← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 238

Sashe 58

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsoki layla taja, tare da juyawa ta nufi kofar fita daga dakin, da sauri benazir ta dauko mayafi, dr shureim ne ya janyo mata trolley din kayanta, lokacin da suka fito falon gidan, yayi dai dai da fitowar su Hajiya sarah da gudu zeenatu ta nufi benazir tana kuka ta ruƙe mayafinta.

"Aunty benazir kada ki tafi kibarni, dan Allah kada ki tafi, Mami Dan Allah ku yi hakuri ku zauna, Idan wani abu mukai muku badaidai ba zamu gyara, Ni dai banso ku tafi"

"zeenatu zonan"! Muryar Alhaji musace ta katse mata koke koken nata, jiki ba kwari ta saki mayafin benazir ta koma wurin shi ta tsaya, ruƙe hannunta yai acikin nashi, Hajiya sarah kamar an rufe mata baki takasa ta6uka komai sai kallon su da take yi, dakatawa sukai da yin tafiya jin muryar Alhaji ubaid

"Wallahi idan kika sa kafa kika bar gidan nan batare da yawuna ba, to ki sani abakin auran ki"!! hankulansu Dr shureim atashe suke kallon shi har suna hada baki wurin furta daddy meyasa?

Dariyar takaici layla tasaki tana tafa hannu tace"sai me donka sake ni? Ni dama ay najima da gajiya dakai tun lokacin da na gane kai bakomai bane face rakumi da akala, Ina amfanin zama da namiji solo6iyo irin ka"?

Rai a6ace ta faɗa tana kallon cikin idon shi, Kalamanta sun ƙona masa rai, daƙyar Ya iya hadiye yawu mai ɗaci ba tare da ya iya furta komai ba.

Dauke idonta tayi daga kanshi ta kalli Alhaji musa, dake atsaye ya harɗe hannuwansa kan kirjinsa fuskarsa babu fara'a

Harara ta watsa mashi kafin tace

"Hankalinka Ya kwanta Ka shiga tsakanina da mijina, In sha Allah zaka ga sakayyar hakan" wani kallon ƙasan ido Ya watsa mata mai wuyar fassaruwa.

"Shureim Benazir, kada ku bi ta idan har na isa daku, Kubarta ta tafi ita kadai tun da bata jin maganata" acewar Alhaji ubaid.

Murmushin takaici layla tasaki, ba tare da ta ƙara furta kalma ba ta juya a fusace tabar falon

"Ka bar su su tafi" Alhaji musa ne ya fada agadarance.

Da sauri benazir taja trolley dinta tabi mommynta, shima shureim yabi bayanta

A bakin motar shureim ta tsaya zuciyarta a kuntace, batai tsammanin zasu biyo bayanta ba

Dr shureim na ƙarasowa Ya buɗe mata back seat din motar ta shiga ciki, sannan ya sanya masu trolley din kayan su a boot, daga bisani itama benazir ta shiga ciki.

Bayan ya shiga ya zauna a driver's seat, yai ma motar key, zuciyarsa cike fal da damuwar abunda Ya faru, yaji takaicin yadda Alhaji musa ya nuna halin ko'in kula akan tafiyar mamin su, abun da Yafi bata masa rai furucin mahaifinsu yansu shikenan yana ji yana gani auran iyayensu zai rabu"?

"Shureim! Ya akai naga ka dakata da yin driving din"? Cikin rauni na murya yace"mommy Kiyi hakuri mu koma, idan kika tafi ya kike so muyi da rayuwarmu? Ke kanki bazaki so abun da zai tarwatsa farin cikin mu ba...."

Shiru tayi tana nazarin maganarshi, ga dukkan alamu jikinta yayi sanyi lakwas

"Mommy, kina atare damu Ya muka ƙare inaga idan baki nan? Duk wani mai nufin mu da sharri zaiji dadin cutar da rayuwarmu, bayan haka mommy tsawon shekara nawa kuna atare da daddy, auren soyayya kukayi kun tara zuri"a da dadi da ba da daɗi kunyi hakuri kun jure zama da juna sai akan wannan dalilin zaki kashe auranki? Mu kanmu bazamu ji dadi ba dan Allah ki tausaya mana mommy ku dubi girman Allah ki fasa tafiyar nan ko dan saboda mu"

benazir ce tayi maganar tana duban fuskar mami kamar zata sanya mata kuka.

