← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 238

Sashe 48

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ki share hawayen nan, Ki tashi muje ki faɗa mata kinjanye" muryarta na kerma ta amsa mashi da toh, shu'umin murmushin gefen fuska yasaki, dama yasan zata amince ko dan saboda abinda yai mata don ya fahinci ba yar hannu bace tana da kamun kai shiyasa ya tsorata ta.

Hanky ta zaro ta share hawayen fuskarta, sannan ta daidaita nutsuwarta, kafin ta buɗe motar, ta fito shima ya fito ta ɗayan bangaren suka nufi hajiya saratu dake atsaye can nesa da su.

Tunkafin su karaso ta nufosu, fuskarta da fara'a tace"Son, Ina fata kun sasanta kanku"!

Nunata zayn yai"ki fada mata abun da kika gaya min acikin mota" amsa mashi tayi da toh kafin ta kalli hajiya saratu zuciyarta cike fal da tsoronsa ta ce"Mun gama magana dashi, Kuma mun fahimci juna" a gigice zayn yake kallon zahra jin abunda tace, zuciyarsa ba karamar hasala tayi ba, bai ta6a tsammanin yarinyar zatay taurin kai ba.

"Zahra kin tabbata yayi maki? Amma meyasa naga idanunki sunyi ja"? Da sauri zahra tace"kaina ne keyi min ciwo, har fada masa nayi, shine yace yakamata na tafi gida na huta, zamuyi magana awaya..." da tsantsar mamaki zayn yake kallonta, gashi ba halin Ya karyatata, don ya fahimci ta kama zuciyar mommynsu.

"Naji dadi my son, dama nasan bazaka ƙi tayin da nayi maka ba, da ace zaid ne ba lallai ya amince ba saboda shi na daddynsa ne kai kuma nawa ne, hakika yau ka faranta raina my son, Allah yayi maka albarka, zahra kema nagode maki sosai da kika aminta da tayina in sha Allah ba zakuyi danasani ba, Ina da tabbacin hakan, Ta fada tare da janyo zayn da zahra tayi huggin dinsu tana ɗan bubbuga bayansu, sai faman farin ciki takeyi yayin da su kuma zuciyoyin su suke a kuntacce da bakin ciki.

"Zayn ko zaka kaita, Gida"? Ta fada bayan ta raba su daga jikinta, da sauri zahra tace"mommy kin manta nazo da mota dina"

"Oh eh hakane, na shafa'a, Muje son mu rakata ta tafi gida" atare da zayn suka raka zahra bakin mota bayan ta shiga ta zauna, hajiya saratu tace"surukata, Anya zaki iya driving dinnan kuwa? Ko dai zayn yakai ki" wani irin mugun kallo zayn ya watsama zahra da sauri tace"a'a mommy, wallahi zan iya, ay ba sosai nake jin ciwon kan ba"

"Toh zahra Ki kula min da kanki sannan ki gaishe min da mutanan gidan"

"In sha Allah ngde ssae"

Harara hajiya saratu ta watsa ma zayn"kai bazakai mata bankwanan ba, ahaka zakuyi auren" yana faman yamutsa fuska yace"bye, sai mun yi waya" aran shi ya furta "zakiyi danasani,"

Bayan ta baro estate din har ta hau kan titi tana driving, zuciyarta bata daina tariyo mata kalaman zayn ba.

Uban tagumi aneelerh ta zabga da hannu ɗaya, tana kallon zahara data kammala bata labari

"Zahra kinyi kuskure wlh, meyasa baki ɗauki shawararshi ba kin fada mata baki son shi? Zahra ina guje maki auran mutun mara kunya irin shi! Kowace uwa burinta ta sama ma ya'yanta uba nagari wanda zasu koyi da shi su kuma yi alfahari da shi ba irin zayn ba, sam bai dace dake ba" zuciyarta ajagule tafada, kwata kwata zayn bai kwanta mata aranta ba, tun kafin ma ta ganshi.

