta dinga surfa bala'e duk yadda alhaji ubaid Yaso Ya shawo kanta shi da su hajiya sarah akan ta bari aduba ta, amma abun Ya faskara a karshe sai dai Alhaji musa Ya sallami likitan Ya tafi ba tare da ya duba benazir din ba, ran Alhaji musa yai mugun 6aci yace tun da ta hana adubata bazai ƙara sanya hannu a zancen lafiyarta ba....ran kowa saida Ya 6aci da abun da layla tayi Alhaji ubaid har Ya gaji da yi mata faɗa, hajiya sarah ce ta basu shawarar su yi gaggawar kaita asibiti don abinciki laifiyarta, ba su tsaya bata lokaci ba, dr shureim Ya dauko benazir da hannu biyu ya tallabota, suka fito daga falon, A mazaunin baya na motarsa ya shigar da benazir, hajiya layla ta shiga ta rungume ta a jikinta, Alhaji ubaid Ya zauna a front seat tare da shureim, yayin da hajiya sarah ta shiga motarta tare da zeenatu kusan atare motocin suka nufi Gate din gidan, Waɗannan gabza gabzan security officers din suka tari gabansu har sai da suka kira Alhaji musa Ya basu iznin su barsu su fita kafin suka basu hanya
Direct suka nufi Obie International Hospital.
__________________ANEELERH
Wuraren ƙarfe tara, Aneelerh ta kammala shiryawa cikin abaya tayi rolling, gaba ɗaya ta ƙagara su karasa estate din kamar tayi fiffike haka take ji, fitowa tayi daga bedroom dinta ta nufi dakin mami, bayan tayi sallama mami ta amsa mata ta shiga daga ciki ta gaishe da ita
Kallo ɗaya mami tayi mata ta fahimci kamar bata jin dadi
"Aneelerh baki da lafiyane naga idanunki sunyi ja?
Kokarin danne damuwarta tayi"mami lafiyata lou, ban samu isasshen bacci jiya ba..."
"Meyasa? Kar dai ace damuwar abun da Ya faru jiya ne"? Girgiza kai tay"a'a mami na tashi yin nafila ne shiyasa banyi bacci da wuri ba..."
"Kunyi waya da su benazir din? Inataso inji ko sun isa gida lafiya"?
"Tun jiya bayan sun tafi nake ta trying layinta baya shiga, har da safen nan saida na kira ba'a ɗaga ba
"To Allah yasa dai Lafiya, Yanzu ina zakije ne naga kin shirya ko hakanan kikai gayu"?
"Mami wani abun al'ajabi na gani jiya awayar zahra, wanda ya daure min kai shiyasa ma na shigo don in faɗa maki"
"To fa, menene ?
Zaro waya aneelerh tayi daga handbag dinta, ta lalubo layin zahra ta danna mata kira,
Bugu ɗaya tay picking"zahra Kin gama shiryawa?
"Eh yanzu zan fito"
"Okey Ki same ni adakin mami dan Allah kada ki bata lokaci"
Bayan ta katse wayar ta dubi mami"gata nan zuwa, abun da zan nuna maki yana awayarta" amsa mata mami tayi da toh cike da zullumin abun da zata gani
Jim kaɗan zahra ta shigo dakin da sallama, Itama ta shiya cikin abaya maroon colour, ta yi rolling, hannun ta ruƙe da wayarta, a bakin gadon mami ta zukunna"ina kwana mami? Kun tashi lafiya"?
"Lafiyalou zahrana, Ina abun da za'a nuna min"?
danna wayar zahra tayi bayan ta buɗo hoton, ta miƙa ma mami wayar tasa hannu ta ƙarba.
kura ma fuskar unaisah ido tayi kamar ta ɗan ruɗe can dai ta miƙe daga kishigiɗan da take ta ɗan kalli fuskar zahra da aneelerh kafin tace"wannan ay hoton Angel ne ko? Yaushe akai wannan hoton? Amma ya akai naga kamar ta ƙara girma anan..." at same time zahra da aneelerh suka saki murmushi saboda sunji dadin yadda mami itama ta gasgata abunda idanunta suka gane mata tunkafin ma su fada mata wa suke hasashen itace
"Mami wannan yarinyar da kike gani sunanta Unaisah, a wurin dinner din prime minister zahra ta dauko hotonta a dakin taron..." da tsantsar mamaki Mami tace"oh wai da ba Angel din bace? Me kama da itace kenan"!
"Mami itace, abunda muke hasashe kenan, zahra ki bata labarin abun da Ya faru a wurin dinner din...." gyara zama zahra tayi gaba daya ta kwashe abun da Ya faru ta sanar da mami
Lamarin yayi mugun daurewa mami kai
Aneelerh ta ƙara da cewa"yanzu haka can estate din zamuje, don mu tabbatar da abun da muke hasashe akan Yarinyar..." jinjina kai mami tayi ita kanta ta goyi bayan suje saboda kamannin Yarinyar dana Angel sun 6aci, bugu da ƙari da taji cewa Yaran tsintattune watakil su dace
"Aneelerh zaiyi wuya ace yarinyar nan ba ita bace, amma dai kuje kawai, Allah Yasa adace"
"Ameen mami, ki tayamu da addu'a Allah Yasa mu samu ganin ta cikin sauƙi, saboda estate din nasu ba karamin tsarone da shi ba, In har ba wani daga cikin Ahlin su Ya gayyace ka ba to basu bari bakuwar fuska ya shiga....."
