← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 208 OF 238

Sashe 208

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba ɗaya hankalinsu ya tashi da abunda Unaisah ta yi, abun da ya ƙara ƙona ma Benazir rai yadda Taj ya yi banza da su ko motsawa baiyi ba daga kan kujerar da yake balle ma harta sa ran zai taimaka mata su shawo kan Unaisah, tayi masa mummunar fahimta, batasan lalurace ta hana shi miƙewa ba, dama da haushin shi aranta saboda tasan shine ya cusa ma Unaisah tsanarta acikin zuciyarta shiyasa harta ƙullaceta arai in bashi ɗin da ya fada mata ba, Uzair da Aneelerh ba zasu ta6a tona mata asiri a gurin Unaisah ba dole sai in a wurin Taj ta ji.

Bawan Allah Taj damuwa ce ƙarara akan fuskarshi, kwata kwata bai ji daɗin abun da Unaisah ta yi mata ba.

"Aneelerh, Ku dawo ku zauna, ku barni da Unaisah, zanyi magana da ita."

Rai a6ace Benazir ta nufe shi kamar zata doke shi ta damƙi gaban jallabiyar shi da hannyenta biyu tana huci ta ce, "You caused everything Taj, I hope you're happy now, kaine ka cusawa Unaisah tsanata a cikin zuciyarta, saboda kaine ka faɗa mata cewa na haifeta nabarta acikin kwamin wanka, wai laifin me na yi maka ne? Wace irin tsana ka yi minne???"

Runtse idanun shi ya yi batare daya iya furta kalma ba, cikin sauri Aneelerh ta damƙi hannun Benazir ta soma kiciniyar 6am6are shi daga wuyan Taj, "Wai miye hakane Benazir? Idan rai ya 6aci ai hankali bai kamata ya gushe ba, Taj bazai ta6a faɗa ma Unaisah abun da ki ka yi don yasa ta tsane ki ba..."

"Ki barni Aneelerh, wlh bazan ƙyale shi ba, yadda ya saka mata ƙiyayyata acikin zuciyarta dole ya je ya saka mata soyayyata a cikin zuciyarta, saboda shine ummul aba'isin komai, wlh he must fix what he ruined."

Ta ƙarashe maganar tare da bangaje Aneelerh, ta ƙara kakkama gaban rigarshi, ɗaurin kallabin kanta tuni ya jima da zamewa, doguwar sumar kanta duk ta hargitse kamar mahaukaciya, yana jan numfashi da ƙarfi ya furta, "Benazir ki sakar min rigata, mara kunya, har yanzu bazaki ta6a canzawa ba, tsakanin ni da ke wanene mai laifi? Da har zaki ce ni ne silar komai? Bayan kece ummul aba'isin duk wani abu da ya faru..."

Ya faɗa yana buɗe idanunsa da suka kaɗa jawur ransa ya 6aci ganin Benazir na neman ta ɗaura masa laifi.

"Tabbas, Ni na faɗa ma Unaisah, kuma Allah shine shaidata ni ban faɗama Unaisah don ta tsaneki ba, fa ce sai don ta tausayamin ta daina azabtar da ni, saboda a lokacin da tana ƙarama mugun halinta sak irin naki ne, bata jin maganata kusan kashe ni ta yi da baƙin cikinta, kin tashi kin tafi kin barni da jinjira ke baki yi tunanin taya zan iya rainonta ba ne? Benazir in bazaki iya godemun ba bai kamata kiji haushina ba!"

Yana huci ya ƙare maganar, fashewa tayi da kuka tamkar ranta zai fita, Still taƙi sakin gaban rigarshi.

Hankalin Aneelerh ba ƙaramin tashi yayi ba, ganin takasa shawo kan Benazir ne yasa ta watsa da gudu ta nufi hanyar fucewa daga falon don ta je ta gaya ma Dr Shureim, tasan shi kaɗaine zai iya dakatar da Benazir saboda bad temper dinta in takai maƙura a 6acin rai ko mai iskokai bazai nuna mata yadda ake bori ba.