Zancen zuci ta soma yi

_wannan hanyar dana ɗaukarwa kaina ba me 6ullewa ba ce, ƙwara in tsaya in ƙwatar mana ƴancin mu, dole Inyi faɗa ko da kuwa zan rasa raina ne saina shiga tsakanin mu da shi_

Ba zato ba tsammani suka ga ta buɗe motar, wani irin farin ciki ne Ya lullu6e su, da sauri benazir ta fito shima shureim Ya fito suka dauko trolley dinsu dake a boot suka bi bayanta.

Kamar yadda suka bar su hajiya sarah tsaye a falon haka suka taras da su, sunyi mamakin dawowar Hajiya layla, ko kallo ba su isheta ba, Kai tsaye ta wuce room dinta

Da gudu zeenatu ta nufi benazir suka rungume juna suna dariyar farin ciki,

Fuskar hajiya sarah dauke da murmushi ta dubi dr shureim"ta fasa tafiyar ne"?

"Eh mommy," ya bata amsa, Har cikin ranta taji dadin dawowarsu.

Mutumin kuwa murmushin gefen fuska Ya ɗan saki, yayi tunanin security officers din gidanne suka hanata tafiya baisan cewa itace tai ra'ayin kanta ba, fucewa yai daga falon cikin takun isa.

Alhaji ubaid dake kallonsu ajiyar zuciya ya sauke.

"Daddy, dan Allah kuyi hakuri da abunda Ya faru atsakaninka da mommy, ku yi kokari ku sasanta junanku"

Jinjina kanshi yai fuskarshi dauke da murmushi yace"kada ka damu shureim, ni dama ban dauka da zafi ba, itace ke da matsalar, in sha Allah zanje na lallashe ta" ya fada tare dakai hannu yadan bubbuga kafadarsa kafin Ya juya ya nufi dakin layla don su sasanta junan su.

Koda ya shiga ɗakin, ya taras da ita zaune agefen gado, kamar mai jin shakkarta Ya raba ya zauna yana duban ta

kafin yai magana tai saurin katse shi da cewa"basai ka bani hakuri ba, ni yakamata na nemi yafiyarka, ka yi haƙuri idan na 6ata maka rai, in sha Allah bazan ƙara ba, zan bi umarninka in zauna har zuwa lokacin da ka so mubar gidan" da wani irin mamaki yake duban fuskarta, kamar amafarki yake jin kalamanta, Wai yau layla ce da kanta take bashi hakuri har take fadin zata bi umarnin shi?

"Allah yasa ba mafarki nakeyi ba" murmushi tayi tare da dubanshi tace"ba mafarki bane mijina, dagaske ne, abun nayi ban kyauta ba, su shureim sun yi min nasiha nima naga rashin kyautuwar hakan shiyasa na dawo.

Ruko hannayenta yai acikin nashi hawaye tuni sun cika idanunsa

Cikin sanyin murya yace"layla bazan iya misalta dadin da naji ba, kin faranta raina ayau, duk da nasan nine mai laifi amma kiyi hakuri ki yafe min, sannan inaso ki sanyani a addu'arki, Ni kaina bansan meyasa bana iya bijirema umarninsa ba, bana son bacin ran musa, saboda ya kyautatamin arayuwa shine silar duk wata nasara da na samu..." bai kare maganar ba tai saurin rufe bakinsa da tafin hannunta, saboda ta tsani taji Yana yabon musa, saboda ita tasan ba hakanan Ya kyale shi ba shiyasa baya iya ganin laifinsa, amma taci alwashin zata gano ainihin wanene Alhaji musa da duk wani abu dayake takama da shi.

Abun da bai ta6a tsammani ba, Yaji layla ta kwanto da kanshi saman kafadarta, bawan Allah sai Ya kara lafe mata kamar wani karamin yaro.

