← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 145 OF 238

Sashe 145

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Greetings, I'm Ahmed Hassan, Chief of Operations. I oversee all field operations and tactical decisions. Welcome!" he said cheerfully.

Na gefen shi wani fari fat hatta sumar kan shi yayi Dyeing ɗinta ta koma fara daga gani ɗan yankin asia ne awayan ce yace"I'm Commander Haroon, Chief of Intelligence. I gather and analyze intelligence and advise the DG and COO" ya faɗa tare da nuna Chief Owais da Big guy kafin yace"We've been expecting you" da fara'a ya nuna su Unaisah

Gaba ɗaya sun nutsu suna sauraron su duk wanda yayi magana idanunsu na akan la66ansa.

'I'm Dr. Zara Saeed, head of Counter-Terrorism Division and leader of high-risk missions."

"Agent Ethan Kim, Tactical Expert, your go-to guy for high-risk missions."

"Agent Jabeer Osman, mid-level operative specializing in infiltration and surveillance."

Bayan sun gama gabatar da kan su, atare suka hada baki wurin yi masi barka da zuwa.

Murmushi kowan nan su ya saki, Har sun ji hankalin su ya kwanta.

"Mu karasa daga Ciki" big guy ne ya faɗa tare da nuna masu hanyar da zata sada su da inda zasu je.

Taj da big guy ne agaba prisoners suna abayan su, Chief da Danish suna abiye da su, yayin da Manyan jami'an ke take masu baya Har suka ƙara so wani katafaren guri kamar falo Ya haɗu ba kaɗan ba, jami'an da suka iske aciki girmamawa suke gaida su chief.

A saman hadaddun sofas din da ke agurin Taj yace su zauna, dama agajiye suke da tsayuwa da sauri suka zauna, daga gefen Danish ta zauna saboda ta lura da mood dinshi kamar baijin dadin shi, tana so ta ɗan kwantar mashi da hankali gudun kada Yaƙi basu hadin kai.

tuni ƙamshin turaren junansu ya shiga hancinan su sosai su ke shakar shi, ga ni'imar sanyin A.c din da ke ratsa jikin su.

Idanunsu na akan su Big guy dake atsaye tare da manyan jami'an nan sun haɗa kai suna tattaunawa atsakanin su daga inda suke basa iya jin me suke cewa.

Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
A lokacin da bai yi tsammani ba, Yaji ta ruƙe yatsun hannun shi a cikin nata, aruɗe ya dube fuskarta tamkar batasan tayi ba, ta wani Basar ta kalli gefe ɗaya.

"Meke damunka"? Ta fada batare data kalli fuskar shi ba

"Na lura tun da mu ka zo kamar babu walwala atare da kai, ka ki sakin fuskarka kamar wani abu na damunka ko baka jin daɗi ne?

Ta tambaya ba tare data kalli fuskar shi ba, Saboda ƙwarjinin da yayi mata.

lumshe idanun shi yayi tare da jan numfashi har saman fuskarta taji saukar iskar numfashin sa wani irin yanayi taji atare da ita.

"Nayi maka magana kayi shiru baka tanka min ba, ko dan na damu da kaine"? nutsuwa yayi yana kallon kyawawan idanunta kwata kwata taƙi yarda su haɗa ido saboda sunyi kusa da juna kuma bata son ta jefa kanta cikin irin halin da suke tsintar kan su duk in su ka haɗu da juna.

Ba zato ba tsammani taji ya shigar da yatsunsa a cikin nata ya yi tighting din su wani irin shock taji har tay kokarin zame hannunta daga nashi amma ya ƙara ƙanƙame su ta yadda bazata iya kwatsar kanta ba.

Arude ta furta"pls ka sakar min hannuna! Kada wani gan mu," can ƙasan makoshi ya furta"Ke kika fara ruƙe min hannu, don haka bazan saki ba" ya faɗa yana kallon idanun ta so yake ta juyo su fuskanci juna ko ya samu nutsuwar da yake samu agurinta amma taki bashi haɗin kai.

Babu wanda ya lura da halin da suke a ciki, Hankalin yan uwan su na kan su Taj da mutanan su.

Bayan wasu ƴan mintuna, taj Ya nufo su gurin su suna ganin shi suka fara sauke ajiyar zuciya dama duk sun takura da zama su kadai

"Batool, Unaisah da ku zamu fara, Bismillah ku taso ku shiga daga ciki" ya fada tare da nuna masu ƙofar Questioning Room din.

Batool harta fara jin faduwar gaba amma da taji tare da Unaisah ne sai taji hankalinta ya kwanta.

Ƙoƙari take ta miƙe Danish Yaƙi sakin hannunta, fargabanta kada daddynta ya gani dakyar ta samu ta ƙwace hannunta daga nashi ta ta ruko hannun Batool suka bi bayan daddyn ta.

Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
bayan sun shiga ɗakin suka tsaya suna ƙare mashi kallo, wasu hadaddun kujeru ne biyu suna fuskantar ɗaya daga tsakiyar su madaidaicin table ne.

ga wani two-way mirror a jikin bangon dakin, wanda anyi shine saboda masu duba wanda ake tambaya su samu damar kallon shi daga Observation Room, tsabar tsaron ɗakin hada Surveillance Cameras (Kyamarorin sa ido) Nau'o'in ɓoyayyun kyamarori masu daukar video recording, ta kowace kusurwar dakin har ta cikin fitilun kwai da jikin kofa duk sune a makale ba zaka ta6a ganin su ba in ba an fada maka akwai ba,

gaba daya sun shagala da kallon ɗakin har saida taj yayi masu gyaran murya kafin suka yi saurin kallon shi

Murmushi yayi masu"ku zauna mana" muryar Unaisah da yar shagwa6a tace"daddy zamu iya cire mayafin daga kan fuskar mu? Wlh ya takura mana"

da kan shi ya cire mata mayafin, Ya yi mata rolling akanta, Ya matsa gaban Batool ya warware mata na kan fuskarta itama ya naɗa mata akan ta, sai dadi takeji ganin yayi mata yadda yayi ma Unaisah.