*UMMIN AMERICA🔥*

Su biyu ne a zaune kan rug din dakinta, ita da Batool sun ƙurawa laptop screen idanunsu, wani korean drama ne su ke kallo ita da Batool, Ummi ta toshe kunnuwanta da Headset kwata kwata bata jin wani sauti daga waje saina abunda take kallo.

Batool ce ta fara jin hayaniyar mutane a cikin gidan, tun tana jin maganganun nasu ƙasa-ƙasa har ta fara ji da ɗan karfi.

"Aunty Ummi" Shiru bata amsa mata ba, bubbuga kafaɗarta ta yi, a ɗan firgice ta dube ta, "Babe lafiya?"

"Kina jin hayaniyar mutane acikin gidan nan?"

"Banji me kika ce ba," Ta faɗa tare da zame headset din ta maida hankalinta akan Batool, "Kamar wasu ne ke faɗa acikin gidan nan, naji hayaniyarsu a cikin kunnena, ki saurara ki ji" Ɗan zare ido Ummi ta yi tare da yin shiru ta kasa kunne a hankali ta fara jiyo maganganunsu...

"Su wanane? Ko munyi baƙi a gidan ne?"

Girgiza kai Batool ta yi, "Wallahi nima bansani ba, kawai yanzu na jiyo hayaniyar su kamar faɗa su ke yi...."

Da sauri Ummi ta miƙe, mayafinta data bari akan gado ta ɗauka tare da yafa shi kan kafaɗarta...

"Ki ci gaba da yin kallon, bari na je na gano mana meke faruwa." Ta amsa mata da toh da sauri Ummi ta fuce daga ɗakin......✍️

Dira ƙafarta keda wuya unexpectedly ta tsinkayi muryar Dr Shureim a cikin kunnuwanta..

"Benazir baki da hankali ne? Meye haɗin ki da shi? Mutum da girmansa zaki shaƙe gaban rigarsa!"

Ya faɗa yayin da yake shigowa falon cikin sauri idanunsa akan Benazir da har lokacin bata saki kwalar Taj ba, Anila tana abiye da bayan Dr. Shureim gaba ɗaya hankalinsu ya tashi sosai, batai aune ba Dr shureim Ya damƙi hannunta ya fusgeta gefe ɗaya har saida tayi taga-taga kamar zata faɗi.

Rai a matuƙar 6ace ya dubeta kamar zai kife ta da mari.

"Uban meya haɗa ki da shi? Dama dalilin da yasa kika matsamin in kawo ki gidan kenan? Saboda kawai ki tada husuma?"

Tana shessheka ta ce,"Yaya Shureim Taj ne fa, My Ex-husband, Uban ƴata dana haifa, Azeezaty itace yarinyata Unaisah....."

A ruɗe Dr shureim yake kallon Benazir sam ya kasa furta kalma saboda yadda maganar ta dira a cikin kunnansa ta rikita lissafin kwakwalwarsa.

Juyawa ya ɗan yi tare da kallon Anila wadda jikinta keta kerma saboda fargaban kato6arar da Benazir ta yi masu, bayan irin gargadin da aka yi masu akan kada su fallasa asirin Taj yana a raye.

"Inna lillahi! Benazir meyasa kika faɗa masa? Meke damunki ne? Kin manta amana na faɗa maki, kuma kika yi alƙawarin ba zaki faɗa ma kowa ba!" Ta faɗa a faɗace kamar zata doke ta.

Taj dai tun da ya sunnar da kan shi ƙasa bai ƙara ɗagowa ba saboda halin damuwar da zuciyar shi ta shiga.

Tana kuka ta ce, "Ai wallahi ƙwara kowa ma ya san yana a raye, in ba haka ba baƙin cikin shi zai kashe ni ne! "

Gaba ɗaya Dr Shureim ya gama ruɗewa, sai faman rarraba idanunsa yake yi akan Taj da Benazir da Anila.

Dakyar ya shanye mamakinsa da wata irin raunanniyar murya ya furta, "Dan Allah ku fahimtar dani! Na kasa ganewa, shin dagaske shine Taj mijinki! Azeezaty kuma itace ƴarki Angel?" Ya tambaya yana kallon su...

Cikin sanyin murya Anila ta ce, "Hakane Yaya Shureim." Ɗan zare idanunshi ya yi tare da maida idanunshi kan Taj da tsantsar mamaki yake kallon shi.