"Kada ka damu, ni bakai min laifin komai ba, In sha Allah zantayaka da addu'a kamar yadda ka bukata, kaima kuma inaso ka dage dayiwa kanka addu'a" amsa mata yai da toh, cigaba da kwantar masa da hankali tayi, har saida ta cika shi da farin ciki ta dinga zolayarsa tana tuna masa farkon haduwarsu kafin su yi aure.

"Yanzu tun da komai Ya daidaita mu koma dining mu ƙarasa yin breakfast din" cikin kulawa mom sarah tayi maganar tana dubansu.

"Aunty ki tayani murna" acewer benazir

"Fada min meya faru"?

"Aneelerh ta kirani awaya har mun yi magana da ita"

Murmushi hajiya sarah tasaki"masha Allah, ina tayaki murna my daughter, wlh naji dadi yanzu yaushe zaki je can gidan na su"?

Kallon dr shureim tayi wanda gaba daya hankalinsa na akan zeenatu dake a gefensa sai dadi take ji sun fasa tafiya.

"Yaya shureim yaushe zamuje? Ni ko yanzu ma kace a shirye nake Allah" ta fada a kagare.

"Gobe in sha Allah zan kai ki" da sauri zeenatu tace"yaya shureim nima zan bi ku, dan Allah ku tafi dani" ta faɗa a shagwa6e tana kallon shi.

"Kada ki damu ƙafa ta kafarki, duk in da zani je a tare zamu tafi" cikin muryar raɗa yayi mata maganar, dariya murna tasaki.

Benazar tace"kwantar da hankalinki rabin raina, gobe atare zamu je"

"Nagode auntyna"

"Ki daina murna, kin manta da daddyn ki halan, ba lallai ya amince ki fita ba" tur6une fuska tai.

"Mommy pls ki roƙan mun shi yabar ni inje" ta fada tana bubbuga kafafuwanta

"Zanyi mashi magana zuwa anjima nasan zai bari mu tafi da ita" acewar dr shureim

Hajiya sarah na murmushi tace"kunfi kusa ay, nasan kana masa magana zai amince, tun da yana ji dakai na gaban goshinsa" dariya sukai gaba dayan su.

______________________Twins❣

A kwance yake kan katafaren gadonsu idanunsa na fuskantar ceilling, yanayin fuskarsa sam babu walwala ya haɗe rai kamar wanda aka aiko ma sakon mutuwarsa, bakomai ne yake damunsa ba face haɗin da mommynsa tayi masa, ya riga da ya san halinta ba lallai ta canza ra'ayin ta ba, shi fa arayuwarshi sam baida ra'ayin yin auren wuri, yafi sha'awar yai sharholiyarsa son ransa, a yadda ya tsara ma kansa sai yakai 45 years zaiyi aure, bugu da ƙari baya jin zai iya auran yarinyar saboda ba'ajinsa ba ce, jiya kafin ya kwanta bacci sai da yayi bincike akanta ta hanyar amfani da wayarsa har ya gano wanene mahaifinta wato karen ƴan siyasa, aransa ya ayyana tayaya shi da ya fito daga babban gida shahararren family da duniya tasan da zamansa, zai auri wannan yarinyar, Bayan haka mommyn sa minister ce daddynsa Ceo ne na babban companynsu Obi Tech, tayaya zai auri interior designer? Companyn ma da take aiki ba nata ba....

Abu ɗaya daya hana shi sukuni, kyawun fuskarta da surar jikin ta, daren jiya dakyar ya runtsa, ba halin Ya rufe idanunsa sai ya tuna lokacin da ta fashe mashi kuka la66anta na kerma, kissing ɗinta da yayi har cikin zuciyarsa yaji wani irin shauƙi da bai ta6a jin sa a wajen wata mace ba, kawai yayi ƙarfin halin tofar da yawu ne don Ya muzanta ta.

Motsin buɗe toilet ne Ya katse masa zancen zucin nasa, A hankali yakai idanunsa ga duban mai fitowa

Zaid ne ya fito waist dinsa daure da towel, suna haɗa ido da juna Ya sakar masa murmushi
Chapter 58 · 0% Book details