← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 130 OF 238

Sashe 130

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta jima tana kallon kanta a cikin madubin, jiri jiri ta fara gani a idanunta da sauri ta dafe cikinta dake yi mata kukan yunwa ga wani kishin ruwa na fitar shari'a, makoshinta ya bushe ƙamas ko yawun da zata hadiya ta samu relief din kishin babu shi abakinta.

juwa ce ta kwashe ta gaba ɗaya jikinta ya rinjayeta ta yanke jiki ta faɗi ƙasa a sume..

Saurari Littafin Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.

Cikin abunda baifi minti ashirin ba kacal, taji safkar ruwa mai sanyi kan fuskarta, dogon numfashi taja haɗi da sauke ajiyar zuciya sam takasa ta6uka komai, ko yatsan hannunta bata iya motsawa saboda rashin kwarin jiki.

cikin mawuyacin hali ta ɗan yi karfin halin buɗe idanunta biji biji take kallon mutumin dake tsaye akanta batasan wanene ba.

Cikin disasshiyar murya ta furta"ruwa!ruwa!ruwan, zan sha! Kishi nake ji..." dakyar sautin muryarta ke fita tana tsaka da sambatu taji an kanga mata wani abu kamar bakin gorar ruwa saitin bakin ta, wani irin sanyine ya ratsa zuciyarta, lokacin da ruwan ya jiƙe makoshinta nan da nan ta fara kwankwaɗarshi makoshinta har wani sauti yake badawa kwat kwat...!!

"Ki sha A hankali kada ki shaƙe" cikin kunnanta ta tsinkayi muryar dattijuwar dake mata magana.

Sai dai kwata kwata bata fahimtarta, tafi buƙatar ruwan fiye da komai ayanzu kamar rayuwarta ta dogara akan shi.

saida tasha mai isarta kafin ta fara numfarfasawa tana haki, wata irin nutsuwace ta shige ta, hatta bugun zuciyarta da fitar numfashinta sun daidaita, ganinta dawo daidai sannu a hankali take kallon fuskar tsohuwar da ta tallabe kanta akan kirjinta, hannunta yana ruƙe da gorar ruwa, tana asanye da alkyabba fara sol mai hula, tsohuwace tukuf fuskarta duk tamoji tamoji, gashin kanta fari fat hurhura ta mamaye ko'ina na gashin, hatta gashin jagirarta fari ne fat, daga ganin tsohuwar tayi gwagwarmaya a duniya, tsufanta bai boye kyawunta ba, bakowa bace wannan face Tsohuwa

*KHALA* dattijuwar arziƙi, fara mai farar aniya, tsohuwa mai zuciyar imani, macace mai tausayi da jinkan mutane, abun da zai baka mamaki tana ɗaya daga cikin Elders na kurkukun ƙaddara sune masu fada aji, tana da ƙarfin iko, amma meyasa ta fita daban acikin su⁉️

Gabriella ta tsareta da idanu tana binta da kallon kurulla, fuskarta da alamun ruɗani

kamar yadda take kallonta haka itama tsohuwa khala take kallon ta.

la66anta na kerma ta furta"wacece ke? Wa ya kawo ni nan? Meya faru da ni? Ki fadamin ina son sani" shiru tsohuwar tayi nata ce mata komai ba.

"Kinyi shiru baki ce mun komai ba, meyasa kike kallona? Wacece ke?....." ta faɗa arude tana tararraba idanu.

Tattausan murmushi ne ya bayyana akan fuskar dattijuwar, cikin sanyin murya ta furta"Sunana Khala, nasan baki sanni ba, kuma baki ta6a jin labari na ba, yau ne karo na farko da kika fara ganin fuska ta..." cike da dattako tayi maganar.

Ta ɗan dakata tana kallon gabriella.

"Yau tsawon makonni Ina jinyarki, Due to the traumatic brain injury that put you in a coma, I know you can't remember what happened to you because you've lost your memory..." tun da ta fara magana Gabriella ta nutsu tana kallonta.

