← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 198 OF 238

Sashe 198

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta dan dakata da bata labarin tana mayar da numfashi kafin ta daura da cewa"Aunty kwatsam tsakar dare ina tsaka da bacci na fara jin yatsun hannayena sunayi min kaikayi, a furgice na farka ina kikarin motsa labbana naji sunki budewa aunty adaren ranar naga bala'e ban kara komawa bacci ba....."

kasa karasa maganar tayi saboda kukan daya ciyota..."

Tunda tafara labarta mata abunda ya faru gaba daya Ta rude tabi ta rikice ta rasa tunaninta, ta razana matuka idanunta azare take jujjuya eye balls dinta, wani irin gumi ne ya fara tsastsafo mata akan goshin ta..wa'iyazubilla bata san sa'adda wayar ta zame daga hannunta ta fada kan floor.

fadawa tay kan mattress Ta lumshe idanunta da suka kaɗa jawur, Hakika hankalin ya tashi Ahakama bata gasgata maganar Marwa ba, saboda ta yarda da pravin ta cikin sauki bazata yarda don afada mata wani mugun abu daya shafe shi ba, Ita tasan wanene Mijinta, In har bashi ya bude baki ya fada mata da kanshi cewa ya aikata ba to ba lallai ta yarda ta cikin sauki ba, kawai tayi believing marwa karya takeyi mata sai dai abu daya dayasa ta jin farga harya haifar mata da kokwanto shine taya akai Marwa tasan akwai aure a tsakaninta da pravin❓

Fashewa tayi kuka tana fadin wallahi karyane, Ni nasan wanene Mijina, pravin ba matsafi bane, kuma baya bin mata, sharri ne kawai akeso ayi masa wlh marwa dana san zaki fadamin wannan maganar da banyi jinyarki ba saboda ke din ba mutuniyar kirki bace, Makira algunguma kawai kinaso ki shiga tsakanina da mijina ne..." kamar mahaukaciya ta dinga sambatu tana bubbuga mattress da hannayenta gashin kanta duk ya hargitse..."

_________________________________✍️

*Chief Owais🔥🌹*

Time da motarshi ta kunna kai cikin gidan baba Obie, tunkafin SA din dake driving dinsa yayi parking Idanunsa suka sauka akan Security details din daddynsa ta window glass din motar yake hango su, sunyi tsayuwar dakaru agaban dankara dankaran motocin su.

Tuni yanayin fuskarsa Ya canza zuwa tsantsar bacin rai, yanzu baida abu mafi tsana a duniyar nan daya wuce mahaifinsa! Baya son ganin shi, ko sunan shi baya son ji, yanzu har takaiga ba zarginsa yakeyi ba tabbaci yake da shi akan cewa yana ɗaya daga cikin Elders na gidan kurkukun ƙaddara shiyasa kwata kwata yanzu baya jinsa amatsayin Uba, Ya toshe duk wata hanya da zata hada su, yanzun ma daya san yana agidan da baizo ba.

Fitowa Yayi daga Cikin Motar, Farar jallabiyace a jikin shi ya naɗe kanshi da arab turban saboda baya son wani yaga raunin dake akan goshinsa, saboda baya son ya daga masu hankali, Walking slowly Ya nufi main palour, with respect maids din dake sintiri suke gaishe da shi bai ko kula su ba ya nufi part din baba Obie tunkan Ya karasa Ya dinga jiyo muryoyin Uncles dinsa suna fira cikin raha ..

Knocking door din yayi,"wanene"? Hajiya saratu ce ta tambaya daga cikin dakin.

"Owais ne"

"Okay, Come In" tura kofar yayi tare da sa kai Ya shiga da sallama abakin shi, kusan a lokaci daya suka dube shi.

baba obie yana daga kishindige kan Tattausan Rug Ya tada kansa saman Pillow, daga gaban shi wooden tray ne na fresh fruits da aka kawo ma sa, Hajiya saratu ce ka bashi Kayan marmarin a baki Yana sha.

yayin da Senate Lateef da Sir Mubarak suke a zaune kan Sofa, Mai girma sharafudeen Yana a zaune kan arm Chair, Ya dauki wankan suit...