"Bawan Allah, ka ji tsoron Allah ka faɗamun gaskiya, da gaske kaine Taj mijin Benazir?" Jinjina mashi kai Taj ya yi alamar Eh.

Baki asake ya kuma mayar da duban shi akan su Anila kamar waɗanda suka yi ma sarki ƙarya sunyi zuru zuru...

Gaba ɗaya sun kasa furta kalma sai kallon kallo suke jefawa junansu...

"Yaya Shureim! Benazir!! Aneelerh!!!

Muryarta na rawa ta furta sunayen su, Kaitsaye sautin muryarta ya daki dodon Kunnuwansu, wata zabura suka yi a firgice suka kai dubansu inda take a tsaye saman stairs fuskarta sharkaf da hawaye idanunta sun kaɗa jawur tamkar an watsa barkono acikin su, yanayin fuskarta ya nuna tsantsar ruɗani da tashin hankali gami da al'ajabin ganin bayin Allahn nan, Tayaya zata manta fuskokin su? Bayan irin haddar da ta yi masu...

"Is that really you? Or am I dreaming? I can't believe my eyes!"

Tashin hankalin da ba'a saka mashi date! Al'ajabine ya ɗaure zukatansu ya hana la66ansu motsawa sai dai idanu da suka bita da su batare da ƙyaftawa, Yau tsawon shekara goma sha takwas da ɗauriya rabon su da yar tahalikar nan tun da ƙaddara ta raba su da ita, ba zasu ta6a mantawa da Aishatu bint Sheikh Imam Malik ba! Ba zasu ta6a manta raɗaɗin da suka ɗanɗana na abun da ya rabasu da ita ba.

"Dama Kunsan Juna ne?"

Daƙyar Taj ya furta maganar yana dubansu, yayi mamakin ganin yadda suka ƙame atsaye idanunsu azazzare kamar waɗanda suka ga wani mugun abu.

Benazir ce ta yi ƙarfin halin furta, "ƘAWATACE AMINIYATACE, ITA ƊIN TAMKAR YAR UWA TA JINI TAKE A WURINMU! YAU SHEKARA GOMA SHA TAKWAS RABON MU DA ITA, TUNDA ƘADDARA TA RABA MU❗❓

*(WAIWAYE ADON TAFIYA)*

*WACECE AISHATU BINT IMAM MALIK? MENENE DANGANTAR AISHA DA ANEELERH DA BENAZIR DA KUMA DR SHUREIM? WACE ƘADDARA CE TA RABA SU❗❓👇*

*DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥*

*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*

Sponsored Post
Tags
Kurkukun Kaddara
YOU MIGHT LIKE
1 COMMENTS
Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Anonymous
30 September 2024 at 10:52
Thank you and jaxakillahu Khairan

Reply

Previous Post
Next Post
GET IN TOUCH
Facebook
twitter
YouTube
Instagram
Whatsapp
SUBSCRIBE US

OPINION
FACEBOOK

COMMENTS
CATEGORIES
Africa
(1)
Al'adu
(1)
Alkamawa
(3)
Article
(3)
Blogger Tips
(1)
Economy
(5)
Education
(2)
Entertainment Gist
(1)
Gyaran-Jiki
(5)
Health
(13)
Jikar Iya
(11)
Kimiya
(1)
Kiwon Lafiya
(54)
Kukan Zuci
(5)
Kwalliya
(4)
Labaru
(25)
Lifestyle
(1)
Ma'aurata
(1)
News
(304)
Nigeria
(5)
Noma
(1)
Opinion
(4)
Picture
(3)
Politics
(15)
Profile
(2)
Q&A
(1)
Ramadan
(9)
Ramadan Tafsair
(1)
Siyasa
(1)
Sports
(72)
Tarihi
(5)
Technology
(1)
Tips
(3)
Video
(3)
YouTube
(5)
Zain Abeed
(1)
Zamantakewa
(1)
Novels Elite
Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content.

Novels Elite
SUBSCRIBE
Posts
Comments
Links
Post a Job

LATEST POSTS
Chapter 208 · 0% Book details