← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 238

Sashe 111

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da motocin su Baba Obie suka ƙaraso asibitin, a gaggauce nurses suka fito da Stretcher, Hajjaty da Abla suka ɗauko marwa da taimakon nurses suka kwantar da ita kan Stretcher, kaitsaye suka nufi cikin asibitin da ita, da sauri su Hajjaty suka mara masu baya tare da su Baba Obie, mutane sai miko gaisuwa suke yi cike da girmamawa musamman da ya shiga ciki Nurses da Docs kamar zasu durƙusa ƙasa tsabar yadda suke gaishe da shi cikin girmamawa, tuni labarin zuwan shi asibitin ya isa kunnan Md Dr. Jidenna dama mutumin shine, yare ɗaya ƙabila ɗaya sai gashi ya fito da sassarfa ya nufi Baba Obie tare da wasu daga cikin docs na asibitin, barka da zuwa suka yi mashi daƙyar yake amsa masu duk sun fahimci baya acikin kwanciyar hankalin....., a Waiting Area su Hajjaty suka zauna kamar masu zaman makoki, sai zullumi da fargaban abunda zai biyo baya suke yi na sakamakon ciwon marwa, babu wani mai kwanciyar hankali acikinsu, fuskokinsu sunyi jawur ruwan hawaye ya jiƙe su.Pravin kuwa Yana ruƙe da qugu ya haɗa uban gumi duk da sanyin A.c ɗin dake a wurin, ya kasa zaune ya kasa tsaye kamar mai fama da ɗan kanoma...

Su kan su likitocin da sukayi arba da Marwa saida suka ruɗe saboda basu ta6a ganin patient mai irin lalurar ta ba, ba wai kuturtar ba toshewar bakin nata kamar ba'a ta6a halittarta da shi ba!! Wasu ƙwararrun Medical team ne suka fara bincikarta, kafin su fara aikinsu sai da suka fara tambayar me ya jawo mata ciwon!! nan fa su Hajjaty da su Abla suka kora masu bayani dalla dalla dangane da yadda marwa ta tashi dare ɗaya da lalurar suka ce su kansu basu san menene makasudin ciwon nata ba...bayaninsu ya ƙara rikita Docs din, wannan wani irin ciwo ne farat ɗaya?

A ƙalla Medical team din sun ɗauki tsawon awanni wurin duba lafiyar marwa, abun ya fara basu tsoro, saboda sunyi gwaje gwaje da aune aune but every result came back inconclusive. No trace of infection, no signs of trauma, lamarin Ya rikirkita su, sunyi iyakar bakin kokarinsu amma still babu wani sakamako daya nuna cewa Marwa tana da wani ciwo ko wata lalura, saima wani abun ɗaure kai lafiyarta qalou....'! Babu irin kokarin da likitocin basu yi ba akanta sun baje fasaharsu da kwarewarsu amma ba wani cigaba sakamakon dai ɗaya ne....❗

tun safe har wuraren karfe biyar na yamma babu wani abu da likitoci suka gano,

Lokacin da likitocin suka fito, sun hada uban gumi akan fuskokinsu kai kace ba A.c a dakin, su kan su sun jigata basu ta6a cin karo da patient din da ya basu ɗan banzan wahala irin marwa ba, duk irin kwarewarsu da kwazon su basu iya gano komai ba....

Su Hajjaty suna a zaune bayin Allah, A asibitin sukayi sallah, ruwa ne kawai ya gifta ta makoshin su, tsabar tashin hankali Ya sa sun manta da yunwar cikin su, koda ganin Docs din sun fito jikinsu na 6ari suka miƙe suna kallon su, ganin sun nufi inda su Baba Obie suke yasa suka bi bayan su, kora mashi jawabi suka shiga yi cikin harshen turanci ɗaya daga cikin su ya fara bayani,

