← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 238

Sashe 25

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tabbas maganar owais gaskiya ne, Yaran nan ba masu cutarwa bane, mutanene kamar kowa, kuma abin a tausayamawa ne....." a tsanake cikin hikma sheikh imam ya fayyace masu komai dangane da halin da danish yake a ciki, wasu sun fahimta yayin da wasu sam kamar kurame basa gane komai.

Gaba ɗaya hall din Ya rikice da maganganunsu, wasu suna hura wutar akore su daga hall din yayin da wasu sukayi shiru basu tanka ba irin su mai girma sharafudden, sun natsu suna bin duk wani mai magana da kallo, ga dukkan alamu akwai abun da suke jira shiyasa suka yi shiru.

Cikin sanyin murya prime minister yace"dan Allah kowa yakwantar da hankalin shi, Idan har saboda ni aka shirya dinner din nan, to ina rokon alfarmar ku bar su na yau kawai su zauna, in sha Allah ba abinda zai faru" idanunshi akan danish ya ƙare maganar, wanda tun shigowarshi hall din idanunsa suke alumshe tamkar ma baisan sunayi ba, su batool daine suka ruɗe jikinsu sai kerma yakeyi bayin Allah sun firgita.

"Meye amfanin kawo su wurin nan? Inace an shirya dinner din nan ne saboda mu ƴan family ba bare ba! Don haka afitar mana da su idan ana son zaman lafiya, idan ba haka ba mu zamu tattara yanamu yanamu mubar masu hall din" rai a6ace hajiya laurat tayi maganar tana faman haɗe rai.

Runtse ido chief owais ya yi, har cikin ranshi baiji dadin irin tarbar da akayi ma yaran ba, zuciyarshi ta raunana duk sai yaji dama bai sa anzo da su ba.

_Cikin sanyin murya mai ratsa zuciya Unaisah ta soma magana"dan Allah ku yi hakuri idan mun 6ata maku rai, wlh ba mu zo da niyar mu cutar da kowa ba, hasalima ba da son ranmu mu zo ba, face don chief ya nuna yana son mu ziyarci danginsa, ba ku san mu ba, muma bamu san ku ba, bai kamata kuna munana mana zato ba, akan

abun da baku da tabbas akanshi_

tun da ta fara magana hankula suka dawo kanta, Idanu zuru zuru cike da mamakin karfin halin ta.

_A hankali ta sanya hannu ta cire facemask din fuskarta tare da jefar da shi gefe ɗaya, Tabarakallahu ahsanul khalikin, Hankalin maza ya tashi da ganin kyakkyawar fuskar unaisah wadda take a jike sharkaf da hawaye_

_Cikin murya kuka taci gaba da cewa"Idan bakusan ganin mu ba sai kun kore mu ba, zamu tafi da kafafuwan mu,' kalamanta sun sanyaya zuciyoyin wasu daga cikinsu, Hakika unaisah ta tafi da imanin wasu daga cikin su, Har mamaki sukeyi yarinya karama ga iya tsara kalami uwa uba gata kyakkyawa da ita_

*Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️*

*Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*

3196407426

First bank

Bature Hafsat Muhammad,

*bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268*

Kurkukun Kaddara
Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 13 Complete
by
Novels Elite Admin
May 29, 2024
Sponsored Link

Novels Elite English

_ *~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋✊~*_

سجن القدر💋✊🔥

~Takun Ƙarshe🔥~

قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع تطورات معقدة💋💘😘

An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘

Daga alƙalamin Boss Bature💋✊

__________________________✍️

Cikin muryar kuka taci gaba da cewa"Idan ba ku son ganin mu ba sai kun kore mu ba, zamu tafi da kafafuwan mu,' kalamanta sun sanyaya zuciyoyin wasu daga cikinsu, Hakika unaisah ta tafi da imanin wasu daga cikin su, Har mamakin ta su ke yi yarinya ƙarama ga iya tsara kalami uwa uba gata kyakkyawa da ita, ba karamin jan hankalin su Captain yasir tayi ba, sun kafe ta da idanun su kamar za su haɗiye ta.

Fashewa da kuka Jemimah tayi muryarta da gunjun kuka ta ke fadin

"wallahi babu inda zamu je, don baku san wahalar da mu ka sha ba mu ka yi gayu hada gyaran gashi saboda mu nuna maku, shi ne ma zaku kore mu, to wlh ba zamu tafi ba... " a faɗa ce ta faɗa tana nuna su da yatsan hannun ta, Hankulan su gaba ɗaya ya koma kanta, ƴar ƙarama da ita sai masifa, idanun ta sun yi jawur da su, ta harzuƙa, dama ya lafiyar giwa, tsana da tsangwama da zuluncin da akayi masu arayuwarsu ya ɗan ta6a lafiyar kwalwarsu, silar maganganun da ake fadi ayanzu ne ya fara motsa haukan kansu, da sauri Unaisah ta janyo jamimah ta ƙanƙameta a jikin ta cike da fargaban kada ta ja masu jaraba.

Dafe goshi Azeeza tayi da hannun ta dake kerma kerma cikin wani irin yanayi na jin tsoro da fargaba ta soma magana muryarta da shessheƙar ku ka

"Inna... lillahi wa'inna ilaihirraji'un Ni dai mu koma gida, ku mai dani gida, ba su san mu, ba su son ganin mu, za su iya cutar da mu....' ba ta ƙare maganar ba, Sajeed yai hanzarin janyota tare da rufe mata fuskarta jikin laps dinsa.

