← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 238

Sashe 123

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Naufal yace"haba kamar dai a jahiliya period? ay haramunne na mijin ya rungume mace, nan fa ba prison bane kan mage ya waye.. " gaba ɗaya suka tuntsire da dariya, Unaisah hada dafe ciki, chief dake atsaye ya goya hannayenshi kan kirjin shi, idanunshi na akan fuskarta wani irin kallo yake binta da tashi ta saki baki tana ta dariya fararen hakoranta tass da su bata ta6a jan hankalinshi irin na yau ba.. Babu wanda Ya lura da irin kallon da chief yakeyi mata gaba daya ya shagala

A hankali ya kau da idon shi Ya juya Ya nufi part din shi.

"Wallahi inason ku yan uwana, kuna faranta min raina, Allah yabarni daku, wallahi mai rabani daku sai Allah, shiyasa naketa zumudin in dawo gida saboda nasan anan ne kadai zan samu farin ciki da kwanciyar hankali...." cikin jin dadi tayi maganar,

Ummi ta ruko hannun"mu shiga daga ciki, mun barki atsaye.." gaba ɗaya suka nufi Sofas din falon, kowan nan su Ya samu guri Ya zauna, shi dai sajeed kalmar muharram ta tsaya mashi arai, so yake yaji wanene muharramin nan da shi kadai zai iya rungumar mace, abun da bai sani ba ita kanta Batool din batasan wanene muharram ba, tabbas ummi ta ta6a faɗa mata amma karatun bai zauna akanta ba.

"Kinyi breakfast acan asibitin" cikin kulawa ummi tayi mata maganar,

"Eh, nayi" labari ta fara basu na Benazir duk suka kasa kunne suna sauraranta

"Matar tana sona nima ina sonta aunty ummi, mun shaku da juna, har grandma dinta muna mutunci da ita dayake adaki daya muke kwana kuma kinsan wani abu aunty ummi.." girgiza mata kai tay alamar a'a

"bata gane cewa ni ba yarta bace, bansan wani hali zata shiga ba idan ta farka daga bacci taga bani akusa da ita..." cikin sanyin murya tayi maganar.

Ummi tace"baiwar Allah, wallahi ta bani tausayi, ubangiji Allah Ya bata lafiya, inayi mata fatan Allah ya bata wata yar" suka amsa mata da ameen

"Wani abu daya bani mamaki aunty ummi, matar tana kama da Batool yadda kikasan ita ta haifeta Allah..." murmushi ummi tayi, batool ta washe baki jin an ambaci me kama da ita"wallahi har naji ina son ganinta" murmushi unaisah tayi"hmmm ai ba ita kadai ke kama dake ba, ranar dana fara ganin yayanta dr shureim saida na ɗan razana, yadda kikasan yayi kakinki, ke gaba dayansu kamar family dinki ne..." wani irin faduwar gabane Ya darsu a zuciyar Ummi, sunan dr shureim da Unaisah ta faɗa ya tsaya mata aranta.

"Dan Allah daske kike? Acewar batool,

"Wallahi dagaske nake, Allah ya zuba masu ruwan kyau, grand ma dinta balarabiyace..."

dafe kai ummi tayi da hannu ɗaya, gabanta na cigaba da faduwa.. Gaba daya sun lura da yanayinta,

"Aunty ummi lafiya" da sauri ta daidaita nutsuwarta cikin sanyin murya tace ba komai unaisah, can kuma tace.

"Unaisah, kikace sunan yayanta dr shureim! Ita kuma Ya sunan ne"?

Murmushi Unaisah tayi kafin tace"Aunty Benazir" ummi tayi jimm kamar mai nazarin wani abu.

"Namanta ban fada maku, wani abun farin ciki daya faru ba.." har suna hada baki wurin furta"menene" dariya ta danyi kafin tace"kun tuna auntyna da nake yawan baku labarinta a prison" kallon juna sukayi batare da sun iya gano wacece ba.

