← Book details Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 238 OF 238

Sashe 238

Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel · about 9 min read

Senate Lateef ya ce, "Baba wace shafewar basira ce ta same ka? Ni abun da ya dauremin kai yadda har ka iya kashe mutun ka sha jinin shi, ka kuma lalata rayuwar yaran da basu ji ba basu gani ba, baba wa ya koya maka zaluncin nan? Har yanzu na gaza yarda kaine kake aikata hakan Baba, Tsawon shekara nawa kana aikata fasadi a doron ƙasa! Wallah baba da ace ka yi hakuri tun fil azal ka yi rayuwarka cikin talaucinka da sai ya fiye mana kwanciyar hankali, shi arziki da daukaka na Allah ne, sai wanda ya so yake bawa, watakil ma kana ɗaya daga cikin wadanda Allah ya tsaga da rabonsu kaine baka sani ba, ka biyewa son zuciyar ka baba, gayanan ka jefa rayuwarmu a halaka, bayan haka jin dadin duniya ƙalilan ne baba, gaba dayanmu mutuwa zamu yi, komai muka mallaka anan gidan duniya zamu barshi, lahiri itace dawwamammiya, wlh da wannan masifar daka jefa mu a ciki wlh gara ace mun taso rayuwarmu a matsayin musakai marasa gata a duniya da dai irin wannan rayuwar, baba yanzu da ka ɗaukakamu ya zaka yi da mu? sai da ka bari duniyar tasan da zamanmu ana yi mana kallon mutane masu daraja da ƙima, masu martaba a idon duniya, yanzu idan suka ji miyagun laifukan da kake aikatawa me kake tunanin zai biyo baya?" Ya jefa mashi tambayar yana kuka yana girgiza kai.

kafafunsa ne suka gaza ɗaukarsa ya zube kan gwiwowinsa, idanunsa sun rune jawur, kumatunsa sun yi jajir, duk ya faffasa labbansa da haƙoransa, gemunsa ya jiƙe sharkaf da ruwan hawayensa, Ko'ina na jikinsa zufa ce take tsattsafo masa kamar babu A.c a falon.

Wlh ya sadaƙas bai ta6a zaton zai ji kunyar zunubban da yake aikatawa ba sai yau da Khala ta fallasa asirin sa a gaban ya'yansa mafi soyuwa a gare shi.

Dukkan ilahirin jikinsa kerma ya ke yi, ga wani irin azababben zazzabi da ya lulllu6esa, mutumin da sai ya yi shekara da shekaru bai yi ciwo ba saboda ƙoshin lafiyar dake gare shi to yau dai hada matsanancin ciwon kai, bazama a raza ciwon zuciya na farat daya ba saboda depression din da ya kama shi, gaba ɗaya suka zauna kewaye da shi kamar malami da almajiransa kuka hada majina, sun kasa tsayar da kan su. 😭

Daƙyar ya iya furta, "Idan na ce ku yi hakuri ban yi maku adalci ba, iya cutarwa na cutar da rayuwarku, ban cancanta na ci gaba da rayuwa ba, nasan a halin yanzu da kuka gano wanene ni kun tsane ni fiye da komai na duniyar nan, don haka na miƙa wuyana a gare ku, nasan na aikata maku ba dai dai ba, Ku yanke mini duk wani hukunci da kuka ga ya dace dani, ku azabtar da ni, sannan ku kashe ni, idan ba haka ba, Ni zan kashe kaina, saboda bazan iya cigaba da rayuwa da abun kunyar da na aikata muku ba..." Yana faɗa yana kuka haɗi da tari.

Sama sama khala dake a kwance kan Sofa take jiyo maganganunsu, baiwar Allah ita kadai tasan halin da take a ciki, ta tona masa asiri burinta ya cika sai dai bata yi farin ciki ba, saboda halin da ya'yan shi suka shiga shiyasa kafin ka fara aikata wani abu mara kyau ka fara tunanin makomarka da kuma halin da zaka jefa wanda ya yarda da kai abun yana da ciwo.

"Ku kashe ni, in har baku kashe ni ba mutane bazasu ƙyale ni ba, ku kashe ni kawai nafi so na mutu a hannunku, ko dan saboda ku dauki fansar abun dana aikata maku, ku kashe ni na ce, in ba haka ba zan kashe kaina..."

Zumbur ya miƙe jikinshi na kerma, Lokaci daya gabansu ya fadi ganin jinin da ya wanke gaban wandon shi.

Har suna haɗa baki gurin ambaton sunanshi, Allah sarki duk da abun da ya aikata hakan bai hana su ɗaga hankalinsu a kanshi ba,

"Mu kai shi asibiti kada ya rasa ranshi!" Sharafuddeen ne ya yi maganar a ruɗe.