"naji dadin samun lafiyarki, inatayaki murna"

Saurari Littafin Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
ta fad'a fuskarta ɗauke da annurin farin ciki, ita dai gabriella takasa gane komai, gaba daya arude take da tsohuwar, bata fahimtarta

"Naji kin ambaci nayi jinya tsawon makonni bana acikin hayyacina, meya faru dani"? Girgiza kai khala tayi"I won't tell you because I don't want you to remember what happened to you, ko dan saboda lafiyarki, a yanzu nafi bukatar kwanciyar hankalinki, saboda ina da buri akanki"! Aruɗe Gabriel take kallonta, harta buɗe baki zata tambayeta wata irin yunwa ta murɗa cikin ta, da sauri ta dafe cikin da hannu tana faman yamitsa fuska ta kalli khala"ki taimaka min da abinci, yunwa nake ji..."

Ajiye gorar ruwan hannunta tayi, tare da taimaka mata ta zauna dakyar, Sandar ta dake ajiye kasa ta ɗauka, ta mike tare da juyawa ta nufi wani teburi dake a dakin hada kujeru biyu a kewaye da shi, daga saman teburin kwanukan abinci ne.

Ta ɗauko bowl ɗaya ta juyo tare da kallon Gabriella

"Bansani ba ko kin iya cin zogale da kuli..." tunkan ta ƙare maganar gabriella tace"Ina ci, koma menene zanci.." murmushi khala tasaki ta nufo gurinta ta miƙa mata kwanon, Hannunta na kerma ta cire murfin ta fara dibar zogalen tana ci, duk da babu ɗanɗano abakinta, kunnuwanta har motsi sukeyi tsabar dadi, hannu baka hannu kwarya take duma loma tana turawa a karamun bakin ta kamar zata shake, kamar kyaftawar ido ta lamushe shi tass hada sanya harshe tana lasar kwanan..dariya khala tayi"kin koshi ko kina bukatar kari" da sauri ta ɗaga mata kai, juyawa khala tayi cikin takun dattako ta koma gaban table din ta buɗe wani kwano mai ɗauke da tsokokin nama taje ta mika mata kwanon"kalacina ne na safe, da naci na rage, bansan yau zaki farfadowa ba, shiyasa ban tanadar maki abinci ba, amma kiyi hakuri da wannan, idan aka kawo min lunch dina zan baki kici ki koshi" kar6e kwanon gabriel tayi hannunta na kerma ta fara daukar tsokar tana ci, sai da tacinye tass khala ta ɗauki gorar ruwan ta miƙa mata, ta kar6a ta sha.

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke wani irin relief taji a jikin ta, duk da bata koshi ba, taji ɗan dama dama a cikinta.

Kokarin mikewa tayi da sauri khala ta taimaka mata ta mike tsaye kan kafafunta, cikin sanyi murya tace"har yanzu baki bani amsar tambayoyin da nayi maki ba, na ruɗe na kasa tuna komai, wanene ya kawo ni nan? Ko kece? Sannan meya faru dani? A ina nake?

"Ki manta da komai, sai ki zauna lafiya, tunawar baida amfani, idan kika bani hadin kai, kuma kika bi sharuddan da zan fada maki zaki tsira da rayuwarki, idan kuma kikayi min gaddama zaki dawwama awahala..." kalamanta sun rikita gabriela cikin rawar murya tace"meyasa zaki hanani tambayarki? Ina son nasan wacece ni! Meya faru dani, ina ji araina kamar na manta wani abu arayuwata, dan Allah ki tuna min..." dafa kafadarta tsohuwa khala tayi"nayi maki alƙawarin zan baki amsar tambayoyinki amma ba yanzu ba, har sai zuwa lokacin da tunaninki ya dawo dai dai..." shiru gabriella tayi gaba daya jin kanta take kamar ba ita ba, kamar ma ba aduniyar mutane take ba.