Bayan sun zauna ya ɗan dafe table din gabansu da tafukansa Ya dubesu da kyau

"Pls kada ku bamu kunya, ku natsu ku kwantar da hankulan ku gurin amsa mashi tambayoyin da zai yi maku, Mutun ɗaya ne zaiyi maku tambayoyin dan haka ku kwantar da hankalinku" kallon juna su ka yi atare kafin suka dube shi.

Murmushi ya sakar masu "ina fatan zakuyi min haka" atare suka haɗa baki gurin first"Eh" yar dariya yayi"lokaci yayi zan tafi, ku kula mun dakan ku"

amsa mashi su kayi da "toh"

Bayan fitar shi daga dakin kusan atare suka sauke ajiyar zuciya, kowa da abun da yake sakawa aran shi, damuwar Unaisah akan Danish tana ji aranta zaiyi wuya ya basu hadin kai.

"Sis Wai wanene Zai yi mana tambayoyin"? Batool ce tayi mata tambayar kafin ta bata amsa suka ji motsin shigowar mutun atare suka kalli kofar ɗakin.

har sai da gaban su ya fadi saboda ba su tsammaci ganin chief owais ba, ta wani bangaren sunji dadi saboda sun san wanene shi sun kuma yarda da shi ɗari bisa ɗari.

Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
Walking Slowly yabi ta bayan kujerun su Ya nufi frigde ya buɗe ya dauko juice mai sanyi ya haɗo da cups biyu ya daura akan table din gaban su, duk wani motsin shi akan idanun su yanayin yadda yake tsiyaya masu ruwan lemun a cup ba ƙaramin tafiya ya yi da imanin su ba, komai nashi cikin aji, ƙasaita da nutsuwa yake yin shi"

kwata kwata bai ɗago Ya dube su ba, har sai da ya gama zuba masu juice din mai sanyi a cups Ya tura ma su agabansu kafin a hankali Ya zauna tare da ɗaura kafarshi ɗaya kan ɗaya, ganin sunƙi daukar cups din yasa shi tunanin ko basu san su ya zubawa ma ba, kamar ya sani kuwa ai gani suke basu kai matsayin da chief zai zuba masu lemu a cup ba.

Da index finger din shi ya nuna masu Cups din, Hakan yasa suka fahimci nasu ne, a tsanake suka ɗauka suka fara sha a hankali don kada yaga sun yi ƙauyanci musamman Unaisah da aji take shan juice din yayi mata dadi ga sanyi.

A gayun ce ta rage kaɗan a cup din ta ajiye kan table, Batool kuwa duka ta shanye shi har tana shaƙe wa cikin raɗa unaisah ta yi mata magana don kada ya ji su

"shashasha, Ki yi irin na yan gayu ki rage kaɗan, kada yaga hadamarki"

baiwar Allah idanunta amarairaice ta kalli cup din ta shanye kaf tsoronta kada Unaisah tayi mata faɗa sunnar dakai ƙasa Unaisah ta yi ganin chief na kallonta wata irin kunyarshi da nauyinshi ne suka kamata.

mayar da idanun shi yayi kan Batool in a cool voice ya furta"kin koshi ko in ƙara maki"? Maimakon ta bashi amsa sai ta kama kallon unaisah, nan take ya fahimci tana jin tsoron tayi mata fada.

bai jira amsarta ba, ya ƙara mata juice ɗin a cup"ki dauka" jikinta asanyaye ta kar6i cup din takai baki saida ta shanye kafin ta ce"thank you"

"Neva mind," ya faɗa tare da gyara zaman shi

"Can we start?" ya fada yana kallon su

Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.

Atare suka amsa mashi da Eh, tun kafin su zo head quarter din an sanar da su da harshen turanci za su yi magana saboda duniya ce zata saurari tattaunawar su.

Shiru ya yi yana duban su da alama nazarin wani abu yake yi tsawon mintuna kafin kasaitacciyar muryarshi ta katse shirun na su

"Da farko Inaso ku gabatar da min da kan ku" Unaisah ce ta fara gabatar da kanta kafin batool ta yi nata introduction din.

"Tayaya akai kuka tsinci kan ku agidan kurkukun ƙaddara"? Kallon juna su ka yi, kafin Unaisah ta fara bashi labarin lokacin da ta gudu daga rigar fulani da yadda Bakar mota tayi parking agabanta aka zuro hannu daga ciki suka dauketa.

"Daga nan ban kara sanin inda kaina yake ba.." tiryan tiryan ta labarta mashi, bayan ta kammala nata cikin kuka saboda duk lokacin da ta tuna rayuwar da sukayi a kurkukun kaddara sai taji zuciyarta ta kare musamman mutuwar unaizah da majnoon dinsu, Ya mai da duban shi ga Batool jikinta sai kerma yake duk ta rasa nutsuwarta gaba daya sun fahimci halin da take a ciki.
Chapter 145 · 0% Book details