Har sai da baba Obie ya dube shi da raunatattun idanunsa, ƙasa ƙasa da murya ya ce, "Duk abunda na yi maka baisa ka daina damuwa da ni ba Sharafuddeen....?" Girgiza kai ya yi, "Ku yi hakuri bazan je asibiti ba, ku barni a gida, in ma mutuwace ta riske ni a cikin ku...." Yana ƙarasa maganar ya shallake su ya juya a hanzarce ya nufi part ɗinsa, da gudu suka bi bayanshi kafin su ƙaraso tuni ya shige ɗakin ya ja ƙofa ya datseta ta yadda ba zasu iya buɗeta ba. 😭

Yanke jiki ya yi ya faɗi kan floor ya dinga birgima yana bubbuga goshinsa kan floor har saida ya fashe jini ya 6alle masa, daga waje suna juyo kururuwar azabar da yake fitarwa mai kuwar gaske kamar zai fasa dodon kunnuwansu.

Da iya ƙarfinsu na karshe suka dinga bubbuga ƙofar hadi da ambaton sunan shi da karfi.

Chief kamar zai 6alle ƙofar da kafaɗarsa ya dinga bangazarta duk da raɗadin da ya ke ji.

"Baba ka buɗe mana ƙofa, bamu gama magana da kai ba, baba kada ka mutu kabar mu, baba dan Allah ka buɗe bamu gaji da ganin ka ba, akwai tambayoyin da baka bamu amsoshinsu ba, baba! baba!!, zamu iya yafe maka amma ka buɗe mana kofar, baba pls, baba pls, idan ka tafi ka barmu a cikin wannan mawuyacin halin daka jefa mu ya kake so mu yi da rayuwarmu! Ka taimaka mana baba, ka fitar damu baba.. "

Ba irin bugun da ba su yi ma kofar ba amma ta ƙi 6allewa, a karshe da suka galabaita a gaban kofar ɗakin nashi suka zazzauna suna cigaba da yin kuka kamar masu zaman makoki.

Gaba ɗaya abun da ke faruwa ƴan aikin gidan basu sani ba, saboda anyi masu iyaka da shiga falon dama ƙa'ida idan za'ayi family meeting ba'a buƙatar bare agurin shiyasa kwata kwata basu leƙo ba kuma basu ji sautin koke koken da ake yi ba, saboda akwai tazara tsakanin sashen su da main falo.

_____________________PRAVIN 🥵

Tun lokacin da khala ta fara fallasa asirin su, cikin rawar jiki ya bar falon batare da sanin kowan nan su ba, bai nufi ko'ina ba sai sashen yan aikin gidan.

A lokacin Hajjaty tana a ƙudundune cikin bargo har ta samu bacci ya ɗan dauke ta, kwatsam ba zato ba tsammani kamar daga sama ta ji an cakumeta, ta fasa ƙara tana kokarin kwache kanta cikin ruɗu da tashin hankali, kwata kwata batasan wanene ba saboda bargon da ya lullu6e fuskarta, a saman kafaɗarshi ya sa6e ta, tana kuka tana ihu tare da ambaton sunan pravin don ya kawo mata ɗauki, juyawar da zai yi keda wuya ya yi arba da hajiya Saratu dake shugowa ɗakin afujajan nan take gabanshi ya yanke ya faɗi ya zazzare idanunshi yana kallon ta kamar yadda take kallonshi da tsantsar tashin hankali akan fuskarta..

Numfashinta na fita da hucin bacin rai ta ce,"Munafiki, Gidan ubanwa zaka kai ta eye? Yan iska maciya amana, wato Kun daɗe kuna cin amanata, yanzu da ka ga asirinka ya tonu shine ka lalla6o ka saci jiki ka shugo don ka dauki kwartuwarka don ku gudu ko?" Ta faɗa tana zare idanunta.

Tsawa ya daka mata har saida ta razana, muryarsa na rawa ya ce, "Ki matsa ki bani wuri in wuce tunkafin in yi maki illah!"

Cikin fusatacciyar murya ta ce, "Illah kuma ta nawa? Ka bani mamaki pravin, Ka karya min zuciyata, munafuki dama na daɗe ina zargin Hajjaty ashe tare kuke aikata fasiƙanci, wai a haka na aure ka na haifa maka ƴa'ƴa, Ka cutar da rayuwata pravin, hakkina da na ya'yanka bazai ta6a bari ka gama da duniya lafiya ba wlh, kuma na rantse babu gidan ubanda zaku je, mayaudaran banza, dole ku gurbi abun da kuka shuka..."