"Duk wanda ya tuna sunanta zan bashi kyauta ta musamman" ta fada cike da nishadi

Nan fa suka fara canki canka,

Hawwa tace"na tunata, sunanta Aunty adama" girza kai unaisah tayi"a'a ita wannan mommy adama take"

"Kamar aunty bahijja ne" acewar hibba, dariya unaisah tayi"no ba haka sunan yake ba"

Sajeed yace"Sunanta aunty laila" dariya unaisah tayi"no ba haka bane Allah indai baku fada ba, bazan baku tsarabar da nayi maku ba.." ta fada tana karkaɗa kafarta gaba ɗaya kamar ta manta da zancen Danish kamar an goge mata tunanin shi a brain dinta.

"Sunanta Aunty Aneelerh, indai ba haka sunan yake ba to kuyi min dundu abayana" dariya Unaisah tayi tare da kallon batool"kin canka dai dai, aranar kafin in bar gida kunsan meya faru...."? Girgiza mata kai tayi, nan fa tafara basu labarin zuwan aunty Anila ko gajiya batayi, sai surutu takeyi kamar parrot, gaba daya hankalin ummi baya atare da su, kamar bata acikin nutsuwarta har saida kunnuwanta suka jiyo mata muryar Unaisah tana fadin"ashe ita aunty aneelerhn kawar aunty Benazir dince, atare mukaje asibitin abun da ya farantamin rai Aunty Aneelah ta haifa min dan kani sunan shi baby junaid, tama yi min alkawarin zata kawo min shi har gida..." wani irin farin ciki ne Ya lullu6e Su Batool.

"Wayyo Allah Angel maimakon ta shigo mu gaisa da ita, meyasa baki fada mata irin kaunar da muke yi mata ba.." parvin ce tay maganar, batool tace"Yaushe zata kawo mana ɗan kaninmu junaid mu gan shi, wlh munji dadin haduwar ki da aunty Aneelerh, saura muma mu hadu da ita amma dai zatazo nan ko"? Daga masu kai tayi"don ma namanta ban kar6i number dinta ba, amma zan ma daddyna magana nasan bazai rasa layinta ba"

"Unaisah! da sauri Ta kalli ummi na'am

"Wai ni kam dama can anan abuja kuke zaune keda daddynki"? Girgiza kai tayi"a'a a joss muke" gaban ummi ne ya ƙara faduwa, karfin hali tayi wurin furta"okey, amma ita auntyn naki Aneelerh, ya kike da ita ne? Ta fada cike da son jin karin bayani

"Matar uncle dina ne Uzair"

Shiru ummi tayi bata kara yin magana ba

Motsin shigowar mutun a falon ne Yaja hankulansu ga kallon kofar, Senior agent din da ya kai su Unaisah mall ne ya shigo hannun shi ruƙe da shopping bags, ya goyo backpack dinta abayan shi, miƙewa tsaye sukayi suna jiran ya karaso

A tsakiyar falon Ya ajiye mata shopping bags din kafin Ya sauke backpack din bayanshi ya ajiye ta"i'm sorry na tsaya amsa kira ne"_ murmushi tayi tare da cewa nagode sosai"

Yace"Never mind" ya fada tare da juyawa ya fuce daga falon

Gaba ɗaya suka zagaye bags din suna kallon su ummi tace"tsarabar mu ce wannan"? Unaisah tace"eh nakune, nima akwai nawa ciki"

Zukunnawa ummi tayi agaban shopping bags din A hankali ta fara curo kayan tana ajiyesu kan rug, su Azeeza sai tsalle suke suna murna ganin cookies da chocolates kala kala dama mayinsu ne, kamar shazu mamu suke wurin shan zaki.

Tun kan aje ko'ina suka fara kokarin kai hannu zasu ɗauka, ummi tace su tsaya ta raba su.

"Unaisah wadannan uwayen kaya haka? Wanene ya siya maki su? da mamaki ta fada tana kallon fa.."