"Zauna mana," Hajiya saratu ce tay maganar ganin yayi tsaye kamar mai nazarin wani abu.

A hankali Ya zauna cikin girmamawa Ya gaishe da su, da fara'a suka amsa mashi, kafin ya matsa kusa da baba Obie ya sumbaci forehead dinsa.

"Sannu da dawowa baba, Ya gajiyar tafiya"? fuskar baba Obie da murmushi Yace"Yawwa shalelena, gajiya tabi jiki musamman da na ga rabin raina" dan murmushi yayi"nayi kewarka, bayan haka Naji dadi da Allah ya dawo min dakai cikin koshin lafiya" still fuskar baba obie da murmushi yake kallon shi, Har cikin ran shi yaji dadin maganarshi.

Tun shigowarshi bai bari sun hada ido da daddynsa ba, shi ko Ya kura masa ido fuskarsa ba walwala ganin yanda Owais yaba banza ajiyar shi, Ko irin gaisuwar nan da suka saba yi in suka hadu da juna baiyi mashi ba, hakan ya jefa shi a yanayi na damuwa.

Hajiya saratu tace"owais ina ka shiga ne? Kusan two weeks bama ganin gifcinka, ko an kira ba'a samunka"! Senate yace"abunda zance kenan, Kwata kwata baya leƙo mu, ko dan kaga kakan naka baya nan ne? Dama albarkacinsa muke ci halan"

"Ba haka bane, wlh kuna araina, aikine ya boye ni"

Sir mubarak yace"kufa haka kuke dakai da dan uwanka baku da magana sai ta aiki kamar agogo bakwa gajiya" dan murmushi yayi Baba Obie yace"karfa ku takura ma shi tom, in ba haka ba yanzu zan kora ku waje, kowa Ya kama gabansa kubarni da abun kaunata"

dariya suka sanya banda mahaifinsa wanda ya zabga ubam tagumi.

"Baba Ya aminin naka, na lura kaji dadin zama agurinsa, kai da kace zakai 3 weeks sai ga shi har ka kara kwanaki akai" yar dariya yayi Owais"ba zaka gane ba, wlh kamar kar mu rabu, dakyar fa escords dinshi suka rabamu a airport, wlh har kwalla saida na zubda saboda tausayinshi daya kamani"

dakyar ya kare maganar, kwalla cike tab da idanunshi.

Jikinsu duk yayi sanyi, tausayin baban nasu Ya kamasu
Sir mubarak yace"har yau har gobe ina mamakin amintakarku baba, na dade banga abokai masu rukon amana da kaunar juna, da suka taso tunkuruciya batare da wani abu ya raba su ba irinku, Ina alfahari da ku, Allah ya ƙara dankon zumunci atsakaninmu da shi"

kalaman Sir Mubarak sun faranta ranshi da fara'a yace ameen
Senate Lateef Yace"baba mezai hana ya dawo nan mana, tunda shi ba iyali gare shi ba, a legos dinma ba wani dangine da shi ba, kai kadaine dai danginsa" numfasawa baba Obie yai kafin yace"ba yadda banyi da shi ba akan ya dawo nan mu zauna, amma yaƙiya shi dai yafi sha'awar zaman legos, hada sabo ke dawainiya da shi amma in sha Allah idan ya halarci family meeting din da zamuyi zanyi kokarin jan hankalinshi akan Ya dawo nan din.."

"Ina pravin dinne? Ina so inyi mashi bangajiya" chief ne ya fada, hajiya saratu tace"Yana adaki"

"Okay, ya fada tare da kallon Sir mubarak"Uncle, Ina zaki? Tsawon kwanaki banji duriyarsa ba, ko na kira bana samun layin sa"

"Ay Zaki tun satin daya wuce suka koma canada.." hajiya saratu tace"ba sallama"? Ta fada ranta adan bace.

Senate Yace"gaskiya ba a kyauta mana ba" Sir mubarak yace"kuyi hakuri, ai ba jimawa zaiyi ba, Idan za'ayi family meeting zai halarta ne"

gaba daya hankalin sharafuddeen baya atare da su, bawan Allah Hankalinsa na akan dansa dake ta kakkauce masa..