"Duk da irin ƙoƙarin da muka yi, mun kasa samun nasara." ya fada yana ɗan girgiza kan shi, "munyi iyakar bakin kokarinmu, munyi duk wasu gwaje gwaje amma bamu ga komai ba, babu wata cuta da tayi silar kamuwarta da ciwon kuturtan da kuma toshewar bakin" tsantsar rudani da tashin hankali ne akan fuskokinsu.. Dr din dake a gefen wanda ya yi maganar ya ɗaura da cewa, "sakamakon binciken da muka yi ya nuna tana da koshin lafiya....." A ruɗe Baba Obie ya ce, "Bangane me kake nufi ba doc! ta yaya haka zai yiwu? Ga abun nan kuna gani da idonku zahiran! amma kuce baku gano komai ba"? Su Hajjaty dake sauraron su sai faman zare idanu suke yi duk sun bi sun ruɗe jin bayanan Docs.

"Mun shiga uku! dan Allah docs ku taimaka mana, wallahi rana ɗaya ta kamu da cutar...." kallon su docs din sukai ɗaya daga cikin su softly ya furta, "We're sorry, but we cannot offer more help, ba abunda zamu iya yi mata......! su kan su Likitocin damuwace ƙarara akan fuskokinsu..

"Dama saida raina ya bani jinnu ne suka shafe ta, Baba abun da yakamata mu koma da ita gida a kira manyan malamai su taru akanta watakil a dace..." Hajjaty ce ta yi maganar tana matsar ƙwalla, idanunta akan Baba Obie wanda yayi jigum saboda damuwa....gaba ɗaya sun yi amanna da maganar Hajjaty dama tun kafin su zo asibitin babu wanda baiyi tunanin jinnu bane, saboda ciwo ne kwatsam Ya afka mata a dare ɗaya ba tare da dalili ba.....

"Dr ba yadda za'ay ku buɗe mata bakin ta? Baba obie ya faɗa yana kallon docs ɗin,

Girgiza kai ɗaya daga cikin su ya yi, "Sorry Sir, We cannot perform any surgery to open her mouth, because we don't know what is causing her illness. Without knowing the cause, we could potentially make things worse. Shawarar da zan baku shine a maida ita gida a nema mata magani." Sautin shesshekar su Abla Ya cika wurin bayin Allah duk sun bi sun ruɗe ga tashin hankali......

Dafa kafaɗar Baba Obie MD Doc Jidenna yayi cikin kwantar da murya ya ce, "Kada ku sanya damuwa in sha Allah zata ji sauƙi, kamar yadda Docs din suka bada shawara kuyi kokarin nema mata magani, saboda rayuwarta tana a cikin hatsari zata iya rasa ranta..." cikin harshen igbo ya yi maganar,

numfasawa Baba Obie ya yi kafin ya ce "To amman yanzu ni babbar damuwata ta ya zamu koma da ita a wannan halin, bamu san ta ya zata ci abinci ba hakan kuma ka ga babbar matsala ne ace mutum ya zauna ba cin abinci balle kuma ya sha ruwa, ina ganin kamar zai fi a barta a nan tun da likitocin baza su rasa dubarar da zasu yi ba su bata abincin, zamu san abun yi kafin gobe" jinjina kai MD ya yi kafin ya juya kan ɗaya daga cikin likitocin cikin harshen turanci ya yi mashi bayanin buƙatar Baba Obie in zai yuwu, amsa ya bashi da bazasu rasa hanyar da zasu yi hakan ba dama da suna bincikar lafiyarta sun saka mata ƙarin ruwa da wasu allurai da zasu ƙara mata karfin jiki ganin ta galabaita. Duk sun ji daɗin hakan, Baba Obie ya roƙesu kan su bata kulawar da ta dace kafin zuwa gobe, cike da girmamawa suka amsa mashi da zasu yi ƙoƙarin hakan. Su Hajjaty sunso su ƙara ganinta kafin su tafi, saidai basu son ƙara karya mata zuciya don sun san yanzu dole tana cikin matsananciyar damuwa ba kamar da aka kasa shawo kan matsalar tata, ba don sun so ba suka tafi kowannan su da tsananin tausayinta a zuciyarshi.