"Ita zahra ba suna mutunci da mutanan gidan ba"? Acewar mami
Zahra tace"hajiya saratu ce, nasan indai na tuntu6eta zata taimaka mana, duk da nasan mawuyacin abune tun da yaran a hannun chief owais suke da zama, Ba lallai su bari mu gan su ba.....
Shiru mami tayi kafin tace"to me zai hana ku kira ɗan jaridan nan shima badaga family dinsu Yake ba kuma ay yasan da zancen 6acewar yarinyar tun da har bayanan an tura masa....."
"Har kiran layinsa nayi kwata kwata baya shiga, watakil ko Ya shiga wurin aiki ne..."
Mami ta gyaɗa kai"shikenan Kuje kawai sai ku kira hajiya saratun, sannan dan Allah idan ba abaku damar shiga ba kada ku takura kanku ku dawo gida kawai inyaso sai ayiwa ɗan iya magana tun da shi ya saba hulda da yan siyasa watakil ku samu hanyar shiga ta wurinsa.....
Amsa mata sukai da toh,
Kafin su miƙe mami tay hanzarin dakatar da su"ku jira mahboob Ya shigo gidan, kwara kuje da namiji"
Zama sukai har saida Mahboob Ya dawo Mami ta sanar da shi komai, ay tun da yaji zancen Unaisah ya gaza samun nutsuwarsa dama yajima da burin su gano yarinyar ba dan komai ba sai don jarin da Yake tunanin zai samu da ita shi uban son banza....
Lokacin da Motarsu ta shararo kan titin obie estate Aneelerh ta jinjinama haduwar wurin kasancewar yau ne na farko da suka fara zuwa, bata gama shan mamakin daular ba sai da Mahboob Yayi parking a gaban tankameman gate din estate din, hankalin su ba karamin tashi yai ba ganin Jami'an dake tsaron shi, sojoji da Jami'an Isod
Babu wanda Yayi gigin fitowa daga cikin motar, Mahboob Yace"mun kawo kanmu, zahra ni fa tsoron tunkararsu nake Yi Allah, Sai dai wani daga cikin ku Ya ƙarasa driving din...
Yar dariya zahra tayi"bansan Iya shege mahboob dalla ka ƙarasa mana sai kace ba namiji ba"?
"Indai saina tunkari wadannan masu fuskar shanun zan zama namiji to wlh na kwammace ku kirani da sunan hajara...." dariya suka sanya gaba ɗayansu....
Mahboob Fa Ya dage akan bazai karasa da su ba...."
Kwatsam biyu daga cikin sojojin suka tunkaro motarsu hannayensu ruke da bindigogi tuni zufa ta fara wanke fuskar mahboob ganin Yana kokarin tada motar Yasa zahra yin saurin cafke hannunsa"haba mahboob meye haka? Wai dama haka kake da shegen tsoro? Harara Ya galla mata"nifa ba tsoronsu nake ji ba, tashin hankali ne ke banso ..." daƙyar Ya ƙare maganar ganin har sojojin sun ƙaraso gare su
Kwankwasa window glass din motar, ɗaya daga cikin su Yayi da kakkausar murya Ya furta"Put down the glass!" Aneelerh ce tayi karfin halin sauke glass din windown Ya zukunno da kansa Yana binsu da kallo idanunsa jawur
"Su wanene ku kuma daga Ina?
Murya na rawa zahra tace"wurin Hajiya saratu muka zo...."
"Okey, Ku kirata awaya don ba'a sanar damu zuwanku ba"
jiki na kerma ta amsa mashi da toh, da sauri zahra ta kira Layin hajiya saratu, kusan sau takwas baya shiga, Hankalinsu ba karamin tashi Yayi ba
"Bari na ƙara kiran ziyad watakil shi Ya ɗaga" aneeelrh ta fada yatsun hannunta na kerma ta curo waya ta kira layin ziyad tana ringin baya picking, hankalinsu duk Ya tashi
Ƙasa ƙasa da murya Aneelerh tace"mun shiga uku zahra shima bai ɗaga ba yanzu ya zamuyi"?
Mahboob da ya gama tsorata Yace"mu koma gida kawai shine mafita in ba haka ba wlh wannan mai fuskar shanun tsaf zai Iya bombing motar mu... cikin muryar raɗa yai magana
Zahra tace"wait bari na kira zayn duk da nasan mayucin abune yayi picking..." koda Ta kira layin zayn sau uku baiyi picking ba, A kira na huɗu ne Ya ɗaga muryarsa kamar ta mashayin giya ya furta
"Waye"? Ko sallamarta bai amsa ba
Cike da jin shakkarsa ta furta"zahra ce"
"Wace zahra"? Sarai fa Ya gane muryarta har saving layinta Yana da shi awaya
"Am..zahra wadda mommynka ta haɗa ka da ita, a wurin dinner din prime minister
"Okey nagane, lafiya kika kira"?
"Munzo estate dinkune an hana mu shiga, sojojin sunce dole sai an basu izni kafin su bari mu shiga
Kafin ta kare maganar Zayn yace"kina hauka ne? Ki rasa wa zaki kira saini? Oh tun yanzu raini Ya fara shiga tsakanina dake! Uban me ma Ya kawo ku estate din?
Hatta su Aneelerh sai da sukajiyo masifar da yake zazzaga mata