Sautin shessheƙar kukan su ya cika hall din, mazan cikin su ne kadai ba su karaya ba, sai dai hankulansu ba a kwance ya ke ba, Mom Turai sarkin tausayi zuciyarta ta karaya ita da Hajjaty har sun fara sharar kwalla saboda tausayi ne da su, ga kaunar yaran da ta ɗar su a zuciyoyin su, da ace suna da damar da zasu ja su a jiki su rungume su da kuwa sunyi hakan.

A hankali unaisah ta ɗaura idanunta akan chief owais, mutumin da bata jima da sanin fuskarsa ba, duk da babu kwanciyar hankali atattare da ita sai da taji ya kwanta mata arai saboda jajircewarsa akan su.

Kamar yarda take kallon shi haka shi ma yake kallon ta, har cikin zuciyarsa bai ji dadin zubar hawayen su ba.

"ba laifin ka ba ne, abun da akayi mana, sai dai inaso ka sani bakowane zai fahimce mu ba ko ya kaunace mu kamar yadda ku kayi mana, zamu tafi kawai....." ta ƙarasa maganar ƙananun la66anta na kerma ta ruƙo hannun batool da na jemimah har zasu juya muryar Sir mubarak ta dakatar da su.

"Duk da bansan su wanene ku ba, ni dai kun kwanta min araina, kun sace min zuciyata, don haka ban gaji da ganin ku ba, ina yi maku maraba da shigowa family din mu...." a ruɗe su hajiya saratu suke kallon Sir mubarak, wanda fuskarsa take ɗauke da murmushi yayin da yake kallon su.

Pravin dake ta faman mazurai, jin maganar sir mubarak yasa shi jin bakin ciki da takaici tamkar ya fasa ihu haka ya ke ji, kwata kwata babu kwanciyar hankali a tare da shi, duk ya rasa sukuninsa kamar wanda yayi ma sarki ƙarya, burin shi a kore su daga hall din.

Sheikh Imam dai lamarin nasu ba karamin mamaki yake ba shi ba, kallon su kawai ya ke yi, Sam baiji dadin halin da su ka jefa yaran ba.

"Meye ribar ku idan kun 6ata ran wadannan bayin Allahn? Farin ciki ku ka yi ko bakin ciki da kuka sanya su zubar da hawayen su? Idan ya'yan ku ne a irin halin da ku ka jefa su za ku ji dadi ne? Daga ni har ku bamu da tabbaci akan abunda muke zargin su da shi, don haka yakamata mu kyautata masu zato, sannan shiekh imam yayi mana bayani, babu wanda baisan wanene sheikh imam ba, kuma mun yarda da maluntarka sa, bai kamata mu musa ma maganar shi ba, bayan haka owais jinin mune bazai ta6a kawo abun da zai cutar da ahlinsa ba, idan ma saboda kuna fargaban kada su cutar da ku ne to ku sha kuruminku owais shi ya ke da alhakin da duk wani abu da zai faru"

cike da ƙwarin gwiwa Mai girma sharafuddeen yayi maganar babu wasa akan fuskar shi, tuni wasu sun fara shan jinin jikin su.

Matsawa Chief owais yayi kusa da baba obie wanda tun ɗazu bai tanka ba, ruƙo hannunsa yayi acikin nashi, a hankali Ya ɗago suka haɗa ido da juna

In a calm voice ya furta"banji kace komai ba baba, umarninka kadai nake jira, In har ka nuna bakason su zauna zan koma da su, Idan kuma ka amince babu wanda ya isa yasa subar wajen nan, sai dai mutun ya tafi" ran shi yakai maƙura awurin 6aci

Lumshe idanu baba obie ya yi yana nazari, na ɗan lokaci yana yanke shawara da zuciyarsa kowa ya ƙagara yaji ta bakinsa domin kuwa shi kaɗai ne zai zartar da hukunci kuma dole ayi biyayya......

Komai dake faruwa akan idanun zahra, tsoro duk ya cika ta ganin rikicin dake shirin 6allewa, tun ɗazu ta 6oye kan ta a bayan su hindu dake a tsaitsaye, jikin ta sai kerma ya ke yi saboda batason tashin hankali arayuwarta...

Pravin Allah Allah ya ke baba obie yaki amincewa da zaman su a hall din ji yake tamkar ya shiga zuciyarshi don ya samu damar tunzura shi akan kada ya bar su, jikin shi sai tsuma ya ke yi.

Chief owais dake kallon shi amsar shi kawai yake jira, cike da fargaban kada Ya kunyata shi a bainar jama'a duk da yasan abune mai wuya baba obie yayi mashi hakan saboda baya son 6acin ransa.

Gyaran murya yayi hankali gaba ɗaya ya dawo kan shi, kafin ya soma magana yana duban kowan nan su

"Bana son abun da zai cutar da ahlina, sannan bana son duk wani abu da zai kawo rashin zaman lafiya a zuri'a na...." tunkafin ya kare maganar, munafuki pravin ya soma sakin shu'umin murmushin farin ciki don yasan karshen zancen zai ce ne a kore su.

"Bawai don bana son yaran bane, ɗa na kowa ne, sai don ina son mu ƙare dinner din nan lafiya, zaman su acikin mu, ba lallai ya zama alkhairi ba, tun da wasu sun nuna basu buƙatar ganin su,......" da tsantsar mamaki chief owais ya ke kallon fuskar baba obie, hajiya saratu da su laura har sun fara sakin fuskokin su sai kace akan su za su zauna....

Chief bai tsaya jin karashen zancen ba, saboda zuciyarshi ta karaya, a raunace Ya sakin hannun baba obie, ya juya ya kalli prime minister wanda tuni ruwan hawaye sun kwanta luff a idanunsa...
Chapter 25 · 0% Book details