Zahra Tana shesshekar kuka ta ruko hannunta"ki tayani da addu'a, ita nafi bukata, Aunty aneeleeh bawai nakasa fada mata bane, Ina son shi ne"

Jinjina kai aneeleeh tayi"inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Shikenan, zan tayaki da addu'a Idan alkhairi ne shi agare ki Allah Ya tabbatar mana dashi, idan kuma akasin hakan zan roki Allah Ya shiga tsakaninku, bayan haka dole su mami suji maganar nan"

kwantar mata da hankali aneelerh tacigaba dayi saida komai ya lafa tukunna aneelerh tace"Ina alkwarina? Kince zaki ɗaukar min hotunan dinner in gani, Jiya da su na kwana araina, ganin kin kwaso gajiyane yasa ban takura maki ba"

Murmushi zahra tasaki tunawa da Unaisah, yarinyar data kwanta mata aran ta.

"Aunty aneeelerh, akwai labari, zaki sha kanun labarai, " ta fada tare da janye baby juanid dake langwa6e ajikinta, kamar maijin bacci Yai shiru Yanata sauraronsu.

Gado Ta nufa ta dauko purse dinta ta curo wayarta donta nuna ma aneeleeh hotunan da ta dauka tare da unaisah

Kwatsam wayar ta fara ringing, da sauri tayi picking ganin sunan abie

Barka da safiya abie ina kwana"?

"Lafiyou, zahra, Ina aneeleeh ne"? Da sauri tace gatanan adakina

"Okey ki fada mata, ƙawarta ta turo min da sako ta layina, ta zo ta same ni a daki ina jiranta!" amsa mashi tayi da toh bayan ya kashe kiran ta dubu Aneelerh dake kallon ta, cike da son jin me abie Ya faɗa mata.

"Abie ne ya kira, yace in faɗa maki Kawarki ta tura mashi da sako ta layin shi kije ki same shi adaki"

Da alamun mamaki Aneeleerh ta furta"ƙawata kuma? Anya kuwa abie ya karanta sakon dai dai? In bahaka ba ni wata ƙawace gare ni da zan bata layin abie"

"Aunty Aneelerh kije kawai ki gani, bamusan menene aka turo ba" amsawa tayi da toh a hanzarce ta mike ta bar junaid adakin.

Ruko hannun shi zahra tayi"zonan In nuna maka hotunan dinner,"

Gefen gado ta zauna tare da daura shi kan laps dinta, ta buɗe gallery tana nuna mashi hotunansu, lokacin data buɗe hoton Unaisah, wuff Junaid Ya fusge wayar daga hannunta Yana fadin"Angel! angel! angel"! Har saida gaban zahra Ya fadi, a matukar rude take kallon shi ba tare data fahimci me yake nufi ba.

*SALSABEEL💫*

Zaune Yake kan sofa hannun shi ruke da wayar shi, Har ya kammala shiryawa, sai faman duba agogo Yake yi, Har ya fara gajiya da jiran su, ɗagowa yai tare da kallon su, suna a zaune tsakar falon suna cin abinci, mutun ɗaya ce ke babu acikin su, Khadeeja dake acan cikin toilet tana wanka, a kalla ta shafe kusan awa ɗaya da rabi har yanzu bata fito ba, gashi har yan uwan ta sun kammala shiyawa.

"Dan Allah ku yi sauri ku ƙarasa, kun ga har karfe sha biyu ta buga" amsa mashi sukayi da toh

"Yaya salsabeel, Khadeeja fa? Har yanzu bata fito ba, ko ban da ita zamu tafi" rubeena ce tayi maganar.

"Bansan ya zanyi da ita ba, so take ta 6ata mana lokaci, bari naje na dubo ta" ya fada tare da miƙewa Ya nufi upstairs.

"Wallahi Dama mu tafi mubar ta a gida, kada ta mana hauka, tun da ya salsabeel Yace wurin gasar kyau zamu je kuma in muka ci za'a bamu kyautar wani abu" acewar hibba.

rubeena na murmushi tace"ni zan cinye ma gasar saboda nafi ku kyau" harara hawwa ta galla mata"a haka din? Dubi kumatunki, kuma ay cewa yai sun fi son mace doguwa mai gashi, mara jiki, me dogon hanci" daure fuska rubina tayi rai a6ace tace"wlh indai bani zanci ba sai dai kowa ya rasa" ta fada tare dakai hannu ta dauki robar zuma ta dinga watsa masu akan rigunansu, azabure suka mike suna faman zare idanunsu ganin ta 6ata wankan su.