Bata ƙarasa maganar ba, sakamakon naushin da ya sakar mata akan kuncinta, nan take gefen bakinta ya fashe ta fara bleeding, azabar zafin da ta ji ne yasa ta dafe gefen bakin, da mamaki ta furta,"Pravin! yau da hannunka ka dake ni? Inna lillahi..! " Rai a 6ace ta yi kukan kura ta haɗa su duka biyun da shi da Hajjaty ta hankaɗa su gaba ɗaya suka kife ƙasa, bargon jikin Hajjaty ya warware baiwar Allah tuni ta jima da sumewa sakamakon buguwar da kanta yayi dama ya lafiyar gwiwa.

Ransa ya 6aci matuƙa, a harzuƙe ya yunƙura ya mike Ya nufi hajiya Saratu batai aune ba, ya damƙi ƙeyarta da hannunshi ya jata ta karfi ya nufi mirror tana ta kokarin ta kwace kanta sai dai ta kasa saboda raunin da zuciyarta ta yi yasa ta kasa ta6uka komai.

Yana isa gaban madubin ya buga kanta jikin shi nan take madubin ya fashe, duk ya sossoke fuskarta, tuni ta fara bleeding, kukan ma ta kasa yi saboda zogin azabar da ya ratsa sassan jikin ta, ya ɗago da kan nata ya wurgar da da ita a galabaice ta kife kan floor ta mirgina numfashinta yana ta kokawar ɗaukewa.

Hakan bai masa ba sai da ya take yatsun hannayen ta da tafin ƙafarsa duk ya murjesu suka faffashe jini ya soma tsastsafowa.

kwata kwata babu imani a zuciyarsa, ga idanun nan nasa sun kaɗa jawur kamar an watsa barkono a cikin su, Ya na huci ya furta, "Allah ya isa tsakanina da ku, Dangin matsafa masu arziƙin jini, Duk ubanku ne ya ja min shiga halin da nake a ciki, shine mugun da ya sa na jefa rayuwata cikin halaka ina zaman zamana lafiya, dama ni ban ta6a son ki ba, dukiyarki ce tasa na aureki da kuma kwaɗayin surar jikin ki, Kin daɗe kina baƙanta min rai ke ga mai arziki ɗiyar ƙaruna, ki yi ta min gorin arziƙi don ina zaune a gidan ku, to ai ga irinta nan, yanzu ai kin gane arzikin naku bana halal bane ko? Ya faɗa yana tottafa mata yawu a kan fuskarta.

"Kuɗin jini ne kuke tunƙaho da su, wlh badan ƴa'yan dake tsakanina dake ba da ba abun da zai hana in huce haushina a kanki, zan bar ki da ranki ne ba don na so ba.."

Ya faɗa yana kallon fuskarta da ta jiƙe sharkaf da jini kamanninta har sun sauya saboda azaba ta gama fita hayyacinta, juyawa ya yi da sauri ya nufi bargon Hajjaty ya janyo shi ya rufa mata a jikinta tare da nannaɗeta a cikin bargon ya mayar da ita kan kafaɗarsa, Ya tsallake hajiya Saratu dake a kwance rai hannun Allah cikin sauri ya fuce daga ɗakin, batare da sanin kowa ba ya gudu daga Estate ɗin......💔

___________________________________✍️

*_(SHIN ME KUKE TUNANIN ZAI BIYO BAYA IDAN SAURAN AHLIN FAMILYN SUKA KARASO SUKA JI ABUN DA KE FARUWA❓GA HAJIYA SARATU AKWANCE RAI HANNUN ALLAH! WA ZAI KAI MATA DAUKI❓ YA RAYUWAR BABA OBIE ZATA KAYA ZAI KASHE KANSHI NE KO KUWA❓ ME KUKE TUNANIN ZAI BIYO BAYA IDAN SAURAN ELDERS SUKA JI LABARIN ASIRIN ELDER YA TONU❓YA LABARIN PRAVIN DAYA GUDU DA HAJJATY GIDAN UBAN WA ZAIJE❓ DA WANI IDO YA'YAN BABA OBIE ZASU FUSKANCI DUNIYA? KUNA TUNANIN BA ZASU FUSKANCI KALUBALE BA AKAN MUKAMAN SU❓ TAYA ZA'A HADA KOWANI PRISONERS DA IYAYENSA❓ TAYA ZA'A KAMA SAURAN ELDER❓ TO WAINI TAYAYA MA AKAI TSOHUWA KHALA TA RAYU?😳 YANZU NE LOKACIN DA ZAKU ƊAURA ƊAMARARKU TAMAU DON JIN YADDA ZATA KAYA🔥💪_*

*Gani ga wane Ya ishi wane Jin tsoron Allah😭 page din nan ya taba zuciyata)*

*DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥🔥🔥🔥😭*

*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*
Chapter 238 · 0% Book details