"Baba Ina neman alfarma, agurin kowannanku" acewar Chief, gaba daya hankalinsu ya dawo kanshi..
Baba Obie Yace"ina sauraronka fadi kaitsaye"

Shiru ya ɗanyi jimm kafin ya ce"inaso a yi family meeting a ranar birthday dina"

da dan mamaki suke kallon shi, basu ta6a canza date na family meeting din su ba.

"Alfarma nake nema, Idan kowa Ya amince min, amma idan bazai yiwu ba, ba damuwa"

Numfasawa baba obie yayi tare da cewa"owais, wannan ai ba wani abu bane, canza date bazai zama matsala ba, nidai bani da damuwa na amince maka, sai dai bansan ra'ayin iyayen naka ba" ya fada tare da nunasu da hannun shi.

Hajiya saratu tace"haba bakomai wlh, nidai na amince masa"

"Nagode Auntyana" murmushi tasakar mashi

Senate lataeef Yace"ka yi tunani mai kyau owais, kaga kowa zai halarci birthday dinka har ma wadanda basa kasar saboda family meeting, Nima ta bangarena na amince"

fuskarshi asake Yace"nagode Uncle senator" ya maida dubansa kan sir mubarak wanda ya hade rai

"Thats impossible, akan me za'a canza date da aka saba yin family meeting saboda kai? Gaskiya ni ban amince ba," hankalin Chief ba karamin tashi yayi ba, hatta sauran Uncles din nasa sunyi mamakin maganarshi haka baba Obie ma baki asake yake kallon shi, cikin sanyin murya chief yace"Shikenan, tun da baka amince ba, na hakura nima abarshi a kwanan watan da akeyi" dariya Sir mubarak yayi"zolayarka kawai nakeyi, kasan ni bani da matsala Owais, tun da har baba ya amince nima na amince maka, Allah ya nuna mana lokacin da rai da lafiya" sanyine ya ratsa zuciyar chief cike da jin dadi Yace"ameen Uncle dina thank you"

"Sharafuddeen Me ke damunka ne"? Muryar Baba Obie ce ta dawo da shi daga duniyar tunanin daya lula, murmushi ya kakaro kan fuskarsa babu komai baba,"

"Ina fata kaji alfarmar da ɗan naka yake nema agurinmu"? Jinjina kanshi yayi"naji baba, Allah ya nuna mana lokacin" iya abunda ya furta kenan.

Wayar Chief ce tayi ringing, mikewa yayi da sauri Yayi masu sallama Ya fuce daga dakin don Ya daga kiran da aka yi mashi..

Bayan ya kammala yin wayar juyawar da zaiyi keda wuya yayi arba da daddynsa bawan Allah fuskarsa A yamutse yake duban shi.

"Owais, Laifi me nayi maka? Meyasa kake guduna ko kallona baka son yi? Why Owais kayi blocking duk wata hanya da zan iya magana dakai" ya fada amarairaice.

kallon tuhuma Owais Ya doka masa da kakkausar murya yace" ka daina boye true colour din ka, yanzu na riga da nasan ainihin wanene kai! kuma wlh alwashi na dauka saina tona maka asiri kowa yasan abunda kake aikatawa..."

waro idanu waje mai girma sharafuddeen yayi da tsantsar rudani akan fuskarshi yace"owais wannan wani irin zancan banza ne? wani irin asirine kake ikirarin zaka tona min"?

Banza yayi dashi bai tanka ma shi ba, matsawa Yayi kusa da shi"owais Ka fadamin dan Allah, me na aikata? Idan ma saboda Sleeping pill din dana bakane yasa kake zargina wlh banyi da wata manufa, nayi ne saboda naji tsoron in rasa ka"

harara Chief Ya galla masa, ji ya ke kamar ya shaƙe wuyan uban nasa saboda tsanar da yayi masa.

Hannu yakai yana kokarin ta6a turban din dake akansa da sauri Owais Ya cafke wrist dinsa a tsawace ya furta"Don't even think about touching me, or you'll face unforeseen consequences"!
Chapter 198 · 0% Book details