"Atare da chief mukaje shopping mall, bakiga wurin ba ya hadu, ni fa bani na zabi kayan ba, shi yace mutumin daya kawo kayan komai yaga idanuna sun kalla ya daukar min shi ko da mara amfani ne" jinjina kai ummi tayi cike da mamakin maganar ta maida dubanta ga kayan, gasunan tili guda.

ta fara ɗaga kayan tana ambaton sunayen su a fili, Fragrance set, hair accessories, gel nail kit, skincare set, jewelry box, lace robes, slippers, diary with a lock and key, throw blankets, shaving kit, smartwatches, earbuds, sports jersey, bluetooth speaker, da sauran su ga Writting material kala kala, can idon ta ya hango mata bras har kala uku da yan panties biyu, dagowa tayi tare da kallon unaisah baki asake tace"waɗannan fa"? Dariya Unaisah tayi tare da sunnar da kanta ƙasa wata irin kunyace ta kamata"wlh Aunty Ummi bansan hada bras acikin kayanba, sune suka daukarmun" dariya ummi tayi"ah toh ni dama nasan bada saninki ba, wannan ay sai dai Batool duk da bansan size dinta ba amma nasan zasuyi mata, ke kuma saiki bari in naki sun kara cukowa" gaba ɗaya su Naufal suka tsuntsire da dariya, daure fuska tayi rai a6ace take aika masu da harara, ummi tace"ku kuma meye nayi mata dariya kawai daga anyi abu cikin raha" kumshe dariyar sukayi

"Sorry my babe, kada ranki ya 6aci, ni da wasa nayi maganar" ta6e baki tayi tana faman wurga masu naufal harara.

Ummi tace"abun dai da yawa wlh, ubangiji Allah Ya saka mashi da alkhairi.." ta fada tare dakai hannu tana kara dudduba kayan"suma dai waɗanda suka daukar maki kayan sun iya taya 6era barna.."ta fada tana yar dariya.

"Hada phone, bayan kina da waya? Da sauri unaisah ta kalli phone box din"

Da sauri batool tace"dan Allah sister ki bani dama bani da waya..." saejeed yace nima inaso dan Allah, haris yace wlh na riga ku dan Allah ni za'a ba, rigima suka sanya da sauri unaisah ta ɗauke phone box din, ta ruƙe a hannunta, ummi tace"kin raba gardama, ki ajiyeta agurin ki" ta amsa mata da toh,

Kwashe kayan Unaisah da Ummi sukayi atare su ka maida su cikin bags din, ummi ta dibar masu chocolates da cookies ta rarrabamasu kowa ya buɗe nashi yana ci, sauran tace"za'a ajiye su adakin unaisah, duk rana zamu dibi kaɗan mu sha idan ba haka ba nasan ba zaku raga masu ba, duka zaku shanye su" amsa mata sukai da toh.

"Unaisah ke da Batool, Ku kwashe kayan ku kai dakin ku, ku ajiye su dakyau" atare suka amsa mata da toh, kafin suka fara kwashe jakukku nan suka kai su dakin su.

*UNAISAH ANGEL*

Around karfe biyu na rana, tana a kwance kan bed dinsu ta ɗaura kanta bisa pillow, ta ɗan lumshe idanunta bakomai take tunani ba face Aunty Benazir, tun bayan data dawo gida hankalinta yaƙi kwanciya ta damu da son sanin awani hali take a ciki? Meya faru bayan ta farka daga bacci?

"Ya Allah kasa kada aunty Benazir tayi kukan rashina, bana son tayi maraicina rashina akusa da ita! Zuciyarta ce ta raya mata me zai hana taje wurin chief ta tambaye shi awani hali Benazir din take a ciki tun da yar uwar shi.

da sauri ta sauko daga kan gadon, ta dauko mayafi ta yafa akanta, taje gaban Shopping bags din da suka ajiye ta ɗauki ɗaya ta zazzage kayan cikinta a gidan drawer, ta ɗebi turare biyu ta hada da chocolates da cookies kala shida ta sanya a ciki tasan ma ba lallai ya kar6a ba, kawai tayi tunanin takai mashi ne.

Miƙewa tayi hannunta ruƙe da ledar da sauri ta fuce daga dakin atsanake take tafiya..
Chapter 123 · 0% Book details