← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 222 OF 238

Sashe 222

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ban tunkare shi da maganar ba, saboda a lokacin ka zo mini da maganar zaka turo magabatan ka ayi maganar auren mu, shiyasa na watsar da maganar na bar komai araina. Bayan mun yi aure da kai, A lokacin Daddyna har ya samu nasarar lashe zabe ya zama gwamnan jihar wanda tun da ya hau mulkin bai ƙara lafiya ba, saboda ciwon ƙafa da ya matsa mashi, ba irin maganin da ba'ayi mashi ba amma ciwon yaki ci yaƙi cinye wa. Wani iko na Allah da zarar an fita da shi kasar waje don a nema masa lafiya sai ciwon nashi ya warke, amma da zarar an dawo da shi Nigeria ciwon na shi yake komawa sabo, a karshe da yan jam"iyarsu suka fahimci ciwon nashi bame ƙarewa bane, sai suka shawarce shi da ya aje mulkin yaje ya nemi lafiyarsa, Shekara daya yayi kafin ya sauka, zaman Jahar ya gagare shi silar hakan iyayenmu suka koma Dubai da zama, Ni kuma saboda auren da na yi ne yasa suka barni a Jos.

A lokacin Uncle Musa ya zama Shahararran dan siyasa, ganin sa yayi mini wuya saboda bai cika zuwa Jos ba tun da iyayen mu suka koma Dubai, ya ɗaga ƙafa da zuwa Jos daga Abuja sai ƙasashen waje, Kuma duk in na kira phone numbers dinsa bana samu.

A ƙarshe na yanke shawarar tura mashi text message, na rubuta mashi komai dana ji ya fadi a cikin wayarsa, sannan na yi mashi barazanar ko dai ya dawo da babyn Shureim, Ko kuma in tona masa asiri a gurin Daddy da Mommy har da ma Ya Shureim din.

Da tura mashi saƙon ko minti biyar ba'ayi ba, sai ga kiran Uncle Musa ya shigo wayata, na yi mamaki sosai saboda tunda nake kira ba'a picking.

Bayan na ɗaga ko sallamata bai amsa ba ya ce, "Benazir! Ni za ki yi ma kazafi? Yaushe kika ji ina yin wannan maganar? Bayan haka ni miye haɗina da yarinyar Shureim da har zansa a binno ta daga rami? Me zanyi da gawa..."?

Bai ƙare maganar ba na ce, "Haba Uncle, wlh baka isa ka raina mini hankali ba! Da kunnena na ji ba gaya min a ka yi ba, Wlh babyn Shureim tana araye kuma ta na a gurin ka, Kai kasan inda ka kaita, kuma na rantse idan har baka dawo masa da ƴar sa ba, saina tona maka asiri.."

Ina ƙarashe maganar na kashe wayar, cike da saran zai neme ni.

Aikuwa ba zato ba tsammani a yammacin ranar da na yi waya da shi sai ga kiran shi ya shigo waya ta, a lokacin baka a gida, bayan na ɗaga kiran na ji yace in fito wajen gidana ya turo da escort dinsa yana jirana a cikin Mota.

Na ɗan ji fargaba amma da ya ke lokacin ina jin tashen rashin ji, bana jin fargaba kuma bana jin tsoron tunkarar koma uban wanene.

Batare da saninka ba, na bi Escort dinsa acikin mota ya kawo ni guest house din Uncle Musa dake anan Joss.

Bayan na fito daga motar, escort din ya rakani har cikin falon gidan, Ina shiga na taras da shi a zaune saman Sofa ya ɗaura ƙafa daya kan ɗaya, fuskarsa kwata kwata babu annuri kamar bai taba dariya ba, Nima na haɗe rai fiye da yadda ya haɗe ta shi fuskar, tunkafin ya bani iznin in zauna na samu guri kan sofa din dake fuskantar shi, na zauna tare da ɗaura ƙafata ɗaya kan ɗaya hakan ba karamin daure mashi kai ya yi ba.

Tambayar farko da ya yi min shine in fada masa gurin wa na ji maganar dana fada masa?"

Na ce in har yana so in fada masa to ya fara kawo min Babyn Shureim.

Lallashina ya fara yi duk dan in faɗa masa, na sanya kaifi nace wallahi ya daina wahalar da kanshi saboda bazan faɗa ba, dole sai ya fara kawo mini yarinyar.

Shu'umin murmushi ya saki tare da cewa bai damu ba in je in fada ma duk wanda zan fadamawa, saboda bani da hujjar da zan iya tuhumar shi, balle har in tona masa asiri, kuma in bi a hankali in ban iya kama barawo ba sai barawon ya kama ni.." na yi dariya hada shewata na ce, "Ka bani mamaki Uncle, ina yi maka kallon mutumin kirki ashe kai din mutumin banza ne! Ka yi zaton bansan komai ba?"

Na faɗa ina zare mashi idanuna, a lokacin yanayin fuskarsa ya sauya zuwa tsantsar al'ajabi da rudani.

"Benazir Ni kike kira mutumin banza? Ido cikin ido batare da jin shakkata ba? Kin manta matsayina agurin ki?"

Harara na galla masa, "Na je na fada Uncle, Wallahi Hakkin Aisha bazai ta6a bari ka gama da duniya lafiya ba, Ka cuce ta Ka cuci Yaya shureim ka kuma cuci Babyn da suka haifa"!

Ina magana hawaye na shararowa kan kuncina.