Tafiya khala ta soma yi tana nufar cikin dakin calmly ta cigaba da magana tana kallon fuskar gabriel

"Sharuddan da zan gindaya maki, na farko koda gigin wasa kada ki ƙetare iyakarki! Ma'ana kada kiyi yunkurin nema ma kanki hanyar da zaki fita daga dakin nan! Babu ruwanki da komai da zaki gani adakin nan! Ki zama tamkar makauniya, bana son mutum mai karanbani da kafiya..." ta faɗa tana jinjina mata kai, ita dai gabriela tayi zuru tana binta dana mujiya saboda batasan komai ba sai yadda akai da ita.

"Idan kika bani hadin kai, zaki tsira da ranki, kuma zan gatantaki, babu abunda zaki nema ki rasa adakin nan.." fuskarta da murmushi tayi maganar, kafin ta juya ta ɗaga sandar hannunta tayi mata nuni da wata ƙofa

Sannan tace"wannan kofar, makewayina ne, idan uziri ya kamaki zaki iya shiga, harma wanka zaki iyayi don kiji dadin jikin ki, arana zaki ci abinci sau uku, idan kadaici ya dame ki, zan baki story books da zaki dinga karantawa, suna da dadi zasu debe maki kewa, ga kuma furanni abun sha'awa zasu faranta maki rai" ta faɗa still da murmushi akan fuskarta.

Gabriella tayi sototo tana kallonta kamar sakarya, wuce wa tsohuwa khala tayi agaban bookshelve ɗin ta tsaya tare da kai hannu cikin shelve tana neman storybooks din da zata bata guda uku ta curo ta juyo ta nufi Gabriel ta nuna mata su.

"su kadai na baki iznin ki karanta, bayansu ban laminta ki ta6a sauran littattafan dake a cikin shelve din ba" jinjina mata kai tay alamar toh, bayan ta kar6i books din khala tace"ki samu guri ki zauna, har yanzu jikinki ba kwari," cike da ladabi ta amsa mata da toh, don yanzu ganinta take kamar mamanta saboda itace mutun na farko data fara gani a idanunta bayan tsawon lokaci data ɗauka a coma..

Ruƙe hannunta khala tayi, taja ta har zuwa gaban table din ta zaunar da ita kan kujera"idan kika gaji da karatun, ki koma kan gado ki kwanta kiyi bacci ki huta" cikin sanyin murya ta amsa mata da toh.

"Akwai inda ke yi maki ciwo a jikin ki"? Girgiza kai tay alamar a'a

"Okey, ko bayan na fita daga dakin, kika ji wani guri nayi maki ciwo a jikin ki, ki kira sunana sau uku, zan ji ki"

"Toh,"

"Good girl" ta faɗa tare da shafa fuskar Gabriella da yatsun hannunta.

"Ki kula min da kanki" lumshe ido gabriela tayi kafin ta buɗe su tuni tsohuwa khala ta bace ma ganinta, har saida taji gabanta ya fadi ganin babu ita, akan table din ta ajiye books din data bata.

ta mike tsaye jikinta na kerma take bin ko'ina da kallo a kokarinta nata gano ina ta shiga, ganin babu ita adakin, yasa ta hakura da nemanta, ta juya ta nufi kofar makewayin da ta nuna mata, ta buɗe ta shiga, makewayine irin na zamani ya hadu komai cikinsa fari kyal, a tsaftace ba kazanta, a hankali take kallon cikinsa, bathtub ta gani ga shower, ga toilet seat, da cabinet, bata tsaya bata lokaci ba, ta cire rigar jikinta ta rataya a hanger, ta zukunna zatay fitsari taji gabanta amatse dakyar fitsarin ke fita nishi ta dinga yi a wahalce ta samu ta kammala.

ta miƙe tana faman sauke ajiyar zuciya, Takura kanta tayi da tunani har saida kwakwalwarta ta fara neman rikicewa tukunna ta hakura tana faman jan numfashi, ta nufi kwamin wankan ta shiga ta kwanta tare da kai hannu ta kunna bathtub faucet ta cika kwamun da ruwa mai ɗumi wata irin ni'ima taji mai dadin gaske.
Chapter 130 · 0% Book details