"Wallahi baki isa ba, Saina rama mana" sarah ce ta fada da sauri ta fisge zumar ta matsa mata a jikin rigarta, fashewa tayi da kuka tana fadin wayyo Allah ya salsabeel sun 6ata min kayana, shikenan ni bazanci gasar kyau ba, zuƙunnawa tayi gaban kayan abincin tana haki ta dauki coke da niygar ta watsa masu, damƙo hannunta Hawwa tayi nan fa faɗa ya kacame a tsakaninsu, daga wadda za'aja ja ma gashin kai sai wadda aka ca6e ma kwalliyar fuskarta, Mubeen dake a zaune yana kallon su sai faman tikar dariya yakeyi

Duk wannan budurin da sukeyi salsabeel bai sani ba, Yana atsaye bakin kofar toilet din dakin su khadeeja, ba irin bugun kofar da baiyi mata ba akan ta fito, amma taƙi ko tanka mashi.

Rai a6ace yace"wallahi idan kika bari nasa kafa nabar dakin nan sai dai ki zauna agida, Babu inda zaki je" muryarta da shesshekar kuka tace"wayyo Allah ya salsabeel ba kaine kace zamuje gasar kyau ba, shine fa nakeso in koma fara" waro ido waje yai jin soki burutsin ta, cike da takaici ya furta"Baki da hankali ne? Tayaya za'ai ki koma fara? Waya fada maki sai farare suke cin gasar kyau? to bari ki ji in fada maki bakake sune suka fi lashe gasar" muryarta da shagwa6a tace"ni dai Allah ba wani nan wayo kakeso kai min don kada inci"

Dafe kanshi yai da hannu ɗaya"ke zaki fito ko ba zaki fito ba" shiru tayi bata tanka masa ba,

Buga kofar yai da karfi"Khadeeja ranki zai 6ace in baki fito ba" still bata tanka mashi ba

Banko kofar dakin akay, Mubeen ne ya fado ciki kamar an wurgo shi, Rigar shi duk ta 6ace da jan bakin su rubina

A ruɗe salsabeel ke kallon shi Yama rasa ta ina zai fara

"Yaya salsabeel, Kaga su rubina sun 6ata min kayana da jan bakinsu, kawai saboda nayi masu dariya suna fada" bai karasa sauraren shi ba yai saurin fucewa da sauri mubeen Yabi bayan shi tunkafin Ya sauko down Ya hango su manne da juna, sun kacame kamar irin kifin gwangwanin nan sai ihu suke Yi,

Wata irin tsawa mai sauti Ya daka masu a firgice suka saki junansu, suna ganin shi suka fara kokarin bare baki zasuyi kuka

Nuna su yai da yatsan hannun shi"kar wadda ta kuskura tayi min kuka" ya fada yana zare masu idanun shi da alama ranshi ya 6aci, Yaji haushin yadda suka 6ata kayan su, abu tun karfe kusan tara na safe ake ta fama yaki ci yaki cinyewa

Sam yakasa yi masu fada, baisan meyasa yake jin nauyin ya furta masu kalma mara dadi ba.

"Yanzu abun da ku kayi kun kyauta"? Sunnar dakai kasa sukai har suna hada baki wurin fadin"dan Allah ka yi hakuri ba zamu kara ba" ta6e baki yai" a haka zamu tafi,tun da kunfi son aganku a haukacen ku"

"Ya salsabeel dan Allah kabari mu canza wasu kayan," harara ya watsa masu, rai a6ace Ya kama hanyar fuce wa daga falon Yana Fadin"ni na tafi sai kun taho"

Watsawa su ka yi aguje suka nufi bedrooms dinsu, Jim kadan suka fito har sun canza kayan jikin su..
Chapter 48 · 0% Book details