"Ashe dama duk kyautatawar da ka yi mana ba don Allah bane, sai don saboda wata mummunar manufa taka, baiwar Allah Aisha saida ta nuna batason zama agidan da ka kama mana haya a kasar germany saboda hankalinta bai kwanta da shi ba, sannan ta nuna rashin jin dadin ta akan zaryar da kake yi cikin gidan duk weekend sai ka zo ka kwana ga kudi da kake kashe mana, ni da kaina na kare ka agurinta na nuna mata cewa kada ta damu Uncle dina mutunne mai son yin alheri kuma dukiyar ka ta halal ce kasuwanci kake yi, sai daga baya na gano komai, arzikin da kake taƙama da shi ba ta hanyar halal ka tara shi ba, mu ka raina ma wayau da sunan kasuwanci kake yi, bayan haka ina zargin kana a ƙungiyar asiri ta yan shan jini, kuma kaine ka haɗa Aisha da mahaifinta, wato ka yi amfani da damar da kake da ita, a lokacin da kake zuwa ka kwana a gidanmu, sai ka bari dare ya yi sai ka saci hanya batare da sanin mu ba ka ke shiga ɗakin Aisha, ka dauketa video da hotuna, wama ya sani ko asiri kake yi mata shiyasa har batasan kana yi mata hakan ba, wallahi ka ci amanar yardar da na yi maka! kuma na rantse da wanda raina yake a hannunshi in har baka dawo mana da babynmu ba saina fallasa asirin ka...."

Tun kafin in ƙarasa maganar, Uncle Musa ya doka min tsawa yana huci kamar mayunwacin zaki, saboda tsabar fusata da bacin rai jikin shi ya dinga fitar da gumi, abun da ya daure mashi kai ya kuma ɗaga hankalinsa shine ta yaya akai duk nasan abunda yake ƙullawa?" Sam ya kasa magana sai huci yake fitarwa, Idanunsa sun kaɗa jawur.

Ganin baida niyar yin magana yasa naci gaba da cewa, "Kuma kaine ka shiga tsakanin Yaya Shureim da Aisha, ka yi masa asiri kasa yayi mata fyaɗe ba'a cikin hayyacin sa ba, komai dake faruwa kana bin diddiginsu kana samun information a gurin yan leƙen asirin ka, Hatta Mahaifinmu baka ƙyalesa ba, kana amfani da sihiri gurin juya shi don yabi ra'ayin ka, bayan haka kaine ka turama Daddy videos din Aisha daka dauka tare da kai sai ka 6oye fuskarka don karsu gane kaine kabar fuskar Aisha saboda tsabar mugunta da zalunci irin naka! kuma kai ne shaidanin da ya tunzura mahaifinmu akan karya kuskura ya yarda Shureim ya auri Aisha in ba haka ba zai rasa kujerar da yake nema kuma mutane zasu juya mashi baya saboda abun kunyar da Shureim ya akaita, munafukin Allah kaita faɗa masa kauli da ba'adi har saida ka shiga tsakanin daddy da Ya Shureim...".

Ban kai ga ƙarasa maganar ba ya katse ni ta hanyar bugun table din gabansa da hannunsa, Jikinshi har wani jijjiga yake yi saboda bacin rai.

"Benazir! Bana so ki jefa rayuwarki a cikin hadari! Ina mai gargadin ki, Tun wuri ki yi gaggawar janye zargin da kike yi mini, tun kafin ki yi danasani" Na yi tsalle na dire na ce, "Wlh Uncle bazan janye ba, saboda ni akan gaskiyata nake, ba zargin ka ni ke yi ba, tabbaci gare ni, kai baka yi mamakin tayaya akai nasan sirrinka ba uhum? Na faɗa ina kallon cikin idanunshi, wlh a lokacin ya razana dani ba kadan ba, amma da yake shu'umin mutunne sai ya dake ya tirje akan cewa ba gaskiya nake fada ba, ƙazafi nake yi masa.

raina a 6ace na juya zan bar falon ban ma jira ya karasa maganar shi ba, har na kusa fucewa Ya dakatar dani ta hanyar kiran sunana na tsaya ina jiran jin me zai ce.

"Ki fada mini komai kike so a duniyar nan zan yi maki shi, amma maganar zaki tona min asiri bata taso ba, Ki yi watsi da maganar nan, nifa Uncle dinki ne, In kika tona mini asiri kamar kin tona ma family din mu ne, ki dawo mu sasanta tsakanin mu" A hankali na juyo na fuskance shi.

"Baka so zaman lafiya ba Uncle, ai wlh in har kana son sasanci to ka dawo mana da babynmu, ni kuma nayi maka alkawarin babu wanda zaiji maganar nan! Ni ita kadai nake so bandamu da abunda kake aikatawa ba, wannan tsakanin ka da Allah ne, duk wanda ya yi da kyau ya sani, kuma dai akwai mutuwa akwai hisabi kowa zai girbi abunda ya shuka ne..." Dafe kanshi ya yi da tafin hannunsa kamar mai fama da ciwon kai,

"Meyasa kin fiye taurin kai da kafiya ne? Yakamata ki iya bakinki Benazir! Har yanzu bakisan wanene ni ba! Sabo da kaza bai hana in yankata! Wlh zan iya salwantar da rayuwarki, kuma idan na kashe ki na kashe banza."

A lokacin gabana ya faɗi na kuma sha jinin jikina amma ban bari ya gane hakan ba, saima na yi dariya na ce, "Idan ma kana tunanin kashe ni shine mafita agare ka, to ka daina, saboda hujjojin dana fada maka ina da su, bani kadai ke da su ba, Nima ina da mutanene da nake yin aiki tare da su, idan yau ka kashe ni, wlh zasu fallasa asirin ka ne duniya tasan me ka ke aikata, ka ga kuwa baka da wata mafita da ya wuce ka bini ta lalama"
Chapter 222 · 0% Book details