Suna a kan hanyarsu ta komawa gida Baba Obie ya tuntu6i layin Sheikh Imam Malik ya sanar da shi cewa yana son ganin shi idan yana kusa, Sheikh Imam ɗin ya sanar da shi baya a gari, amma zuwa gobe da asuba zai shigo Abuja...lokacin da Baba Obie yake yin wayar Pravin yana zaune a gefen shi, tun da yaji Baba Obie ya ambaci yana son ganin Shiekh Imam cikin shi ya katsa, ƴan hanjinshi suka motsa, wata irin kiɗima yayi ga sanyin A.c a motar amma wata irin zufa ce ke tsastsafo mashi, sai faman zare na mujiya yake yi....!

_______________________________✍️

A 6angaren su Aneelerh, tun Bayan sun gama kwasar girkin da akayi ma su, saida kowan nan su yayi kulu wash rabu hani'an kafin suka koma falon, firar yaushe rabo suka fara dama an kwan biyu ba ahadu ba.

Wuni su kayi agidan, kiran sallar azahar ne ya tadasu, dakin baki hajiya adama ta kai Aneelah da Zarah su mami kuma dakinta ta kaisu don suyi sallah, wato su mami sun shagaltu da kallon dakin hajiya adama an zuba kayan alatu kamar dakin wata basarakiya..

yayin da mazan suka tafi masallaci bayan sun dawo a falo suka ƙara hallara, akaci gaba da hira ga launch an kawo masu ita dai aneelah tun zuwansu gidan hankalinta ba kwance yake ba, Ana sai faɗo mata arai take, ga wannan faduwar gaban data dameta hakanan dai take daurewa, zarah ta lura da ita duk wani motsin Anila akan idonta, ta fahimci babu kwanciyar hankali atare da ita, so take su ke6e taji ko lafiya, kiran sallar la'asar ne ya sake tadasu inda kowa ya nufi dakin da yayi sallah dazu

Bayan sun gama sallah ta juyo da kallonta ga Aneelarh da dan yanayin damuwa tace "aunty aneelah miyake damunki tun zuwanmu gidan nan ina lura da ke kwata kwata kamar a takure kike ko duk tunanin Aunty benazir ne" yamutsa fuska tayi "A'ah zarah wlh Ana ce ta tsayamun a rai sannan tunda mukazo gidan nan gabana keta faduwa na rasa dalili raina ya bani kamar wani abu zai faru" cikin sanyin murya ta kare maganar, ruƙo hannunta zahra tayi a cikin mata suka kalli juna

"In sha Allah auntyna babu abunda zai faru sai alkhairi, ki daina sanya damuwa aranki sannan kicigaba da yin addu'a"

Numfasawa tayi kafin tace"nagode da shawararki zahra, bari na kira Ana in tuna mata ta dafa ma baby junaid indomie dan kinsan daya dawo ita yake fara tambaya" murmushi zarah tayi "ina ruwan sarkin rigima" yar dariya Aneelarh tayi, tare da ɗaukar phone ta danna ma Anah kira tashin farko aka sanar da ita layin akashe yake!

kallon zarah tayi"na kira baya shiga!"

Zahra tace"maybe tana a kitchen tana aiki shiyasa ta kashe wayar, ki bari ɗan anjima kadan saiki sake kira"ta fada tare da cewa muje kar a jimu shiru"ruko hannun Aneelah tayi suka fito daga dakin, addu'a anila ta dinga karantawa a zuciyarta amma kamar ana kara mata faduwar gaban. Wannan karan tamkar ana mata dakan sakwara a kirjin ta.. A falo suka tarar da su ummi jiki asanyaye Aneelerh ta zauna tana ambaton sunan Allah, sam hankalin ta baya atare da su mami dake ta fira ko gajiya basayi, can ta tsinkayi muryar mami a kunnanta
Chapter 111 · 0% Book details